Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 28 By Ayshercool

Sosai take sauri, tare da fatan Allah ya sa baba yana nan.Sai dai tayi iya ƙoƙarinta wurin daidaita nutsuwarta, kafin ta ƙarasa gidan.Yamma ta fara yi, yaran gidan sun dawo, sun yi kaca-kaca da shi, duk sun zubar da kayan makarantar su ko ina, ga uban wanke-wanke da aka rasa mai zaman kawar da shi daga wurin.’yan ƙananan yaran gidan ne suka fara murnar ga jauhar, ɗakin mama ta shiga suka gaisa, ta kalleta ta ce “Lafiya na ganki yanzu? Wani abun ne?”Jauhar ta ce “Lafiya ƙalau wurin baba na zo”.”In ce ko dai lafiya, kuma ya san kin zo? Ki tashi ki tafi kar ki saka makakken mijinki ya zo yayi mana tijara da tashin hankali”Anty ce ta leƙo falon ta ce “Jauhar ashe abun da ya faru kenan?”Jauhar ta kalleta ta ce “Anty dama kina nan ina wuni?””Lafiya ƙalau, ashe kuma kama mijinki aka yi da hodar iblis, abu bai yi daɗi ba”.Dammm! Ƙirjin jauhar ya buga, yaya aka yi anty ta san wannan zancen, mama ta ce “Kamar yaya?””Yanzu muka yi waya da rahila, ta ce bata daɗe da barin gidan ba, ta je musu wai an kama shi”.Wani abu ɗaci ya tsaye wa jauhar, kamar ta fashe da kuka, ta ce “Ba ya ta’amalli da hodar iblis, rigima ce kawai ta haɗa su da wasu, shi ne dai na je na sanar musu, kar ya zamana ba su sani ba””Dan ubanki ni zaki yi wa ƙarya dan ki kare mijinki, ai rahila ba zata yi miki ƙarya ba”Walida ta ce “Taɓ, Allah ya kiyashemu taɓewa, hodar iblis abun ba arziki ai na zata a sara suka kawai ya tsaya ashe babban kai ne”Duk yadda ta so ta riƙe hawayenta ta kasa, ta fashe da kuka, suka din ga aibata Al’amin, gashi ba ta tarar da baba a gida ba, babu alamar za su tausaya mata, ko su rarrasheta, kawai ta tashi ta ɗauki jakarta tana kuka, ta fice.Hafsa ta ce “Allah sarki jauhara da tuni ana china ko gidan Alhaji mu’azzam ana shan A.C” suka din ga dariya.Ta kwashi ƙafa ta nufi gida, tare da ƙudirce wa ranta da yardar Allah, babu abin da zai saka ta sake zuwa gidan nan da matsalarta, ƙarshen ƙiyayya da tsana dai ana nuna mata a gidan nan.Kamar daga sama ta ji an buga mata tsawa “Ke bamu hana ki shigowa unguwar nan ba?”Sai a lokacin ta tuna abun da ya faru, cikin tsoro ta kalli mai yi mata tsawar, sai dai ta kasa magana, ta bishi da ido.”Ba magana nake yi ba””Nawa ubanka ya bayar aka shimfiɗa unguwar da za a hanata shigowa mahaifarta?” Ta ji wata muryar daban.Ta kalli matashin yaron, guduma kenan ɗan gidan mai unguwa, da su Walid suka bawa ragamar kula da gidan Al’amin da shige da ficen jauhar, har ta je gidan su Al’amin ta taho nasu gidan yana biye da ita.Saroro ta yi tana kallonsa, dan ba ta san shi ba.”Waye kai? Meya kawo ka unguwar nan?”Guduma ya nuna masa Jauhar, ya ce “Wannan, wallahi kana taɓa ta zamu ɓalla ƙarfe a wurin nan, mu rabu salin alin” ɗayan ya ja da baya ya basu hanya, guduma ya ce wa jauhar “Mu je”Ita dai ba ta iya yi masa magana ba, ta cigaba da tafiya ita yanzu gaba ɗaya hankalinta da lissafinta yana kan halin da take ciki a yanzu.Misalin ƙarfe uku da rabi na dare, jirginsu ya sauka malam Aminu Kano international airport, direba ya zo ɗaukarsa.Duk da a gajiye yake, saboda doguwar tafiyar da ya yi, hankalinsa da lissafin sa yana kan, ya ƙarasa gida garin Allah ya waye, ya je ya ji ba’asin dalilin fasa aurensa da yarinyar da ya ƙallafa rai a kanta, kullum cikin tunanin ta yake, kuma tun da aka ce, an fasa bashi ita, ya ji ya ƙara ƙaunarta, ta shiga ransa fiye da yadda yake tunani.