Karfe A Wuta Chapter 9 By Ayshercool
Har ƙarfe goma na dare, Nabila tana kiran wayar Nasir, domin jin ko yana lafiya, amma shiru wayarsa ba ta shiga, abu kamar wasa hankalinta ya fara tashi, zuciyarta ta din ga raya mata wani abun ya same shi.Da sauri ta tashi ta fita farfajiyar gidan, tana cigaba da kiran wayarsa.”Ke Arfa, me ki ke yi a wurin nan da daddare haka?” Ta ji muryar Abba babu tsammani.Cikin damuwa ta ce “Abba Yaya bai dawo ba, kiransa aka yi kwantar da tarzomar faɗan daba, kuma haryanzu bai dawo ba”.Abba ya ce “Yana nan lafiya in sha Allah, da ki ka dawo nan kina sintiri,ai ba bin sa zaki yi ki nemo shi ba, harkar aiki ne yana nan lafiya in sha Allah”Abba yana rufe bakinsa, sai ga ƙarar motar Nasir, yana ta horn ba ƙaƙƙaitawa, gaba ɗaya suka nufi gate a tare.Suka tsaye har ya shigo yayi parking ɗin motar.Ya fito yana kallon su da mamaki ya ce “Abba lafiya na ganku a nan tsaye?”Major ya ce “Arfa ce ta fito tana jiran dawowarka, ya ya aka yi wayarka ba ta shiga gaba ɗaya?””Tana cikin mota ne abba, ina ga network ne amma a kunne take”Cikin zaƙuwa ta ce “Yaya, komai lafiya dai ko?”Ya ce “Alhamdilillah, an sha artabu dai, yaran sun ninka yawan da muke tunani, mun kama wasu, wasu sun gudu, amma mun kama su da yawa”.Mama ce ta fito ita ma, tare da su sauda, suna yi masa sannu da zuwa yana amsawa.Arfa ta ce “Amma dai ba su yi maka rauni ba ko?” Yayi murmushi ya ce “Da sun yi mini rauni, ai da baki ganni a haka ba”Nabila ta ce “To Alhamdilillah, bari na je na kwanta na yi bacci a nutse, tun da kana lafiya”Ya ce “Ki bar wayarki a kunne, za mu yi magana” Ta jinjina masa kai ta bar su a wurin ta tafi, mama kuwa kamar ta bi Nabila ta naɗa mata duka, ta kalli yadda Nasir yake wani sassanyan murmushi kamar shashasha, shi ma ji ta yi kamar ta kwaɗe shi da mari, duk ƙoƙarin da take yi a kansa na nesanta shi da Nabila, abu ya ci tura.Ta daure ta ce “Shiga ciki ka ci abinci, ka je ka nemi wuri ka kwanta”.”No na tsaya na ci abinci a hanya ma, sai da safe, gajiye nake kwanciya zan yi”Major ya ce “To Allah ya tashemu lafiya” suka watse.A galabaice suka koma mafakarsu, domin kuwa sun sha artabu da jami’an tsaro, duk da an kama wasu, wasu kuma sun tsira da ƙyar. Sai dai sun yi wa su madaki mummunar ɓarna, dan ma Aminu ya yi musu kashedin babu ruwansu da cewa za su kashe madaki, saboda ya san hatsabibancinsa.Yana zaune suka faɗo ɗakin, suna ta mayar da numfashi, jikin rigar ɗan mama face-face da jini.Walid ya ce “Boss, an yi aika-aika amma kwaɓarmu ta so yin ruwa, dan an kama da yawa daga cikin yaran nan da muka gayyato, amma fa yaran madaki sun yi ɓarna, dan sun taɓa wanda ba su ji ba, ba su gani ba, duk da mun yi yinƙurin daƙile hakan”.Maimakon Al’amin ya yi magana, kawai ya tashi tsaye ya shaƙo wuyan walid, ya haɗa shi da bango, ya ware masa idanunsa ya ce “Ina ƙwayoyin da ka kwashe a nan wurin?”Cikin takaici walid ya ce “In fita yi maka aiki, in dawo da ƙyar amma ka shaƙe ni?” Yayi maganar muryarsa na fita da ƙyar saboda shaƙar da ya yi masa.”Suna ina na ce?””Na kwashe su na fita da su, dan ba zan bari ka kashe kanka ba, allurar da ka ke yi wa kanka ma, ba abun da take yi maka sai ƙara