Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Page 60 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SIXTY📍

Kallon juna deen da baby tee sukayi a tare gabansu na faduwa, suna mamakin videon wani scene ne haka da sultan yake nunawa da rawar jiki……
Deen ne ya fara dauke kansa yana tabe baki irin ko oho dinnan…..
Kurawa wayar ido umm da ummi sukayi suna kallon ikon Allah, videon ya fara ne tin daga inda saif ya shigo gurin walking majestically, kamar wani shirin film sai ga baby tee ta tawo tayi hugging dinsa, a take shi kuma yayi hugging dinta back kamar abinda yake jira kenan dama, zaro ido sukayi ganin deen yayi sama da baby tee sun bar gurin… Swiping to the next video ummi tayi sai gasu sun dawo a tare suna rike da hannu juna……
Wani irin bacin rai umm taji ya dirar mata, babban abinda yafi harzukata shine ganin uban mutanen dake zagaye da gurin, fisabilillahi me mutane zasuyi tinani? Duk hankalin deen datake ganin gurin tsawatarwa idan akayi ba daidai ba shine ze bada contribution a abu irin wannan, in ita baby tee bata da hankali da kunya tazo ta rungumeshi a cikin mutane baze tureta ba? Ko ya wanka mata mari? Saidai ma rungumeta dayayi har dasu daukanta suka bar guri? What nonsense? tukunna ma daya dauketa suka bar gurin ina sukayi? gashi kuma sun dawo hannuwansu rike dana juna irin su nunawa duniya su cikakkun marasa kunya ne kome? wani kalan rashin kunya ne wannan dan Allah? She’s just too disappointed wallahi!..
Ummi ma wani iri taji a ranta kamar ta wankawa sultan daya kawo gulman mari, ita da tasan abinda zasu gani kenan a videon wallahi da bazata bude a gaban umm ba, sai ta kalla ita kadai ta musu fada a boye batareda su umm sun sani ba saboda duk iyayen da sukaga ya’yansu a irin wannan yanayin a cikin mutane dole hankalinsu ya tashi……
As a justice daga kallon fuskokinsu kawai mami tasan something is fishy, something very wrong ma kuwa, gashi sun ki cewa komai sun bar video sai replaying yake and from the sound tasan definitely wasu couples ne saboda yanda aketa su ‘awwwwn’, ‘God when’, ‘I go love oo, ‘so romantic’ harda masu ‘the way he grab her waist’ da sauran shirmen zamanin yanzu.. But why are they so shocked? Shine tambayar da take yiwa kanta?
Mikewa tayi taje ta zare wayar daga hannun ummi sannan ta koma ta zauna ta dawo da videon farko……
Wani irin bude ido tayi tana kallon abinda ke faruwa a videon unbelievably, ranta in yayi dubu ya baci, everything seems like a film, wani kalan stupidity of the highest order ne wannan, babban abinda yafi bata takaici shine yanda suke denying junansu a gaban kowa, so nawa ana tambayar deen yana sonta amma kullum amsar dayace shi bayaso, shi me zeyi da ita, itama magana kadan sai tace khaleel dina, shine zasu zo suna rungume rungume a cikin mutane ko tinanin yanda za’ayi yawo dasu basayi, ga duniya data zama na social media saidai kawai mutum ya ganshi yana yawo a yanar gizo, tin ba’a je ko ina ba gashi suma sultan ya biyosu da video har daki Allah kadai yasan ina videon zaije yanzu, as an inquisit she can’t believe this is their first time because they look so comfortable with each other, amma ko menene wannan ze zama na karshe saboda zata dauki mummunan mataki akansu and she’ll make sure she deal with them mercilessly!……
“Wai me kuke kallo ne haka naga fuskokinku kamar anyi mutuwa?”…..
Anna da hakurinta ya kare akan taga an mata bayani ko an nuna mata ta fada tana mikewa tsaye…..
Shiru taji babu wanda ya kulata, karasawa tayi ta fizge wayar daga hannun mami ta hau kallon videon itama…..
Murza ido tayi implausibly tace;
“Menene wannan haka? Su waye? Kai sultan wuce ka dauko min glasses dina inga wasu mutanen banzan ne wannan da kyau”…
A sanyaye sultan da duk jikinsa ya mutu ganin yanda kowa yayi wani iri daga kallon videon ya mike, shi har zuciyarsa bada wani abu yazo ya nuna vidoen ba, hasalima burgesa sukayi kuma duk a tunaninsa couples ne su kuma an san da zaman relationship dinsu shiyasa yazo ya nuna, apart from that kuma yaga they’re family so ba wani abu bane dan sunyi hugging juna saboda al’adar larabawa data shiga kansa saboda zaman dubai sai yake ganin hakan bakomai ba…… Shiga ciki yayi ya daukowa Anna glasses dinta ya kawo mata….
Karba tayi ta saka glasses din ta cigaba da kallon videon, inta kalla kadan sai ta dago ta kalli deen da baby tee dan ta tabbatar su din take gani a videon kuma kayan dake jikinsu ne……
A lokacin deen da baby tee ji sukayi kamar su nitse a kasa saboda tsabar tsarguwa, su dai har lokacin basu gane me take magana akai ba duk kuwa da yanda kowa yake expressing nasa reaction, dukda sound din da suke ji besa sun dago komai ba saboda lokacin da abun ya faru gabadaya hankalinsu ya gushe kwata kwata ko ihun mutane basu ji ba balle su san ana musu video, they are just so lost into each other, abinda sukasa a gaba kawai shine……..
Sakko da glasses dinta kasa anna tayi tana musu kallon kasan ido taga yanayinsu amma deen ko alamar damuwa babu sai ma dauke kai da yayi, baby tee ko gabadaya ta gama tsurewa hankalinta duk ya tashi, ga wani mugun tsoron daya kamata kamar lokaci guda…….

