Hausa novels

Zakuna Biyar Page 19 By Princess Teema

Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa game da sunkuyar da kai suka gaida Dr’s ɗin cikin girmamawa. Hannu Dr Mark ya ɗaga masu alamar sun ji kafin su wuce ba tare da yi masu magana ba. Miƙewa nurses ɗin suka yi suna binsu da kallo har suka kurewa ganinsu, dawo da kallonsu a kan juna suka yi, ɗayar ta ce. “Sister Maya kin san wani abu ne?”…….. Kai Maya ta girgiza alamar a’a bata sani ba. “Dr James ya haɗu over, kin san da cewa son gaske nike mashi?”. Ta faɗa tana ɗan ciza laɓɓa……… “Sister Zinta i think ai kin same shi kin gama, ko bake kika ce mun ya yi inviting ɗinki zuwa waiting toom ɗinsa a yau da yamma ba?”. “Haka ya ce in same shi a waiting room ɗinsa bayan tashi daga aiki, amma kuma ai ban san dalilinsa na kiran nawa ba! Maybe ma wani aikin zai sanyani, kin san shi baya rabuwa da sanya mutane aiki”. Ta kai karshen maganar tana ɗan tura baki a cikin mask ɗin.”Amma ai idan aiki ne baya taɓa cewa a same shi a waiting room kai tsaye haka, sai dai office, ni a nawa ganin kamar ya kyasa dake ne, in kuwa haka ne ki shirya faɗa da sister Lazy, dan ba zata taɓa yarda wata ta raɓesa ba”…….. Siririn tsaki sister Zinta ta ja tare da wucewa gaba tana faɗin. “Idan har na samu hankalinsa ya dawo kaina wacece kuma wata Lazy? Ba dik taƙamar da take mana da nuna ta fimu ɗin saboda shi yana kulata bane? Dame ta fimu? Kada ki manta ita ma fa ɗalibar lafiya ce kawai kamarnu”. “Uhm ni dai ina ji maki tsoron balainta, dan mafaɗaciya ce”……… “Ita ɗin banza, dik taƙamarta dan tana aiki a karkashin office ɗinsa ne, shiyasa nima na zage ina son komawa karkashin office ɗin nasa”. Maya zata yi magana daga bayansu suka ji an ce. “What are you doing here at this time da yakamata ace kuna bakin aiki?”…….. Da sauri suka juya, wata malamar lafiya ce dai kamar su, tana sanye da kayan aikinta, kana ganinta kaga irin masifaffun nan masu zubin taliya ƴar murji, idanun nan a tsaitsaye, gashin idon kamar wacce aka shuka shinkafa a ƙasa, suna tsaye zara-zara ga tsawo. “Sorry sis Lazy”. Suka faɗa a tare suna haɗa baki kafin su wuce su cigaba da tafiya zuwa in da zasu ce. Can ƙasa sister Maya ta ce. “Bana faɗa maki ki guji balain sister Lazy ba, kina ganinta tamkar wacce ake yi wa loading na masifa a kanta kowacce rana, kullum da sabon salon balain take zuwa”. Cike da tsoro Maya ta karisa maganar.”Sai kuma ta yi, kawai yanzu inai mata biyayya ne saboda a karkashin office ɗin Dr James take aiki, amma ba wai dan ta fini da wani abu ba”. Sister Zinta ta faɗa……… Suna tafiya suna hira har suka shiga wani sashe a cikin hospital ɗin. Wani glass room suka shiga mai ɗauke da tarin chemical dayawa, an shisshirya chemical ɗin a cikin transparent glass, kowani chemical da sunansa a manne a jikin kwalbansa. Lap gown and hand gloves suka sanya a jikinsu tin daga bakin kofa kafin su karisa cikin wajen, ga tarin computers daga gefe dayawa, kayan gwaje-gwaje suma akwaisu dayawa a ciki. One thing about sister Maya and Zinta, dik cikin W-S-HOSPITAL ɗin nan sun fi kowa hakuri, hankali, natsuwa, kamala, kame mutunci da kuma kula da kansu, basa da faɗa, basa zuwa wajen hayaniya, akwai girmama manya, akwai tausayi da sanin darajar ɗan adam, sai dai kuma akwaisu da balain son yara, dik in suka ga yaro rasa natsuwarsu suke yi, su yi ta faman ɗauka, sun taɓa ganin jariri a hannun sister Lazy, suka dinga rokonta ta basu su rike, har da durkusawa ƙasa suka yi mata, ta ce masu babyn Dr mark ne, in suna so su je su rokesa, in ya yarda a basu to zata basu su rike.Su kuma suna balain tsoron waɗan nan 3 doctors ɗin, dan haka suka hakura, amma har ruwan hawaye sai da suka yi, rauninsu shi ne yara. Wasu kyawawan ƙananan transparent glass bottle suka ɗauko, a cikin wani katan baff, suka zauna a saman wasu chairs dake gaban manyan glass na chemical ɗin, a hankali suka fara ɗibar kowani chemical suna aunawa suna zubawa a cikin bottle ɗin daidai misali, sai sun auna kilonsa kafin su shirya shi cikin kwali, idan kwalin ya cika sai su ɗauka izuwa wajen da ake shirya chemical irinsa su hau shiryawa cikin glass ɗin. Sun sanya eye protection a idanunsu kafin su fara aikin, suna yi suna hira a in da sister Maya ta ce. “Kin san wani abu sister Zinta?”