Ajiya A Duhu Book 1 Page 5 Complete Novel
*_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU….💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_**_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._*_My TikTok account 👇_*https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1*_Instagram👇🏻_*https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv*_Arewabooks_*Read My Book “AJIYA A DUHU” on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_🅿️➖0️⃣5️⃣______________Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyiMaganin cire tumbiMaganin farin jiniMaganin matsiMaganin mataMaganin sa ni’ima da dandanoDulka Amare Set na gyran jikiSet na amaryaTabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and BrestMagungunan gyran BrestMagungunan Karin hipsMaganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500Garin bata gaban kishiya 500Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500Za a bakisu akan 3800Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki________________……Da sauri ta kauda idanun nata tamkar bata ganshi ba. Sai ma cikin wayancewa ta ɗago Amrah tana faɗin, “Wai haka kika ƙara lukucewa matar nan?”. Dariya Amarhn tayi da kai mata mintsini a gefen hannunta itama tana faɗin, “Ke dai zauna nan kamar za’a hureki. Ni kin san bana wasa da cikina”. Murmushi kawai Manaal ɗin tayi batare data bata amsa ba. Hakan yasa Amrah jan hannun Munaya tana mata wasa. Da wannan damar Maanal ta ƙarasa cikin falon sosai. Cike da girmamawa ta kai duƙe duk da kallon wulaƙancin da Hajiya Yaya ke mata da sauran yaran ta shiga gaidata a mutunce. A yatsine ta amsa mata sau ɗaya ta ɗauke kanta. Hakan ya ƙona ran Maanal matuƙa amma sai ta daure, fuskarta da ɗan murmushi ta maida ga sauran yaran ta shiga gaishesu dan duk sun girmeta. Babu wanda ya amsa mata sai ma tsoki da wasu suka ja mata. Dai-dai nan saurayin nan dake zaune a dining ya miƙe zai fita a falon yana kai waya kunnensa alamar zaiyi magana. “Ina kuma zakaje Yazeed?”. Uwar ta ƙatse masa hanzari da ƴar tsawa-tsawa. Cikin dakiyarsa ya juyo da hannu yay mata nuni da waya zaiyi, batare da ya jira sake cewarta ba ya fice abinsa. “Hummm! Wai shi mai wayo fa Mamma”. Ɗaya daga cikin ƴammatan ta faɗa fuska a kumbure. Kafin wani ya bata amsa Maanal taja hannun Munaya suka fice suma. Duk rakata sukai da harara, sai kuma wadda tai maganar ta miƙe zumbur tana faɗin, “Ina zuwa bari na muku leƙen asiri. Dan nasan ko rantsuwa zanyi babu kaffara dan ita Yaya ya fita a falon nan babu wata waya da zai amsa”. “ALLAH nima na fahimci haka Nanah, dan tunda ta shigo ya dakata da cin abincin ma sai wani binta da kallo yake. Kinga muje”. A hasale Hajiya Yaya ta furta, “Aiko da naci ubansa a gidan nan yau. Tunda na rabashi da yarinyar nan na kuma haramta masa alaƙa da koda inuwarta ma balle ita. Amma kuje ku ganar min yana ina”. Ai kafin ma uwar ta rufe baki sun fice da sauri har su uku. A dai-dai fitowar tasu kuma Manaal ke shigewa sashen Hajiya Basariyya. Hajiya Basariyya itace mace ta biyu a gidan. Itama dai ɗin ba kanwar lasa bace ba. Dan ba mutuncin ne da ita ba. Sai dai ita akwai banbanci tsakaninta da Hajiya Yaya. Dan a zahiri baka isa fahimtar ita ɗin wacece ba saboda macece mai fuska biyu. A zahiri akwai faran-faran da jama’a da son nuna ita ɗin ta ALLAH ce. Shiyyasa mutane da yawa sai ta gama musu illa suke farga da ita ɗin wacece. Macijin sari ka noƙe ce ita ta bugawa a jarida. Yaranta biyar itama a gidan kuma duk mata, dan ita bata da namiji ko ɗaya. Huznah da Maanal ta fara haɗuwa sanda ta dawo itace ƴarta ta farko. Itama ɗin dai family nata