 

Download>>> Abban Sojoji Book 2 Complete

Gyara zaman glasses dinta tayi ta kalli sultan tace;
“Kai sultan ungo wayarka ka fita”…..
Tashi yayi da sauri gumi na karyo masa ya karbi wayar ya fice…….
“Rufomin kofar nan!”…..
Cewar anna tana nuna ummi maman sultan…
Tashi ummi tayi ta rufo kofar ta dawo ta zauna…..
Baby tee na ganin an rufe kofa ta kara tsurewa, cikin tsoron da taji ya kara taso mata ta fashe da kuka tana kankame deen……
Wani irin yarr deen yaji a jikinsa besan sanda ya zagaye kugunta da hannunsa yana janyota jikinsa ba……
Shigewa jikinsa ta tayi tana sakin wani irin kuka me ban tausayi….
Sosai kukanta ya daga masa hankali har ya manta da mutane a cikin parlourn….. Mintsininta yayi lightly a kunne ta dan rage sautin kukanta, sannan yayi kasa da muryarsa sosai a hankali cikin rarrashi yace;
“Shhhhhhsh stop crying pretty!”…….
Tsagaita kukantayi murya chan kasa yanda babu wanda ze jita sai shi tace;
“I’m scared, me mukayi?”….
“Nima bansan abinda mukayi ba, but I promise you babu abinda ze sameki, whatever it is I’ll take the blame all alone baby girl!”…..
Shiru tayi tana sauraronsa but her heart is still beating very fast…..
Sake baki anna dake tsaya akansu tana kallonsu tayi, sai taji duk wasu maganganu daya tanadan musu sun kafe mata ganin sun wuce inda take tinani, sai kawai ta koma ta samu guri ta zauna tayi tagumi tana kallonsu…
Mami ce ta fara dagowa taga yanayin da suke ciki, mikewa tayi a harzuke tayi kansu tana fadin;
“Ashe rashin kunyar ku ta kai kuzo ku maimaita mana rungume rungumen da kuka gamayi a waje? Saboda gaku fitsararru, marasa hankali marasa tarbiyya? Yo ko rasa mafada kukayi ai be kamata kuyi wannan haukar ba bare kuna dashi, ko tinanin abinda zaije ya dawo bakwayi, sai kace da keya kuke tinani, kun bani mamaki wallahi especially you saif kullum aka tambayeka if you have anything for her the answer is always no! Kema kuma kullum akayi magana khaleel khaleel khaleel! Shine zakuzo kuna shashanci a gaban mutane, toh wallahi zakuci kutumar ubanku! Saketa dan ubanka!”……
Kin saketa deen yayi saboda yanda jikinta ke rawa cikeda tsoro, sai a lokacin kuma suka gane kan zancen da suke da kuma videon da suke magana akai even though su basu gani ba, amma abun ya basu mamaki yanda akayi musu video basu sani ba, sannan deen ya kudirta aransa ze ci uban sultan daya kawo gulma…..
Tasowa umm tayi a zuciye ta fuzgo wani wayar charger dake kan tv stand tayi kansu dashi ta fara zuga musu, deen daya hango tawowarta ta wutsiyar ido yayi saurin tura baby tee a chan cikin kirjinsa ya mata rumfa yanda dukan baze sameta ba…
Haka umm ta dinga zuba musu wayar charger sai masifa take ta inda take shiga bata nan take fita ba….

