Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 57 Complete Novel

*ASM Bk2057*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
…………. Bayan gama sallar Magrib Hajiya ta nufi gidan su Fatuu lokacin da ta zo daidai shagon Amadu ta d’an d’aga Murya tace “Ahmad ya kasuwa” jin haka yasa ya kallo wajen yana ganinta da yake akwae wuta da sauri ya fito lokacin har ta karya kwanar shiga suka had’e da fara’a ya gaishe da ita ta amsa ta k’ara ce mashi ya kasuwa yace Alhamdulillah, ganin yana k’ok’arin bin ta su shiga gidan tace ya koma wurin sana’ar shi ta gode yay mata a fito lafiya ya juya, tana shiga cikin gidan tay sallama jin ba’a amsa ba yasa ta k’arasa wurin kopar parlon ta k’ara yin wata sallamar da d’an d’aga murya lokacin gwaggo dake cikin d’aki ta ji ta amsa, tana lek’owa ganin mai yin sallamar yasa ta k’arasa fitowa da sauri ta nufeta jikinta sanye da hijab tun bayan da ta gama sallar Magrib bata Mik’e ba zaune take tana yin tasbih ta jiyo sallamar, sannu da zuwa tay mata ta gaishe da ita tana d’an murmushi Hajiyar ta amsa ta nufi cikin parlon tun ma kafin gwaggon tace mata ta shiga, bayan ta shige tabi bayanta daga d’an can gefen kujerar da Hajiya ta zauna itama ta zauna tana k’ara gaishe da ita bayan ta amsa tace “Barka an dawo” gwaggo tace “Yauwa eh wllh”,
“to Allah ya kyauta gaba ya k’ara mata lafiya, ai kun auna Arziki da Allah ya tashi k’afadun ta ba tare da wata matsala ba” yadda tay Maganar fuskar ta a d’an d’aure cike da girmamawa Gwaggo ta hau bata hak’uri tace ai hak’uri ya zama dole tunda aikin gama ya riga da ya gama wanda aka cuta an cuce shi” d’an murmushi kawae gwaggon tay Hajiyar tace “Ya jikin Fateemar?” tace mata da Sauk’i bari a kira ta tana d’akinta,
“In tana bacci ne ki rabu da ita”,
tace “ban tunanin shi take yi kawae dai tana kwance ne tun bayan da muka dawo sai da dalili take fitowa” tana k’arasawa ta mik’e ta nufi hanyar fita Hajiya na fad’in ai dole tay ta kwanciya wannan uban jini da ta kwararar, lokacin da ta d’aga labulan a kwance ta same ta idanunta a rufe tana sanye da doguwar rigar bacci kanta sanye da hula, nufar ta gwaggo tay ta tsaya a bakin gadon ta kira sunanta jin shiru bata amsa ba yasa ta gane bacci take ta sunkuya ta kai hannu ta d’an bubbuga shoulder d’inta, a hankali ta bud’e idanun suka sauka akan gwaggo tace mata “Sannu ya k’arfin jikin?” hannu ta kai tana muttsike idanun tace mata da Sauk’i gwaggon tace “ba abunda ke maki ciwo?” Kai ta d’aga kafin tace “kawae jikin ne ba k’wari” kai ta jinjina “Wannan dama sai a hankali, ga Hajiya nan tazo ganin ki ki taso” amsa mata tay da to ta fara kokarin saukkowa, a tare suka tafi gwaggon na gaba tana biye da ita suka nufi parlon, bayan gwaggo ta shige da yar sallama itama ta shiga idon Hajiya a kanta ta mik’a hannu tana ce mata tazo ta zauna kusa da ita da yake a saman 2 seater take zaune, a gefenta Fatun ta zauna a hankali ta gaishe da ita ta amsa kafin ta kai hannu ta dafa Shoulder d’inta tana tambayar ta ya jikin tace mata ta samu sauk’i sosae,
“To Ya jinin yana zuba sosae ne?” ta tambaya sunkuyar da kai Fatuu tay tace “a’a kad’an ne kaman zai d’auke” jinjina kai tay tace “ai kin zubar da jini dole yay saurin d’aukewa” shiru Fatun bata ce komae ba Still kanta na k’asa, “Yanzu akwae abunda ke damun ki a jikin?” d’an girgiza kai tay tace “a’a kawae k’arfi ne babu sosae” tace “Wannan sai a hankali zai dawo kina dae cin Abinci sosae ko?” Kai ta d’aga mata alamar eh tace yayi kyau kafin ta sake tambayar tana shan suma magungunan da aka bata tace mata eh, shiru ta d’anyi kafin ta dasa “Fateema ina son tambayar ki kuma gaskiya nike son ki fito ki fad’a man kin ji ko?” d’agowa tay ta kalleta ta d’aga mata kai alamar to,
