Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 47 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                           FORTY-SEVEN📍

      Saida gaban khaleel ya fadi a lokacin da suka hada ido da deen amma ganinsa rungume da wifey dinsa sai yaji ransa ya baci duk wani fargaba da yaji da ganin deen ya kau sai ma wani abu dayaji ya tokare masa wuya na ganinsu a haka amma sai ya kasa motsawa daga inda yake saboda abinda yaji daga shigowarsa, ashe dan uwanta ne, dan uwan ma cousin shi ko ina zesa ranshi da jin wannan abu…….

   Sun tafi ba dadewa khaleel ya farka ya ganshi a gadon asibiti, mamaki ne ya kamasa ya shiga tambayar kansa ya akayi yazo asibiti, a hankali kuma sai ya shiga tariyo duka abinda ya faru a ranar, wifey ce ta fado masa arai ya mike ba shiri, saidai yana tashi yaji wani jiri na dibansa ga tsami da jikinsa yayi na dukan daya sha, daurewa yayi ya fara takawa zuwa kofa, taku biyu yayi yaji duniyar na juya masa gabadaya, sai farkawa yayi ya gansa a wani daki daban ba wanchan daya gansa da farko ba, yunkurin tashi ya sakeyi cikin ikon Allah yaji ciwon ya ragu, a daddafe ya samu ya karasa bakin kofa, daidai nan doctor ya shigo, babu yanda Doctor beyi dashi ba akan ya bari ya samu sauki sai a sallamesa amma kememe yaki saboda babu abinda yake muradin gani sama da fatima zainab, babban tashin hankalinsa kuma yasan dole tana tare da deen, Abby da yake only hope dinsa shima be gansa ba kuma baya tinanin yana asibitin, dole ba yanda Doctor ya iya yayi discharging dinsa, fita harabar asibitin yayi batareda yasan inda ya nufa ba, luckily for him yana fitowa wani yazo ya sameshi ashe wanda Abby ya bari ya zauna a asibitin kafin ya dawo ne, bayanin waye shi yayi ma khaleel sannan yace masa Abby yana zuwa ze dawo, ce masa yayi kawai ya kaisa inda abby yake baze iya jira sai yazo ba, babu musu ya kaishi gidan, a daddafe yake tafiya dan har lokacin jikinsa na masa mugun ciwo dan ba karamin duka yasha a gurin deen ba, amma ya dake ya karasa ciki kamar yanda akayi directing dinsa, su kansu securities din gidan sun gane gidan ba lafiya yake ba shiyasa duk wanda yazo basa hanashi shiga kamar an sasu, yana shiga ko idanuwansa suka masa mummunan gani…….

     Ganin irin kallon da khaleel yake musu yasa deen harararsa zeyi magana kenan yaji baby tee ta saki wani irin ihu sai kuma jikinta ya fara rawa, kankameta ya sakeyi  sannan yayi bismillah ya fara mata karatu a cikin kunnenta  amma inaa jikinta sai rawa yake ga wani fiffizgewa da take, cikin tashin hankali mami tayi gurin da suke, alamu deen ya mata da karta karaso ganin yanda take fizgewa, Abby da dad da suka yo kansu suma ce alamu Deen ya musu da su koma, rasa abunyi mami tayi ta dauki wayarta ta shiga kiran mallaman da suka zo wanchan lokacin har sukace zasu dawo, a ranar ne kuma tabi khaleel suka gudu, sun dawo din kuma sai mami tace musu suje kawai zata nemesu yanzu yarinyar batanan…… 

Ajye wayar tayi bayan sun ce mata gasu nan zuwa ta kalli umm dake duke har lokacin bata dago ba, hannunta ta ruko da niyar dagota ta lallasheta dan tasan umm is such an emotional person, sai dai me? kawai taga hannun ya biyota, a rude tashiga girgizata sai a lokacin ta gane bata numfashi, salati kawai mami takeyi cikin rashin sanin abun yi, saiga mami tana hawaye batasani ba…..

 Daga sama kawai sukaji salatin mami, ba shiri Abby yayi kanta yana fadin;

     “boddina ki tashi ga baby tee dinki, dan Allah ki tashi”…. 

Haka itama mami taketa sumbatu an kuma ransa wanda zeyi tinani dauko ruwa a zuba mata, shi deen be masan abinda suke ciki ba saboda bige bigen da fatima zainab keyi yasan yayi kuskuren sakinta saita hargitsa parlourn gabadaya…. 

