Hausa novels

Ruwan Zuma Page 13 Hausa Novel

(13) Bayan tafiyar Laila, Alhaji Abdul ya kira Jennifer ya had’ata da Haydar suka fita tare. Haydar bai bar ma’aikatar ba sai bayan azahar. A gajiye ya koma gida ya zauna a rumfarsu Ammi ta kawo masa ruwa. “Ali yaya dai?�? Tace dashi ganin yanda ya shigo a jikkace kamar wanda ya wuni yana aiki. “Wallahi Ammi na gaji ne, tunda naje ban zauna na huta na minti biyar ba.�? Ya bata amsa yana cire rigarsa ya ajiyeta a gefensa. “A hankali zaka saba, bari na kawo maka abinci kaci sai ka kwanta ko zuwa la’asar ne.�? Bayan yaci abinci ya dawo cikin hankalinshi ya fara bawa Ammi labarin yanayin aikinsa da kuma albashinsa. “Zasu dinga bani dubu talatin da biyar duk wata, Idan kuma na kai wasu watanni biyar ko shida suka ga na iya aiki zasu k’ara mini matsayi da kuma albashi. Ammi kici gaba da mini addu’a domin inaga wannan aiki dana samu shine cikar burinki wanda kika tsaya kai da fata akai sai nayi karatu.�? “In Allah ya yarda Haydar. Kai dai ka rik’e gaskiya da amana a duk inda ka tsinci kanka, hakan shi zaisa ka samu nasara akan abunda kasa a gaba.�? Ammi ta shafa kanshi tamkar k’aramin yaro tana kallonshi cike da so da k’auna. “Ammi ki shirya gobe zamu je gidan Hajiya Laila ki mata godiya domin hakan ya faru ne duk ta sanadinta.�? Washegari kamar suka dira a gidan Laila. Ammi dai tunda suka shiga take kalle-kalle tana yiwa Aliyu magana kan gidan. Suna shiga falon Laila Ammi ta shak’i k’amshin turaren wutan dake ciki tace, “Amma uward’akin naka Shuwa ce ko?�? “Ammi don Allah kiyi shiru.�? Shine abunda ya fad’a yana mai zama a k’asa, shiru Ammi tayi amma sai da ta harareshi tukun. Itama a k’asan ta zauna tana shafa lallausar carpet d’in dake malale a falon. Suna zama Laila ta fito daga kitchen hannunta d’auke da tray mai d’auke da ruwa, juice da kuma glass cup biyu. “Sannunku da zuwa. Sannunku.�? Shine abunda take fad’a tana ajiye tray d’in a k’asa. “Maman Haydar don Allah ki tashi ki zauna a kujera.�? Ta fad’a tana zama a kujera fuskarta d’auke da fara’a. “Karki damu Hajiya, k’asan ma yayi.�? “Maman Haydar baza ayi haka ba, ai bazan ji dad’in zama a sama ke kuma kina k’asa ba.�? Da haka Laila ta zamo daga kan kujeranta ta zauna a k’asa wanda hakan ba k’aramin mamaki ya bawa Haydar da Amminsa ba. “Ina wuni?�? Laila ta gaisheta tun kafin su bud’i baki su fad’i wani abu. “To Hajiya za’ayi haka? Keda gidanki zaki zauna a k’asa?�? “Babu komai Ammi, haka kake kiranta ko Haydar?�? Haydar da har lokacin yana cikin mamaki ya d’aga kai alamar ‘eh�? kana ya gaisheta. “Ina wuni Hajiya, mun sameku lafiya?�? Ammi ma ta gaisheta tana mai d’an sunkuyawa kad’an. “Lafiya kalau Hamdallah, kun zo lafiya? Ya hidima?�? “Lafiya Hajiya, ya kuma d’awainiya da Ali? Da fatan baya miki rashin hankali?�? “Ammi!�? Haydar ya kwa6i mamarsa yana mata ido. “K’arya nayi? Kana da hankalin ne?�? Ammi ta danna masa harara kana ta maida dubanta ga Laila wacce ke dariya sosai. Hakan ba k’aramin burgeta yayi ba, wai uwa da d’anta ne haka? Inama itama zata yi haka da Ummii! Ai da tafi kowa jindad’i a duk duniyar nan. “Ke Shuwa ce ko?