Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 13 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

   THIRTEEN📍

   Ganin mama ta suma yasa tayi wani ball da ita,sai ga mama ta tafi wul wul wul sannan ta diro kasa,a take ta farfado daga suman datayi. Birgima mama ta hau yi tana fadin…….

    “Dan Allah dan annabi kiyi hakuri kimin rai karki kasheni”……

 Hade rai fatima zainab tayi ta karaso inda mama take tace

      “Aiko dole ki tafi inda kikaso aikani”……. Fashewa da kuka mama tayi a haukace tace

     “nashiga uku dama baki mutu ba?”…

“Kin dauka zaki iya kasheni ne lokacina beyiba,toh idan naso yanzu yanzu sai na kasheki,kuma na kashe banza wallah”……. 

“Wayyooo Allahna dan Allah kiyi hakuri karki kasheni sharrin shedan ne,wlh na tuba”…… 

Mama ta fada tana jan jiki,tana kallen kallen inda zata iya shigewa ta boye…..

     “Ku mutane dama haka kuke,shedan na zaman shi a gefe sai ku kirashi ku sakashi a lamarinku alhalin ba ruwansa,toh ki bude kunnuwanki da kyau ki saurareni”….. 

Fatima zainab ta fada tana zama akan kujera sannan ta dora kafa daya kan daya

     “ Ashe ke mahaukaciya ce,dabbiya,mara hankali,mara tinani,shashasha wacce batasan meke mata yawo a brain ba? Toh ni bazan kasheki ba danni ba jahila bace irinki,amma ki sani dole zan dau mataki akan ki”…. 

Ta fada tanayiwa mama wani mugun kallo,ita ko mama sai kallon kofar kitchen take tana tinanin yanda zatayi wuff ta shige

  “Badai saboda daddy kike duk wannan abun ba? Toh dole zaayi dayan biyu,ko daddy ya karasa tsige igiyar dayake tsakaninku inga babu alakar komai a tsakaninku ko kuma in auresa sai muyi zaman kishi da hujja,kiga yanda zansa ya wulakantaki san raina daga bisani kuma insa ya tsinke igiyarku gabadaya sannan ince ya sakeni in auri danku!”……

Mama ji tayi kamar an buga mata dutse a kokon zuciyarta,ai in daddy ya yanke duka igiyarsu  tashiga uku,sannan ko a mafarki bazatayi kishi da fatima zainab ba dan wallahi tafi karfin tayi kishi da sa’ar ‘ya’yanta kome ze faru kuwa! Tunowa tayi da tariga ta gama da daddy yanzu,kuma sai abunda tace yasa ta yin wani murmushin azaba jin yadda jikinta ke mata ciwo,ita Allah yasa ma bata samu karaya ba,dan tindazu take kokarin shigewa kitchen amma takasa motsawa,nishi tayi tace 

    “Wallahi nafi karfin inyi kishi dake,kuma aurenmu nida alhaji mutuka raba takalmin kaza,baki da labarin sai yanda nayi da alhaji yanzu” 

Mama ta fada tana fuzgo maganar cikin tsoro da fargaba….. 

Wata muguwar dariya fatima zainab tayi tace 

    “Au haryanzu baki dena biye biyen boka da malamai ba? Toh ki zuba ido ki gani,ba boka ba mallam amma wallahi sai dayan biyun abunda na fada ya faru,bazanyi kaffara ba kuma”…….. 

Zaro ido mama tayi jin abinda tace,cikin kidimewa a ranta tace nashiga tara ba goma ba ya akayi yarinyarnan tasan ina biye biyen malamai?,mazewa tayi tace

     “Nima ba boka ba mallam kuma duk abunda kika fada baze faru ba”…. 

Sake fashewa da dariya tayi tace 

    “Lallai wuyarki ta isa yanka,ke a ajiye batun alhaji ya sakeki ma,ki saurari kayan fadar kishiya nan da sati daya!”…….. Ta fada tana ficewa daga part din….