…… Kai ta girgiza a lokacin da take ɗibar nata chemical ɗin. “Ina son DR MARK sosai, yana burgeni, amma ban san meyasa yake mugun bani tsoro ba, ko motsinsa na ji sai hantar cikina ta kaɗa”. “Uhm watarana komai zai wuce, mu dake mu yi aiki tukuru mu koma karkashin office ɗinsu, kin san basa ɗaukar wanda ba kwararre ba a karkashin office ɗinsu, shiyasa kika ga na kara dagewa dan in zama irin nurses da suke aiki tare da su, kamar dai wancan fitinanniyar Lazy, amma ke ina ga tsoron matar DR MARK kike ji shiyasa kike shankarsa over har haka”………………… “Hmmmm, bana tsoron matarsa, saboda ban taɓa ganin tana masifa ko wani abin mara kyau ba a cikin makarantar nan. Ni babban abin takaicina ma shi ne yadda basa ɗagowa su kalli mutum”. Zinta da shegen son gulma ce tai ƙasa-ƙasa da murya wajen cewa. “Kuma na ji an ce Dr James har hugging na Lazy yana yi, har kiss da sauransu”………. “Ina fatan shiruna ya zame mun alkhairi”. A cewar Maya da bata cika son zaman gulma ba, dan ma dai Zinta best friend ɗinta ce yasa idan tana gulma bata tashi ta bar wajen, amma tana ƙoƙarin hanata gulmar, banda haka ita ba’a gulma da ita, kunji ta ce tana fatan shirunta ya zame mata alkhairi, dan tasan abin da Zinta bata sani bane, abin da ya fi kiss Dr James yake yi da Lazy, amma ba zata faɗa ba ko dan ma kada zuciyar Zinta ɗinta ya buga.”Matsalata dake kenan Maya, komai sai ki ce kina fata shirunki ya zame maki alkhairi, to da kike wannan magana wani zanje in faɗawa ne? Ko dai kina tinanin wani na jinmu ne?”…… Kai ta girgiza tana cigaba da gwada chemical ɗinta, a natse ta amsa da. “Ba wani zaki faɗawa ba, kuma babu mai jinmu, kawai dai manta da maganar, ya batun shirin partyn da zamu yi next month na kammala karatun ajin farko?”. “Na shirya mashi, amma kin san idan na tina karatun aji na biyun da zamu shiga aka ce ya fi kowanne wahala gabana faɗuwa yake yi? Ina jin kamar ba zan iya ba, yanzu wannan karatun ma da ya muka kare? Wahala kan wahala”……. “Zaki iya ƴar uwata”. Ta faɗa cike da ƙoƙarin kwarara mata gwiwa…… “Ina sa ran na iya sosai”……. Da haka suka cigaba da hira suna shirya chemical ɗin nan har suka kammala, sannan suka fito, a lokacin yamma ta kawo kai, karfe 5 suke tashi daga aiki sai su koma wajen kwanansu na ɗalibai, za su shiga class daga 7 na safe zuwa 1 na rana, da sun fito zasu wuce wajen practical, karatunsu ba kamar na sauran likitoci bane, su special ne, suna karatu ana haɗa masu da aiki kullum dan su kware.Kamar yadda AZURE BARRACK take yaye jami’ai gifted haka WS-HOSPITAL take yaye likitocin da babu irinsu a duniya, mayun bincike mayun aiki tamkar ba ƴan adam ba, a yanzu ba zaku gane komai ba, sai tafiya ta yi nisa damu a cikin WS-HOSPITAL zaku fahimci karatun! Mu je zuwa ku dai.A lokacin da suka fito wajen lap ɗin almost 5:20, a gurguje suka yi shirin tashi, suka cire lap gown na jikinsu da hand glove ɗin, sannan suna shirya tsab. Dawowa wajen sashen su Dr James suka yi, a nan Sister Zinta ta ce. “Maya mu je ki rakani waiting room na Dr James”………. “Kin san halinsa ƙawata, shi baya son ya ce abu a saɓa mashi, ke kaɗai ya kira, idan ya ganmu tare ransa zai ɓaci, kinga hakan zai sa ma ki rasa damar da yake son baki, ba zan so ki rasa wannan dama ba, ki je ke kaɗai kin ji? Zan jiraki a section B”.Ta san maganar Maya gaskiya ce, ba’a mashi abin da bai ce ba, amma tana mugun tsoron zuwa ita kaɗai ne, dan shakkarsu take ji. Cigaba da kwarara mata gwiwa Maya ta yi har ta yarda zata tafi ita kaɗai, tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi waiting room ɗin nasa dake gefen office ɗinsa, kafin ka shiga office ɗinsa kofar room ɗin yana daga gefe. Ciki ta shiga bakinta a ɗauke da excuse.Babu kowa a ciki sai wani irin ni’imantaccen kamshi dake tashi, ga sanyin Ac dake buga ko’ina, sofa set set guda ɗaya ne a cikin room ɗin, a tsakiyar sofas ɗin akwai wani lallausan Dubai rug a wajen, sai karamar dispenser, sai kuma wata karamar freezer daga gefe dan zuba drinks su yi sanyi, ga kuma wata karamar show glass mai ɗauke da glass cups masu kyau kuma very luxury. Ɗakin dai ya haɗu sosai.A saman sofa ɗaya ta zauna, tin da suke basu taɓa shigowa sashen su Dr James ba, dan su aikinsu a wajen Chemicals yake, ta wannan ɓangare suka fi kwarewa, sai sun je aji biyu zasu koma sashen dabbobi, daga sashen dabobi dama sai babban sashe watau na su Dr James. Zaman good 30 mins ta yi, sai faman tinane-tinane take yi da kalle-kalle, ta yi tinani ya fi dubu kan dalilinsa na kiranta, amma ta rasa gane dalili, sai kawai ta yi shiru. Ta gaji da zama da zuba idon ganin shigowarsa, amma shiru, sai a lokacin da cire tsammani, ta shiga wata tinanin, ta manta da zai shigo sai ta ji an turo kofar room ɗin. Tin daga ƙasa ta fara kallonsa, yana sanye da sportswear ba kayan aiki ba, da alama ya ɗan jima da tashi aiki, still fuskansa da nose mask, and ya ɗaura jacket a kan kayan saboda wani irin fitinannen sanyin da ake zubawa, kafarsa sanye da ankel socks and crops farare. Ai yana shigowa ta miƙe tsaye a wani irin slow tana kallonsa, kowani motsi nasa a kan idanunta. Dr James irin mazan nan ne masu burge mata da shiga rai, ga shi da salo ɗan gaye. A saman sofa ya kariso ya zauna, sai da ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya gama shan kamshinsa kafin ya ce. “Get out of my office!”