“Ina son inji shin zaki cigaba da zama da Yayan ki matsayin mijin ki ko kuwa baki so in raba ku?” Dammm! gaban Fatuu yay wani irin bugu ta kasa d’agowa balle tace wani abu ganin haka yasa Hajiya cewa ba shiru zata yi ba ta bud’e baki tay Magana a hankali ta saci kallon gwaggo suka had’a ido tana ganin haka ta juyar da fuskar ta daga barin kallon Fatun ta koma kallon gefe Hajiya tace “ki daina kallon ta ba abunda zata ce maki tunda ai ba ita zata zauna da shi ba dole kece zaki yanke kar Kiji wani abu ki fad’i man ra’ayin ki kan hakan” wani abu Fatuu ta had’iya ta rasa ma wace amsa zata bata duk ta rud’e kanta a k’asa sai zare ido take tana motsa hannuwan ta da bakin ta, da d’an d’aga Murya Hajiya tace mata dare nayi tayi magana d’agowa tay duk ta dabarbarce murya na rawa tace “…..Duk abunda…kuka za6a man yayi man” d’an murmushi Hajiya tay tace “To Fateema in muka za6a maki abunda bai maki ba fa tunda mu ba sanin abunda ranki zai fi so mukai ba kuma dae baso muke mu takura maki ba shiyasa aka baki dama ki fad’i abunda ranki ke so, kinga mu bamu zamu zauna da shi ba don haka kar Kiji komae ki fad’i kina son cigaba da zama dashi matsayin miji ko kuwa a raba ku” k’ara kallon gwaggo tay taga bata kallonta ta maida idon k’asa abu biyu ne suka hanata magana na farko kunya na biyu kuma tana kokonton amincewa ba kamar yanayin da take gani tattare da Haisam d’in,
“Shikenan tunda baza kiyi Magana ba bari in tashi in tafi, ni dae bazan yanke hukunci ba yazo kuma bai maki dad’i ba tunda ai harda irin hakan tasa aka fasa wanccan auren ko an za6a maki wanda baki so duk da harda k’arin halin shi” ganin tana k’ok’arin mik’ewa yasa gwaggo ta canza harshe tay ma Fatun Magana da d’an d’aga murya tace bazata bud’e baki tay magana ba, tana yamutsa fuska kaman zata saka kuka itama ta juya harshen tace mata tana so amman kunya take ji ta fad’i mata hakan, Hajiya da ta fasa mik’ewa ta kya6e baki tana bin su da ido har suka gama sannan tace “wato matsalar ka zauna cikin wad’anda ke yin yaren da baka iya ba kenan har gulmar ka sai ayi a kuma zage ka tass ba tare da ka sani ba k’arshe ma har kai ta washe baki kana tunanin abun kirki ake fad’a kaiga sakarai” murmushi kawae gwaggon tay Hajiya dake kallonta tace to mi suka ce a fad’i mata gwaggo tay mata bayani, wata irin kunya ce ta lullu6e Fatuu kan ta a sadde, d’an murmushi Hajiya tay tace “ina ruwan Fateema to miye abun jin kunya mutumin da dama Mijin ki ne kawae amsa zaki bada, shikenan Allah Ubangiji ya shige mana a Al’amarin tashi kije Allah yay maki Albarka ya k’ara maki lafiya damu baki d’aya, a hankali ta amsa da Amin ta mik’e ta nufi hanyar fita sumi sumi har lokacin bata d’ago fuskar ta ba, Bayan fitar ta Hajiya ta kalli gwaggo tace “Sai ku fara shiri ran Juma’a in Allah ya kaimu zata tare a d’akin mijinta nan part d’in shi” rasss kirjin gwaggo yay bata yi tunanin haka da wuri ba a d’an rud’e tace “to..Amman Hajiya bai yi wuri ba kuwa har a shirya ta tare a ranar?” Hajiya dake kallon ta ta cikin glasses tace “to Dije wane irin shiri ne za’ai da har nan da Juma’a bai isa a gama ba?” Cikin yar inda inda tace “dama wai Saboda kayan d’aki tunda wanccan wanda suka yi su sun fanshe su yanzu dole sai nayi ma Mahaifin nata Magana sai a siya wasu koda anan ne sai kuma sauran dae abubuwa” tana Maganar tare da yin nuni da hannuwan ta har ta k’arasa Hajiya da ta ta6e baki tana saurarar ta tace “To wane kayan d’aki kuma, ina ce a part d’in nashi akwae su kuma ba abunda sukai yanzu in an siya mata wasun su wanccan ya za’ai da su, ki bar zancen wasu kayan d’aki tay amfani da wanda ke akwae acan abunda ma nasan zaman na d’an lokaci ne Saboda karatun ta data