akwai kuɗi, dan Yayanta daya riƙeta hamshaƙin mai arziƙi ne. Kuma babban aminin Alhaji Usman Chalawa ne, suna huɗɗar kasuwanci sosai da har wasu ma ke ganin dukiyarsu a cuɗe take da juna. Shiyyasa itama bata yarda Hajiya Yaya ta ɗaga mata hanci ta ɓangaren dukiya dan kar ce tasan kar. Kowa najinsa a wani shege. Komawa su Nanah sukai nasu sashen cikin taɓe bakuna. Dan Manaal na ƙoƙarin shiga sashen Hajiya Basariyya shi kuma yayansu nama ficewa a gidan da motarsa. Tun ma kafin su ƙaraso Hajiya Yaya data cika tai tab ta fara jeho musu tambaya cikin huci dan macece mai ƙiba sosai. Irin ƙibar nan bata wasa ba. Dan ko daga nesa ka hango ta kasan ALLAH yayi manyan mata a wajen nan. Zaune duk suka zube cikin takaicin rashin samo abinda za’aci mutuncin Maanal da uwarta yau a gidan. Nanah tace, “Mamma yama fita a mota. Ita kuma ta wuce sashen Momyn Suhana”. Cikin ƙwafa da takaicin itama bata samu yanda take so ɗin ba ta ce, “Ya taimaki kansa. Dan wlhy da yau har shegiyar uwartata sai sun bar gidan nan. Kai na tsani mutanen nan a rayuwata”. “Ai bake kaɗai ba Mamma”. Cewar ƴarta ta biyu mai tana huci. Auren nata ne ya mutu kusan shekara uku kenan tana gidan. Dama ita kawai ta aurar, rana ɗaya akai bikinsu da su Shahidah yayun Maanal. Sauran kuma ALLAH bai kawo ba, ko muce ruwan ido da jiran ƴaƴan masu hannu da manda irinsu ya hanasu auruwa. Burin kowannensu da ma uwarsu shine suyi auren ƙwarya tabi ƙwarya.. Buɗe shafin zagin su Manaal sukai a falon kamar sun tare musu numfashi, sai Amrah ce keta ɓata fuska dan ita bata son hakan. Ita birgeta ma Ammien take a rayuwarta mace mai dattako da sanin ya kamata. Babu ruwanta da duk abinda iyayen nasu keyi a gidan sabgar gabanta takeyi kawai da ƴaƴanta. Ko su duk abinsu bazasu taɓa cewa ga randa Ammien taima wani abu mara daɗi ba, amma tasa miyasa basa sonta da yaranta?… A ɓangaren Maanal can ma door bell ta fara dannawa kafin ta shiga. Shima dai sashen Hajiya Basariyya da suke kira da Momyn Suhana ya matuƙar haɗuwa. Girmansa kuma ɗaya dana Ammie. Ita dai bata falon sai su Huznah da ƙannenta dake cin dafaffen gyaɗa suna hira. Duk sun zubar da kohon a saman lallausan carpet ɗin tsakkiya ko’a jikinsu. Dan sun san mai-aiki ce zata gyara basu ba. Har zata juya batare data musu magana ba sai ga Hajiya Basariyya ɗin ta fito daga kitchen riƙe da kofi tana waya fuskarta da murmushi. “A’a ƴan Jos an dawo kenan?”.Ta faɗa cikin katse hanzarin Maanal kamar tuni ƴarta Huznah bata kawo mata labarin dawowar Maanal ɗin ba tun ɗazun. Juyowa Maanal ɗin tayi fuskarta kadaran kadahan ta ɗan kalla Hajiya Basariyya ɗin da nata fuskan ke ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa, sai dai acan ƙasan zuciyarta wani irin maƙoƙon tsanar Maanal ɗin ne ke mata kaikawo. Risinawa Manaal tai tana gaisheta. Nan ma ta amsa cike da fara’a tana nuna ma Maanal ɗin kujera da faɗin, “Haba sai kace wata baƙuwa zauna mana Maanal ga ƴan uwanki nan na bikin cin gyaɗa ka kuci. Da fatan dai kun dawo lafiya? Kuma komai ya kammala?”. Kai kawai Maanal ɗin ta jinjina mata kanta a ƙasa, sai dai yanzu da ɗan gajeren murmushi a fuskarta. Ganin bata zauna ɗin ba Hajiya Basariyyar ta sake nuna mata kujera. Kai ta girgiza mata da kama hannun Munaya ta ce, “A’a Momy mun gode dama munzo gaisheki ne kawai”. “Masha ALLAH aiko ina godiya. Sai dai ni bana cin miƙe gaskiya azo mini hira dai. Suma su Shahidah ki faɗa musu ina godiya sun barni da jira. Tun ɗazun har abinci nasa akayi dasu ga gyaɗa da aka dafa amma shiru kake ji”. “Zan faɗa musu in sha ALLAH Momy”. Maanal ta faɗa cikin muryarta mai zurfi da nutsuwa. Daga haka ta