. A ɗan kaifafe ya faɗa, saboda ya ji haushin yadda ta kara 30 mins a kan lokacin da ya bata, shiyasa bai shigo da takardun da zai bata ɗin bama, ya ga lokacin da ta shigo ɗakin ta Camerar dake ɗakin, karfe 5:30 ta shigo, shi kuma 5 yasan suke tashi, kuma 5 ya ce ta zo ta same shi, shi ne zata ɓata mashi lokaci, ba zai ɗauki wannan iskanci ba. Tsoro da shakkarsa yasa bata yi ƙoƙarin bashi hakuri ba, da sauri ta wuce ta fita. Tana fitowa suka ci karo da sister Lazy dake ƙoƙarin shiga office ɗinsa hannunta rike da tarin files na manyan ayyuka dana rahotannin dabbobi. Tana ganin sister Zinta ta fito daga waiting room ɗinsa ta dakata tare da juyowa gareta, sai dai kafin tai mata magana Zinta ta wuce da gudu tana ƙoƙarin toshe bakinta saboda wani irin kukan da yake shirin kubce mata, ta ji zafin rasa wannan dama, tin bata wuci 16 years ba take dakon wannan dama, shekara biyu kenan tana aiki tukuru dan ta samu attention ɗinsa, yau ta samu amma ta sake rasawa, dole ta ji zafin wannan abu. Da gudu ta nufi in da zata samu Maya. Zaune ta iskota rike da wani littafi tana dubawa. Da gudu ta zo ta ja hannunta tana faɗin. “Sister mu je”….. Maya na shirin tambayarta lafiya, amma ganin tana kuka yasa ta fasa tambayar tata tare da miƙewa kawai ta bi bayanta. Da gudu suka wuce sashen kwanan ɗalibai dake can nesa da lap ɗin, kuma shi ne section A a wajen, na ce maku sashe 5 ne a cikin wajen, sashen kwanan ɗaliban lafiya shi ne section A, sashen dabbobi shi ne section B, sashen chemical shi ne section C, akwai section D da section E wanda labari bai isar damu wajen ba bare mu san me a cikinsu.Da gudu suka koma hostel ɗinsu. Ita kuwa sister Lazy da sauri ta shigar da takardun office na Dr, jikinta har tsuma yake wajen yin gaggawar fitowa ta bi bayan sister Zinta dan ta je ta ji me ya haɗata da Dr James da har zata shiga waiting room ɗinsa kuma ta fito tana kuka, ko dai akwai abin da yai mata ne?.Kai tsaye sashen kwanan ɗalibai Lazy ta nufa, sai huci take yi, dan a duniya idan ana son aga fushinta wata ta raɓo Dr James, a cewarta zata iya kisa a kansa. A lokacin da ta shiga room ɗinsh suna zaune sister Zinta na faɗawa Maya abin da ya faru sai ganin Lazy a kansu suka yi, cike da tsoro suka mimmiƙe tsaye, ɗaure fuska tamau Lazy ta yi, in a harsh way ta ce. “Ke me ya kaiki room na Dr James?”……. Tsuru-tsuru da idanu Maya ta yi, dan akwaita da tsoro sosai, gara ma sister Zinta da ɗam kwarin zuciyarta.Hannu tasa ta goge hawayen dake zuba mata, cikin girmamawa ta ce. “Shi ne yai inviting ɗina zuwa wajen……..”. Bata iya karisa maganar ba sakamakon wani bahagon marin da Lazy ta sauke mata, cikin fushi ta ce. “Ke har kin isa Dr James yai inviting ɗinki zuwa wajensa? Wacece ke? Dame kike taƙama?”.Note, yauwa na ji kuna cewa dikka malaman asibitin nan kamanninsu ɗaya, ba haka na ce ba, ce maku ma yi suna ɗan kamanceceniya, amma kowacce da irin halittarta da kuma yanayin kamanminta, kyan fuskarta da kyan jikinta, ko yanayin hasken skit ɗinsu ya bambamta, kawai dai shekarunsu ne dikkansu ɗaya watau 18 years, in da suke kamanceceniya kuma shi ne yanayin jiki, ƴan caras-cas dasu zubin ƴar tsana na ce maki.Dafe kuncinta sister Zinta ta yi, idanunta suka kara kawo ruwa sosai, bata da bakin iya ramawa saboda sister Lazy a karkashin office ɗinsu Dr James take, dole ne su yi mata biyya. Zazzaro fararen idanunta Maya ta yi, tana son ja da baya sister Lazy ta cakumo wuyar rigarta, cikin faɗa ta ce. “Kece kike zugata ta shiga gonata ko? An faɗa maku Dr James mara aji ne shi da zai kula irinku? This should be the first and last da zan sake ganinku a arear da yake, ku ba a section B kuke aiki bama? Me ya kaiku side ɗinsu?!”. Ta faɗa tana shaƙe mata wuya.Gagara amsa mata suka yi, cakumo wuyar rigar Zinta ma ta yi, tsabar mugunta ta haɗa kansu ta gwara da juna kafin ta ce. “Dik wacce ta sake shiga gonata sai na lahira ya fita jin daɗi!”. Su kuwa tsabar tsoronta babu wacce ta iya koda kara ne, dik da sun ji zafin buga masu kai ɗin da ta yi, amma suka shanye har sai da ta gama zazzaga masu jajjagen balain nata, ta kwashi kafafunta mai kama da na sauro ta nufi waje fuuuuu, sannan ne suka zazzauna a gefen bed ɗinsu tare da rushewa da kuka a tare. Sai da suka yi mai isarsu suna luguiguita gaban goshinsu, sannan ne suka yi shiru, suka rungumi juna cike da takaici da danasanin zuwa side ɗinsu Dr James. Almost 30 mins suna a haka kafin su miƙe zuwa toilet ɗinsu, abinku da ɗaliban lafiya, ko’ina a cikin toilet ɗin nasu tsab-tsab har sheki yake yi, fuska suka wanke a wajen wash hand base, sannan suka fito, saman gado suna koma, kowacce ta fito da littafanta ta fara nazari kan Chemicals da suke karanta a yanzu, babu wacce ta sake cewa ƴar uwarta uppan suka shiga karatu. Ita kuwa Aunty masifatu kanwar jarabatu watau sister Lazy kai tsaye room ɗin Dr James ta nufa tana ta wani uban huci, ran ƴan mata ya ɓaci. TO MY PEOPLE ME KUKE TINANI A WANNAN ƁANGARE? MU JE ZUWA!.CRYSTAL PALACE.