gama ai dole ta bi shi inda yake zaune tunda ba yadda za’ai tay zaune nan mijin ta na wata uwa duniya, kuma ko bayan ta taren kina iya ganin ma ya canza mata wasu kayan d’akin tunda wanda ke akwae yanzun ma ai daga can K’asar wajen ya siyo su don haka ki bar zancen su kiyi sauran yan shirye shirye da ba’a rasa ba suma kada kice zaki wani takura kan ki tunda an riga an d’aura ba wani abu da ake buk’ata kawae ki sanar ma makwabta da Abokan Arzik’i don a shaida auren tunda abun surutu bai ma Mutane wuya kuma ma dai wani surutun dole ayi tunda yanzu tazo ta samu ciki kuma tazo daga baya ta haihu duk mutane basu san da auren ba ai kinga dole ayi surutu ko, in da wata matsala kiyi magana ina sauraren ki” godiya gwaggon tay mata daga baya tace “akwai kayan kitchen da ya siya mata na waccan auren suna nan ajiye ban san ko za’a iya kai mata ba tayi amfani dasu” tace “Eh to bai kamata aita ajiye su ba, bari muga tunda akwae d’ayan d’akin da yake aikin injiniyan cin nashi kuma an kwashe komae tunda yanzu ba’a nan yake ba sai abunda ba’a rasa ba inaga sai a jera mata kayan a cikin shi ya zama kaman kitchen dama kuma zagaye yake da table sai a k’ara gyarawa yadda zai yi Sosae, shikenan ko in kuma da wani abun sai ki fad’a don nafi son mu gama Maganar da ta danganci tarewar yanzu” d’an shiru gwaggo tay akwae abunda ke damunta a rai saidae ta rasa ta yadda zata yi mata Maganar Hajiya ta lura hakan yasa tace mata tayi magana inda wani abu ta kalleta cikin yar in ina tace “d…dama wai naga su can sauran dangin nashi da Matar shi basu san da Maganar auren ba shi ne nace…to ba matsala ta taren?” Hannu Hajiya tasa ta ruk’e ha6a “Oni Dije kin fi ni sanin abunda ya dace ne ko kuwa tsoro kike in sun sani za’a cinye maki Fateemar?” da sauri gwaggo ta girgiza kai alamar a’a ta hau bata hak’ura Hajiya ta dasa fad’in “ki bita da Addu’a kawae in sha Allahu komae zai zo da Sauk’i tunda shi ya k’addaro komae nasan hakan duk cikin hikimar sane shiyasa nima na d’auki Al’amarin da Sauk’i” kai gwaggo ta jinjina tay Addu’a tare da k’ara yi mata godiya daga haka ta fara k’ok’arin mik’ewa gwaggo ma ta tashi don tay mata rakiya,
Fatuu na komawa d’aki ta nufi gadonta ta haye can k’arshe ta zauna had’i da jingina bayanta a jikin bango sai zare ido take tama rasa shin murna ya kamata tayi ko mi, canjin da take gani a wurin Haisam duk shi ya Sagar mata da gwuiwa har take jin shakku game da zaman su tare gani take kaman shi bazai so hakan ba saboda in don laifin da ta yi ne ai ta bashi hak’uri, gani take da yana son ta ko yana son cigaba da zama da ita ai da ya hak’uri ya sake mata, tana haka Gwaggo ta shigo bayan ta dawo daga raka Hajiya, gadon ta nufa ta zauna a baki idonta a kan Fatuu da itama ta k’walalo ido tana kallon ta can tay yar ajiyar zuciya ta fara Magana “Sai ki fara shiri ranar Juma’a in Allah ya kaimu zaki koma gidan Hajiya can part d’in Yayan naki” dadamm! k’irjin Fatuu yay wata irin Fad’uwa ta zaro ido kaman zasu Fad’o a razane take kallon gwaggo jin abunda ta fad’a wanda kwata kwata bata zaci jin hakan ba, ko da ta amince ba tay tunanin da wurwuri haka ba, jin bata ce komae ba yasa gwaggo cewa bata ji abunda tace bane ta d’an yamutsa fuska kaman zatai kuka tace “Gwaggo da wuri haka kuma ya za’ai hakan bacin ba wanda ya sani a dangin shi ko ita fa Aunty Fanan bata sani ba” da alamun damuwa akan fuskar gwaggo tace “to nima nayi ma Hajiya Maganar hakan amman tace ayi Addu’a kawae Allah ya shige mana gaba” idanun ta ne suka ciko da k’walla ita tasan hakan ba k’aramar matsala za’a iya samu ba can suka fara zubowa sharr gwaggo dake kallonta tace mata ai ba kuka yakamata tayi ba suyi Addu’a kaman yadda Hajiyan tace komai sai