***Kwanaki kaɗan ya rage jauhar ta fara jarrabawa, amma ba ta iya karanta komai, ga uniform ɗin ta, ga litattafanta sai dai ba ta da nutsuwar da za ta yi karatu, duk ta ƙare tayi rama ga rashin abinci dama damuwar da take ciki ba ta barinta ta ci abincin.Walid sai da yayi mata faɗa a kan zuwanta gidansu ba tare da saninsu ba, tare da jaddada mata mugunta da gaba mai tsanani da take tsakaninsa da Al’amin.Tana kwance a falo, maman halimatu ta shigo gidan, ta tarar da ita a kwance cikin damuwa ta ce “Jauhar, rayuwa za ta yiwu a haka kuwa? Yanzu da mutuwa yayi ba dole ki yi haƙuri ba, kin addabi kanki, kamar ko abinci ma fa ba kya ci” kamar ta soso mata wurin da yake yi mata ƙaiƙayi, ta hau rera kuka, ta zauna ta rungume ta ta din ga rarrashinta.Ta ce “Sako hijjabinki mu je gidana, kya ɗan sake ki sha iska, zaman kaɗaicin nan ba abun da zai amfana miki sai ɓacin rai”Haka ta bi maman halimatu, dan ba ta da wani zaɓi face hakan, ta zuba mata abinci ta bata, sai dai ta cakala ta bar shi ta ce ta ƙoshi.Halimatu ta zauna kusa da ita ta ce “Anty jauhar dan Allah ki daina kuka, zaki yi rashin lafiya ” tayi maganar tana goge mata hawaye. Akwai shaƙuwa sosai a tsakanin jauhar da yaran layin, wasu ma ko iyayen su ba ta sani ba, amma su tana hulɗa da su, ta yi wa matan kitso, ta koya musu karatu idan tana da abinci ta ba su, ko ‘yar alewa ko abun kusa da baka, shiyasa suna son taruwa a gidan idan master baya nan, sai dai rashin walwala da ba ta yi yanzu ya sanya duk suka watse suka daina zuwa.Baban su halimatu ya dawo, dama juahar na tsakar gida, ta gaishe shi ya amsa sama-sama, ya shige falo, ya fara ƙwalawa salamatu kira.”Baban halimatu sannu da zuwa “”Me matar mutumin nan take yi mini a gida? Haka kurum da tsinannen kwashe-kwashenki, ki janyo mana masifa muna zaman lafiya”Cikin takaici ta ce “Haba dan Allah, menene a ciki, tana zaune ita kaɗai cikin damuwa shiyasa na ce ta shigo, amma ka san haka kurum ba mai shige-shige ba ce ba”.”Ke ki ka sakata a damuwar da zaki cirota, ambulance uwar taimako “Jauhar na jin su sama-sama, ta tashi ta ɗauki mukullin gidanta, ta fice ta koma gida.Jauhar ta kama addu’a iya yin ta, su liti fafur sun ƙi gaya mata kotun da ake yi wa Al’amin shari’a, kuma suka ƙi gaya mata prison ɗin da yake.Baba yana karyawa da safe, ya ga kiran waya da baƙuwar lamba, ya ɗaga ya ɗan yi gyaran murya yayi sallma.”Wa’alaikum Salam, barka da safiya baba”.”Yauwwa barka dai, da wa nake magana?””Alhaji mu’azzam ne baba, ina ƙofar gida na zo, na ce Allah ya sa ba ka fita ba”.Jikin baba yayi sanyi, ya ce “Ahh ina nan ban fita ba tukuna, ashe ka dawo””Eh baba na dawo””To gani nan” Ya miƙe zai fita, mama ta ce “Ina zaka kuma kai da waye?””Baƙo” ya bata amsa a taƙaice.Ya fita tsakar gida, hafsa ta shirya za ta tafi makaranta ya ce “Ke haryanzu baki tafi makarantar ba me ki ke yi?””Ba ni da lectures ne da wuri, shiyasa yanzu zan tafi””To Allah ya tsare” ta amsa da amin.Baba ya fito suka gaisa, ya ce “Malam mu’azzam ka dawo ashe?”Cikin girmamawa ya ce “Eh baba, na sameku lafiya?””Alhamdilillah””Masha