�? Ammi ta sake yin tambayarta ta d’azu wacce Haydar yak’i amsa mata. “Ammi!�? Haydar ya sake kwa6arta yana ta6a k’afarta. Buge hannunsa Ammi tayi kana ta juya gurin Laila tana murmushi. “Ni Shuwa ce kuma Kanuri.�? Ta amsa mata tambayarta, a ranta kuma tana jin Ammin ta burgeta. “Ai ina shigowa gidan naji k’amshin turarenmu, dana ganki kuma sai na tabbatar da hakan. Gade tahaawili bilhen fok waladi, inti kula Allah ikaffi leki hawa’ijki hinel-khair. Shukran.�? “Ohh, kema Shuwa ce?�? Laila ta zaro ido tana k’are mata kallo. Shigar hausawa Ammi tayi ta atamfa riga da zani da kuma hijabi wanda wannan ba shigarsu bace ta Shuwa. Sai a lokacin Laila taga d’an kamanninsu a fuskar Ammi wanda dashi suke gane junansu a cikin mutane dubbanni. Ammi bata amsa maganar kai tsaye ba illa kad’a kai da tayi amma kuma murmushi dake fuskarta ya d’auke d’iff na wasu sakanni lokaci d’aya kuma ta dawo da fara’arta tamkar ba ita ba. Haydar dake gefe ya kafe idanunsa a kan Ammi zuciyarsa na tafarfasa tamkar zata faso k’irjinsa. Lokaci d’aya yaga Ammi da Laila sun 6arke da hira ta harshen Shuwa, yanda suke karya harshe cikin kwarewa zai baka sha’awa amma banda Haydar wanda yake jin kanshi ya fara ciwo nan take. Ganin duk hankalinsu baya kanshi yasa ya tashi ya fita daga falon yana jin duniyar na juyawa kamar zai fad’i a k’asa. Kujerar roba ya samu ya zauna a kai kana ya dafe kanshi da hannayensa biyu, yayinda tambayoyi bila-adadin suka fara zarya a kwakwalwarsa. Bai san lokacin daya d’auka zaune a gurin ba sai gani yayi Laila da Ammi sun fito suna dariya tamkar wad’anda suka jima da sanin juna. Mik’ewa yayi tsaye yana k’ak’alo murmushi wacce iyakarta fatar baki ya dubi Laila yace, “Hajiya muna k’ara godiya, Allah ya saka.�? “Gaskiya sai dai Allah ya biyaki, nima gashi daga zuwana ta bani turaren wuta da kuma laffaya guda biyu da turmin zani biyu. Ka tayani godiya Haydar.�? Kafin ya bud’i baki yayi magana Laila ta rigashi tana cewa, “Ma fe mushkila Ammi. Nice da godiya domin naji dad’in zuwanki.�? Sai da suka k’ara tsayuwa na minti goma suna yare sannan suka mata sallama suka tafi. Haydar yak’e kawai yake yi a gaban Laila gudun kar ta gane halin da yake ciki, amma suna fita fuskarsa tayi daidai da yanayin da zuciyarsa take ciki. Sai daya tabbatar sunyi nisa da gidan sannan ya dakata daga tafiya ya tsaya. Ammi da take bin bayanshi tazo ta wucesa tamkar bata ganshi ba, sai dai bata yi taku uku ba taji muryar Haydar a dodon kunnenta cikin murya mai d’auke da bak’in ciki, takaici, da kuma wani abu da za’a iya kira ‘hope�? a muryarsa yana cewa, “Ammi mu Shuwa ne?�?Tsayawa tayi na sakanni goma zuciyarta na bugawa sannan tace, “Mun gama wannan maganar Haydar. Kazo mu tafi gida.�? Taci gaba da tafiya ta barshi a gurin har ta 6ace masa daga gani. Hawaye ne masu zafi suka sauk’a akan kumatunsa kana wasu suka cigaba da biyosu babu k’ak’k’autawa. “Abun mamaki ashe Mamarsa shuwa ce! Kar kaga yanda muka yi hira, wallah abun burgewa.�? Mas’ud yayi kasak’e yana kallon Laila tana bashi labarin Haydar da Amminshi wanda suka ziyarceta d’azu da rana. “Baka ce komai ba tun d’azu ina ta magana. Ko dai ka gaji ne?