aga yazo da Sauk’i cikin kuka tace “amman gwaggo ni ina tsoron kada azo a samu matsala fa in daga baya suka sani suka ce basu yarda bafa basu son auren tunda kinga Aunty Fanan yar’uwar su ce” shiru gwaggo tay ta sauke idanun ta k’asa ita kanta abunda yafi damunta kenan a cikin rai can ta d’ago tace “Addu’ar dae kawai zamuyi tunda ba abunda yafi k’arfin ta, koda nayi mata magana kan hakan nuna wa tay ban fi ta sanin abunda ya dace ba kin ga ai bazan yi jayayya da ita ba ko” shiru Fatuu tay tana goge kwallan dake zubo mata ana haka Amadu ya d’aga labulan d’akin ganin gwaggo yasa shi shigowa yana fad’in ashe tana nan yaje d’aki bai sameta ba hannun shi ruk’e da k’atuwar leda ya nufo su a bakin gadon ya aje ledar yace gashi nan in ji Ya Haisam yana gaida mai jiki kai gwaggo ta d’aga, ganin yanayin fuskar ta yasa shi tambayar ta lafiya ya juya kan Fatuu dake ta goge k’walla ba shiri ya kai zaune yana tambayar gwaggo jikin nata ne ta girgiza mashi kai alamar a’a,
“To miya ke faruwa ne naga kunyi jugum jugum ga damuwa akan fuskokin ku ita harda kuka don Allah ku fad’a man?” Shima har yanayin fuskar ta shi ya sauya yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fad’a mashi zancen da Hajiya tazo tayi, d’an bud’a ido yay alamar mamaki sai kuma ya washe baki yace “to shine abunda yasa maku damuwa ku da zaku yi farinciki auren zai d’ore wanda mu hakan dama muke fata” d’an murmushin yak’e gwaggon tay tace “ba wai ba’a farincikin bane kawae damuwar tamu game da dangin nashi ne da basu san da zancen auren ba ita gudun ta kar daga baya kuma azo a samu matsala suce basu amince ba” da sauri yace “ku ma cire wannan tunanin in sha Allahu ba wata matsala da za’a samu koda ma an samu Allah zai kawota da Sauk’i don haka mu mik’a komae gare shi ayi Addu’a kaman yadda Hajiyan tace, kuma kun manta ne gaba d’aya dangin na shi da matar ta shi duk tana da iko da su don haka ayi yadda tace kawae” jinjina kai gwaggo tay ya juya kan Fatuu yana murmushi ya d’an kwanta kan gadon ya kai hannu ya kamo hannun Fatuu guda yana fad’in “u should be happy Allah ya amince Romeo ya zama naki ba kuka ba” tura mashi baki tay yasa dariya gwaggo ma murmushi ta bisu da shi, sakin hannun Fatun yay ya koma ya zauna yana kallon gwaggo yace “to yanzu ya za’ai Maganar kayan d’aki gashi an sa k’urarren lokaci ko da yake ai indai da kud’i har a siya ko?” Fad’i mashi yadda sukai da Hajiyar game da hakan tay yace “shikenan ma an hutar da mu naji dad’i wllh in akwai buk’atar ayin ko nan gaba sai ayi matan in kuma zai tafi da Ita can d’in ne bama sai an yin ba” juyawa yay kan Fatuu dake ta bin su da ido yana dariya yace “Waya ga su yar fillo a jirgi za dai asha hauka nasan” k’ara tura mashi baki tay ta d’an harare shi yace “ni kike harara, kifa bar ganin wai ke matar aure ce baki fi k’arfin in kikai man ba daidai ba in zane ki ko da kin bar gidan nan ne zan iya bin ki har can gidan in maki hukunci” gwaggo dake dariya tace “shi kuma mijin nata sai ya bika da ido kai ta dokar mai mata ko”,
“Wllh yadda yake tubarkallan nan ma sha Allah yace zai rama mata ai sai ya karairaya ni nasan” ya k’arasa yanata dariya itama gwaggon dariyar take Fatun dai sunkuyar da kai tay tana d’an murmushi yayin da zuciyar ta ke suffanto mata surar Haisam,