Allah, baba tun ina china na samu wani labari, hankalina duk bai kwanta ba, na yi iya ƙoƙarina wurin dawowa, baba ko wani laifin na yi ka hana ni auren jauhar?”Baba ya girgiza kai ya ce “Wallahi ko ɗaya, kawai dai ka san matar wani ba ta auren mijin wata, Allah bai ƙaddara aurenku ba, ina mai baka haƙuri, na yi maka laifi ban kyauta ba, da kuɗin aurenka a hannuna na aurar da ita, amma ka yi haƙuri dan Allah”A razane ya kalli Baba ya ce “Aure aka yi mata?” Baba ya jinjina masa kai a sanyaye ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un”Hafsa kuwa har ta sako kai za ta fita, ta hango Alhaji mu’azzam, ta koma cikin gidan da gudu, ta samu mahaifiyarta a ɗaki ta ce “Anty, saurayin nan na jauhar ne ya zo, Alhaji mu’azzam gashi can da baba a waje”A sukwane ta tashi ta ce “Haba dai?””Wallahi da gaske nake””To maza ɗauko kayayyakin nan ki yi amfani da su ki fita kafin ya tafi”Can kuwa Baba sai haƙuri yake bashi, yana yi masa nasiha, dan shi bai san ma an yi mata aure ba sai yanzu, gaba ɗaya ya shiga damuwa, aƙalla zai bawa jauhar shekara ashirin da wani abu, ya girmeta nesa ba kusa ba, sai dai ta shiga ransa sosai da sosai, duk da ya sha yinƙurin ƙara aure a baya, amma matarsa tana hanawa, bai taɓa shiga damuwa na rashin wata ba sai jauhar, kamar ya zubar da hawaye haka yake ji.Jiki a sanyaye ya ce “Shikenan baba babu damuwa, na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya basu zaman lafiya da zuriya ɗayyiba”.Baba ya amsa da “Amin”Suka yi sallama, ya shiga motarsa amma ya kasa tuƙin, ya kifa kansa a sitiring motar, yayi shiru ya ji gaba ɗaya duniyar tayi masa wani iri, babu irin zargin da bai kawo a ransa ba, na dalilin hana shi auren jauhar.”Malam ya dai” da sauri ya ɗago kansa ya ce “Jauhar””Ba ita ba ce, yayarta ce, tun ɗazu na ganka a nan baka tafi ba, lafiya?””Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah in tambayeki mana?””Ok, Allah ya sa na sani” tayi maganar tana sake gyara tsayuwarta cikin iyayi.”Ko kin san dalilin da ya saka aka fasa bani aurenta, tun da kin ce ke yayarta ce””Eh to, rashin ji ta fara yi, baba ya yanke shawarar aurar da ita kawai, tun da baka nan”Alhaji mu’azzam ya ce “Wani irin rashin ji?””A tunaninka wane rashin ji mace za ta yi, a aurar da ita babu shiri?”Cikin matsanancin mamaki ya ce “Jauhar ɗin?”Hafsa ta ce “Ita fa, ko dan kana ganinta a haka? Dama ba sonka take yi ba, akwai wani saurayinta ɗan daba, da ta ƙallafa rai a kansa, ta fara rashin ji, kawai baba ya aurar da ita, ai ka ga ba zai gaya maka haka ba” yayi shiru yana kallon hafsa, kawai ya ji maganganun nata ba su shige shi ba, ya gyaɗa kai ya ce “Shikenan, Allah ya basu zaman lafiya”Ta ce “Amin, dan Allah ko zaka sauke ni a hanya, school zan tafi ko a titi ne sai na sauka na samu abun hawa?”Ya ce “Bakomai bisimillah”Jauhar ta idar da sallar la’asar, ta ga kiran walid a wayar Viper, ta tashi ta ɗaga da sauri, suka gaisa, ya ce “Wani tunani na yi, akwai uban gidansa da muke yi wa aiki, ɗan majalisa ne, sai dai Viper ne kawai yake iya samunsa kai tsaye, na ce ko wurin P.A ɗin sa zamu je, ki gaya masa dan ni ba shiri muke yi da shi, na taɓa marinsa idan mu ka je da ke wataƙila su saurareki”.Cikin ɗoki ta ce “To shikenan, Allah ya sa dai su fito da shi