Khaleel ne ya dauko ruwa ya mikawa Abby, sai a lokacin suka dinga mamakin yanda suka manta basu zuba mata ruwa ba, diba Abby yayi ya shafa mata a fuska, sai da ya shafa mata sau uku sannan ta fara tari alamun ta farfado, chan kuma saita bude ido cikin sabon kukan daya taso mata tace;

     “Allah ya isa! Allah ya isa bazan taba yafewa ba! Huraira kin cuceni! Yanzu dama baby tee dina ce fatima zainab? Abby I can’t forgive you too! Kun cuceni!”…..

Sai kuma numfashinta ya sake daukewa, kuka sosai mami ta fashe dashi sai maimaita innalillahi take, ruwa aka sake shafa mata ta kuma farfadowa kamar dazu, saidai wannan karan mami hanata magana tayi, hadata da Allah da annabi tayi kartace komai she should just relax dan batasan yanda take passing out haka…. 

Sallamar mallaman ne ya sata yin shirun dole, direct inda deen da baby tee ke zaune suka nufa lokacin ta dena rawar jikin da take saboda karatun da yake mata a kunne sai wani kuka da takeyi kasa kasa da deen yake jin shi har ransa……

   Wani ruwa mallamin ya fito dashi yayi bismillah ya fara watsa mata, ruwan zam zam ne da ganyen magarya da akayi karatun karya sihiri masu zafi a ciki kamar haka; 

       Fatiha x 1, Ayatul kursiy 1, A’araf verses 106-122, Yunus verses 79-82, Kaafiroon ×3, Falaq ×3, Naas ×3…….

      Allahummma rabban nas azhibul baas washfi antash shaafee laa sheefa’a illa shifa’uka shifa’an laa yughadiru saqaman- ×3…..

       Bismillahi arqika wallahu yashfeeka min kulli shai’een yu’uzika wa min sharri kulli natsin, Allahu yashfeeka bismillahi arqika ×3…

 PS; (wannan sahihin maganin karya sihiri ne, you can give it a try Insha Allah, Allah yasa mu dace)…..

   Kukanta ne ya tsawaita yayinda suke zuba mata ruwan, wani irin rawa jikinta ya farayi kamar tarwatsa gashi baa so ta zame, ba karamin namijin kokari Deen yayi ba gurin riketa, dagabaya kuma sai ta hau yin ihu tana wani irin kuka me ban tausayi, dakatar da zuba mata ruwan sukayi aka mikawa deen robar akace ya bata sauran a baki, karba yayi ya matseta ya samu ya bude bakin da kyar sannan ya ruba mata ruwan, hancinta ya toshe har saida ta shanye sannan ya zare hannunsa, yana sakinta wani bacci me nauyi ya kwasheta a jikinsa……

Sakin baki duka yan gurin sukayi suna kallonta banda deen da baya ganin fuskarta, mami ce data kasa shiru tace;

     “Allah me iko! Kai wannan duniya ina zata damu! Umm dago ki gani wallahi baby tee dinki ce”…….

Dagowa Umm da har lokacin take jinta kamar ba daidai ba tayi tana kallon baby tee, abun aljabi sai gashi yarinya ta juye kamanninta sak na Umm  kamar an tsaga kara an karya yanda ko makawo ne ya shafa yaji yasan yarta ce, ashe dama haka sihiri yake tasiri?Har asa kana ganin mutum amma ka kasa tantance kamanninsa? Subhanallah!…… 

Tashi Umm tayi ta karasa inda suke, Deen yana rike da ita kamar yan jaririya  sabon jego, yasan tayi bacci amma haka kawai yaji bayasan kwantar da ita gashi kuma ba kallonta yake ba, tausayinta yakeji sosai kamar ya mata kuka, babu abinda ya tsaya masa arai irin abinda makirar matarnan ta fada wai tayi degree a karuwanci, tsoronsa daya kar Allah yasa hakan ya faru dan a hotel ya fara ganinta anan kuma yake yawan ganinta so what does that mean?…

Yana cikin wannan tinani yaji Umm ta hadasu duka ta rungume, kiss din farin ciki ta fara manna musu ta ko ina a fuskarsu shida baby tee kamar yanda takeyi yanzu saboda zaman UK daya dan chanja mata abubuwanta, kai tsaye take nuna affection dinta, kau da fuskarsa deen yayi yana turo baki yace;

     “Umm sai ki dinga yiwa mutane abu kamar wasu babies”….

Pecking kumatunsa tayi tace;

     “You are my babies ai”…..

    “Sai dai baby tee banda ni gsky”…..