“To yanzu shikenan sai dae a jira ranar akaita ko akwae abunda zaki?” Amadu ya tambaya tace “Eh zan bada ayi mata su cin cin tunda za’a sanar da makwabta zancen Auren nasan daga baya za’a shishshiga sai ranar Juma’a d’in ayi Abinci Saboda wanda zasu zo” kai ya jinjina “hakan yayi amman fa kar kiyi su da yawa ayi daidai daidai, to su yan Adamawa fa za’a sanar masu ne naga kaman lokaci ya k’ure ko?” d’an jimm tay kafin tace “zan kira Baffanta in sanar mashi komai amman zance mashi ba sai sun zo ba su bari sai daga baya in an samu natsuwa” kai ya jinjina yace hakan yayi sai kuma yace “Yanzu shikenan haka za’ai bikin Romeo da Juliet d’in lami ba wani d’an cashewa gaskiya yakamata a d’anyi mana ko yar dinner ce mu shaida muna biki” gwaggo dake murmushi tace “aikuwa dai haka zaku yi hak’uri don ba wani abu da za’ai” gyad’a kai yay “shikenan amman fa mun biyo bashi ko daga baya ne dole ayi mana in komae ya daidaita dangin shi sun sani” ta6e baki gwaggo tay “tunda ibada ne ya zama Farilla dole sai an yi ko” k’ok’arin mik’ewa ya fara yi yana fad’in bari ya d’aukko plates su yi shagalin abun farinciki ya nufi hanyar fita, plate guda biyu ya d’aukko babba da k’arami ya duk’a ya bud’e ledar abubuwan daya saba kawo wa ne a ciki ya zuzzuba a plate d’in ya mik’a ma gwaggo ta kar6a shima ya d’auki wanda ya zuba a k’aramin plate ya mik’e idon shi akan Fatuu data takure a guri guda yace “ki saki jiki Amaryarmu dis is worth celebrating don haka ki saki ran ki kici ki k’oshi” ya nufi hanyar fita yana fad’in dole ma ya d’inka sabuwar shaddar kai Amarya daga haka ya fice gwaggo ta d’an girgiza kai da d’an murmushi ta juya kan Fatuu da tay zuru tace ga abu nan taci, girgiza mata kai tay alamar a’a ganin ta damu sosae yasa ta shiga kwantar mata da hankali tace ta saki jiki taci don jikinta na buk’atar su ko kuzarin ta ya dawo cike da tsokana tace mata ko so take a kaita d’akin miji haka sukuku da ita Amarya da ake son ta da kuzari Fatun ta duk’ar da kan ta gwaggon nata murmushi, daga baya ta d’ago suka fara ci tare da gwaggon lokacin take ce mata ta kira Fauzy ta fad’a mata don su fara shirye shiryen su k’unshi da gyaran kai har tana cewa yakamata ma in an gyara kan ai kitso ita dae Fatun shiru tay, bata wani ci sosai ba tace ta k’oshi amman gwaggo ta matsa mata saida ta k’ara ci daga baya ta bar d’akin da sauran da suka rage, tun bayan da gwaggo ta fita tay zaune zugudum ta rasa Mike mata dad’i ita dai har ga Allah zallumin zama part d’in nashi take ba tare da dangin su sun san da auren ba sam hankalinta bai kwanta da hakan ba, tana haka Gwaggo ta k’ara shigowa hannunta ruk’e da cup mai d’an girma a bakin gadon ta tsaya ta mik’a mata ta ce ta shanye abun ciki maganin sanyi ne ba tare data ce komai ba ta amsa ta kafa baki nan da nan ta shanye shi tass don dama ta saba bata tun kwanakin baya harda itatuwan tsarki da na sha duk ce mata take na sanyi ne, bayan ta shanye ta mik’a mata Cup d’in ta amsa ta juya Fatun ta bita da kallo don a yanzu ta gane ko magungunan miye take bata da sunan na sanyi, can wata zuciyar ta raya mata ko shiyasa ma lokacin da abun ya faru Ya Haisam d’in ya rikice mata tamkar bashi ba duk da rok’on shi da ta rink’a yi amman a banza, tuno lokacin yasa ta saki d’an murmushi tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamar kunya tana haka ta tuno da magungunan da Fauzy ta kawo mata na yar kwalbar inserting d’in shi ake bayan wasu mintuna sai a wanke da ruwan d’umi wata zuciyar ta raya mata tay amfani dashi yanzu sai kuma ta tuna da jinin da take hakan yasa ta bari sai ya d’auke sai wanda ake ci da nama gashi yanzu ta gama cin naman saidae ba dama ta sa a gaban gwaggo d’ayan kuma da peak milk tunanin ko taje shagon Kawu Amadu ta amso Madarar tay amman kuma ta k’oshi sosae gashi yanzu gwaggo ta bata wani k’arshe ta yanke gobe tayi amfani dasu kawae ta sauka don taje ta wanko hannu ta sha ruwa, tun bayan da ta kwanta bacci ya k’aurace ma idanunta sai juye juye take tana tunanin wane irin zama za tay da Ya Haisam matsayin miji kuma ta koma part d’in shi ganin abun take kaman wasa wllh, can kuma ta koma