🔥Zaune Seraphina take a saman gadonta, tana rike da waya tana dannawa, ta shiga world live a wayar tana dudduba labaran duniya dan jin me yake gudana. Lokaci guda ta zunduma ihu tare da miƙewa tsaye. Da gudu Madam da ɗiyarta Aisha suka shigo dan jin meyasamu Seraphina take ihu kuma, a tsakiyar gado suka iskota tana murmushi ta kurawa waya ido, cikin kiɗina Madam ta ce. “Babyn daddynta lafiya? Wannan ihun fa?”. Da gudu ta diro ta zo ta rungumi Madam tana faɗin. “Mom ki zo mu yi murna, ana hira da Admiral, my hero, jarumin da babu biyunsa a duniya, kinga hira da shi ake yi a kan IRON FIST ɗin nan da suka addabi al’umma, an miƙa masu case ɗin ne su kamosu, mom admiral basu taɓa karɓar aiki kuma su faɗi ba, yanzu karshen IRON FIST zai zo, zasu daina ta’addanci da kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba”. Dik a kiɗime take magana tana haɗe words, daɗi yasa bata san ma me take faɗe ba.Kun san waye wannan da Seraphina ta ruɗe a kansa? Gaskiya bai taɓa karɓar aiki kuma ya faɗi ba, kwararre ne, jami’in SEAL U.S Special Operations ne, idan ana maganar Seal a waje to ba’a kiran dik wani jami’i, Seal yana nufin SE Sea ruwa kenan, A Air sama kenan L Land kasa kenan, a takaice SEAL na nufin Sea, Air, and Land. Su ɗin sojoji ne da ke iya yaƙi a ruwa, sama, da ƙasa, Su ne ƙwararrun sojojin U.S Special Operations da aka basu horo mai tsanani sosai da babu biyunsu, su zasu iya aiki a kowanne irin muhalli, teku, kogin, bene, cikin ruwa, kan ƙasa, da kuma ayyukan da ake tsallaka cikin jirage ruwa da sama, ba kamar sauran sojoji suke ba, a sauran sojoji zaku ga na ruwa daban, na ƙasa daban, Air Force ma daban, kuma kowannensu da irin horon da ake bashi, to su haɗe masu horon dikka ake yi a masu, imagine! Baa ɗaukar mutum horon Seal sai idan ya karɓi horon aikin soja, dan haka kawai ba zai iya karɓar horon seal ba, ba kowa yake iya haye horon ba ko da ya karɓi horon soja, za’a ɗauki mutane 50 amma da kyar 5 suke iya hayewa basu mutu ba, a horon suke mutuwa, manyan tekuna ake jefasu a masu horon sojojin ruwa, sanna a masu horon sojojin sama, azo a masu horon sojojin ƙasa, ga training na sirri da ake basu kan kwarewa a ɓangaren fasaha da sarrafa computer, wlh dik US su ne jami’an da babu biyunsu, kuma basu da yawa saboda ba kowa yake iya tsallake horonsu ba.To shi wannan guy da Seraphina take haukar cewa yana burgeta shi ne O-9 Vice Admiral na Seal Special Operations, mutum ne da babu wanda yasan fuskansa, kullum suna sanye da covering nose mask, kuma idan ba babban aiki irin kama IRON FIST ba ba zaku gansu a hira da wasu ba, basa shiga jama’a saboda suna ɓangaren jami’an sirrinsu ne, shiyasa basu bari an san face ɗinsa ba.Su uku ne mafiya kwazo a hukumar Seal, wanda matsayinsu yake tafe a jere. Da O-10 Admiral mai matsayi kaman ace GAT a hukumar sojan ƙasa, sai O-9 Vice Admiral mai magana a wannan hira ta yanzu da Seraphina take gani, sai kuma O-8 Rear Admiral upper half, su ukun nan daban suke, kuma ba’a taɓa kallon complete face ɗinsu ba, tin Seraphina bata yi wayau sosai ba take kaunarsu a jami’an Seal, dan time to time tana bibiyarsu a wayar mom ɗinta, tana mugun son jarumai ne yarinyar.Amma kun san wani abin mamaki? Wannan da ake live da shi ɗin fa ba kowa bane face Aryan, a idanun duniya su ne seal, a bayan duniya sune IRON FIST, yanzu gwamnati ta gagara kama IRON FIST shi ne aka damƙa masu case ɗin, dan an san dik US babu jami’ai masu aiki da cikawa biyun, to my people ya kuke ganin wannan wasa zata kaya? Zasu gagara kama IRON FIST ne su zamana karo na farko a rayuwansu sun faɗi a mission? Ko kuma zasu kama kansu ne a matsayinsu na IRON FIST? Ga shi dai sun karɓi mission ɗin, sun kuma rattaɓa hannu! Me kuke tinanin zai faru? Zasu yi aiki da basira a wannan ɓangaren ne ko kuwa dai ya zasu yi?.IRON FIST a bayan fage, US SEAL SPECIAL OPERATIONS a idanun duniya, jami’an da duniya ke girgiza da jin sunansu, gaskiya su Lion akwai ƴan rainin wayau, to yanzu ya zasu gudanar da wannan mission fisabilillahi? Gasu can a AVARIS suna gudanar da bincikensu a kan aikinsu na IRON FIST, sun hau live sun sanar da sun karɓi aikin kama IRON FIST, kai ana wani iya shege a littafin FIVE LIONS, nima zan so ganin ta yadda zasu kama kansu kam!.Da yake dik wanda ya kwana a Us ya tashi yasan su waye Seal Special Operations (SSO) bari in taƙaita masu sunan, kowa yasan su waye jami’an SSO, hakan yasa Madam ta ce. “Kai Alhamdllh, lokacin kawo karshen waɗan nan IRON FIST ɗin ya yi babyn daddynta”. Matsawa Seraphina ta yi, ta shige jikin