   “Harda kai yaro, har yanzu kallon that little boy da yake bina ko ina a UK nake maka”…..

Murmushi kawai yayi ya kalli baby tee dake baccinta peacefully ya dawo da kallonsa kan Umm yace;

     “She looks so much like you Umm! Ina mamakin yanda muka kasa gane hakan”…..

Girgiza kai Umm tayi cikin wani irin abu da taji yana taso mata tace;

      “I’m still surprised too saif”…..

Daya daga cikin mallamin ne yace;

     “Aikin sihiri ne amma ko wanchan zuwan da mukayi kamanninku daya nagani shiyasa na tambayeki ko kece mahaifiyarta, Insha Allah tana farkawa zata dawo daidai sai dan abinda baa rasa ba”……

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

 Mami ce ta karba da fadin;

      “Nima ranar dana kira ki sanda sukayi accident ita da saif wallahi sak ke nagani, kamar wacce aka rikewa baki na kasa fadamiki ranar, koda kikazo kuma sai na kasa tina komai kawai nace miki na manta”……

      “Ikon Allah, ni dai bazan taba yafewa ba wallahi! Kuma duk sujjadata sai na isarwa Allah!”…..

Umm ta fada tana laluben inda ammy take a parlourn, su gabadaya ma sun manta da ita saboda matsattsalun da keta tasowa daga wannan sai wanchan….. 

Hangota tayi a chan gefe ashe ta sume tintini ba wanda ya lura, zata mike kenan deen ya ruko hannunta, girgiza mata kai yayi alamar kar taje sannan yace;

       “Ai abu be kare ba, ki bar komai a hannuna kawai umm!”……

    Sannan ya kwantar da baby tee akan kujera ya dora kanta akan cinyar Umm, flash ya zaro daga cikin aljihunsa ya karasa gaban tv yayi connecting, tsuru mutanen dake parlourn suka masa suna tinanin me zeyi…….

   Saida ya hada komai sannan yayi playing voice din da yake da tabbacin muryar alhaji habibu ne a flash din daya tsinta….

 Tsit parlourn yayi idon kowa akan tv…….

     “Wai me kake jirane ka kasa aiwatar da abinda ya kamata? Abinda a lokaci daya zaka iya yi a wuce gurin?”….

   “Minti nawane kayi ka gama? Raping dinta ne bazaka iya ba sai da magani?”….

      “Budurcinta kawai muke bukata and we’re the richest in the world, kujerar gwamna is assured for you kai kuma!”…..

    “Eh duk yanda zakayi kayi, yarinya na gidanka amma ka rasa yanda zaka mata fyade? Gaskiya ka bani kunya”…,..

     “Ka tabbatar komai ya kammala a darennan, kasan boss ya gaji da baka chances!”……

Wayen’nan sune maganganun dake cikin flash din wanda ke dauke da muryar alhaji habibu….

Salati da sallalami ne kawai ke tashi a parlourn banda daddy da alhaji habibu da sukayi tsuru tsuru da ido……

Katsesu khaleel yayi da mikawa deen flash din dake hannunsa yace;

    “Yi playing wannan shima!”…..

Tin a lokacin daya fara zargin daddy ya fara bincike akansa, har Allah yasa ya samoshi saidai be nitsu ya duba abunda yake ciki ba amma yana da tabbacin sirrinsu daddy ne and he doesn’t mind tona musu asiri indai wifey dinsa zatayi rayuwa kamar kowa, kuma duk inda zeje yana tafe dashi gudun kar ya ajye ya nemeshi ya rasa….

 A yamutse Deen ya karba kamar wanda aka bawa kashi, inserting dinshi yayi sannan yayi connecting kamar wanchan, yana dubawa yaga ashe video nema wannan ba voice ba…..

Kunna videon yayi saiga mutane biyar sunyi appearing a parlourn daddy, iya alhaji habibu da daddy kawai suka gane sauran basu shedasu ba……

     Daddy ne ya mike tsaye yace;

     “Ni haka kawai nake jin gwara in aureta tinda ga dama ta samu, kar kuce tausayinta nake amma bansan karban budurcinta ta hanyar fyade”…..

Dariya wani daga cikinsu yayi yace;

     “Ashe ka shirya mutuwa kenan, in ma saboda danka kake wannan abun gwara ka dena dan wallahi saikayi”…..

Alhaji habibu ne ya karba da fadin:

     “Kyale shi ni banga abun aure bama, kawai kayi drugging dinta ayi abinda zaayi a wuce gurin, ba shikenan ba”….