tunanin ya Aunty Fanan zata ji in taji Maganar auran na su ita da yan gidansu har saida gabanta ya fad’i tunowa da Mahaifiyar Fanan d’in wato Hajiya Maryam jikinta ne yay wani mugun sanyi don ta santa tana da kirki amman fa jarababbiya ce ta gaske a hankali tunanin ta ya koma kan yan gidan su Haisam su wannan bazata iya yanke hukunci a kan su ba kawai dae tasan suna da kirki sosae kuma tana Mutunci da wasu daga cikin yan gidan kaman Nameer, Jidderh dasu twins wannan sun ma maidata tamkar yar’uwar su haka Mahaifiyar Haisam d’in ta san ta sosae kuma duk in tazo tana zuwa ta gaishe da ita cikin sakin fuska take amsa mata bata san in suka ji zancen auren ko zasu amince ba, damuwa ce kwance akan fuskar ta haka taci gaba da tunane tunane har bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Washe gari da niyyar zuwa Makaranta ta tashi ta hau shiri ba 6ata lokaci gwaggo na cikin Kitchen ta iske ta bayan ta amsa mata gaisuwar ta ta bita da kallo ganin ta sanye da Uniform yasa tace mata ba dai Makaranta wai zata je ba tace eh ai ta samu sauk’i, girgiza kai gwaggo tay “koda kin samu sauk’i bazaki je ba gaskiya har sai shi Mijin naki ya baki izini tukun kar ai rashin hankali” yamutsa fuska tay kaman za tai kuka tace “amman gwaggo ko da ai da auren nike zuwa ko har ma in zauna a can” gwaggo dake kallon ta ta d’an d’aure fuska tace “da kika ce lokacin baki san da auren ba yanzu kuma kin sani don haka duk abunda zaki sai da izinin shi” idanunta cike da k’walla tace “to gwaggo in kika ce sai ya bada izini har sai yaushe kenan zan ci gaba da zuwa kina gani fa ko jiya bai shigo ba Kawu Amadu ya ba sak’o” tace “ba kina da waya ba ki kira shi mana ki fad’i mashi” tura baki tay tana cigaba da yamutsa fuska had’i da kikkafta idanu gwaggon ta mik’o mata abun breakfast tace taje tayi yadda sukai da shi to ta amsa ta juya, tana komawa d’aki ta aje kayan Breakfast d’in akan Carpet ta koma bakin gado ta zauna sai k’unci take ita sam bata son ta kira shi don bata san mi zata ce mashi ba da sunan neman wani izini shi da ko kiranta bai yi ba tun bayan da suka dawo har yanzu sai ita ce zata kira shi, tana ta zaune cikin 6acin rai can dubara ta fad’o mata da sauri ta kai hannu ta d’aukko jakar goyonta ta bud’e wayarta ta fiddo ta fara kiran Abbas tana fara yin ringing ya d’auka bayan ta gaishe da shi yay mata ya jikin ta amsa daga nan tay shiru jin haka yasa shi tambayar ta da wani abu ne murya kaman zata yi kuka ta fad’i mashi makaranta take son zuwa amman gwaggo ta hana wai har sai Ya Haisam ya bada izini kuma tun jiya daya maido su ma ita bata k’ara ganin shi ba tambayar ta yay har ta samu sauk’in da zata iya cigaba da zuwa School tace mashi eh har yana cewa kodae ta bari ta k’ara warwarewa amman ta kafe kan ta samu sauk’i ko ta zauna ba abunda take sai kwanciya kuma can ana ta wuce ta, sigh yay jin haka yace ta bashi wasu mintuna zai sake kira tace to, bayan sun gama wayar ta saukko ta fara yin breakfast don ranta ya bata zata je Makarantar tana cikin yi sai gashi ya sake kira bayan tayi picking yace ta zama cikin shiri ga Mijin nata nan zai zo ya kaita ya k’arasa yana yar dariya tace ta gode, cire wayar tay ta bita da kallo jikinta ne yay sanyi jin shi zai kaita aje wayar tay taci gaba da yin Breakfast d’in, tana gamawa ta jiyo horn d’in shi har saida gabanta ya fad’i ta d’an yi jimm lokacin taji ya k’ara yin wani ta yunk’ura ta mik’e, gado ta nufa ta goya jakar ta ta sa hijab dake aje saman gadon bayan tasa fararen takalman ta na makaranta ta d’auki tray d’in kayan breakfast d’in ta fita, kitchen taje ta aje su ganin gwaggo bata ciki yasa ta fito ta nufi d’akinta tana zaune kan carpet itama tana yin breakfast d’in ta