 

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

“Saif ka bani mamaki! Ashe kallon kitse nakewa rogo? Idan ita hankalinta ya gushe kai ina ka kai naka hankalin? Sai ka biyemata ku aikata wannan nonsense din a cikin mutane, sannan ku gama rashin da’arku a waje shine muma sai kunzo kun nuna mana mu tabbatar da ku isassu ne? Toh bamu kukayiwa ba kanku kuka yiwa kuma kun nunawa duniya ku yan iska ne, yaran banza yaran wofi! Wait is there any illegal relationship going on between you two? Is there? Baza kuyi magana ba? Au kareta kakeyi dan kar insameta? Saketa! Saketa nace! Bazaka saketa ba! Yan iska fitsararrun banza marasa tinani! Wallahi me rabani daku yau sai Allah a gidannan, sai kunyi min bayanin duk wani kulle kulle da kuke shiryawa”……
Wayennan sune ire iren maganganun da umm take a fusace meanwhile tana zuba musu wayar charger har lokacin…..
Tasowa ummi da taga abun ya fara yawa tayi ta karasa kusa da umm tace;
“Dan Allah dan annabi umm kiyi hakuri ki kyalesu karki musu illa, be kamata idan rai ya baci hankali ya gushe ba, ki bari mu bi abun a san…..”…
Bata direta ba mami ta katseta cikin fushi tace;
“Wani irin maganar banza kike fadi ummi, irin wannan danyan aikin har za’a tsaya a wani bisu a sannu, waye ze wani basu listening ear bayan sun ruga sunyi abinda sukeso suyi duniya ta sheda kuma muma sunzo sun tabbatar mana a gabanmu mun sheda, ki barta ta illatasu bamu da asara tinda haka suka zaba”……
Komawa ummi tayi ta zauna cikin rashin sanin abunyi, umm kuma ta cigaba da gashi…..
Kamar wacce aka tsikara anna ta mike da sauri tayi kan umm, a gigice tace;
“Ke jamila mikomin charger nan, baki da hankaline kike yiwa jikokina irin wannan dukan, kisa sukayi ko zina sukayi da kike nema ki illataminsu”…..
Budar bakin umm tace;
“To wayasani ma ko suna zinar?”…..
A kidime anna tace;
“Ni kike gayawa haka jamila? Allah baze sa inga haka a zuri’ata ba, ke kenan in ranki ya baci bazaki iya controlling kanki ba? So kuke ku nunamin ban isa da ya’yanku ba, Toh idan kika kara dukansu Allah ya isa ban yafe ba tinda ke na isa dake!”…..
A fusace umm ta wurga musu wayar charger ta bar parlourn, mami na ganin ta fita tabi bayanta da sauri…… Ummi na ganin haka itama tsulum ta fice…..
Su umm na shiga suka tarar da eesha a chan kuryar dakin sai kuka take…..
Ajiyar zuciya anna tayi ta kallesu har lokacin suna manne da juna tace;
“Toh ku saki juna duka sun tafi, in kuma zaku cigaba da rashin kunyar a gabana ne sai insan inda dare ya min yanzu”….
A hankali deen ya zame baby tee daga jikinsa, ya dagota yana kallon fuskarta, sosai ta jigata a haka ma ko duka daya be sameta ba, sai yaji tayi mugun basa tausayi dukda ita taja musu, hannunsa yasa yana share mata hawayen dake zuba a fuskarta……

 

