Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 38 Hausa Novel

A parlor ya tarar da yaran suna zaune suna shan shayi da burodi wanda Hafsa ta dafa musu ruwan zafin. Ya nemi waje ya zauna ya dauki remote ya canza channel.Ya fi minti tallatin da zama shi da yaran suna ta hira sannan ta sauko, ta sha kwalliya sai kamshi takeyi. Bayan ta amsa gaisuwar yaran kai tsaye ta wuce part dinta, nan da nan ya tashi ya bi bayanta yayinda Nasreen da Shukra suka rufa masa baya. Nan da nan ta soya kwai ta hada musu da shayi suka zauna shi da ita a dining table suka karya.Suna gama karyawa shima Mustaphan ya shirya suka fito tare. Har zasu sauka daga bena sai kuma ya bata mukullin motar yace ta fito ta jirashi zai yi sallama da Khadeeja.A parlor dinta ya sameta tana kwance a kan doguwar kujera da remote a hannunta yayinda Hammad yake cikin baby rocker dinsa yana ta wutsil-wutsil. Tana daga kwance ta amsa sallamarsa, ya karasa kusa da kanta yace ‘Zamu fita ni da Naja, itama yau zata koma aiki.’Tace ‘Ok, a dawo lafiya.’Har ya juya zai fita tace ‘Ta dai barwa yara abincinsu ko? Ga shi zasu je islamiyya ko da yake na san sun yi wanka in lokacin yayi ko Hafsa sai ta tayasu shiryawa su wuce.’Ya juyo ya tsaya ya zuba mata ido na dan lokaci; ya ma rasa ta ina zai fara. Ya kan rasa yaren da zai yiwa Khadeeja magana da shi idan ta fara wannan taurin kan nata, lokuta da dama ya kan dauka cewa tana jin tsoronsa amma fitnar da yake gani a kwayar idonta idan tana wannan taurin kan tana bashi tsoro. Ya cije lebensa sanna yace ‘Fita fa nace miki zamu yi, ya kike so tayi da abincin ranansu?’Ta tashi zaune ta gyara zamanta sannan tace ‘Yanda nakeyi idan zan tafi makaranta ko?’Ya jijjiga kai sanna yace ‘Khadeeja please kada ki saka min ciwon kai da safen nan, ga yara nan ki basu abinci in ya so idan mun dawo ta basu na dare. Idan kuma kin ga dama ki barsu da yunwa.’Ta kalleshi suka hada ido tayi masa gajeran murmushin yake ta zame ta kwanta ba tare da ta ce masa komai. Haka shima ya juya ya fice zuciyarsa cike da wasi-wasi saboda ya san wannan murmushin nata ba wai yana nufin zata kula da su bane, amma dai ya tafi yana addu’ar Allah ya sa ta kula masa da su.Sai bayan la’asar suka dawo tare kamar yanda suka fita, a lokacin yara suna islamiyya. Don haka cikin wallwala ya karas ciki don ya san Khadeeja ta kular masa da yaran. Sai da ya leka parlor dinta ya gaya mata ya dawo sannan ya wuce dakinsa.Yara suna dawowa daga islamiyya suka wuce parlor din Naja inda suka jiyosu ita da Abbansu. Kafin wani yayi magana Shukra ta fada jikin Naja tace “Yauwa Anti kin dafa bana abinci ko? Wallahi yau gari muka sha mu da Anti, tace idan kin dawo zaki dafa mana abinci.’Ta kalli Mustapha sanna ta sake kallon Shukran, kafin tace wani abu Mustaphan ya janyo Shukra jikinsa yace ‘Gari kuka ci Shukra?’Ta daga masa kai. Nan take ragowar yara suka tabbatar masa da haka aka yi.Ya kalli Afaf wadda shigowarta kenan tana kokarin zama yace ‘Ke ba sai ki dafa muku ko indomie bace?’Ta zumbura baki ta kawar da kai ba tare da tace komai ba.Yayi gajeren tsaki sannan ya dubi Nasreen yace ‘Ina Hafsa? Ita ba sai ta dafa muku ba?’‘Itama garin tace ai, Anti bata ce ta dafa komai ba haka tace mu jira Anti Naja ta dawo itace da girki.’Ya kalli Najan wadda take ta fama cika tana batsewa, ya mike a fusace ya fice daga parlor din.Tana zaune a parlor dinta tana shan kunun alkama ya sameta, kafin ta gama amsa sallamarsa ya fara magana a fusace ‘Khadeeja wane irin raini da wulakanci ne zai saka ki bawa yara gari, ke ba zaki girka musu abinci ba kuma ba zaki saka yarinyarki ta girka musu ba.’Ta ajiye kofin kununta ta kalle shi tana jijjiga kai sannan cikin halin ko in kula tace ‘To ai mai girkin bata bar musu abinci ba kuma bata barwa yarinyar tawa wani abu tace ta dafa musu ba, shi yasa da aka ji yunwa na hada mana gari duka muka sha. Ina laifi?’Ya fesar da iska mai zafi saboda yanda takaici ya kamashi, baya son yanda idan Khadeeja zata yi masa fitna take zama da nutsuwarta shi kuma tana saka shi yana yin spark. ‘Khadeeja, don Allah me kike so ne kike min wanna wulakancin.’