Madam tana gwada mata yadda SSO suke magana a live, live ɗin da ya tara manyan jami’ai daga sassar duniya, manyan shugabanni, kowa kawai burinsa yai magana da su, su kuma da Aryan ne da guru a wajen suke magana, Lion yana barci, bai ma san ana yi ba, kuma shi ne admiral ɗin da ya rattaɓa hannu a kan misson na kawo karshen IRON FIST a duniya, amma kunga ɗan duniyan barcinsa yake hankali a kwance, sun je yawo ne suka dawo, yanzu ba jimawa dawowarsu daga Arewacin ƙasar Avaris, sun je binciken da suke yi ta bayan fage, dik a gajiye ya dawo shiyasa yake barci.Idanu Madam ta zuba tana ganin yadda manya ke magana, idan Aryan zai yi magana sai kowa ya haɗa natsuwansa, gasu ƴan gayu ne ƴan kwalisa, akwai shegen iya ɗaukar wanka su ukun nan, kuma kaya iri ɗaya suke sanyawa, komai ɗinsu iri ɗaya, zo ku ga yadda ake magana cike da jarumta ga sharp voice, sannan ga class da tsantsar natsuwa sai IRON FIST. Da sauri Seraphina ta ce. “Mom ki bani wayarki in kira daddyna in faɗa mashi ya kunna world live ya ga SSO suna magana, bana son kiransa da wayana dan kada live ɗin ya katse, ina son in faɗa mashi kuma ina kallon live”. Da yake na faɗa maku dikkansu fuskokinsu a rufe sai bata gane Aryan ba, kuma iya face ɗinsu ne a Camera, sannan suna sanye da p-cap daga shi har gurun. Ita ma Madam bata gane Aryan bane, da yake ita dama bata san ainahin face ɗinsa ba, Seraphina kawai ya nunawa, idan zai shigo gidan kuma shi yasan hanyar da yake shigo kai tsaye sai room na Seraph kaman wani aljani.Da sauri Madam ta bata wayar, shigar da number Aryan da ya bata ta yi, jikinta har yana rawa wajen shigarwa, sai ta ga ashe Madam tana ma da number, danna mashi kira ta yi. Suna tsaka da live ɗin sai ta ga vice admiral ya miƙe tare da barin wajen, turo baki ta yi tare da cewa. “Mom ina vice zai je?”.”Kai babyn daddynta akwaiki da rigima, to gama wayar mana sai ki fara neman jin ina zai je”. Madam ta bata amsa cike da mamakin halin Seraphina da shegen son jaruman mutane…… Tin ɗazun Aryan ya yi picking call ɗin yana jinta tana zubawa Madam shiriritarta, da ya ga alamar ta mance da ta kirasa sai ya ce. “Baby what’s going on?”. Murmushi ta yi tare da ƙara manna wayar a kunne da kyau, cike da farinciki ta ce. “Daddy ka kunne wayarka ka duba Us military world live yau my hero’s suna live”…… Mamaki ne ya kama shi, shiru ya ɗan yi kafin a ransa ya de. “Blood is thicker than water, watau Seraphina bata sansu bama sonsu take yi, bata taɓa ganin Lion and Guru ba, amma suna cikin ranta sosai, bare shi da ta san face ɗinsa, tana tsananin son shi sosai, ALLAH mai iko.Sayayyar voice ɗinta ne ta katse shi da cewa. “Daddy baka jina ne? Please ka je ka gansu, jarumai ne, zasu kawo mana karshen IRON FIST masu kashe mutane fa”…… Face ɗinsa ne ta ɗan canza, a sanyayye ya ce. “Baby baki son IRON FIST ne?”…….. Da sauri ta gyaɗa mashi kai tare da cewa. “I hate them daddy, mugaye ne, suna kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, daddy su fa suka kashe mom and daddyna, don sune terrorists na ƙasar nan, nasan for sure su suka kashe mammyna!”. Ta kai karshen maganar idanunta na cikowa da kwallah. “Is okay baby, Don’t cry, I agree that you don’t like IRON FIST, but don’t cry over them, I’m going to hang up now, I’ll call you back later, I’m doing something right now”. Ya kai karshen maganar da alamar damuwa a tattare da shi, bai ji daɗi ba yadda kowa yake masu kallon manyan ƴan ta’adda. “Daddy make sure you watch the live ka ji?”……. Da sauri ya amsa da okey tare da katse kiran. Nisawa yai tare da ɗan jingina da jikin sofar parlon ɗakin da suka kama, yai shiru yana tunanin kukan Seraphina, da yanzu yana CP babu abin da zai hana shi zuwa gareta ya rarrasheta, yasan sai ta yi kuka tin da tai maganar iyayenta, shiyasa yai saurin katse kiran dan kada ya ji kukanta, yasan Madam zata rarrasheta shiyasa bai damu sosai ba. A fili ya ce. “Zayra’an baka yi wa Seraphina adalci ba ko kaɗan, me laifinta zaka ce baka sonta a kusa da kai? Ka manta hakkinta dake kanka? Ka manta ita ɗin amana ce a kanka da ALLAH zai tambayeka ka rike amanar? Ya ka yi da ita? Gaskiya baka kyauta ba!…..”. Jin motsin fitowa ne yasa yai shiru tare da ɗago kai ya kalli kofar shigowa, guru ne ya fito yana zura hannayensa a cikin aljihun pj’s ɗin jikinsa. A kusa da Aryan ya zauna, cikin natsuwa da sanyin murya ya ce. “What are you thinking bro?”. Ɗago idanu a kansa Aryan ya yi tare da cewa. “Nothing, ka gama magana dasu ne?”