maka zafin zuciya”Fusata yayi da maganar Walid, ya ƙara shaƙe shi, Ɗan mama ya tashi da sauri yana yi wa Al’amin magiyar ya rabu da Walid.Walid ya ce “Idan ka kashe ni ma, ba zaka huce ba, ai na yi maka alƙawarin kawo maka sabuwar ƙwaya, amma wannan kashe kanka zaka yi, idan ka cigaba da sha, dan ba ta karɓe ka ba.” A fusace ya hankaɗe Walid ƙasa, ya koma ya zauna ya dafe goshinsa.Wayarsa ce ta yi haske, ya ja wayar yana dubawa.”Aminu ka daina wannan gangancin da ka ke yi, idan ka sake shiga hannun mutanen nan, kar ka yi zaton za su hukuntaka da adalci, dai-dai da abun da doka ta tanada, ka nutsu ka daina wannan mugun wasan, ka mayar da hankalinka a kan burinka” iya ƙarfin sa ya saka wurin yin jifa da wayar, ta dagargaje a tsakiyar ɗakin, ya tashi zai fita.Duk da mugun ciwon da jikin walid yake yi masa, saboda artabun da suka yi, amma haka ya tashi ya sha gaban Al’amin ya ce “Ina zaka je ne?”Hankaɗe Walid yake ƙoƙarin yi, amma walid ya sanya ƙarfin sa, ya tura shi baya.”Ka rabu da ni walid, ya zan yi ne? So suke sai na haukace, waye wannan? Me yake nema da rayuwata? Wace manufarsa ce da su a kaina? Me kuma suke buƙata yanzu?””Easy master”Cikin ƙaraji ya ce “Na ce kar ka sake kirana da wannan sunan””Sorry boss, na san komai ai, ka kwantar da hankalinka””How? Duk abun da suka yi mini bai ishe su ba, wai yaya zan yi ne? Kalli idona walid, ba na bacci fa, zuciyata kullum zafi take yi, ba na iya saka komai a bakina na ji ɗanɗanonsa, ya zan yi ne?”Walid ya ce na sani, ya amsa yana yi wa ɗan mama inkiya da idonsa.Viper ya a sake cewa “Ka san kwana nawa na shafe ba na bacci? Ba kwanaki ban ba fa kawai, shekaru ne, ba na baccin da ya kai awanni biyar, ka san me nake ji kuwa?”Walid ya ce “Ban sani ba, amma na san da yawa daga abubuwan da ka lissafa”Jikinsa na tsuma ya ce “Wallahi zuciyata ci take yi da wuta, ka sani, wallahi idan na riƙe makami sai na yi kisan kai” yayi maganar yana rintse idanunsa, a lokacin da ruwan allurar da walid yake yi masa, ya fara ratsa jijiyoyin jikinsa.A nan take jikinsa ya saki, ya zubawa walid ido.Walid ya ce “Ko ba zaka yi baccin ba, ka rufe idanunka master, za ka samu releif” shiru yayi, domin ba zai iya motsa kowacce gaɓa daga jikinsa ba.Ɗan mama ya ce “Walid, anya ba zamu yi wani abu a kan lamarin nan ba kuwa? Ba za a kai shi ya ga likita ba? Kar ya haukace tuburan fa”Walid ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa alamar ɗan mama ya yi shiru.A hankali al’amin yake buɗe idonsa yana lumshewa, sai dai ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi.***YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR TOFA.Cikin tsananin ƙyanƙyami take ƙarewa ɗan ƙaramin ginin ƙasar kallo, rabin katangar gidan ta zube, sai ciko aka yi da kara da buhu, aka rurrufeta.Abunka da mutumin ƙauye, cikin mutunci da girmamawa, matar gidan ta karɓeta, tana yi mata sannu da zuwa.Ta yi mata iso, har cikin ɗakinta, ta ba ta abun zama.Kamar ta zauna a kan kashi, haka ta ɗan ɗosana ta zauna, tana kame jikinta ta kalli matar ta ce “Baki gane ni ba ko?”Matar ta ce “Eh ban waye ki ba””Ni ce barrister da na karɓi case ɗin ƴar ki, na zo mu tattauna ne, in yi magana da