     Ya dade be jisa a cikin tashin hankali irin wannan ba,sai ya rasa mezai dafah yaji dadi,gashi mutumin ya gudu kuma ya rasa ta ina yabi…. Tinanin kiran Deen ne ya shigo kansa,yayi maza yayi dialing number amma sai tayita ringing be dagaba,fita daga gidan yayi yana tinanin ina ze nufa yanzu,yasan kuma be isa yaje gidansu a yanzu ba,yanke shawarar komawa abuja yayi,ya tafi airport ya siya ticket fortunately ya samu jirgin daze tashi yanzu…..

Yana isowa abuja ya sake trying number Deen,Allah ya taimakesa ya dauka a lokacin….. A rikice yace

    “Deen where are you,you’re not safe”…..

   “I’m safe,stop calling me,I don’t want to implicate you”…. Yana fadin haka ya kashe wayar….

Sai a lokacin hankalin sameer ya dan kwanta,duk yanda akayi kenan Deen yasan da plan din tinda har bayaso yayi implicating dinshi,yasan kuma Deen ze dauki action akan abun as smart as he is……..

A nitse ya cigaba da fitowa daga airport din,kamar ance juyo ya hango khaleel rike da traveling bag alamun dai yanzu ya diro kasar… Wani farinciki ne ya kamasa ganin yanda Allah ya kawo masa khaleel cikin sauki,dama ze kirasa a waya,sai kuma gashi sun hadu face to face……. 

Daga sama khaleel yaji anyi hugging dinsa,juyowa yayi da sauri yana tinanin waye haka,mamaki yayi ganin sameer,take ko ya hade rai……..

Wani huge smile sameer yayi yace

   “Bro abun ya kai har haka?,kana ganina ka hade rai?”….

   “Abun yafi haka ma” khaleel ya fada ba alamun wasa a fuskarsa…..

   “Toh Allah ya huci zuciyarka,yanzu kai kana tinanin duk abinda na fada gaskiya ne? Haba dude yama zaayi inso yarinyar dana san kadade kanaso,kofa ganinta banyi ba ranar kawai nayi creating abubuwa dana fada ne dan in tsokaneka,sai kuma naga ka mayar dashi babba, abunda yasa na kara tunzuraka kenan amma wallahi har cikin raina wasa nake,trust me kaima kasan bazan iya maka wannan betrayal din ba,dama kuma zan kiraka in baka hakuri wallahi”….. 

Sameer ya fada looking so remorseful…..

Numfasawa khaleel yayi,har cikin ransa ya yadda da abinda da sameer yace,dan dagaske beyi tinanin sameer ze iya haka ba,in wani ne yace mishi sameer zeyi masa haka baze yarda ba,kuma har a yau ya kasa believing sameer ze iya masa haka,sai kuma Allah yasa sameer yayi clearing komai,ya kuma tabbatar masa da wasa yakeyi,wani sanyi yaji a ransa kamar anyaye masa duk abinda ke damunsa….

Murmushi yayi ya dafa kafadar sameer yace

   “Ni dama nasan you don’t mean it,amma it was an expensive joke,dan Allah karka sake min haka”…

   “Insha Allah,I promise” Sameer ya fada kamar gaske….

    “ Daga ina kake haka sam?”…. 

    “Daga kano nake wlh,p man ne yamin kiran gaggawa shiyasa ban samu baka hakuri ba harna tawo”……

   “Oh Allah sarki nima wani urgent abu ne ya kawoni wlh,hankalina yanzu baa kwance yake ba”…

   “Subhanallah!,muje in raka ka dama na dade ban gaida momma da daddy ba”… Sameer ya fada dan so yake ya shigewa khaleel sosai….

Khaleel ji yayi kamar yace aa sanin fatima zainab na gidan,sai kuma yaga be kamata ba ganin yanda sameer ya nuna damuwa akansa….. Jerawa sukayi har suka karaso inda driver ke jiran khaleel,shiga sukayi ya jasu suka nufi gidansu khaleel….