�? Girgiza kai yayi kana ya gyara zamanshi ya dubeta tsaf da dukkan hankalinsa yace, “Why do you like the boy?�? A take fara’ar fuskarta ya d’auke ta tamke fuska kamar ba ita ke dariya d’azu ba tace, “Mas’ud na fad’a maka babu wata alak’a tsakanina da Haydar sai tausayawa da kuma had’uwar jini, bayan nan babu wani abu na daban. Kuma zan so ka daina zargina akan abunda kasan bazan ta6a aikatawa ba.�? “Wani zargi kenan?�? Ya tambayeta yana nazarinta. “Kana zargin soyayya ce a tsakaninmu mana! Wai me kuka d’aukeni ne kai da Abul? Yarinya k’arama wacce bata san kanta ko kuma abunda ya dace ba? Da banida hankali da tunani zan kai har wannan lokacin ban jawowa kaina zagin duniya ba? Idan a daa banyi ba to ku mini adalcin cewa a yanzu ma bazan yi ba. �? Tayi magana cikin 6acin rai sosai. Daga hannu biyu Mas’ud yayi alamar surrender kana ya koma jikin kujerar ya jinginu ya kalleta a lalace kamar bashi ake yiwa masifa ba. “Tambaya kawai nayi Kalti. Amma zan fad’a miki gaskiya koda hakan zai sa kiyi fushi dani; bana son yaron, kuma ban yarda dashi ba.�? “Ba’a ce dole sai wanda ka yarda dashi zanyi huld’a dashi ba Mas’ud. Kaga mu bar maganan nan kafin raina ya k’ara 6aci.�? Tace dashi tana mai maida hankalinta kan Tv ta fara canja tashoshi. Bai k’ara magana ba ya tashi ya fita daga falon dama nata ya shigo ya koma cikin nashi. Kamar ta bishi amma wata zuciyar ta haneta tana fad’a mata cewa su suke nemanta da fad’a. “Menene illar Haydar da suke ta magana akanshi? Me yayi ko me zai iya yi?.�? Ta yiwa kanta tambayar a bayyane bayan tafiyar Mas’ud d’in. Da daren ranar Laila ce kwance akan gadonta tana daddana wayarta, whatsapp ta shiga tana kallon status d’in mutane wanda bata cika yin hakan ba sai ta rasa abun yi. A hakan ma sai ta canka take yi wanda take tunanin ya saka abun k’aruwa ko makamancinsa. Na Haydar ta shiga taga hotonsa ne akai har guda hud’u wanda yayi a guri da kuma sutura mabanbanta. Duba lokacin da yasa tayi taga ashe tun da safe ya d’aura hotonan. Yanzu da wannan ake tunanin zata yi soyayya? Yaro d’an shekara ashirin da tara wanda ta bashi shekara goma sha d’aya? Ina ma zata fara tunanin soyayya dashi? Me suka d’auketa ne? Bata ce bashi da kyau ba, bata ce bashi da ilimi ba, kuma bata ce bashi da hankali da nitsuwa ba. Amma tazarar shekarun dake tsakaninsu kad’ai ta isa ta hana irin wannan tarayya a tsakaninsu. To wai shin basa ganin jimawan da tayi a zaune babu miji ne? Meyasa suke tunanin zata yi soyayya a yanzu bayan ko a daa da take cikin k’uruciyarta bata yi ba? Dariyar takaici tayi tana kad’a kai, “Kamar sun raina mini hankali ne.�? Shine abunda ta fad’a ta kashe wayarta gaba d’aya ta kwanta bacci. Awa uku da haka ta tashi a firgice dalilin mafarki da tayi, mafarki bana tsoro ko fargaba ba, a’a mafarki tayi tana tarayya da mutum wanda har lokacin fuskarsa na yawo a idanunta. “Ya Allah karka jarrabeni da haka. Allah ka rufa mini asiri ka suturtani. Wannan wani irin k’azamin mafarki ne?