ita”Nan da nan hawaye ya cika idon matar ta ce “Tana banɗaki, bari ta fito”rufe bakinta ke da wuya, yarinyar tayi sallama a ɗakinta, muryarta ƙasa-ƙasa.Mahaifiyarta ta amsa, barrister kuwa zuba mata ido ta yi, yadda yarinyar take ɗingishi, take tafiya da ƙyar, har ta zo ta zauna.Ta kalli uwar ta ce “Kun kaita Asibiti ne?”Ta ce “A’a, tun dai a can an kaita, maigadin gidan ne ya kaita, har aka yi mata ɗinki a goshinta, gashi nan in da aka ya ji mata rauni. Dan Allah baiwar Allah ki taimake mu, kamar yadda Allah ya taimake ki, a karɓar wa yarinyar nan hakkinta. Saura ƴan kwanaki aurenta, ya lalata mata rayuwa, idan zancen nan ya fasu a garin nan yaya zan yi?”Ta kalli yarinyar sannan ta kalli uwar ta ce “Baiwar Allah kuma hadda halinku, na son abun duniya duk yadda hukumomi ke jan kunne a kan kai yara aikatau meyasa ba kwa ji? Meyasa zaki kaita aikatau, maimakon makaranta?, a ƙa’ida fa kema sai an hukunta ki”Cikin rauni da damuwa ta ce “Baiwar Allah da ina da yadda zan yi yaushe zan kaita aikatau? An yi garkuwa da mahaifinta an ce mu kai kuɗin fansa, mun tattara dabbobi da gonaki mun sayar, mun bayar a kai a sako shi, sun rike ƙanin mahaifinta da ya kai kuɗin, sun haɗa su su duka sun kashe, gona ɗaya ta rage mana, ita ma wani mutum duk ya tarkata ya ƙwace, wai zai gina kamfani, an ce za a bamu diyya, gonar miliyan uku an bani dubu bakwai, abun da zan girka na basu su ci, ita da ƴan uwanta, bani da shi, nima ba cikakkiyar lafiya ce da ni ba, kuma ita ce babba, makaranta tana zuwa ajinta uku a sakandare, kuɗin da ake biya na makarantar ba ni da su, ya zan yi?” Tayi maganar kuka yana ƙwace mata.”Shikenan ya isa haka?, Amma kuma irin haka kin yi gaggawa zuwa gidan radiyo ki faɗa, ai wurin jami’an tsaro yakamata ki je”.Maman ramma ta ce “Na je, dan da aka kira ni na je can birnin asibiti, da ƙyar aka karɓe ta wai ba ɗan sanda, daga can na je wurin ƴan sanda naga suna nema su cuce ni, wai ƙarya muke yi, babu yadda za ayi a ɗauki ƴa ta aiki a wannan gidan har ayi mata fyaɗe. Ba ki ga sintirin da na yi ba, na rasa abun yi shiyasa na kai wurin masu radiyo ko Allah zai saka a taimake mu”Ta jinjina kai ta kalli yarinyar ta ce “Ramma ko?” Ta jinjina kai alamar eh.”Gaya mini yaya aka yi abun ya faru?” Ta ɗaga kai ta kalli mahaifiyarta, sai ta fashe da kuka ta kasa magana.”Hajiya ɗan bamu wuri mu yi magana” babu musu, ta tashi ta fita ta bar ɗakin.”Kin ga ki yi shiru ki kwantar da hankalinki, ki yi mini bayanin yadda abun ya faru, in ga ta ina zamu ɓullowa lamarin”Shiru ta yi tana tuna yadda lamarin ya kasance.”Ke!” Ya kirata cikin tsawa, bayan sun haɗa ido da ya shigo, ƙara razana ta yi, dan ba ta yi zaton wani zai shigo yanzu ba, a dai-dai wannan lokacin, da ta duƙufa tana ta aiki a falon gidan.cikin tsuma ta kalleshi ta ce “Na’am”.”Ina masu gidan?” Yayi maganar yana ƙare mata kallo, matashiyar yarinya ce, da ba ta wuce shekara goma sha huɗu ba, irin farkon tashen balagar nan, ƙirjinta ya fara tasawa, wannan ne karo na biyu da yake ganinta a gidan. Tun a ranar farko yake jin wani abu na fuzgar shi a kanta.Cikin rawar murya ta ce “Ai ba su dawo ba tukuna, gyaran gidan dai muke yi”.”Ke kaɗaice