…… Kai ya jinjina alamar yeah, sannan ya ce. “Bro akwai gagarumin matsala a arewacin Avaris, musamman da muka je barrack na arewacin ƙasan, wai menene banbancin arewaci da gudancin ƙasar? Meyasa commond hukuncinsu daban-daban, kundin dokoki jahohinsu da hukuncinsu daban-daban, meyasa? Horon sojojinsu daban-daban, a barrack na gudancin nan ka duba yadda suka hora su Nirash! Komai a wadace, ga tsari da muhalli mai kyau, meyasa barrack na arewaci da yunwa ma ake hora sojojin? Abinci kaɗan za’a basu sai dai su kira iyayensu daga gida su tura masu in suna son ci su ƙoshi, ga wahalar horo, ga rashin muhalli mai kyau, gabaɗaya barrack ɗin sai a hankali bare kuma ɓangaren wajen kwanan ƙananan sojoji, makamansu tsofaffi matattu, horon ma ba cikakken horo ake basu ba face azabtar da gangar jikinsu, meyasa komai ya banbanta? Ko kuɗin da ake baiwa sojojinsu ya banbanta, salarinsu ɗaya, but why allowance ɗinsu yake banbanta sosai? Meyasa danger allowance, ration allowance, operation bonus na sojojin kudancin ƙasa ya banbanta dana arewacin Avaris? Barrack na kudancin ƙasar ka kalli yadda su Nirash suka rayu a ciki, cikin gata da kulawa, wasu sashe har AC ne da su, wajen kwana mai kyau, sojoji su rayu da kwargo da samun kula, ga natsuwa da sanin aiki, suna samu horo matuƙa, amma barrack na arewacin Avaris komai a lalace, dubi irin gadon da su Nirash suke kwana a kai a nan, to dubi irin gadajen dake barikin arewacin ƙasar! Komai a lalace cikin wahala da ƙunci. Hankalina ya yi mugun tashi sosai bro, kuma a haka ƴan arewacin suke rayuwa?”. Shiru Aryan ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya ce. “Gudanci basa tsoron mutuwa! Basu yarda a takasu ba! Sun san ƴancin kansu! Ba dai a cikin mission na su Nirash uku a kudancin ƙasan ɗaya a arewaci bane? Ga jira lokacin a nan ne zaka gane menene dalilin dikka wannan banbanci”……. Cike da mamaki guru ya ce. “Me haɗin mission na su Leo da banbancin dake tsakanin Arewacin Avaris da kudancin ƙasar?”. Ciro wayarsa Aryan yai tare da yin playing na voice ɗin Seraphina dake waya da Rimsha a yanzu kafin ya amsa. “A cikin wannan mission ɗin zaka gane ainahin gaskiya, a nan zaka fahimci daga ina matsalar arewacin ƙasar ta fara ta kuma samo asali, yanzu dai ba sun je yaki da ƴan ta’addan dake haurowa kudancin ƙasar suna samu mafaka ba? To ka jira su juya mission kan arewaci zaka gano komai, dalilin kenan dayasa Lion ya ce kada mu sanya baki a mission ɗin, dan akwai abin da yake dubawa a mission ɗin”. Shiru guru yai yana nazarin kalaman Aryan, lallai kuwa yanzu ba zai gane komai ba, sai su Leo sun juya Mission a kan arewacin Avaris. Nima na ce a yanzu ba zaku gane komai ba, amma mu je zuwa zaku gane.Miƙewa Aryan ya yi tare da nufar kofar fita yana cigaba da sauraren su Seraphina, yaran nan sai shirin ALLAH, hira suke yi sosai kan SSO, Rimsha ma ta ce ai ita babbar fan ɗinsu ce, musamman Admiral wanda ni da ku readers muka san shi da Lion kuma Zayra’an, sun mutu a kan SSO yaran nan, sai bawa Seraphina labari Rimsha take yi kan ranar ma SSO sun yi live da jami’an Paris, ta bibiyi live ɗin, har da cewa zallar ilimi da jarumta ce kawai yake magana a wajen.Seraphina ta ce. “Ni dai bana banbantasu tin da kullum da fuskokinsu a rufe, kawai dai nasan ina son SSO gabaɗayansu”…. Rimsha ta amsa da. “Nima bana banbantasu, kawai dai nasan su uku ne, kuma dik ina kaunarsu, kin san dama jami’ai irinsu basa nuna fuskokinsu ga duniya saboda sun fiye yin aikin sirri, shiyasa suke nufewa, dan suna shiga ko’ina yin aiki, idan al’umma ta shaida kamanninsu ai kinga akwai matsala ko?”.Seraphina ta amsa da. “Haka ne, suna da hujja ɓoye kamanninsu wa duniya, amma ina fatan ganin face ɗin ko ɗaya daga cikinsu ne ko sau ɗaya a rayuwata”…… Dariya Rimsha ta yi kafin ta amsa da. “Baki da hankali my star lady, a ina zaki samu damar ganinsu? Ki dai cigaba da yi masu addu’ar ALLAH ya cigaba da karesu yana dafa masu a dik in da suke”. My people wai na ce ya kuke tinanin Seraphina zata yi a ranar da zata gane cewa daddy Aryan ɗinta ne ɗaya daga cikin SSO? Ya Rimsha zata ji idan ta gane uncle Aryan ɗinsu SSO member ne? Ya zasu ji ranar? A gefe guda kuma sun tsani IRON FIST, kai akwai cakwakiya fa, ku dai mu je zuwa. Ba ƙaramin daɗin sauraran hiransu Aryan yake ji ba, sai ma idan Seraphina ta yi magana tana ɗan shagwaɓe muryan nan, dik rasa kansa yake yi, sai ya ji tamkar ba’a duniya yake ba, tsabar daɗin hirarsu da yake ji har ya fito daga hotel ɗin bai sani ba, yana ta tafiya kawai abinsa. Da Seraphina ta ce. “Rimsha do you know something?”