Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 54 Hausa Novel

Ba a fi sati daya da kwashe kayan Khadeeja ba Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya sake fentin saman aka gyara ta kwashe kayanta ta koma. Yaran kuma gaba daya ta tattarosu ta dawo da su kasa tare da masu aikinta guda biyu. Dakinta da parlor dinta nan ta mayar dakinsu Afaf, suna ji suna gani babu yanda suka iya. Shi kanshi Mustapha abun bai yi masa dadi ba amma ya kasa magana; yana matukar mamakin abinda ya sa baya iya hana Naja abinda take so a ‘ya kwanakin nan.Cikinta yana cika wata tara ta sake haifar ‘yarta mace, haka ta dage ta shirya taron suna fiye ma da wanda ta shirya a haihuwar Rukayya. Aka sakawa yarinyar suna Maryam.Washegarin suna su Anti Wiyya da sauran dangi suka soye naman suna suka gyara koma, sannan suka tafi suka bar Anti Wiyya ita kadai wadda zata kara kwana biyu saboda tayata jego.Tana zaune a parlor din sama Anti Wiyya ta shigo da sallama, bayan ta amsa ta karasa ta zauna a kusa da ita sannan tace ‘Wannan mai wankin naki gaskiya ya iya wulakanci, sai da ya fuskanci ana taro sannan ya gudu. Ni dai wallahi ko kayan sakawa gobe bani da su duk sun yi datti, ga shi duk jikina ciwo yake balle na zage na wanke kuma ‘yar aikinki ma dai ta fini gajiya.’‘Ai mai wankin nan yayi wa kansa, in sha Allahu gobe Abban Rukayya zai samo mana wani mai wankin kowa ya huta.’ Ta fada tana gyara zama.Anti Wiyya tace ‘Don ma dai ‘yayanki basa moruwa ne in banda haka ga Habib can a kasa yana wanki ai da ko kala daya ne ya wanke min.’Ta gyara zama ‘Au ai ban san ma yana gidan ba kwaso kayan duka bari na kirawoshi zai wanke miki yanzu.’Ba tare da bata lokaci ba ta juya ta koma kasa inda ta kwaso kayan nata yayinda ita kuma Naja ta kwalawa Afaf kira ta sakata ta turo Habib.Kusan a lokaci guda suka isa parlor din, shi ya tsaya daga bkin kofa yayinda ita kuma ta karasa ta zube kayan a gaban Naja.Yana daga tsaye a bakin kofa yace ‘Anti gani.’Tace ‘Mai wanki ya kwana biyu baya zuwa, ka kwashi kayan nan ka wankewa Anti.’Ya kalli kayan ya kalleta yanda take muzurai; ba wai bata saba yi masa hakan bane, ta riga ta saba musamman tun bayan da khadeeja ta bar gidan. Kawai dai ya kan yi mata binda zai iya wanda ba zai yi ba kuma ya bar mata kayanta. Ya sake kallon kayan yace ‘Ah ku barshi dai yanzu zan fita sai na samo muku wanda zai wanke ku biya shi.’Har ya juya ya fara tafiya tace ‘Kana nufin ba zaka wanke ba ko me.’Ya dan dawo ya kalleta ya kalli kayan, har ya bude baki zai yi magana kuma sai ya fasa, ya fice ya barta nan a zaune da kayan.A fusace ta mike tana huci, kafin tayi magana Anti Wiyya tace ‘Ai na gaya miki wadannan yaran basa moruwa.’‘Ni ka tafi ka bari ina magana ko Habib? Saboda ka ga ni ba uwarka bace kuma ba khadeeja bace ko? Saboda ba a isa a saka aiki kayi ba ko? To wallahi bari Abban naku ya dawo, sai dai ko ni ko kai a gidan nan don idan dai ba zan moreka ba sai dai ka bar gidan wallahi.’Wiyya tace ‘Ah to, yaron da bana jin ya haura sha takwas ya dinga yi miki irin wannan rainin, wannan nan da ‘yan shekaru ai sai ya kai miki duka.’‘Wallahi bari ubanshi ya dawo, dole ya bar min gidan nan idan ba haka ba ni na bar masa gidan. Idan ma Khadeejan ce take zuga shi ta janyo masa.’Haka Wiyya ta skaata a gaba ta kara zugeta kafin ya dawo.Ana idar da sallar Magriba ya shiga gidan, Habib ne ya bude masa gate tare da Baba maigadi yayi masa sannu da zuwa sai dai bai rakashi har cikin gidan ba. Kamar yanda ya saba a parlor din kasa ya sami yaran suna zaune suna kallon TV, bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce sama. Da da ne Nasreen da Shukra sai sun rakashi har dakinsa, sai dai yanzu saboda yanda Naja take yawan korarsu tana nuna