kama hannun Munaya tana mata sallama. Da harara duk suka bita har Hajiya Basariyyar. Sai da ta gama ficewar harda turo ƙofar Huznah taja tsoki da faɗin, “Ni wlhy Momy ina mamakinki, kiyita wani musu magana mai daɗi. Shegu sunzo sun gaje mana gida baka isa kai magana ba Daddy ya kama faɗin yayansa ne suma na halak. Ko ina suka zama ƴaƴan nasa agololi. Ni ko wanda ma yakema kallon ƴaƴan nasa ƙilama da cikinsu tazo.” “Hummm”. Kawai Hajiya Basariyya ta faɗa tana kaiwa zaune batare data kula maganar Huznah ɗin ba. Hakan ya sake bama yaran haushi suka cigaba da zagin Maanal dan kamar ma sunfi tsanarta fiye da sauran ƴaƴan Ammien. Duk da kuwa sunƙi jinin Hameed ma da Waleed da Ammien ta haifa a gidan suke matsayin uba ɗaya dasu. Balle da Daddyn ke tsananin nuna musu soyayya. Dan yanzu haka ma yana tare dasu ƙasar Amurika yin hutu. Duk da dai yace taro zaije ya tafi da su. Amma babu wani taro kawai yaje dasu ne dan hutawa na sati har biyu… Rai ɓace Manaal ta koma sashensu. Sai dai yanda bata gayama kowa abinda ya faru ba babu wanda ya tambayeta. Sai ma zama tai suka fara hirarsu. Babu jimawa kuma Daddy ya kira Ammie ta video call. Daga nan suka gaisa da shi ya bama Hameed da Waleed da Ammien ta haifa a gidan. Ƙanensu kenan guda biyu. Yarane matasa da zasu iya kai shekara sha biyar da sha uku. Suma duk kamanin Ammie suka biyo kamar su Maanal ɗin. Sai dai su farare ne sun kwaso hasken fatar Alhaji Usman Chalawa sosai kasancewarsa farin mutum tas.. Suna cikin hira da ƙannen nasu ne babu zato akai knocking ƙofar falon. Kafin wani yay magana a cikinsu mai knocking ɗin har ya shigo. A take Maanal ta shanye fara’ar fuskarta da maganar da take da Waleed ko nace faɗa irin na sako duk da kuwa ta girmesa sosai. Kauda kanta tai da jan mayafin abayarta daya zame ta rufe gashinta da ƙyau, yayinda su Amaal ke masa barka da shigowa. Shiko yana amsawa da ɗan murmushi hankalinsa akan yaransu dake gaishesa duk da sai da ya gama ƙarema Maanal kallo a kai-akaice. Gaban Ammie da hankalinta itama ke kansa tana ɗan murmushi ya ƙaraso. Cike da girmamawar da yake bata ya rissina yana gaisheta. Da kulawa take amsawa itama, kafin ta ɗora da faɗin, “Baka wuce Abujan ba kenan?”. “Eh Ammie fasawa nai saboda wanda zanje wajensa yace yana Lagos sai gobe zai dawo. Nima kawai sai na bari sai goben na tafi dan bana son naje naita zaman jiransa ina kuma da abinda zan ɗanyi anan ɗin”. “To ALLAH yayi jagora. Yay muku albarka, ya kuma saka muku hannu a dukan al’amuranku”. “Amin ya rabbi Ammie Nagode sosai”. Ya faɗa cike da jin daɗi yana maida hankalinsa kan Maanal dake ƙoƙarin tashi tabar falon. Kansa tsaye ya furta, “Ke ƴar hidimar ƙasa yaushe kika dawo?”……..✍️ Hummm yanzu fa aka fara shimfiɗar bama wasan ba. Mi kuke tsammani. Yazeed, ga kuma RK. Ga Maanal da bama musan alƙiblarta ba. Shin wai mi aka AJIYE A DUHUN nan ne? Ya dai kamata a haska mana mu gani ko zamu tayasu lalube🏃🏃🏃🏃🏃.Maza garzayo cikin tawagar littafan zafafa biyar da zasu zo muku da sabon salo na musamman in sha ALLAHU. Kowanne da salonsa da kuma takunsa. Mi kuke jira, ai sai kawai kuzo ayi tafiyar nan daku karku bari sai wasu sun baku labari.😘😘😘👌A fa dun inda ZAFAFAN suke ZAFAFAN ne🫣😘😘👍🏻✨ZAFAFAN DAI ✨1 ƘALBIM (Mamu gee)2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)3 DUNIYAR MU (Huguma)4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)Book 1:-500Book 2:-1000Book 3:-1500Book 4:-20000022419171Access bankMaryam Sani GumiShaida:- 09033181070Kati MTN:- 09032345899Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF89825722Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