. Rimsha ta amsa da aa. Seraphina ta ce. “Ina jin daddyna a raina sosai, tin shekaran jiya bai zo wajena ba, ina kewansa sosai, and bana son in ce ya zo saboda mom ta ce in daina takura mashi da yawan cewa ya zo zai daina sona sosai, amma ina cikin damuwa sosai, shi kuma yaki zuwa ban san meyasa ba”. A shagwaɓe sosai ta karisa maganar.Ai sai ga malam Aryan ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman hair ɗinsa yana watsawa, yana jin wani irin nishaɗi na musamman, kai shi kansa ba zai iya faɗa maku a wace duniya yake ba, ga shi sai tafiya yake ta yi ba tare da yasan in da ya dosa ba……. Rimsha ta amsa mata da. “Kawai ki kirasa ki ce kina kewansa, ai tin shekaran jiya ne bai zo ba, kinga ko mom ɗin ce nasan in kika faɗa mata ba zata hanaki kiransa ba tin da an jima, kawai ki kirasa”. Ta amsa mata cike da son sanin tarihin Seraphina, ta san dai Madam ta ce mata marainiya ce bata da iyaye, to waye wannan daddyn? Gara mom da take cewa Seraph ta faɗa mata Madam Rohisha ce, amma dik da haka tana son sanin tarihinta, amma ta gagara tambayarta. Da sauri Seraphina ta ce. “I remembered something Rimsha, kin san da cewa daddyna yana kama dake? Your eyes and lips iri ɗaya da nasa, kuma skin ɗinsa up white ne irin naki”……. Ai da jin wannan magana Aryan bai san time da ya dawo cikin hankalinsa ba, ɗan zare idanu yai tare da kara natsuwa yana sauraronsu. A ransa ya ce lallai kin cika jinin IRON FIST, na kara shaidawa jininmu ce ke, kaga yarinya da basira, tab!.Ita kuwa Rimsha ta ce. “Kai anya kuwa kin gansa da kyau? Ko dan kina kewata ne yasa kike yi wa kowa kallon kama dani?”……. Da sauri ta ce. “No Rimsha, for sure yana kama dake, kinga ɗan bakinsa? Like yours, sai ma idan yana magana, dimple ɗinku iri ɗaya, his big-big eyes, kai kuna kama sosai. Shiru Rimsha ta ɗan yi kafin ta ce. “Kai anya ba uncle Aryan bane to? Dan dik cikin uncles ɗina mun fi kama da shi, dani da shi and Yah Vash dik da Ammie muke kama, su uncle Faryan kuma da Abba suke kama”…….. “In kuwa haka ne to ina ga shi ne, but zan ɗauka maki pic ɗinsa idan ya zo, sai in tura maki ki gani idan shi ne”. Seraph ta faɗa cike da mamaki. Tsayawa jikin wata karanta Aryan yai tare da gyara nose mask ɗinsa yana mamakin yaran nan, watau Rimsha har ta samu damar kallon fuskansa tasan da waye yake kama ko? Dole ya kara taka mata birki daga zuwa kusa da shi, ita kuma Seraph yasan maganinta ne, wayar ma zai kwace ya huta da bala’in da suke son jefasa, ka ji yara, shi yanzu idan su Ammie suka san shi ne Champion na IRON FIST Ina zai sanya kansa wai?.Yayi nisa cikin tinani bai san time da suka yi ending na call ɗin ba, sai jinsu shiru ya yi, katse kiran ya yi yana ƙoƙarin tura wayar a aljihu kenan guru ya iso wajen yana faɗin. “What brought you here bro? Ka sani dogon walking”. Sai a lokacin ya ɗago kai ya fara kallon hanya, yayi nisa da hotel nasu, lallai jin gulma tai daɗi. Ɗan shafa kansa ya yi zai yi magana kenan daga gefensu suka fara jiyo hayaniya da ihun jama’a. Kallon juna suka yi, sai kuma suka sake kallon wajen, a natse suka fara takawa a tare suka nufi wajen dan su duba menene. Suna yin kwana suka isko wata matsakaiciyar kasuwa a wajen. A bakin gate ɗin suka tsaya tare kallon juna. Guru ne ya ce. “I think something bad is happening inside”…….. “What am I thinking kenan”. Aryan ya faɗa.Magana suka yi da ido ta hanyar cewa su shiga su duba. A natse suka fara takawa izuwa ciki. Tin daga nesa suke hango jama’a a kwakkwance a ƙasa kamar ba lafiya ba, kafin su farga sai ganin wasu tsageru suka yi a tsakiyar kasuwar suna gilmawa izuwa cikin shaguna hannunsu rike da bindigu zasu kai su goma, dikkansu fuskokinsu nannaɗe da rawani, sai jajayen idanu zaka gani.Kallon juna suka sake yi, Aryan ya ce. “I think they are armed robbers”….. Guru ya amsa da. “Dama waɗan nan ai daga gani ba tambaya ƴan fashi da makami ne”………. A daidai wajen wani shago suka tsaya, shagon irin na uztazan nan ne masu sai da su dabino, zamzam, bakaruwa ta makka, jallabiyoyi da rawani dayawa. Masu shagon din sun kwanta a kasan tebur dake cikin shagon, sun natsu tsit saboda harbin bindigun da armed robbers ɗin suke yi.Kusan a tare suka miƙa hannu suka zari rawani ɗai-ɗai, dik da nose mask dake fuskokinsu hakan bai hana sun kara naɗe fuskokinsu da kyau ba, kai tsaye suka nufi in da armed robbers ɗin suke. Sai faman fashi suke yi suna kwashe kayan al’umma suna wani irin muzurai tamkar kwarto a gidan General na soja.Kai tsaye wajen wani gaton shago na atamfofi Aryan ya shiga. Shi kuma guru ya wuce gaba. Manyan armed robbers biyu ne a cikin shagon, ɗaya na rike da bindiga yana wani zazzare idanunsa, ɗayan kuma na ta faman kwasan kaya, ga masu dukiya bayin ALLAH suka kwance luff a ƙasa, suna ji suna gani za’a kwashe masu halak ɗinsu, guminsu saboda tsoron wannan shegiyar kurmar abar da bata da sabo kuma bata jin yaren kowa face na kisa watau bindiga.”Siiiiiiiiiitttttt”. Aryab yai wa guy dake rike da bindigar. Da sauri ya juyo da jikinsa da bindigar, babu tausayi ya nufi harbin Aryan, bai san Champion namu na amana Champion ɗin ne da gaske ba. Wata lace dage rataye a sama saitin kansu Aryan ya jawo tare da rufewa guy ɗin idanu, sannan ya kama hannunsa ya huya bindigar, a lokacin ya ɗana kunamarta zai yi harbi, Aryan