Uncategorized

Macijine Shi Page 17-18 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 17/18

______________Ƙara fattu ta kwalla cike da tsoro,dan ta saddaƙar kawai ta gama faɗuwa,saidai kuma maimakon tajita akan ƙasa ,saitaji ta faɗa kan wani abu mai matuƙar taushi kamar katifa.

Da sauri ta buɗe idanunta dan ganin inda ta faɗa,cikin mamaki take kallon bawan Allah nan,dan hannunsa ta faɗo, lokacin da yaga tayi baya zata faɗi ,bai ma san lokacin daya zabura yayi kanta ba ,tare da tareta ta faɗo akan hannunsa .

Kallon kallon sukewa juna basa ko ƙiftawa, yayin da bawan Allah ya zazzaro idanu waje ,irin wanda idan mutum yaga abin tsoro ɗin nan.

Ita kuma fattu mamaki take yaushe ya taso yazo gareta harya tare ta ?bata kai ga faɗuwa ƙasa ba?

Baffa ne yayi gyaran murya tare da faɗin “subhanallah,fattu sannu, Allah ya taƙaita wahala  da tuni kin faɗin ƙasa ,bawan Allah sannu kaji,kana fama da kanka amma zuciyarka mai tsafta bazata bari wani ya cituba,ina mai godiya gareka”baffa ya faɗa cike da jinjinawa bawan Allah nan,lallai akwai wani abu da Allah ya ɓoye tsakaninsa da fattunsa, haƙiƙa fattu kam,zuwa yanzu ta sami mai taimako,kuma yanzu ne ya kamata su fara neman dangin Fattu ,dan zuciyarsa na raya masa wannan bawan Allah alkairine ga rayuwar fattunsa.

Ahankali bawan Allah ya miƙar da fattu tsaye ,yana kallon ta sai dai fuskarsa sam ba walwala ,da alama dai irin mutanen  nan ne marasa yawan fara’a .

Fattu kuwa da sauri ta juya baya tana mai dafe ƙirji ,dan hango zanin da baffanta ya lulluɓawa mutumin a ƙasa,kuma da alama bai ma san zanin ya daɗi ƙasanba.

Da sauri shima ya ankare cewar ba zanin fa ajikinsa ,wato yana tsaye tsirara ne.cikin azama ya durƙusa ya ɗauki zanin yana cukuikuyewa ajikinsa, idonsa akan fattu yana fatan Allah dai yasa wannan yarinyar bata ganshi haka ba,dan ma dakin ba wani haske sosai.dan tocilolin sun kalli wani direction  ɗin ne da ban.

Zama yayi cike da jin haushin yadda zanin jikin nashi ya daɗi kasa,wai ma to ina kayansa ne?me yasa y ganshi haka ba kaya ne?

Daga kanshi yayi yana kallon baffa daya miƙa masa kwaryar da fattu ta miƙa dan abashi magani.

Karɓa yayi shikam nadan yasan menene aciki ba , kallo yabo kwaryar dashi,yana jin wani irin tashin zuciya ,dan kwaryar ta tsufa sosai ,tayi baƙi saboda ruwam rubutun da ake zubawa a cikinta.

“Maza ka shanye bawan Allah zakaji sauƙin ciwon kan”baffa ya faɗa yana nuna masa alamun ya sha da hannunsa ,dan gani yake kamar bayajin me suke faɗi.

Kafa kansa yayi yana shan maganin ,bayan ya runtse idanunsa.saida ya ɗansha da yawa kafin ya miƙawa baffa kwaryar.

Saidai ko minti ɗaya baiyi da sha ba ,ya kama yunƙirin amai.aikuwa tasss ya mayar da maganin nan,sannu kawai baffa ke masa.

Juyowa fattu tayi lokacin daya fara aman, dan tunda ta juya musu baya bata ƙara juyowa ba,saida taji yana aman.

Ahankali ta buɗe bakinta tace “sannu hamma”ta faɗa ahankali.

Kallonta yayi ,tare da kawar da kansa can gefe yana jingina da jikin katangar karan,ba tare da yayi magana ba .itama bata damu da sai yayi maganar ba,dan su tunaninsu bayajin me suke faɗi.

Cikin nutsuwa fattu ta gyara gurin da yayi aman,kanta aduke ,har zuwa lokacin gabanta yaɗuwa yake .shi kuwa bawan Allahn nan yana daga jikin bango Ya lumshe idanunsa ,kamar mai barci.saidai duk abinda fattu keyi idonsa na kanta,mamaki yake da irin kyan da yarinyar ke dashi,gata da nutsuwa komai nata gwanin burgewa.tana da hankali bata da rawar kai duk da ƙaranci irin na shekarunta.dan ya san wannan bata wuce 14/15ba amma Masha Allah,tana kyan diri irin na cikakkun mata ,kalli hips ɗinta kamar wanda aka ɗora mata shi Dass abinta. Jikin fattu ne kawai ya bata cewar kallo ta mutumin nan keyi,dan haka ahankali ta ɗago kanta ,shikuwa daidai lokacin ya ɗan ƙara buɗe idanunsa yana kallon ɗan ma dai-dai cin lips ɗin ta, masu  taushi , sai sheƙi suke.aikuwa carab ta kama shi yana  mata kallon ƙurillah.