ɗin” ya amsa mata da amin.Hafsa kuwa cike da salo da kisisina, da tasirin sihiri, sai da ta karɓi lambar Alhaji mu’azzam, har bakin department ɗin su ya kaita, sai dai idan zai yi mata magana sai ya kirata da jauhar, sai dai hakan bai dameta ba, lambarsa kawai da ya bata, ya sanya ta din ga jin kamar ta ma riga ta aure shi an gama.Tun safe jauhar ta shirya, ya din ga kiran wayar Walid da ta liti, amma ba ta shiga, tun tana saka ran za su zo, har ta fara sarewa, sai azahar walid ya zo, kamar ta yi masa kuka ta ce “Tun safe nake kiran wayarku, ina jiranka amma shiru ba ta shiga”Walid ya ce “Ai wayar nan ta sa ma kawo ta zaki yi”Cikin mamaki ta ce “Saboda me?””Akwai dalili, yanzu idan kin shirya ki zo mu je can wurin P.A ɗin ki gaya masa, da mun je shiga zaki yi, mun gama magana da wani yaronsa” ta ce “To”Suna tafe tana yi masa magiyar, dan Allah ya kaita ta ga master, amma ya ce “Shi fa ya ce kar a kuskura a kai ki, yanzu idan muka kai ki tijara zai yi mana”.Cikin damuwa ta ce “Haushina yake ji, ba ya son ganina ko?”Ya ce “Gaskiya ba na ce ba, ya ce dai kar a kuskura a kai ki, kuma ranar Litinin zaku fara jarrabawa, ki je ki fara”Mamaki ne ya kama ta, ya aka yi ya san lokacin da za su fara jarrabawa?Tayi ajiyar zuciya ta ce “To yaya jikin sa ya warware?”Walid ya ce “Eh ya warke””Ina nan ina ɗan haɗa ‘yan kayayyakin abinci, sai in baka ka kai masa””Kar dai ki takurawa kanki”Jauhar ta ce “Ban takura kaina ba, amma dan Allah idan ka je ka ƙara bashi haƙuri, wallahi laifina ne ban gaya masa an kawo abun ba, kuma mantawa na yi”Ya ce “Manta kawai, dama Allah ya riga ya ƙaddara faruwar hakan”.Suna zuwa ofishin, ba su wani sha wahala ba, aka shiga da Jauhar, ta gaishe shi ya amsa mata, ya ɗan ƙare mata kallo ya ce “Kamar na taɓa ganinki”Jauhar ta ce “Eh, akwai ranar da na je wurin mijina, na tarar ka je kai da yaya walid an fito da shi a police station”.”Oh matar mai zamani ce, Viper?”Ta jinjina masa kai ta ce “Eh nice”Ya ce “Allah sarki, ya gida ya fama da rigimammen mijinki”Tayi murmushi tana wasa da yatsun hannunta.”Yaya aka yi?”Jauhar ta sauke numfashi ta ce “Dama, mijin nawa aka kama, har an kai shi prison an ƙi sakinsa, shi ne na ce bari na zo wurinka dan Allah ko zaka yi wa honorable magana, ko za a fito da shi”Ya girgiza kai ya ce “Al’amin ba zai canza hali ba, me kuma yayi a wannan karon?””Ba laifinsa bane, abu aka kawo aka ce na ajiye masa, ban san ko menene ba, kuma na manta ban gaya masa ba, jami’an tsaro suka zo suka yi bincike cikin dare, suka kama shi, wai sun ga hodar iblis a cikin kayan”Cikin mamaki ya ce “Hodar iblis kuma? A ina ya sameta?””Ai ba shi ne ya kawo ba, ba ya ta’amalli da ita””Taɓɗijan, a wannan karon case ɗin babba ne, bari na kira honorable duk da ba ya gari”.Ya kira honorable Indabo, ya sakata a hansfree tana jin duk abun da suke faɗa, suka gaisa. P.A ya ce “Honorable, mutumin ka fa ya janyo babbar jagwal ga matarsa nan a gabana ta zo a taimaka mata a fito da shi””Wa kenan?””Ma dogon zamani mana”Indabo ya ce “Kuma dai? Me kuma yayi?””To wai hodar iblis ce, aka kama shi da ita?””What! Coacine? Yaron nan yana da hankali kuwa, a ina ya samu coacine kuma?””To ina zan sani, matarsa dai ta ce ba laifinsa bane ba””Please count me out of this please, haka