ya tayashi danna harbi kai tsaye ya fasa kan mutuminsu dake ɗebar kaya yana zubawa a bugu.Sake hannunsa ɗaya daga jikin bindigar mutum ya yi yana ƙoƙarin buɗe lace na fuskansa, Aryan bai bashi wani dama ba ya kai mashi wata bahaguwar naushi a ciki, kafin ya gane me aka yi mashi ma Aryan ya kwaci bindigar tare da saitasa, take ya tarwatsa mashi ƙwaƙwalwa, a tsarin IRON FIST basa kama masu laifi, kawai idan suka isa waje kashesu dik suke yi, basa sa tsammanin ɓata gari zasu shiryu, kai bama sa basu dama, abin da suka sani kawai dik wanda ya kashe a kashesa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar dasu, dan haka basu da lokacin ɓatawa wajen baiwa makasa damar ko zasu gyaru.Ko da sauran ƴan fashin suka ji karar harbin da Aryan yai basu wani damu ba, saboda suna harba bindiga sama ai dan firgita jama’ar kasuwar, so sun zaci sama mutanensu suka harba, sai suka cigaba da jidan kaya suna zubawa a buhu tamkar halaliyarsu.Waje Aryan ya fito rike da bindigar, kowa ya gansa sai ya zaci armed robbers ɗin ne, dan ya nannaɗe fuska da rawani, cikinsu kai tsaye ya shiga, kafin ma ya isa guru ya kashe mutum 4, kafin su farga an kashe masu bindigun 10 dikka saura masu kwasan kaya su zuba a buhu.Nan suka farga da cewa su Aryan fa ba mutanen ba ne su bane, nan suka fara ƙoƙarin kokawa da su. Ganin haka yasa su Aryan suka jingine bindigun hannunsu, marasa bindigun ma sun kai su 10, dik sun fito tsakar kasuwan suka yi wa su Aryan zobe. Tini su Aryan suka ajiye bindigu suka hau gwada masu jami’an SSO suke, kuma IRON FIST renon AZURE suke. Dik wanda suka yi wa duka ɗaya sai ya baje a ƙasa, baya sake tashi, dama dik kayan maye ya cinye dik wani quality nasu.A daidai wannan lokaci jiniyar motar ƴan’sanda ya fara karaɗe ko’ina a arear alamar suna zuwa. Cikin zafin nama su Aryan suka ɗauki bindigunsu, dik suka harbe armed robbers dake baje a ƙasar, basu bar ko mutum ɗaya da rai ba, sannan suka yasar da bindigun suka gudu ta tsakanin shaguna, suka haye katangar kasuwar suka dira ta baya. Ba zasu yarda a gansu ba ai, kada ku manta jami’an SSO suke, suka kuskura suka haɗu da ƴan’sandar nan to za’a samu matsala, dan ƴan’sansa zasu ce su buɗe fuskokinsu, su kuma ba zasu yarda ba, idan aka matsa zasu haɗa da ƴan’sandan dik su kashe ne, so gara su gudu kawai. Basu zame ko’ina ba sai hotel ɗinsu, suna shiga suka hau haɗa kayansu, barin AVARIS a yau ya kamasu, idan ba haka ba sai an san SSO suna ƙasar AVARIS, dan dik waɗan dake kasuwar sun ga kalar fatarsu ai, zasu faɗa, kuma ma dole za’a nemesu tin da sun kashe almost 20 armed robbers, kunga kuwa nemansu wajibi ne. Sun yi sa’a time da suka koma hotel ɗin Lion ya farka, yana zaune tsakiyar bed rike da waya yana ƙoƙarin kiransu kenan sai gasu nan. Ba tare da ɓata lokaci ba suka sanar mashi ga abin da suka aikata, harara ya dallawa Champion ba tare da ya yi magana ba. Guru ne ya ce. “Bro no time”. Shi ma hararar ya samu babu alamar Lion ɗin zai yi magana, har suka gama shiryawa bai kulasu ba, sai da guru ya haye saman bed ɗin ya jawo hannunsa yana faɗin su je, sannan ne ya ce. “I can’t go anywhere”……. Aryan dake ƙoƙarin jan luggage box ɗinsu ne ya dallawa Lion harara kafin ya ce. “Do you heard what you said kuwa?”.Shiru babu alamar zai sake tanka masu, sai ma gyarawa da ya yi ya kwanta abinsa. Cikin fushi Aryan ya yi tsalle ya dira a tsakiyar gadon, dan in sun biyewa Lion wlh tsab zai ja masu aiki, dan wani lokaci Lion iskancinsa yawa ne da ita, sai ka kai zuciya nesa zama da shi. Hannun rigar jikinsa Aryan ya naɗe tare da sunkuyawa ya cicciɓi Lion sama sai saman shoulder ɗinsa yana faɗin. “Ba zan iya juran iskancinka na wannan lokacin ba”…… Guru da iskanci shi kuma ya yi saurin damke hannayen Lion dukka biyu ya dawo da su ta bayan wuyan Aryan ya rike gam wai dan ma kada ya ce zai kwaci kansa, da hannu ɗaya Aryan ya rike Lion, ɗayan hannunsa kuma ya ja luggage box ɗinsu suka fito parlo. A tsakiyar parlo Aryan ya sauke Lion tare da cewa. “Lets go”…… Wani irin kallo ya dallah masu da waɗan nan shaggun sharp eyes ɗin nasa masu rikitarwa kafin ya juya zai koma ciki, watau idan kana neman ɗan duniya ka samu Lion ka gama, tin da sun nuna a ƙage suke su bar hotel ɗin shi ne sai ya kuntata masu, ga shi ba zasu iya matsawa ko nan da can su barshi ba, iskanci kala-kala cike da cikinsa guy ɗin nan.Ai cikin zafa Champion ya damko wannan tuntun jekar kitson nasa yana faɗin. “Baka isa ba”…… Da sauri guru ya tare gabansa yana faɗin. “Bro please”. Wani irin kallo Lion ya dallah mashi kafin can ƙasan maƙoshinsa ya ce. “Give me a way to pass”…… Jan tuntun gashin nasa da karfi Aryan ya yi har sai da Lion yai baya, dawowa ta gabansa Aryan ɗin ya yi, ya zamana su ukun suna fuskantar juna. Aryan ne ya ce. “

Back to top button