          

    Tun bayan sungama waya da sameer yake tinanin yanda ze fita daga gidan,shi in dan tashine be damuba zeta zama a gidan har sanda akaga daman sakinsa,saidai tinaninta ya hanashi sukuni,san sanin WACECE ITA na kara masa yawa,duk wani dan abu dayasani a kanta nanan makale a zuciyarsa,be manta da daddadar muryarta ba da kullum yakeji kamar a lokacin take masa karatun,be manta lallausan jikinta kamar na mage ba,be manta da zarazaran gashi idonta kamar wacce tayi fixing ba,inama ta bude idanuwanta sosai ya gansu,da yanzu ya kara a cikin dictionaryn dake zuciyarsa da yake rubuta komai nata a ciki….. Kai dole ma yayi wani abu,dole ya bar gurin dan yanaji kamar jininsa ze hau idan be ganta a yau ba…… 

Mikewa yayi yasa wayarsa a silent sannan ya tura ta karkashin pillow,a hankali ya murda kofar kamar yanda ya zata ya ganta a bude,komawa dakin ya sakeyi ya dauko wani powder daya gani a drawer yanada yakinin ita suka shaqa masa,murmushi yayi yana tinanin zeyi using way dinsu against them,zasuji abinda akeji suma,face mask din dake cikin aljihun kayan da yazo dashi ya dauka yasa sannan ya sake fitowa….. Luckily ba kowa a corridor din harya karaso parlour, komawa da sauri yayi jin motsi a parlourn,Allah ya taimakesa ba danno kai yayi ba…..

Zaune suke su goma sha daya suna shayeshayensu hankalinsu kwance dan basu taba ganin kidnappern da be basu wahala ba kamar Deen,har mamaki suke ganin yanda ya sake hankali kwance,har tsaro suka rage ganin basa bukatar hakan….. 

   “Kai baba jibi zaa kashe wanchan wawan”…Daya daga cikinsu ya fada

“Ah haba haka boss yace kenan?” Wani ya kara fada yana zukar sigari

   “Wlh ina fadamaka,ba shi ya sake ba yana ganin ana mishi duk abinda yakeso besan an kusa aikasa barzau…….. 

Maganarsa ce ta makale jin an bada musu abu a parlourn,take duk suka zube a sume…..

Mamakine ya kama Deen,it means he’s mistaken wanda yake tinanin shi yayi kidnapping dinsa bashi bane kenan….

“who’s behind this” 

yafada kamar yana magana da wani

“Koma waye I’ll surely get you! Yanzu dama ba Dad bane yayi kidnapping dina ba?,God bless the unknown girl,da badan ke ba da yanzu ina chan thinking Dad ne yayi kidnapping dina,ze kuma sakeni at any time,ashe kasheni ake kokarin yi,Allah yasa inganki  in fadamiki kin taimakeni”….. 

Ya fada yana daukan bindiga daya sannan ya fita daga parlourn…… 

Yana zuwa get me gadi ya taso da sauri,buga masa bindigar dake hannunsa yayi,nan da nan me gadi ya zube a gurin,bude get din yayi ya fita a guje…..

Gudu ya shigayi ganin isolated area ne,har Allah ya taimakesa ya karaso titi,motoci ya shiga tsaidawa amma duk wanda ya tsayar sai suki tsayawa ganinsa da bindaga gashi ba kayan yan sanda ko sojoji a jikinsa,yana cikin wannan halin ya hangosu daga chan nisa sun tawo a guje……

Tsayawa yayi a tsakiyar titi yanda dole a tsaya mishi…..

Wani uban burki ta taka saura kadan tabi ta kansa,ita sam bata lura da mutum a tsaye ba….

Bude motar yayi ya shiga ganin sun kusa karasowa batareda ya kalli me driving din ba yace 

   “Dan Allah ja mu tafi,kasheni suke sanyi”…..

Taka motar tayi a guje ta yanki wata hanya sannan ta nufi gidan alhaji ganin yafi kusa da nan…….

Really busy,need your prayers fam🥹❤️

~Unique Barakancy~

Back to top button