kurum na je fito da shi, ‘yan adawa su sami na yi mini yarfe, ace nima safararta nake yi? Dama dai wani rashin jin yayi ba wannan ba, ni fa dama Saboda aikina na cin zaɓe siyasa dole sai da irinsu, shiyasa nake fito da shi, amma ban da haka meye haɗina da shi, zan nemi wani ya cigaba da yi mini ayyukana ni babu ruwana”P.A ya ce “A’a honorable, wani kaya fa sai amale, wallahi ba kowane matashi ne yake da ƙwarin da yake da shi ba, kar ka yar da shi wani ya ɗaka””Ka san dai yanzu bana gari ko, dan Allah ka bar ni, ni yanzu lissafin siyasata na saka a gaba, idan ina buƙatar sa a gaba, na fito da shi” ya kashe wayarsa.P.A ya kalli Jauhar da jikinta yayi sanyi, mamaki ya cika mata kai da zuciya, wato yana amfani da jini da lafiyar Al’amin ne kawai dan cimma nasa burin, abun ya bata mamaki sosai da sosai.”Madam, kin ji abinda honorable ya ce, amma ki yi haƙuri zuwa ya dawo, mu gani zan cigaba da lallaɓa shi, kar ki damu da abubuwan da ya faɗa, kansa ne ya ɗauki zafi, amma shi da Aminu ba ta ɓaci, in dai wannan harkar ce, ba shi da sama shi”.Ba ta ce masa uffan ba, ta tashi ta fita, yanayin yadda ta fito ne, ya tabbatar masa da akwia matsala.Ya ce “Yaya? Wani abun yayi miki ko maganar banza yayi miki, na shiga na ci ubansa”Ta girgiza masa kai alamar a a.”To meyafaru?””Honorable ɗin ya ce babu ruwansa, ba zai shiga maganar ba saboda kar sunansa ya ɓaci” tayi maganar hawaye yana gangarowa daga idanunta.Walid ya yi shiru, tare da jinjina kai ya ce “Shikenan, bakomai mu tafi”Haka suka tafi duk jiki a sanyaye, ta ce “Yanzu shikenan babu abun da za ayi? Haka zai cigaba da zama?””A’a zai fito, haryanzu ba a gama shari’ar ba ma, dole za a nemi wata hanyar”.Jauhar ta ce “To shikenan, dan Allah ranar juma’a ka zo ka karɓi kayan da na tara, sai ka kai masa”.Walid ya ce “Shikenan, in sha Allah, amma kar ki je ki saka damuwa a ranki, idan da wata matsala, ki kira ni a wayarki”Ta girgiza kai ta ce “Bani da waya””To ki ara a ta maƙwabta, barinki da wayarsa akwai matsala, haka ya karɓe wayar Viper ya tafi da ita.Ta cigaba da faɗi tashi, wasila ta din ga aiko mata da abinci, sai dai sam jauhar ba ta son hakan.Aka fara exams, sai dai ba ta iya mayar da hankali wurin yin wani abun kirki, wataran kuɗin motar ma gagararta yake yi.Sai dai tana iya ƙoƙarin ta wurin aro jarumta, da ɓoye damuwarta, idan ta shiga cikin ‘yan uwanta ɗalibai.Sannu a hankali ta fito daga harabar makarantar, ta tarar da yaya saifu.Murmushi ta yi ta ce “Yaya saifu, kai ne?”Ya ce “Eh, hau babur ɗin na kai ki gida” cikin murna ta ƙarasa ta rirriƙe shi ta hau, ta ce “Na zo gida sau biyu ban same ka ba”.”Yau ai gani, mu je gidan naki”.Ya ja babur ɗin, ta ce “Allah ya sa ba laifi na yi maka ba, na ganka kamar ranka a ɓace”.Yayi mata shiru, suka ƙarasa gidanta, ta buɗe musu suka shiga.Ta kawo masa ruwa a jug, dan na rijiya yanzu take sha, ko kuɗin sayen ruwa ba ta da shi.”Waliyiyya””Na’am yaya saifu””Meyafaru da mijinki?” Tayi shiru ta ƙi magana.”Ki yi mini bayani ina jinki”Kawai ta fashe da kuka, yayi mata shiru tayi mai isarta, ya koma kusa da ita ya zuba mata ido ya ce “Jauhar, wani irin zama ki ke yi a gidan nan, na san akwai ƙalubale da ki ke fuskanta a gidanmu, amma atleast ai ko ni kya gayawa, sai ji na yi ana zancen