�? Ta fad’a tana fashewa da kuka mai sauti. Monday Haydar ya fara zuwa aiki kamar yanda Alhaji Abdul ya fad’a masa. Tuni kuwa ya bar aikinsa na daa ya bar Nasir da sauran abokan aikinsa cikin kewarsa. Sati d’aya da fara zuwanshi ya saba da aikin, k’arfe bakwai da rabi zai sameshi a office babu fashi, daga nan kuma zasu tashi k’arfe biyu na rana ya dawo gida sai kuma wata safiyar. A cikin satin babu abunda ya k’ara had’ashi da Laila na magana balle aika. Haka kawai yaji yana kewarta yana son ganinta domin basu ta6a dad’ewa har haka bai kai mata aika daga shagonsu ba. Ranar jumma’a bayan ya taso daga sallah ya dawo gida ya zauna a rumfarsu yana kallon wayarsa. Hoton Laila d’aya da yake dashi shi yake ta kallo yana tunaninta a ransa. Ammi ce ta fito daga d’akinta itama ta zauna amma babu wanda yayi magana cikinsu. Tun ranar da suka bar gidan Laila har yau magana mai yawa bata k’ara shiga tsakaninsu ba. Sai dai duk safiya Haydar zai gaisheta sannan idan tana buk’atar wani abu zata mishi magana ya kawo mata. Tashi yayi zai shige d’akinsa Ammi ta kira sunansa. “Ali. Kai zaman da muke yi hakan yana maka dad’i?�? Shiru yayi yana kallon k’asa. Ita ta masa laifi amma ita ke dawo da laifin kansa idan ya nuna fushinsa. “Kar dai ka manta duk duniya baka da kowa sai ni.�? “Saboda kin k’i fad’amin sauran mutanen ne Ammi, amma zan jira har lokacin da kika ga ya dace ki sanar dani. Ko a yanzu kin shirya fad’a mini?�? Ya juyo da dubansa gareta hawaye na taruwa a idanunsa. Tashi tayi ranta a 6ace ta shige d’akinta ba tare da tace dashi komai ba. “Guess ba yau ba kenan.�? Ya furta a hankali ya shige nasa d’akin. Hawayen da ya taru a idanunsa ya shanye amma shi kad’ai yasan yanda zuciyarsa take zafi tana azalzalarsa. Ko minti biyu bai yi a ciki ba ya fita daga gidan gaba d’aya. Kai tsaye kantinsu yaje ya samu abokan aikinsa a daa suka gaggaisa cikin raha ana cewa yayi kud’i yana dariya. Lokaci k’ank’ani ya nemi damuwarsa ya rasa dalilin ganinshi da yayi cikin jama’a kamar yanda yake muradi. Bayan kowannensu ya koma bakin aikinsa ya rage daga Haydar sai Nasir a gurin biyan kud’in kaya. “Me yake damunka ne mutumina?�? Nasir ya tambayeshi yana nazarinsa. “Babu komai.�? “Anya kuwa? Kaga yanda ka shigo kuwa fuska a had’e?�? “Dama ya kake so na shigo?�? Haydar ya tambayeshi yana hararansa. Dariya Nasir yayi ya bugi kafad’ar abokin nasa suka cigaba da hiransu kamar yanda suka saba. Nasir da Haydar abokanan juna ne tunda suka had’u a Jami’a aji d’aya, ko da suka gama makaranta sai samun aiki ya musu matuk’ar wahala kasancewarsu ‘yayan talakawa. Suna zaman buga-buga wani makwabcin su Nasir ya bud’e wannan super market d’in ya d’auki Nasir aiki a ciki. Shi kuma ganin har lokacin abokinshi na zaman kashe wando sai ya rok’i Ogan nasu ya bawa Haydar aiki kuma aka ci nasara ya d’aukeshi. “Ina uwar d’akinka ne?�? “Tan nan. Yau kusan kwana goma kenan bamu had’u ba. Kuma abun mamaki bata k’ara kirana ba tun ranar data kaini ma’aikatar.�? “Tunda kaji shiru ai kai zaka je ka gaisheta domin su manyan nan wani lokaci mantawa suke da kashinmu. Kaci gaba da biyayya kawai mutumina ka yagi rabonka.