Novel Document

Deen House (Romantic Story) By Oum Hairan

DEEN HOUSE (Romantic Story) Written By Oum Hairan

Posted by AiHausa Novel
Price 500
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 27 Jan, 2023
Upload Time 8:29 am
Hits 218 Views
Author

Oum Hairan

Writer Group

Nil

Novel Genre

Comment No Comments

DEEN HOUSE (Romantic Story) Written By Oum Hairan

Tsugunne jikin famfon wata matashiyar yarinya ce da a ƙiyasin shekarunta ta baya bazata wucce sha bakwai ba, wasa takeyi da kifin tarwaɗar da yaketa wutsil-wutsil a cikin ruwa tana Murmushi ji tayi an rufenta idanu ƙamshin turaren da ya ziyarci hancinta zuwa cikin kwanyarta shine ya alamta mata waye ne tayi dariya kyawawan haƙoranta suka bayyana tace “Yaya Zain ka shammacemu nasan ko umma batasan da zuwanka ba yau” sakar mata idanun yayi yace “Zainab bakida wayo kekam yayyafi fa akeyi ke dama gayyar Limoniya kika zauna kike wasa da kifi anan gurin jibi yanda duk kika jiƙe jikinki”

Umma dake fitowa tace “Yawwa gara da Allah ya kawo ka koda yake kai dama karkatacciyar kukarta ne me sauƙin hawa dama dai DEEN ne ƙila da tuni ta nemi gurin ɓuya, sannu ashe kana tafe amma baka sanar damu ba?” Murmushi yayi yana kama hannun Zainab zuwa gindin famfon ya zazzaga mata klin ya kunna ya fara cuɗa mata hannun yana cewa “yar tsohuwar Babata wlh gudowa nayi daga camp kewarku ta dameni musamman wannan ƙwailar ƙanwar tawa koda yake naga babu laifi ƙirjin ya fara abin arziƙi…..”

 

 

Turo baki tayi ta zame hannunta tana dira ƙafa tana cewa “Allah! Allah nidai Yaya Zain ka bari zan daina kulaka kuma zan daina ma ce maka Yaya…..” Cafka yakai mata yace “to bari na ɗinke bakin rashin kunyar saiki daina cemin yaya da hujjarki” ɗiba tayi da gudu tayi ɗaki yabita Umma na musu dariya tana cewa “kaidai Zain bazaka girma ba yaran nan duk ka sakar musu sun raina ka saikace abokan wasanka to in kungama shashancin kuzo ga abinci nan”

Suna shiga ɗakin ta faɗa jikin Bahijjah dake kwance tana dariya tana cewa Allah Yaya na tuba nabi Allah bazan ƙara ba” tureta Bahijjah tayi tace “kefa inda kikasan goyon gwauro haka kike” ganin Zain ya shigo ta buga tsalle itama ta rungumeshi tace “Wayyoh bro dama mun cika da kewarka Umma bata barinmu zuwa ko ina tunda ka tafi munyi munyi da ita ta barmu muje mu zaɓo ankon bikin Yaya Deen amma ta hanamu gashi har saura sati Uku bikin”

Zama yayi a gefen gadon yace “Ai fa kice gara dana gudo to yanzu bari muyi sallah muci abinci sai muje mu zaɓo wanda yafi na kowa kyau” ihu suka soma yi Zainab harda rawa suka fice Umma na kitchen suka isa gareta sunayi mata sannu ta dago tace yan banza kunƙi tayani aiki Saida kukaga cine sannan zaku kama yimin sannu to ku adana abarku zatayi muku amfani a wajen mazajenku”

Dariya sukayi suna ɗan soshe soshe soshen rashin gaskiya ta fito daga kitchen ɗin tana cewa saiku zubawa kanku in kunga dama ku zubawa yayanku Deen koma ku barshi kunfini sanin sauran”

Kokowa suka fara kowacce na cewa itace zata zuba abincin Zain dake bayansu ya matsa yace “duk ku bani ai dani zaaci abincin” miƙa masa Bahijjah tayi flat ɗin tana mawa Zainab gwalo Zainab takai mata duka ta goce ta fice tana dariya da haka suka isa falon suka baje sunacin abincin wannan ta ɗauko nama wannan ta fizge ta bawa Yaya Zain Umma na kallonsu tana Murmushi shaƙuwar ƴaƴan nata tana sanyata farin ciki komansu gwanin ban sha’awa kowa buri yake yaga ya faranta zuciyar yan uwansa.

Daidai nan Deen yayi sallama saɓe da jakarsa dukkanninsu babu wanda bai ɗago ba gaban Zainab ya faɗi lkcn da idanunta ya sauka kan fuskarsa mara tagomashin walwala a ranta tace “Wannan badon kyau da Allah ya bashi ba da bazai rinƙa ganuwa ba dan jaraba kullum fuska kamar hadari ya gangamo….”

 

 

Tana wannan tunanin taji yace “Sannu Abulle” gabanta ya faɗi cikin in…ina tace “Barka da dawowa Yaya” bai amsa ba sai ƙwafa da yayi yace “kai kuma meye ya dawo dakai?” Sosa kai Zain yayi yace “Wlh interval training muka samu shine kawai naji inason zuwa gida” jinjina kai yayi yace “yayi maka kyau ke Zainab ki kawomin lemo da abinci na ɗakina” batasan sanda ta kalli Umma ba tanason yin magana tanajin tsoron masifar Deen haka tayi ƙasa dakai tana jujjuya cokali cikin haɗin salat ɗin da tasa domin ta ɗiba.