an kama shi da cocaine, a tsakar gida ko baba ba ma bai sani ba, da yaya ki ke rayuwa ke kaɗai? Da yaya ki ke samun abun da za ki ci?””Yaya saifu, ni cin abinci ko akasin haka bai dame ni ba, fatana da burina ya fito, ba shi da laifi, ko a yaya yake na yadda shi Allah ya zaɓa mini, ba ya dukana ba ya zagina. Ban san dalilin da ya sanya su mama suka zaɓi na aure shi ba, na karɓi ƙaddarata, na je gidan ai, amma yanayin karɓar da na samu na san ba zan yi nasara ba, kuma ban ma samu baba a gida ba”.”Jauhar, a raba auren nan, ni ban ga alamar za a samu ɗa mai ido ba a auren nan ba, rannan fa cewa aka yi sai da ya zo ya tafi da ke, ‘yan daba za su saraki, wace irin rayuwa ce haka? Ko khul’i ayi a raba auren nan” Tayi shiru ta sunkuyar da kanta.”Yaya ki ka yi shiru? Ko kina son shi ne?”Ta girgiza masa kai alamar a’a.”To kin amince a raba auren?” Nan ma ta girgiza kai.”Ki yi mini magana jauhar, idan kin amince in yi wa baba magana, a raba auren nan””Dan Allah kar a raba, ni dai a fito mini da shi dan Allah”Saifu ya ce “Wai son shi ki ke yi ne?”Cikin kuka ta ce “Idan aka raba auren za ace mini bazawara””To a kanki aka fara? Ba sai ki koma makarantar ki ki yi a tsanake ba?”Ta girgiza kai ta ce “Dan Allah ni dai yaya saifu kar a kashe mini aure, duk abun da yake yi zai daina a hankali, sharri ake yi masa ba ya ta’amalli da hodar iblis” saifu yayi shiru yana kallon ta, ya fara tunanin any ba son shi take yi ba, ya ma kasa gane me take nufi.”Shikenan, ƙyale baban ma, yanzu da an yi magana da shi, sai ya gaya wa matansa, wace kotun ake yi masa shari’a? Akwai wani baban abokina, sai na yi wa abokin nawa magana a san abun yi”Cikin murna ta ce “Na gode sosai yaya, ban san wace kotun ba ce ba, wai ya hana a kai ni, amma akwai lambar abokinsa, da tare muke up and down, ka ga daga nan ma sai mu je na ganshi”.”No, tun da ya ce kar ki je, ba sai kin je ba, duk abun da ake ciki, zan din ga sanar miki, amma ki kwantar da hankalinki dan waliyiyya, tun da kin na ce, ke uwar soyayya Allah ya bar ƙauna, amma wallahi na tsani mijin nan naki”Ta ce “Dan Allah ka daina faɗa, ba zan ji daɗi ba, a din ga yi mana addu’a, ba na jin daɗi idan aka aibata shi”Ya ce “Iyee lallai waliyiyya baki ya buɗe, ki na so dai ki gaya mini ki na son mijinki maybe ma fiye da ni, to wallahi ki fi so na a kansa”Ta ɓoye fuskarta tana dariya ta ce “Wallahi yaya tausayi yake bani kawai, idan aka raba auren nan, akwai damuwa, kuma ina saka ran komai zai zama tarihi in sha Allah”Ya ce “Tafi can, kya ma faɗi gaskiya, kuma ko ba yau ba, kar ki sake wani ma ya san na shiga maganar nan, ai mu na da alfarma shige-shige yayi mana rana” jauhar tayi murmushi, ya bata kuɗi ya tafi.Kusan sati ba ta ƙara jin ɗuriyar saifu ba, ga babu su walid balle ta ji wani abu daga gare su, sai da ta ari wayar wasila, ta kira walid ta ce ya zo ya karɓi kayan da zai kai wa master.Ta saya masa maggi, mai, da sauran ɗan abun da ba a rasa ba, da prisoner zai buƙata.Ya karɓa tare da ƙara bata haƙuri, da ba ta tabbacin, yana nan suna ƙoƙarin fitar da Mijinta.Saifu ya sake komawa makaranta ya sameta, cikin murna ta hau tambayar sa, ya ake ciki?.”Ke mijinki abun da aka yi masa shiri ne kawai, na bibiyi abun ni da abokina, zaki sha mamaki idan na gaya miki