Labarai

Innalillahi wa’inna Ilaihirraji’un: Amarya, Sirikinta, Mata Biyar Da Wasu 6 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota Da Ya Rutsa Da Su A Jihar Neja

Amarya, Sirikinta, Mata Biyar Da Wasu 6 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota Da Ya Rutsa Da Su A Jihar Neja

Mutane 13 da suka haɗa da wata sabuwar amarya, wasu mata biyar, sirikinta, da wasu mutane shida sun mutu a wani hatsarin mota kusa da Lukoro a Edati, jihar Neja.

Goma daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun kammala karatu ne a kwalejin kimiyyar lafiya ta Sultan Abdulrahman College of Health Gwadabawa, sun hallara ne domin murnar ɗaurin aure tsakanin wani wanda ya kammala karatun digiri, Umar Jibril Muhammad da wata ɗalibar lafiyar haƙori mai suna Amina.

Mummunan hatsarin da ya afku a yammacin ranar Juma’a 26 ga watan Junairu, 2024, an danganta shi da gudun wuce gona da iri.

Hatsarin ya haɗa da wasu motoci guda biyu: Toyota Corolla mai kalar toka da ta taso daga Mokwa zuwa Bida da wata motar bas kirar Nissan ta kasuwanci da ta taso daga Minna babban birnin jihar Neja zuwa Ogbomosho a jihar Oyo.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Neja, Tsukwan Kumar, ya ce hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar wasu manya mata takwas, da manya maza hudu, da kuma yaro namiji daya.

Ya kara da cewa manya mata hudu, babba namiji daya, yaro namiji ɗaya, da mace ɗaya sun samu munanan raunuka.

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Bida domin kula da lafiyarsu, yayin da aka kula da gawarwakin waɗanda suka mutu.

An miƙa mutanen tara ga ‘yan uwansu a wurin da hatsarin ya afku bayan an tantance su, sannan an kai sauran hudun zuwa babban asibitin Kutigi.

Back to top button