shiga ta d’aura idonta a kanta Fatun tace mata gashi nan yazo zata tafi gwaggon tace “to a dawo lafiya kinga ai hakan yafi da ai abu kai tsaye” bata ce komai ba tana shirin juyawa gwaggo ta sake cewa “amman fa gida zaki dawo don zama a Makaranta ya k’are in ma kina da kaya ki kwaso su yau kin ji ni?” Kai ta d’aga mata kawai ta juya ta fita, bayan ta fito ta nufi d’ayan side d’in Motar ta kai hannu ta bud’e lokacin da ta shiga idonta ya sauka akan shi har saida gaban ta ya d’an fad’i tay saurin d’auke idon ta ta rufo kopar, juyawa tay ta d’an kalle shi yana sanye da jallabiya ta gaishe dashi ya amsa ba tare da ya kalleta ba yaja Motar suka fara tafiya ta juyar da fuskar ta gefe wani abu taji ya tokare mata k’irji wai ita Ya Haisam ke sharewa haka idanunta ne suka ciko da k’walla da sauri ta fara K’ok’arin maida su don bata son su zubo mata, har suka isa fuskar ta na gefe ya parker inda ya saba aje ta tace mashi an gode ba tare da ta kalle shi ba tana niyyar juyawa don ta bud’e kopar taji yace mata “Wait” dakatawa tay still bata kalle shi ba saida taji yace mata ta amsa sannan ta juya ta kalli kud’in da yake mik’o mata yan dubu duba bin kud’in tay da ido kafin ta d’ago a raunane ta kalle shi suka had’a ido da sauri ta kawar da nata ta furta “ka bar su” shiru bai tanka mata ba bai kuma janye kud’in ba yamutsa fuska ta fara yi tana d’an kikkafta ido a K’ok’arin ta na kada tay kuka ta sake juyawa still kallonta yake fuskar shi ba yabo ba fallasa ta sake ce mashi tana da kud’i nan ma bai tanka ba bai kuma janye kud’in ba bata da yadda zatay ba don ta so ba tasa hannu ta kar6a wani irin bak’in ciki ne ya turnuk’e ta ta shiga ayyana wato ita ga mayyar kud’i, ko tambayar ta ya jiki bai yi ba sai wasu kud’i zai bata, can k’asan mak’oshi ta furta mashi ta gode tana shirin juyawa ta bud’e taji yace mata ya jikinta har bata san lokacin data juya ta kalle shi ba kaman mai jin zancen zuci, d’auke idon tay ta ce mashi ta samu sauk’i daga haka ta juya ta bud’e Motar ta fice, saida taji ya juya Motar ya tafi sannan ta tsaya da tafiya ta juyo tana kallon Motar idanun ta cike da k’walla sharr suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa kafin ta juya ta nufi aji, tana shiga suka had’a ido da Fauzy aikuwa ta taso da gudu ta nufo ta tana fad’in Oyoyo Bestie nah, tana zuwa ta kankame ta gaba d’aya hankalin yan ajin ya dawo kan su, sakin ta tay tana kallonta da murmushi da alamun mamaki tace mata wai har ta warke ta d’aga mata kai, kama hannuta tay suka nufo cikin ajin ana ta mata sannu da jiki tana amsawa, koda suka zauna akan seat d’in su haka a kaita tasowa ana zuwa yi mata ya jiki harda Zainab Muhammadu nan ta hau ce ma Mutane wllh su zo su nemi yafiyar ta zargin ta da sukai na tana da ciki bada aure ba aikuwa wasu sukai ta ce mata ta yafe masu su basu san ita matar aure bace tace ta yafe suna haka malamin su ya shigo kowa ya koma seat d’in shi, gaba d’aya damuwa tay mata yawa har ta kasa tsaida hankalin ta kan abunda ake koya masu saidae ta sunkuyar da kai kota kai hannu ta dafe goshi ko ta d’an cije baki Fauzy duk tana lura da ita saidae ba damar tayi mata magana, basu samu damar yin Magana ba don malamin na fita wani na shigowa har saida akai break sannan Fauzy ta tambaye ta wai mi yake damunta ne ta lura tana cikin damuwa nan ta kwashe zancen tarewar ta ta fad’a mata har Fauzy bata san lokacin data saka yar k’arar murna ba cike da farinciki tace “to keda zaki farinciki ma Allah ya cika maki burin ki Aure ya d’ore Ya Haisam ya zama naki sai kita damuwa” d’an yarfa hannu tay ta cije baki tace “Fauzy bazaki gane ba ne ina hango gagarumar matsala a tattare da hakan dangin shi fa basu sani ba haka ma