a gidan kenan?”Cikin rashin wayo ta ce “Eh, amma zulai ta je sayo katin waya, zata dawo, tare muke aiki da ita, wai a satin nan za su dawo”.Yayi wata irin ajiyar zuciya ya ce “Ɗaukko mini ruwa a kitchen zan sha” ta jinjina kai, ta ajiye duster hannunta, ta tafi da sauri har da gudu.Sai dai tana shiga kitchen ɗin, ya bi bayanta, ya mayar da ƙofa ya rufe.Turus ta tsaya tana kallonsa, jikinta yana rawa, taga ya fara tunkaro ta.Ta ja da baya ta miƙa masa ruwan, amma ya haɗa da hannunta ya riƙe.”Dan Allah ka sakeni, in ƙarasa aikina”Babu tausayi ko imani, ya ce “Nawa aikin zaki fara yi tukuna, kafin nata”Ganin akwai alamun ƙarfi a tare da ita, ba zata tsaya ba, ya sanya ya gaura mata wani lafiyayyen mari. A take hancinta ya fara zubar da jini.Ta ƙwala ihu, ya sake buga kanta da cabinet na kitchen, goshinta ya fashe, nan ma jini ya hau zuba, ga goshi ga hanci, dan haka ta kasa magana, jikinta ya saki.Haka ya keta mata haddi, ta hanya mai muni da rashin tausayi ya tashi ya fice ya barta.Idonta biyu, amma ta kasa taɓuka komai, ko ɗaga hannunta ta kasa yi.Zulai ce ta dawo ta tarar da ita cikin mummunan yanayi, a rikice ta fita ta kira ɗaya daga cikin masu gadin gidan, suka ɗauke ta suka kaita Asibiti.Aka ƙi karɓar su, sai da aka kira matar gidan aka sanar mata, suka yi magana da likitoci ta waya.Sai dai duk abun nan, ramma ba ta san ko sunansa ba, balle ta san ɗan waye shi.Kafin matar gidan ta dawo, ta aiko a bawa ramma kuɗi, a bata haƙuri su koma ƙauye, ko warkewa ba ta yi ba aka sallame su, shi ne mamanta ta ɗauke ta suka tafi gidan radiyo.Ramma ta bawa barrister labarin komai, tana kuka mai taɓa zuciya, goshinta ga ɗinkin da aka yi mata a asibiti, ga na ƙasanta da yake addabarta da raɗaɗi.Tayi ajiyar zuciya ta ce wa mahaifiyar ramma ta shigo.Bayan ta shigo ta zauna, ta kalle su ta ce “Baiwar Allah, dan cuta na san an cutar da ku, amma za ki sake jefa kanki a halaka, gara ku yarda ayi masalaha.Babu wata kotu, ko wani alƙali, da zai tsaya miki ya ƙwato muku hakkinku, saboda yaron nan ɗan gata ne gaba da baya, ubansa suke da ƙasar.Dan haka ki yi haƙuri, a baku wani abun, ki samu ku sai abinci, a kuma kaita asibiti, idan ta warware ta koma makaranta.A take ramma ta fashe da kuka, mahaifiyarta ta ce “Haba baiwar Allah, shikenan bawa dan talaka ne, ba zai samu adalci ba, kuɗi zasu ƙare, mutuncin ƴa ta fa? ni gaskiya so nake a karɓa mata hakkinta”.Barrister tayi shiru tana zancen zuci “Ko yaushe mutumin ƙauye ya wani san ƴancinsa? Da matar nan take zaƙewa?'”Naira miliyan uku za a baku, kuɗi hannu, ki yi tunani zan sake dawowa. Idan kuma kun ƙi, zan cire hannuna, duk matakin da uban yaron ya ɗauka a kanku babu ruwana, ina sake gargaɗinki, babu ke babu magana da wani ɗan jarida ko makamancin haka, idan kunne ya ji jiki ya tsira” ta ciro kuɗi a jakarta, ta ajiye musu, ta tashi ta fice.