Ɗan hararar ta yayi tare da kawar da kansa ,aransa yace “wannan ta cika kallon mutane “

Kuji fa masu karatu ?ko tsakanin shi da fattun wake kallon wani?

Da sauri fattu ma ta kawar da kanta,azuciyarta tana mai cewa “kuji min mutum shi yana kallon mutane amma kuma baya son akalleshi”

“Abba waye yakawoni nan?kuma me nakeyi anan?sannan kuma ina kayan?

Baffa da fattu suka ci

tsinkayi murya mai shegen daɗi da amon sauti cikin nutsuwa.da mamaki gaba ɗaya suka bishi da kallon ,ba wanda yayi magana dan sai sukaga kamar bashi yayi maganar ba ,dan yana yadda yake bai ko buɗe idonsa ba lokacin da yayi maganar.

Jin sunyi shuri ba wanda yayi magana ne ,yasa bawan Allah buɗe idanunsa da suka ɗan yi ja kaɗan yana kallon baffa,sannan ya ƙara maimaita tambayarsa cikin Hausarsa da bata fita sosai.

“Ashsha -ashsha ikon Allah yaro ashe kana jin Yaren Hausa ?Alhmdllh.sannu kaji bari na baka kaya saika saka,inyaso zuwa wayewar gari nayi magana kaji”baffa ya faɗa yana mai buɗe wata tsohuwar bakonsa ,kaya ya daukowa bawan Allah nan ,waɗanda dasu yake zuwa sallar juma ‘a .wani yaɗi ne yollow share dashi ,anyi masa ɗinkin riga da wando dogaye .miƙa masa baffa yayi yace “kasa Waɗan nan tukunna yanzu kaji”

Karɓar kayan yayi yana mai ƙare musu kallo,to ina nashi kayan da za’a bashi Waɗan nan kayan wani iri dasu haka?ɗari kansa yayi ya kalli baffa yana son yayi magana ,amma sam ya kasa,dan ba ɗabi’arsa bace yawan magana ,yana matuƙar jin wahalar yin magana ,shiyasama tun farko yaƙiyi musu magana .

Kallon fattu yayi wacce ke zaune can nesa dasu kanta aduƙe,tana wasa da yatsun hannunta ,sannan ya kalli baffa ,ya kalli kayan hannunsa kuma .

Fahimta baffa yayi cewar ,yana son saka kayan ne ,kuma yana buƙatar fattu ta bar gurin,dan haka baffa yace “fattu muɗan bashi guri ya kimtsa ko”baffa ya faɗa yana mai kama hannun fattun sukayi wajen ɗakin.

Bayan fitarsu daga ɗakin,shikuwa  kallon yabo kayan dashi yana juyasu ahannunsa, kusan minti uku kafin ya saka rigar ,dube dube yake ko zaiga boxern sa ,saidai ba alamun boxer aɗakin nan,dan haka ya saka wando yana mai turo baki da ɗan yamutse fuska.sauƙinsa ma ɗaya kayan wanke suke tas ɗasu,sai ƙamshin kilin suke.lol.

Koda ya saka kayan zamansa yayi a inda ya tashi tare da lumshe idanunsa ya faɗa duniyar tunani ,shikam a iya tunaninsa baisan meye dangantakar da da Waɗan nan mutanen ba,abinda zuciyarsa tafi yarda dashi shine,wata ƙila yayi hadarine suka ganshi suka taimakeshi.

Baffa ne yaji shiru baice musu ya kammala saka kayan ba,kuma ga fattu sai rawar ɗari take, dan zuwa wannan lokacin an jima da ɗauke ruwan saman da ake tsugawa,dare ya raba sosai.

Dan haka saiya ɗan leƙa cikin ɗakin.aikuwa azaune ya hangoshi ya jingina kansa da jikin katanga ,sannan idanunsa alumshe .

“Ayya ashe ma ya ida shiryawa fattu, shigo daga ciki kar mura ta mamaki naga kinata rawar sanyi,bana so kije ɗakinki ki kwanta saboda hansai idan ta ganki zata je ta sanar da lamiɗo kina nan”baffa ya faɗa yana mai tura ƙofar dakin nashi ya rufeta.

“Sannu bawan Allah”baffa ya faɗa cike da tausaya wa.