an yi wani mugun sara a kan gaɓa, amma ba zan gaya miki ba, in je zaƙin soyayya ya ja ki ki gaya masa ba idan ya fito, ki haddasa husuma, baban abokin nawa yayi magana, sun ce ayi haƙuri ya ƙarasa wata ɗaya, kotu za ta wanke shi ya fito, ashirin da biyu ga watan gobe za a sake shi””Wayyo Allah, yaya saifu kusan watanni uku fa kenan zai yi a prison?””Au baki gode ba kenan?”Jiki a sanyaye ta ce “A’a na gode sosai yayana, Ubangiji Allah ya saka maka da gidan aljanna, to zaka kai ni na ganshi?”Ya ce “Amin ya rabb, yana prison na ciki gari, kuma ban ce ki je ba, kar ki kuskura ki je, kin ji na gaya miki””Amma yaya meyasa?”Saifu ya ce “Saboda haka na ce miki, kuma ke ma kin ce ya ce kar ki je, kar kuma gaya wa wani gashi zai fito shi ma bai sani ba”.Jauhar ta ce “To shikenan, na gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi””Amin ki koma gida, ki cigaba da exams ɗinki, idan da wani abu, ki neme ni a waya, kar ma ki sake zuwa gidan nan da wani batu a kan aurenki, tun da ki na son abun ki ki yi zamanki”Tayi murmushi ta ce “Ban san menene son ba dai yaya, ban san me ake ji ba, da farko dai na san ina jin tsoronsa sosai, amma yanzu kuma tausayin sa nake ji”Yayi murmushi ya ce “Ga kuɗin mota, ki sauka lafiya, yau ba zan je gidanki ba”Ta karɓa cikin murna tayi masa godiya, ta tafi gida.Ta ji sanyi a ranta jin cewar zai fito, sai dai tana cikin damuwa na rashin sanin halin da yake ciki, ya ji sauƙi ko kuwa, yana samun abinci ko kuwa?”Da ta samu kuɗi, take yin sayayya, ta ari waya ta kira walid, ya zo ya karɓa ya kai masa.Sana’a tuƙuru jauhar kamar tayi ƙwace, dama ga azumi yana gabatowa, ana samun ɗinkuna, dan haka tana samun aikin stone da beads, sai dai ba ta iya sakin jiki ta kashe kuɗin, saboda akwai abun da take son yi.Ita ce mayafai, har da su kantu da aya,  haka take saya ta soya ta ɗaura a leda yara na saya.Har guga take karɓar kayan maman halimatu, ta ta da ta yara tayi mata, ta biyata.Sana’oi kamar zata yi ƙwace, duk da ana yi mata mugunta a kan wasu abubuwan, mussman gidan mai ɗinki, da take yi mata aikin stone ta fara yi mata mugunta.Ta ƙara tsananta addu’a, da roƙon Allah, a kan Allah ya kuɓutar mata da mijinta, ya shirya mata shi.Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, saura kwanaki biyu Al’amin ya fito, jauhar ta yi ta gyaran gida, ta ƙara gyara masa ɗakinsa.Ranar da zai fito ɗin, ta yi girki, sai dai kuɗin hannunta ba su da yawa, duk mutane sun riƙe mata kuɗi, dan muɗin hannunta ba za su ishe su kuɗin mota ba ita da shi.Ta dafa ruwa ta zuba a flask, ta shirya tun ƙarfe tara, ta tafi prison ɗin, gashi damuna ta ja baya, an fara wani irin sanyi mai ratsa jiki.Ta nemi shiga cikin prsion ɗin, aka ce mata a waje za ta jira, idan yau za a sake shi, za ta ganshi ya fito.Tana nan zaune, wasu suna ta fitowa, ‘yan uwansu suna ta murna, sai dai shiru-shiru ba ta ganshi ba.Nan hankalinta ya tashi, ta sake nufar wurin masu gadin ta ce “Wai haryanzu ban ganshi ba, kuma yau aka ce mini za a sake shi””Waye ya ce miki za a sake shi?” Wani gandiroba ya tambayeta.”Yayana ne””Yayan naki alƙali ne? Ko shi ya kawo shi nan ɗin, wanda zamu saki kenan yau sun gama fitowa””Innalillahi na shiga uku” ta faɗa a raunane.

Ayshercool 08081012143

Back to top button