***Kamar zai tashi sama, saboda tsananin tashin takaici da haushi, ya ce “Madaki, wace irin shiririta ce wannan ku ka yi, ta yaya zaku bari, jami’an tsaro su sake kamaku?”Cikin muryarsa da ta riga ta fashe irin ta mashaya ya ce “Kai ka san ba laifinmu ba ne ba, wani banzan bakware aka kawo mana, kai zaka tsawatar, ka saka a sake su, dan idan babu su babu aikin nan””Shikenan, na ji, ka saurare ni da kyau, zuwa hankali ya riga ya kwanta, mutane sun manta da abun da ya faru watan baya, ina son a cigaba da yi mini aikina, amma a wannan karon yankin yamma da gari zaku je, yaron kar ya wuce ɗan shekaru goma zuwa sha biyar, jininsa nake buƙata, a zuba a babban dam ɗin da yake rarraba ruwa a yankina, tun daga mazaɓata, sai ku kawo mini ƴan marainan yaron, da hanjinsa. Sa’ar aikin ranar laraba ce bayan al’muru. Idan kujerata ta cigaba da tabattuwa kuma zaku mora”Madaki ya ce “Wannan ba zai yi wahala ba, ka huta kawai, kujerar nan ko an so ko an ƙi, mai hawanta sai bayan ka mutu honorable””Eh, amma ba yanzu zan mutun ba ai, sai an kwana biyu tukuna, zan aiko maka kuɗi, ayi abun da yakamata larabar tsakiyar wata za ayi, yaranka kuma za a sake su””Sai da kai honorable, ka ci dubu sai ceto””Yauwa yayi”.Nabila kuwa sannu aka din ga yi mata a wurin aiki, ana tambayarta yaya jiki, ta din ga amsa musu da yauwwa.Ofishin barrister Habib ta je, ta gaya masa yadda suka yi da matar, da duk abun da ta yi documenting.Ya karɓa ya duba sannan ya kalleta ya ce “Yayi, amma me ki ke gani a kan case ɗin? Do you have interest on it?”Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Wani case na jiyo, na wata yarinya da aka yi wa fyaɗe,amma ana ta ɓoye abun, amma na ji an ce su barrister Naja’atu sun shiga case ɗin, hankalina ya fi karkata a can”.”Wai ke menene haɗinki da wannan naja’atun ne? Ki kiyayi kanki da lamarin matar nan,tun da sun shiga case ɗin, ki ƙyale su, case ɗin wannan hajiyar ki tsaya ki mayar da hankali a kai ki yi”Ta marairaice ta ce “Amma barrister menene aibun hakan, tun da class mate ɗin ka ce, ka haɗa ni da ita dan Allah, ina son irin aikace-aikacenta na jin ƙai”Ya cire medical glass ɗin sa ya kalleta ya ce “Wai ke meyasa ki ke da taurin kai ne? Ke ma ki kafa naki harkar jin ƙan marasa gatan mana, dole sai kin zama ita, ke kin san wacece Naja’atu kuwa? Zahirinta ki ka sani, baki san baɗininta ba, go and work on this case now”.Tsatstsare fuskar Barrister ta yi da kallo, a ranta ta ce “An zo gaɓar da nake so, hasashena ya tabbata, zan cigaba da matsa ka, har sai ka amayar da abun da ka ke ɓoye mini”A fusace ya ce “Ba zaki tashi ba, ki ka tsare ni da ido?”Miƙewa tayi tana zumɓura baki, ta ɗauki file ɗin ta fice.***Kaiwa yake ta yi yana komowa, a katafaren office ɗin sa, hannunsa riƙe da waya a kunnesa, yana jiran a ɗauka.Har fitar da ran za a ɗauka, aka ɗaga. Cikin harshen turanci ya ce “Haba sir, kai fa nake jira kayan nan su iso, almost 2weeks, ayi ta ga kaya nan amma shiru, ni na riga na gama clearing road, a yankinmu na arewa, ka hanzarta na fara jin ƙishin-ƙishin canjin controllers na coustom, bana son a kawo waɗanda za mu yi ta fama”Daga cikin wayar mutumin ya ce”Sai fa ka yi haƙuri, kayan ne ba a gama loda su ba, kuma nima dole sai na gama da controllers ɗinmu na nan, kuma ka daina ɗaga hankalinka, babu wani wanda ya isa a ƙasar nan, ya sha abun da ba mu muka dama ba, ranar laraba kaya za su shigo, amma sample ce allurar, ba a shigo da ita da yawa ba, sai an ga yanayin aikinta tukuna, har