Zain ne ya ɗago fuskarta yace “Yadai ƴar mummunar ƙanwata?” Zuciya taja tace “Yau fa bani zankai masa abinci ba kuma yasani tunda shine ya rubuta time table ɗin da hannunsa amma kanaji wai nakai masa”

Dariya abin yabawa Zain yace “Au kai abincin harda Time table don matsayi kaga iyalan Elizabeth turawan ƙarshen zamani, toma banda abinki meye a cikin daukar abinci kije ki dangwarar ki fitowarki” yanda yayi maganar yana gwada mata yanda zata dangwarar da kwanon yasasu duka suka tuntsure da dariya tace “lallai ma Ya Zain wato kaga Shikenan watan mutuwata ya kama don na tabbata indai nayi masa haka wlh ko Abba bazai iya kwatata a gurinsa ba bare kai ƙarfi ne dashi kamar Shari’a rannan daya sani wankin vest ɗinsa na manta ban wanke ba Ni nayi tunanin ma ɓalla hannuna yayi don daina jinsa nayi a jikina”

Tashi tayi ta nufi kitchen Zain yabita da kallo ta ɗauki abincin ta jera a tire ta ɗora lemo da ruwa saikace na magidanci ta ɗauka ta nufi ɗakin Deen ta taɓa ƙofar tare da sallama shiru taji hakan ya sanyata yin ƙarfin halin tura ƙofar ranta yayi fari tas ganin baya cikin ɗakin tasan wanka ya shiga hakan ya bata damar miƙewa ta nufi hanyar fita daga ɗakin taji yace “Ke ina zaki?” Wani dokawa gabanta yayi hawaye ya nemi ƙwace mata tayi saurin sharewa ta tsaya a jikin ƙofar ƙirjinta yana neman fasowa ya fito.

Ji tayi yana takowa ta bayinta hucinsa yana matsarta Tsoronta yana ƙaruwa har ya haɗe tazarar dake tsakaninsu yasa hannunsa ya dafe hips ɗinta ya kwantar da kansa a saman kanta yace “Zainab!…” Cikin firgici da tsoro tasa hannunta saman nasa muryarta a kashe tace “Please Yaya Deen…..” Saurin katseta yayi da ɗora mata hannu a baki ya saki weast ɗin nata ya ja hannunta ya kaita gaban abincin cikin Muryar da take firgitata idan suka kaɗaice yace “Inajin yunwa amma bata wannan abincin ba Zainab inajin kamar bazan iya ƙarasa kwanakin da suka ragemin ba narasa meye yasa kullum feeling ɗina ƙaruwa takeyi inajin kamar naci babu…..

Toshe kunnenta tayi cikin bugawar numfashi na tsoro tace “Na shiga uku Ni Zainabu Abu wannan wacce irin masifa ce Ya Deen toni meye nawa meye zanyi maka…..” Numfashinta taji yayi tsiri sama yana neman ɗaukewa dawowarta hayyaci yasata fahimtar meye yake faruwa ashe haɗe bakinsa yayi da nata ya manna ƙirjinta a ƙirjinsa.

Gabaɗaya yanayinsa jirkita yakeyi yana wani tsotsar lips ɗinta da sauri da sauri tare da sake manna tudun ƙananun boobs ɗinta a ƙirjinsa yanajin wata azababbiyar sha’awa na ƙara bijiro masa  itakuwa banda kuka da taketa kokawa dashi babu abinda take yi shi kansa kukan idan tayi bala’i ne a gurinta domin idan ta fita za’a gane akwai wani abu gashi ya rantse mata muddin ta yarda wani yasan abinda yake tsakaninsu sai ya azabtar da ita da azaba mafi tsanani a rayuwarta.

Sabon salon da taji ya fara sauyawa ne yasata dole ta sake sautin kukanta saboda jin yana ƙasa da zip na rigarta tayi wani kukan kura ta tureshi ta maƙale hannunta saman ƙirjinta da bata sanyawa bra ba ta durƙushe a gurin tace “Don….don Allah kada kaci mutuncina Ya Deen ka tausayawa rayuwata kada kayi amfani da raunina ka cutar dani wlh Allah bazai Barka ba……..

Zubanta idanu yayi jikinsa gabaɗaya yayi sanyi da yanda yaga tana kukan to amma shima abin tausayi ne akanta idan ta ƙyaleshi yasan iyakarsa kuma koda tsautsayi yasa ya wucce nan zai gyara da kansa.

Da wannan huɗubar ta shaiɗan sukaji an ƙwanƙwasa ƙofar ta maza ta gyara rigarta tare da zuge zip din yaja ajiyar zuciya yace “Yes” turo ƙofar akayi Bahijjah tace “Sannu Yaya kekuma Umma tace ki taso mu tafi Islamiyya” zumbur ta miƙe ta nufi ƙofa har tana ƙoƙarin ture Bahijjah.

Ɗaga murya yayi yace “Duk ranar da tsautsayi yasa kika bari na sake dawowa batare da kin gyaramin ɗaki ba zakisha mamaki, Zainab iskancinki yana ƙaruwa ne saboda ana barki Umma da Abba sun ɗaure Miki gindi to ni zan saita lissafinki……

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

 

 

 

Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.

 

Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com

 

 

Author’s Contact

  • Name : Oum Hairan
  • Wattpad Handle : @ 
  • Nick Name : Oum Hairan
  • Whatsapp Number : 
  • Nationality : Nigeria
  • Email :
  • Group :  Writers Association

The Book is not free

Back to top button