Cikin damuwa daddy ya sake fadin;

     “Ba zobe mukasa akayi na bata ba da niyar dauke hankalinta amma dubi koda tazo yau ba zoben! Ga shegen dan iskan chan daya gudu da ita, na dauka kasa an kona prison din da aka sashi sanda muka masa sharrin kisa?”…….

Tsaki alhaji habibu yaja yace;

      “Hmmm ai wannan yaro dole ya bakunci lahira anan kusa dan zamansa a duniya barazana ne ga rayuwarmu, ni bansan ya akayi ya gudu be kone ba, ga ubansa alhaji abubakar na neman takarar gwamna shima, idan bamu dakatar dashi ba kasan bayanda zaayi kaci, amma garin yayi ya gane kudirinka har ya dawo ya dauke fatima zainab ko ya sake gano wani shirinmu ne?, na fara tsorata da lamarin yaronnan gaskiya”…..

     “Nima haka wallahi komai ya dagule min na rasa yanda akayi ya dawo, ga khaleel son yarinyar nan ya rufe masa ido, idan ban yiwa tufkar hanci ba komai ze iya faruwa, kana ga shi yaje ya cecesu bayan nasa akashe yaron chan a kawomin ita”….

     “Karka damu kanka akan khaleel, kidnapping dinshi kawai zamuyi mu boye sai komai ya lafa sannan, yaron nan Saifuddeen shine damuwarmu yanzu!”…….

A nan videon ya tsaya sai kuma maganganu kasa kasa da basajin abinda ake cewa……..

A fusace Deen yayi kan su daddy, hannun hagunsa yasa ya shako wuyan daddy, dayan kuma ya shako alhaji habibu dashi, cikin huci yace;

      “Wasu kalan marasa imani ne ku? Yanzu kun samu abinda kukeso? Nace kun samu?”…..

Kakarin amai daddy ya farayi cikin i’ina yace;

     “Bbbb…amu sa…mu ba, ne…mmansu mu….ka…yi mu..ka..ra…sa”……

Gwara kansu yayi saida goshinsu ya fashe yace;

      “Kafin ku kasheni, ni zan kasheku yanzu”….

Nan ya shiga jibgarsu kamar ba gobe, dauke kai khaleel yayi cuz he knows they deserve it saima maida idonsa da yayi akan baby tee yana kallonta with so much adoration, shi fa dagaske yake ko ze rasa kowa a duniya indai ze sameta to zeyi farin ciki…..

Mami ce ta kira wani cousin dinsu da yake major na sojoji tace ya turo musu sojoji azo a kwashesu duka kafin su nitsu susan abunyi…..

Ko minti biyar baayi ba horn din motar sojoji ya fara tashi a kofar gidan, shigowa sukayi har parlourn mami ta nuna musu wa’yenda zaa kwashe saidai kememe Deen yace besan zancen ba, shi abarsa ya hukuntasu da kansa, hakuri akaita  bashi akan zasu ajyesu ne kawai a gurinsu in yaso sai yazo ya hukuntasu achan, hakan ne ya sasa yin ball dasu sannan ya koma kan ammy dake sume su sunma manta da ita ma, zaro wayar stabilizer yayi ya zuga mata guda daya lafiyayye, ba shiri ta farka daga suman karyen datayi, mikewa tayi ta fita Deen ya bita yana zuga mata wayar har suka karasa bakin get, ko kafin su karasa bakin get jikinta duk ya fashe bakinta sai zubar da jina yake, Rokonsu daddy ya farayi a wahale akan dan Allah badan halinshi ba su taimaka subawa khaleel aurenta saboda son da yake mata tsakani da Allah, babu wanda yace ko uffan dama Deen beji ba aka tattara su daddy aka sasu a mota aka hada da ammy da deen ya rako da duka, zasu ja motar su tafi kenan saiga mom ta dawo tsirara kamar yanda ta fita dazun sai sambatu yake har lokacin, dauke kai Deen yayi yace su hada da ita…….

   Dawowa ciki Deen yayi yana wani wura hanci irin an katse mishi jindadin nan…..

Gaban Abby khaleel yaje ya duka ya dafa kafafuwansa yace;

     “Dan Allah Abby ka cikamin alkawarin dakamin, ka aura min fatima dan Allah, wallahi ina sonta tsakani da Allah”….

Dafa kansa Abby yayi cikin tausayinsa da yaji ya karu aransa ganin yanda Deen yayiwa mahaifinsa dukan rashin mutunci a gabansa yace;

      “Fatima bata da wani miji sai kai khaleel!”…..

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button