da tablet ma””To na ji, amma ka tabattar ranar larabar za su iso?””Ko tantama babu””To shikenan, godiya nake”ya katse wayar, cikin shauƙin irin ribar da zai mayar idan kayan suka tsira.Zaune take a ƙasaitaccen ɗakin baccinta, jikinta sanye da riga da wando na nylon, masu sauƙin zafi.Ta zauna ta nutsu, ta zubawa kayan kan table ɗin gabanta ido, tana ta saƙe-saƙe a kan ta sha ko kuma kar ta sha.Kwalabe ne na magunguna, da ƙwayoyi haɗi da allurai.Wata matashiyar mace ce tayi sallama, ta amsa mata, ta ƙaraso hannunta riƙe da cup ta na shan wani abu.”Sweetheart, ya dai na ga kin saka kayan nan a gaba kina kallo?”Tayi ajiyar zuciya ta ce “Tunani nake yi da zuciyata, in sha ko kar in sha””So you are going to quit abusing drugs?”Ta girgiza kai ta ce “Is not that easy dear, jikina is resisting it, ba sa ɗauka ta sai na sha su in a very high doses, ba na son su huda ni, a fara ganewa. Mun yi magana da honorable a kan sabuwar allurar da suka yi order daga Mexico yana ta yi mini yawo da hankali””Haba barrister, ke fa ta hannun daman honorable ce, ba zai yi miki yawo da hankali ba. An samu wani zazzafan malami fa”Ta ɗago idanunta ta kalleta ta ce “Wow, are you serious?””Yes of course, aikinsa tested and trusted ne, amma kafin muje a kan buƙatarki, anya ba zaki duba a manyan mutanen nan, mu kai wani ba, ki yi aure yadda zai zama backup kar abubuwa su zo su taɓarɓare fa, ko ki samu wani kamar tsohon mijinki, ki aura”Ta taɓe baki ta ce “Ba zan iya aure ba, na riga na saba da rayuwar ƴanci, ba zan yi aure in zauna ƙarƙashin wani yana juya ni yadda yake so ba. Ai tun da na yi joining organization ɗin nan kin san in da na dosa”.Ta ce “Na sani dear, amma duk da haka, religion da tradition yana da tasiri sosai da sosai a arewacin najeriya, ba na son wani ya gano wani lagonki, ayi amfani da shi wurin yaƙarki”Ta girgiza kai ta ce “Muddin ba zan samu wanda zan gindayawa sharuɗa ya bi ba, zan iya zamana a haka, i have so many ways to satisfy my feelings, when i need it, ba dai duk su ake yi wa a auren ba? Kin san komai ai ke.Ki saka mana time, mu je wurin mutumin, ba na son sunana ya ɓace, har sai na cika burina, na kammala aikin da na karɓo a wurin shugabannina, sai na tabattar da samun daidaituwar jinsi a tsakanin mutanenmu na arewa”Badi’a ta yi dariya ta ce “Ki huta baby, ki ɗan yi caji, sai ki kwanta, ko in fita da ke ne?””No, ba na son na yi bacci da yawa, zan sake komawa wurin matar nan, a kan case ɗin ɗan gidan honorable, naga alamar za ta yi taurin kai, idan taƙi yadda kawai mu bi hanyar da muka saba bi””Hmm, talaka akwai ƙi faɗi, kuɗin ne ba zata karɓa ba kenan? Sa yi biyu babu kuwa””Manta da su, idan ki yi waya da journalist ɗin nan, manta sunasa nake yi, ki tura masa kuɗi, a cigaba da ɓoye wanda ya yi laifin, a sanarwa da duniya na shiga case ɗin, a sassaka a social media ma, a dai yi ƙoƙarin ɗauke hankalin mutane daga kai” ta ƙarasa maganar tana tuttula ruwan maganin da ke cikin wata ƙatuwar kwalba tana lumshe ido.Yau Abba kamar ya san Nabila so take ta lallaɓa ta fita, ya zauna a gida bai fita ko ina ba.Tayi iya tunanin ƙaryar da zata sharara masa, ta fita amma ta kasa tunawa, dan idan ya