Download>>> Boddiya Complete Hausa Novel Document

Kallonsu anna tayi cikeda tausayawa tace;
“Saifu juyo muyi magana!”…..
Ba musu ya juyo yana kallonta without uttering a word, da da ne sai sunyi rigima akan saifun datace amma dake bata wannan yake ba yanzu ko damuwa beyi ba…..
“Inaso ka fadamin abinda ke tsakaninku tsakani da Allah sannan meyasa kukayi haka a cikin mutane?”…….
Numfasawa yayi yace;
“Anna it’s not what you all are thinking, abinda ya faru shine zahrah tazo ta rikeni wai kanta ke ciwo precisely kamar jiri takeji a lokacin, anna kinga bayanda za’ayi in ture wanda bashida lafiya so I hugged her back, gudun mutsaya a haka a cikin mutane yasa na dauketa na kaita ciki, bayan mun shiga ciki na bata magani shine tace zata koma then I escorted her gudin kar wani abu ya sameta, I don’t know how everything got twisted haka har dasu video mu duk bamusan anyi ba”……
Gyada kai anna tayi cikin yarda da abinda yace, ita tasan dama dole there’s other side of the story, kuma kowa a family yasan saif mutumin kirki ne, ko harkar mata baya shiga, mutumin da aketa bi yayi aure ya kasa kawo mata ne za’a zargesa, instead of a tambayesu aji meyasa sukayi haka kawai sai iyayensu suka hau ci musu mutunci, jamila harda hadawa da duka sai kace wasu kananun yara, girgiza kai tayi tace;
“Ni nasan there’s more to this story dama kuma tin farko ba haka naso abi abun ba amma tinda iyayenku sunyi nasu ikon sai dai ince kuyi hakuri, sannan ku kwantar da hankalinku musamman ke zara’u naga kin daga hankalinki sosai, karki damu babu abinda ze sameki, kada kuma kiji haushin mahaifiyarki tayi hakane a ciki fushi saifu yasan halinta but trust me zata sakko kamar komai be faru ba, sannan zan musu bayanin komai in sun gama fushi fushin nasu, jeka abunka saifu”…
Mikewa saif yayi yayi hanyar kofa, baby tee na ganin haka ta tashi tabi bayansa da sauri….
Besan tana binsa ba sai da yakai bakin kofa, juyowa yayi kawai ya ganta a bayansa, murmushi yayi ya shafa kyakkyawar fuskarta yace;
“Why are you following me zahrah?”…..
Marairaicewa tayi tace;
“Karka tafi kabarni dan Allah, wallahi tsoro nake ji”….,
“Zahrah bakiga yanda ran umm ya baci bane? So kike ki bini ta kuma cewa munyi wani abu?”…..
“Ni dai kawai ka tafi dani, karta dukeni”…..
Hancinta yaja yace;
“Bazata dukeki ba baby girl, just stay with anna babu me tabaki”……
Matsawa gab dashi tayi tace;
“Nidai inajin tsoro kaji”…..
Kallonta yayi yana mamakin yanda ta zama very touchy this days abu kadan saita manne masa, shi kuma kamar wanda akayiwa asiri sai ya kasa tureta, zaro wayarsa dake aljihun hagunsa yayi ya mika mata yace;
“Gashi, anytime you feel unsafe I’m one call away baby girl, kinga number da zaki kira”……
Ya fada yana nuna mata number dayan wayanshi dake daki, karba tayi tace;
“Toh ka bani wayata mana”…..
“I’ll bring your phone later pretty yanzu baya hannuna”….
Ya fada yana pecking gashin gaban goshinta sannan ya fita ya barta a tsaye hannunta dafe da inda ya dora bakinsa…..

Da mamaki bappa yake kallon wayar sudais dake dauke da irin videon da sultan ya nunawa su umm, zaro ido bappa yayi yace;
“Su waye wayen’nan din?”……

Ta dade a tsaye a inda ya barta tana shafa gurin dayayi kissing dinta kafin daga bisani ta koma cikin parlourn, gabanta ne ya fadi ganin irin kallon da anna take mata duk a tinaninta anna taga sanda deen yayi kissing forehead dinta…..
Guri anna ta nuna mata a kusa da ita tace;
“Zauna mana zahra’u”….
Zama baby tee tayi ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa……
Kallonta anna tayi, tayi kasa da murya tace;
“Kina son saifu ne zahra’u?”…..
Ga mamakin anna sai taji baby tee tace;
“Eh ina sonsa”……

Back to top button