musu su dinga tsayawa a kasa ya sa sun hakura, haka ya haye shi kadai zuciyarsa babu dadi; saboda shima yana kewar wannan rakiyar.A dakinsa ya sameta tana ta cika tana batsewa, domin ko sannu da zuwa haka tayi masa tana ta faman zumbura baki. Bayan ya amsa yace ‘Me ya faru ne naga kina ta wani bata rai?’Ta sake hade rai sannan tace ‘Ya za ayi a gidan nan ace ban isa na saka Habib aiki yayi ba? A gaba kowa zan ce Habib yayi aiki amma kai tsaye ya ce min ba zai yi ba? Ai ba haka yake yiwa Maman Hammad ba, ko da yake na ji suna cewa yana zuwa wajenta ban sani ba ko itace take zugashi ya dinga yi min rashin kunya.’Ya ajiye jakarsa ya zauna a kan kujerar gaba mudubi ya fara cire takalmansa yana cewa ‘Kada ki saka Khadeeja a cikin wannan maganar, da zata sa wani yayi miki rashin kunya da tun tana nan zata saka su. Habib din me kika ce yayi ya ki yi?’‘Wankin kayansa yake yi shine na kirawoshi na bashi kayan Anti Wiyya kala daya nace ya taimaka ya wanke mata amma yaron nan ya ki, kuma yana kallo mai wankin namu ya gudu. Itace ta ke ta fama kula da gidan kayanta duk sun yi datti amma a gabanta Habib ya ce ba zai wanke mata kala daya ba don wulakanci don ya nuna mata ban isa ba.’Ya mike ya cire kayansa yana cewa ‘Ki dauko kayan idan na fito zan bashi ya wanke in ya so zan gayawa Baba Maigadi ya zagaya nan makarantar almajirai ya samo yaro a wajen malaminsu wanda zai dinga zuwa yana wankin.’Kafin tace wani abu ya shige bandaki. Ta zubura baki ta ja tsaki don ba haka ta so ba, so take ayi masifa ta sami damara da za a ce Habib ya bar gidan. In ya so sai ta san yanda zata yi da Afaf, tana gamawa da wadannan biyun ta san gidan ya zama nata, musamman da yake Shukra ita matsoraciya ce duk yanda ma aka juya ta haka takeyi.Jimawa kadan ya fito ya sake kaya sannan ya wuce ya zauna a dining table ya fara cin abinci. Yana cikin cin abincin ya dauki waya ya kirawo Habib, ba tare da bata lokaci ba ya hawo ya same shi.‘Abba gani.’ Ya fada yana tsaye daga gefe.Ya ajiye cokalin da yake hannunsa sannan yace ‘Habib me yasa Antinka ta saka ka wanki ka ki yi?’Yace ‘Abba ba kin yi nayi ba, wankin ne da yawa kuma nace gobe zan samo musu yaro ya wanke a biya shi.’‘Kala dayan ne da yawa? Kayan ma da ba nawa bane.’ Ta fada tana wasu muzurai.Yace ‘Ni dai kayan da aka bani zasu kai kamar kala biyar ko fiye, ban sani ba ko ba su aka nuna miki ba.’Abbansu yace ‘Ka ga Malam, bana son wani karin bayani. An ce kaya kala daya ne kuma gobe ake so ayi amfani da su. Kace a baka kayan ka wanke yanzu in ba so kake ranka ya baci ba, kuma daga yau bana son a saka ka aiki ka dinga kin yi. Ba zan dauki taurin kai da rashin kunya ba.’Ya bude baki zai yi magana sai kuma ya fasa, ya juya ya fice.Ya dubi Najan yace ‘Kije kice mata ta bashi kayan ya wanke.’Ta tashi ta fice.Yana zaune a tsakar gida wajen Baba maigadi Shukra taje ta kirawoshi. Yana shigowa ya ci karo da wankin a zube a bakin kofa; tabbas wankin sun fi kala biyar. Yana shiga cikin parlor din kafin yayi magana Naja da take tsaye tace ‘Gasu nan kaje ka wanke, kuma wallahi idan basu fita ba sakewa zaka yi har sai sun fita.’Ta juya ta haye sama ta barsu a nan shi da kannensa.Ya juya ya dawo ya tsaya a kan wankin yana kare musu kallo yana tunani; tabbas ba zai yi wankin nan ba, ko da kuwa kala dayan ta bayar kamar yanda tace. Kuma yanda yaga a gaban Abban tace kala daya ne kuma ta dauko kaya da yawa haka ta bashi ya san ta shirya wata makarkashiyar.Ya san ba lallai Abbanshi ya saurareshi ba saboda tana gabansa tana tsara masa zance, kuma ya san idan har yayi wannan wankin to ta sami damar da zata mayar da shi dan aikin gida kuma ba zai yi ba. Haka ya kewaye ya fice ya bar wankin a nan inda ta ajiye su.

Back to top button