Matar shi Hajiya ce kadae ta sani yanzu in suka zo daga baya suka ce basu amince da auren bafa?” Da sauri Fauzy tace “ni wllh ban ganin za’a samu wata matsala, karfa ki manta gaba dayan su Hajiya na iko dasu tunda kuma ta amince ai ta zauna na tabbatar bazata bari a raba auren ba kawae muci gaba da Addu’a” shiru kawae tay idanunta sun cika da k’walla can suka zubo sharr da sauri Fauzy ta dafa Shoulder d’in ta ta shiga bata hak’uri cikin kuka tace “Fauzy abunda yafi damu na Ya Haisam ya canza man yanzu da nike ganin ya zama mallaki na, in don laifin dana yi mashi ne na bashi hak’uri duk da in zai man Adalci ai bani kadae keda laifi ba ko, ni ina ganin gaskiya kaman gara in hak’ura da auren shi tunda na fahimci bai sona kawae nasan zai amince ya zauna da ni ne k’ilan don Hajiya tay mashi dole kinga to wane irin zaman aure zamu yi haka, koda nike son shi nafi son shima ace yana sona ko d’an yaya ne” yar ajiyar zuciya Fauzy ta sauke tace “ni gaskiya ina tunanin k’ilan akwae wani dalili da ya sa ya canza maki amman ba wannan ba kuma da dukkan alamu yana son ki shiyasa tun farko bai sake ki ba kaman yadda aka tsara, kuma in ma fushin yake Saboda rasa cikin kinga hakan ya tabbatar da yana son kine shiyasa yake son cikin har yay fushi da kika zubar, kuma da bai son ki gaskiya a ganina bazai amince yaci gaba da zama da ke ba tunda shi fa namiji ba’ai mashi dole irin wannan” shiru tay kaman mai nazarin wani abu can tace “ina ganin kaman hakurin da kika bashi bai isa ba mi zai hana ki same shi ki bashi hak’uri sosae, da kaman ki k’ara iske shi can G.r.a d’in nike gani” d’an waro ido Fatuu tay tace “in je in k’ara bashi hak’uri kuma, gaskiya ni bazan je ba Fauzy hakanan ya wulakanta ni ai na bashi hakurin ko” hannu Fauzy ta kai ta dafa Shoulder d’inta tace “k’ilan abun yay mashi ciwo ne sosae, kinsan su irin su gane masu yana da wuya amman tunda har kika ga ya nuna to tabbas bai ji dad’in abun bane kije ki same shi ki bashi hak’uri sosae ba fad’uwa bane wllh karki manta shi Mijin ki Aljannar ki na a tafin kafar shi kuskurene ace yana fushi dake haka indae fushin yake da gaske Saboda abunda kika aikata don haka nidai a gani na kije ki bashi hak’uri tun kafin ranar Juma’ar tayi” shiru Fatuu tay tana juya zancen zuwa bashi hakurin a cikin ranta can wata zuciyar ta tuno mata da lokacin data fasa mashi glass har Haulat ta bata shawarar taje ta bashi hak’uri kuma shawarar tayi mata amfani wanda itace silar komae a tsakanin su, yin wannan tunanin yasa ta kalli Fauzy tace “shikenan zan je d’in amman bansan lokacin da yake can ba gashi in na koma gida bansan yadda zan ce ma Gwaggo ba har ta barni in fito” Fauzyn ta tambaye ta yana zuwa aiki ne tace mata a’a ya bar aiki nan tunda ya bar K’asar, sake tambayar ta tay yaushe rabon data gan shi tace mata shi ya kawo ta tace “kinga da ace can ya tafi sai kiyi sauri tunda anyi break duk da ma an kusa dawowa sai kije ki dawo mai Napep d’in da ya kai ki sai ya jira ki ku dawo” d’an jimm Fatun tay kaman mai yin tunani can tace bari ta gwada zuwa k’ilan can ya wuce in kuma bai can sai ta dawo ta mik’e Fauzy ma ta mik’e tace bari ta rakata, suna fitowa waje suka samu Keke Napep Fatuu har zata shiga ta dakata takai hannu cikin aljihun rigarta ta fiddo kud’i cikin wanda ya bata ta mik’a mata tace tay break ta shige cikin Napep d’in Fauzy ta d’aga hannu tana mata sai ta dawo da fatan Allah yasa ta iske shi ta amsa da Amin yaja suka tafi ita kuma ta juya……………
…
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :Â Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :Â @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:Â Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.