‘Ba wulakanci nake maka ba. Abu daya kawai nake so shine kayi adalci, yanda nake bukatar hutu daga kwana saboda jego haka nake bukatar hutu daga hidimar gida da ta yara, don dama wallahi dagewa nakeyi. Idan kuka gama arba’in din muka fara rabon kwan sai na dinga hadawa ina karba.’Yaja dogon tsaki ya yarfar da hannu, har ya bude baki zai yi magana kuma sai ya fasa. Ya juya ya fice daga parlor din. …….. Duk yanda yake tunanin Khadeeja zata saurara masa hakan bai samu ba. Yana so ya mayar mata da kwananta da ya karab ya bawa Naja amma kuma yana son karin lokaci don ya kara sabawa da Najan. Haka dole ya hakura ya zuba musu ido; sai dai duk wani jin dadi da yake sa ran zai samu daga wajen Najan baya samuwa saboda yanda take wuni a gajiye saboda hidima. Suna kwanciya bacci yake kwasheta; gashi kullum cikin yi masa mita take a kan ita ya mayar da hidimar yara wajen Khadeeja. Duk da kusan Khadeejan ta sallama musu Hafsa tana tayata. Ita kuwa Khadeeja gaba daya haushinta yake ji don gaba daya ya daina kulata, a yanda yake ji yanzu ma baya jin zai kulata koda tayi arba’in din idan dai ba itace ta kawo kanta ta bashi hakuri ba.Duk yanda Naja ta zata kula da yaran nan zai yi mata sauki abun ba haka bane, domin da kyara take kaiwa yamma saboda gajiya. Gashi Khadeeja ta sallama musu Hafsa kullum cikin taimaka mata take; abu daya da Khadeeja ta hana Hafsa yi mata shine girki. Ta so kwarai ace ta dinga barwa Hafsa tana yi musu girki idan ta fita, amma Khadeeja ta ki bari. Don haka kullum kafin ta fita aiki sai ta dafa musu abincin rana kuma idan ta dawo sai tayi na dare. Gashi duk da suna shiri da Afaf ta gane Afaf ta fita son jiki, don duk yanda take jin zasu tayata aiki hakan ma bai samu ba.…….Yau satinta biyu da tarewa; yana zaune a parlor dinta shi da yaransa kamar yanda suka saba suna kallon TV bayan sallar isha’i. Ita kadai ce a tsaye tana kokarin jera abincin dare a dining. Tana jerawa tana mita a ranta yanda yaran basa tayata aiki, ko da zata ce su tayata to fa idan dai yana nan ba zasu tayata ba; sai dai tayi aikinta ita kadai. Gashi kuma baya son Hafsa ta dinga yi masa girki. Bayan ta gama jera abincin suka taso gaba dayansu suka zauna harda ita suna cin abinci.Jollof sphagetti ce da kifi; ana cikin cin abincin Shukra ta daga kifin da yake kwanonta tace ‘Abba a cire min kaya.’Har ta bude baki zata ce Afaf ta cire mata yayi sari yace ‘Ki mikowa Antinki ta cire miki.’Haka Afaf wadda take zaune a tsakanin Najan da Shukran ta dauki plate din da yake gaban Shukran ta mikawa Naja. Ba tare da ta ce komai ba ta sa hannu ta bara kifin gida biyu ta cire kayar sannan ta mikawa Afaf wadda ta sake mikawa Shukra.Haka har suka gama cin abincinsu babu wanda Naja ta sake yiwa magana.…….Tana zaune a gefen gado tana shirin kwantaw bacci ya tura kofar ya shigo da sallama, da kyar ta amsa sallamarsa saboda yanda take jin haushinsa. Gani take kamar da gayya ya bari matarsa ta sallama mata yaran sannan kuma sun kai su kula da kansu amma komai sai yace sai tayi musu.Ya karasa ya hau gadon ta bayanta ya kwanta, tana kwanciya ya janyota jikinsa. Ta dan tureshi tana cewa ‘Bacci fa nake ji Habibi, wallahi na gaji. Kuma ka ga gobe yara zasu makaranta kuma zan je aiki.’Ya kara kankameta yana laluba jikinta yana cewa ‘Sannu, bari nayi miki massage yanzu gajiya zata sauka.’Ta dage ta janye jikinta ta zauna a kan gadon, hakan ya sa shima ya tashi ya zauna a kusa da itayana kallon fuskarta kamar mai neman amsa a fuskar tata. Kafin yayi magana ta langabe kai tace ‘Habibi ni dai don Allah ka mayarwa da maman Hammad kwananta, in ya so mu cigaba da yi kwana bibbiyu yanda tsarin yake.’Da mamaki ya kalleta suka hada ido sannan yace ‘Kin gai dani kenan Baby.’

Back to top button