Jinjina kai kawai bawan Allah yayi ,ba tare da ya buɗe idonsa ba.

Zama baffa ya gyara ya ƙara cewa”ko zaka iya tuna wani abu daya danganci rayuwarka”?ya faɗa cike da fatan cewar bawan Allah nan bai manta komai na rayuwarsa ba.

“Ikon Allah ,saikace wanda yayi lossing memery zan manta da rayuwata “bawan Allahn ya faɗa cikin ransa,amma a zahiri ,ɗan buɗe idonsa yayi ya kalli baffa,sannan ya maida idonsa kan fuskar fattu wacce itama shi take kallon kamar ta sami talabijin.

“Kai wannan yarinyar ta cika kallo wllhda wani idanunta masu kama da ruwan Gwale”ya faɗa cikin zuciyarsa yana mai hararar fattun ,kafin ya ɗauke idanunsa daga kanta ya maida kan baffa .

Saida ya kai kusan minti biyu kafin ya buɗe baki ahankali kamar baya so yace “my name is  ADEEB 

MUHAMMAD ASHRAF “ya faɗa yana jinjina kansa tare da kallon baffa.gani yayi baffa yana kallonsa alamun kamar bai fahimceshiba.

Lumshe idonsa yayi cike da gajiya ,sannan yace “sunana ADEEB MUHAMMAD ASHRAF”yana faɗin haka ya mayar da kansa ya jingina tare da lumshe idanunsa.

“To- to masha Allah  malam Adeeb ina ne garinku ? Baffa ya faɗa cikin gamsuwa da jin cewar shiɗin musulmine. Dan da yana ta kokwanto shin  musulmi ne shi ko arne? Amma zuwa yanzu ya sami nutsuwar jin cewa shiɗin musulmine.

Shiru yayi kamar bazai yi magana ba, kafin ya buɗe baki  yacewa baffa”nidan MISRA ne” ya faɗa yana kallon yadda baffa yayi zugum cike da tunanin ina yakejin Misra?

“Ikon Allah malam adeeb duk da dai Ni ba  sanin Misra a ina take nayi ba,amma nasan garine mai matuƙar nisa ,to zahiri gaskiya nan kana Nigeria ne ,cikin ƙauyen ƴar ruga dake jahar Gombe”baffa ya faɗa yana kallon Adeeb wanda mamaki ya mamaye ilahirin fuskarsa , Nigeria kuma ?yaushe yazo Nigeria?bayan rabo da da Nigeria tun last year?

“Who brought me hare”?ya faɗa cikin mamaki da sanyin murya.sai kuma ya ɗan rufe idonsa tare da dage kansa kafin yace “waye ya kawoni nan?

Shiru baffa yayi ba tare da yace komai ba,na tsawon lokaci ,kafin ahankali ya nuna masa fattu yana mai cewa”haƙika wannan yarinyar itace solar haɗuwar mu dakai ,kuma anan garin ta ganka —–nan dai baffa ya bashi labarin abinda ya sani ,da kuma abinda ya faru yanzu harya koma asalin halittar da.

Tunda baffa ke magana Adeeb ya saki baki yana kallo da sauraron baffa,mamaki yake wai shine ya zama maciji?as how ? Me ya faru dashi ?waye ya maida shi hakan?ya Allah who’s known how long yake cikin garin nan,ko yaya ƴan gidansu? Ko wane hali suke ciki yanzu?yasan yanzu haka hankalin amminsa yayi matuƙar tashi fiye dana kowa ,lallai dole ya bar garin nan ko ta halin ƙaƙa.

“Na gode sosai da taimakon rayuwata da kuka ,amma bani da wani masaniya  akan  abinda ya sameni, ina don barin garin nan gobe-dan akwai gagarumin abinda ke gabansa,saidai i promise you I will get you back,zan dawo gareku”ya faɗa cikin wani irin yanayi na ban tausayi,dan gaba ɗaya jikinsa asanyaye yake ,sannan damuwa ta cika fuskarsa taf! Da gani maganar ta shiga jikinsa sosai .

Cikin murmushi baffa yace ba komai malam Adeeb Allah yayi mana jagora ,saidai ina neman alfarma agareka”baffa ya faɗa cikin damuwa.

“Ba komai Abba ka faɗi duk  abinda kake don faɗi and I promise zanyi maka shi”ya faɗa cikin sanyin murya mai cike da tarin damuwa.

“So nake ka tafi da ƙanwarka can garin naku ,domin ka taimaka mata wajen saduwa da asalin iyayenta baffa ya faɗa cikin tsantsar damuwa yana mai kallon fattu,wacce taji maganar baffa kamar sauƙar aradu …….

Masu karatu mu tara next page 

Taku ce anty mammy Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.

Back to top button