�? Murmushi kawai Haydar yayi yana kallon abokin nashi yana tunani na daban. Da haka aka kira sallah la’asar suka fita zuwa d’an k’aramin masallacin dake had’e da kantin nasu. Suna idar da sallah Haydar ya mik’e tsam ya fita daga masallacin ya tari achaba yana cewa, “Ka kaini Jakara.�? Yana shiga cikin gidan ya hango Abul a tsakar gidan shi da wani mutum babba wanda yake zaton k’anin Laila ne da yake zaune a gidan. A take yaji kamar ya koma amma dai ya isa gurinsu domin bazai tafi ba sai gaisa da Laila kamar yanda yayi niyya tun farko. Ganin mugun kallon da Abul ke aiko masa yasa ya maida hankalinshi kan Mas’ud wanda shi nashi kallon da sassauci. Sallama ya musu Mas’ud ya amsa suka yi musabaha. Ko da ya mik’awa Abul hannu k’in kar6a yayi kamar bai gani ba ranshi a 6ace. Shiru dukansu suka yi babu wanda ya kulashi kuma basu cigaba da tad’insu ba. Haydar yaji kamar ya nitse k’asa ko ma ya 6ace domin a take ya gane mutanen gidan basa buk’atar ganinshi. “Don Allah Hajiya tana ciki ne?�? “Kaji ko Uncle Mas’ud? Uban me yazo yi gurinta? Ka fita mana daga gida tun kafin in maka abunda baka zato.�? “Abul bance kar kayi magana ba?�? Mas’ud ya daka mishi tsawa. Shiru yayi amma bai daina aikawa Haydar mummunan kallo ba. “Baka yi waya da ita bane cewa zaka zo?�? Mas’ud ya tambayeshi ba tare da ya amsa tasa ba. Girgiza kai yayi yace, “A’a kawai nazo gaisheta ne. Tana ciki ne?�? Ya sake tambaya yana gyara tsayuwarsa cikin dakewa. “Haydar.�? Ya jiyo muryar Laila a bakin k’ofar shiga falonta. Saurin d’ago da kai yayi yana kallonta yayinda itama shi take kallo amma fuskarta babu d’igon walwala, sai ya ga kamar ta rame kad’an. “Na’am Hajiya, dama nazo gaisheki ne.�? Ya juya gareta yana murmusawa. “Sai ka gaisheta a nan kayi tafiyarka.�? Fad’in Abul duk da cewa Mas’ud ya kwa6eshi d’azu. “Abul bana son rashin kunya zan 6ata maka rai wallahi. Haydar bismillah ka shigo falo.�? Tace dashi tana matsawa ciki. “Kalti ku gaisa a nan.�? “Baza mu gaisa a nan d’in ba. Haydar ka shigo nace.�? Wannan karon ranta a 6ace tayi maganar tana aika musu harara dukkansu. Haydar daya kasa gane laifin me ya musu sannan meyasa suke mishi haka ya ja tunga ya tsaya yana girgiza mata kai. “Ina wuni.�? Yace da ita yana k’ak’alo murmushi. Jikinta ne yayi sanyi domin tasan ya gane cewa ba’a son ganinsa ne kurum. “Lafiya kalau Haydar. Ya sabon aiki ya Ammi?�? Bayan sun gama gaisuwar ya tsaya kallonta ba tare da ya k’ara cewa komai ba. Wannan karon Laila ce ke sauk’e idanunta k’asa domin Idan ta kalli kwayar idanunsa tana tuno da mafarkin da take yawan yi. Mas’ud shima ya zuba musu ido, Abul kuma dake gefe harara yake aikawa Haydar ta ko’ina kana yace, “Mallam ka tafi tunda kayi abunda kazo yi.�? “Idan kuma nace ban gama abunda ya kawoni ba fa? And….�? Ya tsare Laila da ido wacce har lokacin ta kasa tsayawa ta kalleshi na sakanni biyu kyawawa. “Laila Ina sonki, Ina k’aunarki. Don Allah kar kiga k’ank’antar shekaruna kice zaki gujeni akanshi. Wallahi Laila kullum da tunaninki nake kwanciya kuma dashi nake tashi, ki tausaya mini karki koreni har sai kinji me yake cikin zuciyata tsawon lokacin da muka d’auka tare.

Mum Fateey 👌

Back to top button