tsitiyeta zai gane ƙarya take yi, gashi weekends ne babu aiki.Cikin ikon Allah, aka samu tarzomar su madaki da Viper ta ɗan lafa, saboda an jibge jami’an tsaro a unguwannin.Nabila har alla-alla take yi, ranar Monday tayi ta fita aiki, daga nan ta tafi nata wuri.Ranar Litinin tun sassafe wasu daga cikin iyaye mata, suka fara sintirin karɓar belin ƴaƴan su da aka kama, a ofishin su DSP Nasir.Nasir yana zuwa ya tarar da su, an ce musu su jira sai ya zo.Tsakanin iyaye da ƴaƴa sai Allah, amma wannan rashin juriyar yana ɗaya daga abun da yake taka rawa, wurin sake sangarta yaran.Bayan sun gaisa da su, ya ce “Da farko ina mai baku haƙuri, domin kuwa ba za mu bayar da belin yaran nan ba, sai mun kai su gaban alƙali tukuna. Yaran nan ku kanku sun fi ƙarfin ku, ba kwa iya tsawatar musu, suna barazana ga zaman lafiyar al’umma, dan haka ku yi haƙuri a wannan karon babu sabo babu ɗaga ƙafa, sai dai na yi muku alƙawarin duk wanda muka kama ba shi da laifi, zamu sake shi, masu laifi kwai zamu kai gaban hukuma”.Bai tsaya jin mai zasu ce ba, ya wuce office ɗin sa.Koke-koke wasu daga cikinsu suka fara, yayin da wasu suka din ga janyo masa jafa’i kala-kala, wai an zalunce su, an rufe musu ƴaƴa.A cikin office ɗin sa ya karya, kasancewar ya makara, bayan ya kammala, ya je in da ake tsare da yaran, tare da taimakon wasu daga cikin jami’an tsaro, ya fara tuhumar su, da ƙoƙarin zurfafa bincike akan su gaya masa in da viper yake.Wanda aka ritsa ɗin ana tuhuma ya ce “Wallahi Yallaɓai, da ne dai kafin ya je prison, na san in da yake, har gidansu na sani, muna yi masa aiki sosai da sosai, amma tun da ya fito bamu sake ganinsa ba, su Walid da tarago ne suka san in da yake, tarago kuma madaki ya kashe shi, walid kuma wallahi shima ba a ganinsa, muna yi masa aiki amma bamu san in da yake ba”.Nasir ya ce “Ta yaya ku ke karɓar order daga wurinsa?””Randomly, suke zaɓar mutum ɗaya su kai masa takarda, ko aje a ajiye takardar a in da muke taruwa shikenan”Nasir zai sake magana, wayarsa ta fara ruri, ya zura hannu a aljihunsa ya ɗaukkota, ya ɗaga ya saka a kunne, tare da yin sallama.”Kana ina ne?””Na shiga wurin aiki sir””Yaran nan da ka kama, ka sake su, kowa ya tafi, kuma ka janye jami’an tsaron da ka jibge a unguwar” cikin tsananin mamaki ya tashi tsaye ya ce “Sir, yarane da suke ɓarna fa, har kisan kai aka yi a ranar, yaya zamu….”This is an order from higher up Nasir, ka saki yaran nan, nima umarni aka bani daga sama, Aminu Viper muka ce ka kamo mana, ba yaran unguwa ba”Ya taune lips ɗin sa na ƙasa cikin ɗacin rai ya ce “Amma sir, muna kan binciken wanda suka yi kisan kan ne”.”Ka sake su nace, is an order”Nasir ya ce “Ok sir, as you wish”ya kashe wayarsa, jikinsa yana wata irin tsuma, ya tuna yadda a garin kamo yaran, sai da suka kusa kashe shi, a artabun da suka yi, ga kisan kai, ga miyagun makamai da suka kama yaran da su, amma an bashi order ya sake su, anya kuwa ana son kawo gyara da matsalar tsaro a ƙasar nan!?Ƙarfe a wuta paid book ne, few pages zan bayar free, masu buƙata za su iya contacting ɗi na, su fara subscribing, miƙaƙƙiyar tafiya ce, mai cike da sarƙaƙiya da ban al’ajabi.
Ayshercool 08081012143
