*ASM Bk2012*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
2 Years Back……..
Ranar wata Asabar Fatuu ta farka da Safe don yin shirin zuwa islamiyya, tana zuwa toilet don yin fitsari kawae sai taga jini jage jage a k’asanta, a razane ta fara k’wala ma Gwaggo kira tun acikin toilet d’in amman shiru gwaggon bata amsa ba sakamakon bacci da take, hannunta ruk’e da k’asan skirt d’inta ta fito ta nufi dakin gwaggon tana cigaba da k’wala mata kiran, bayan ta shiga d’akin gadon da take kwance ta nufa tana kiranta a firgice lokacin gwaggon ta farka idonta akanta cikin harshen fulatanci ta tambayeta lafiya, da d’ayan hannunta tay mata nuni da tsakankanin cinyoyinta gwaggon ta kai idanunta wurin ta k’ura ido tana kallo, can ta d’ago da alamun damuwa ta kalli Fatun, ganin yanayin fuskarta yasa Fatun cewa Gwaggo ko jinin hailan ne yazo…..”tsit tayi sakamakon kallon data ga gwaggon nayi mata, can ta mik’e tace mata su je tace to tay gaba tana tafiya a gwaggwale sai kace yar shayi, toilet d’in suka koma tace mata ta cire kayanta ta wanke wurin da kyau amman banda sabulu sai tayi wanka tace to, komawa tayi d’akinta ta d’aukko mata towel ta kai mata kewayen tay tsaye a gefe tana jiranta har ta gama sannan suka nufi ciki tare tace ta shiga d’akinta tana zuwa, d’akinta ta koma ta samo mata wani yankin kallabinta mai tsabta da taushi ta koma d’akinta, lokacin da ta shiga Fatun na zaune gefen gado sai wuwwurga ido take ta mik’a mata tace “ki amfani da wannan ki tare kafin in fita…..” tun kan ta k’arasa Fatun ta turo baki tace “kam gwaggo pad fa ake sawa ba tsumma ba”,
a harzuke tace “to banda shi, baki ji nace kafin na fita ba in siyo maki tunda Amadu bai sayar da ita” tana tura baki tace ” to ko cikin taki ne ba sai ki ban ba….” tun kafin ta k’arasa gwaggon takai hannu zata make mata baki tana Fad’in bari ta buge bakin maras kunya tunda tayi da ita tana amfani dashi, da sauri ta goce lokacin kuma taji wani abu ya zubo mata ta d’an d’aga towel d’in ta lek’a gwaggo tay tsaye tana kallon ikon Allah, a firgice ta d’ago tace “gwaggo gashi nan ya zubo da yawa!” tsoki ta ja ta juya ta nufi wardrobe d’inta ta d’aukko mata pant ta dawo ta bata tace ta tashi tasaka in ta gama tasa kaya tace to gwaggon ta juya ta fice, bayan ta gama shiryawa cikin doguwar riga ta d’auki towel d’in da hannu d’aya cike da kyankyami ta nufi d’akin gwaggon lokacin tana zaune gefen gado da alama Al’amarin ya jefata a damuwa,
“Gwaggo wannan yadda shi zanyi ne jinin ya 6ata shi” ta Fad’a tana d’age baki,wani kallo mai kaman harara gwaggo ta bita dashi kaman bazata tanka mata ba sai kuma tace “tunda baki da hankali ai sai kije ki yadda d’in”,
“To ya zanyi dashi”? Ta tambaya kaman zatayi kuka,gwaggon tace ” kije ki kama wurin ki wanke shi tass ki shanya”
Tura baki tay tace “Kai gwaggo bafa jinin yankewa bane baki ga daga inda yake fitowa ba kuma sai kice in wanke” banza tayi mata tana harararta hakan yasa ta juya tana d’an k’unk’uni taje ta wanke gwaggo na jinta zata shiga d’aki ta kwala mata kira tazo d’akin, nuna mata k’asa tay tace ta zauna tayi zaman cin tuwo tay mata k’uri da ido,saida ta d’an dauki lokaci suna kallon juna kafin ta fara Magana “ina son in gargad’e ki game da wannan abun da kika fara saura kije ki bud’e baki kina shelar kin fara Al’ada don kina yin hakan zai d’auke ya daina zuwa kwata kwata kuma mace bata haihuwa in bata yin shi don haka in dae baki son ya d’auke to kija bakinki kiyi shiru” tana dakatawa Fatun tasa hannu ta kama lips d’inta alamar bazata fad’i ma kowa ba sai kuma ta cire hannun da d’an murmushi tace “ashe dae shine kenan yanzu na balaga ko?” kai kawae gwaggon ta d’aga mata,
“Wayyo, yanzu dole in rink’a yin Azumi duka kenan, amman dae ai in ana yin shi ba’a azumin da salla ko?” ta wurga ma gwaggon tambaya nan ma kai ta d’aga mata, kafin taci gaba da cewa “sannan zan kara gargadinki, Fatuu ba ruwanki da maza, nasan halinki sarae amman ki k’ara kiyayewa kar ki yarda wani yay maki wayo yay maki abunda bai dace ba don yanzu tunda kin fara Al’ada to ko hannunki Namiji ya kama zaki samu juna biyu ne”? Zaro idanu tayi a tsorace tace “cikin shege irin na d’iyar yar wajen aikin ku?” kai nan ma ta d’aga mata a tsorace ta fara girgiza kan tace “to bazan bari ba gwaggo ai kinga dae koda Bello na gidansu Umar ya kama man hannu can da dad’ewa har na falle shi da mari ai na gaya maki ko?” kai ta d’aga tace “eh kin gaya man amman yanzu kar ma ta kaiga kin bari an kama hannun” da sauri tace “toh”,
“Sannan sai kin dage da yin tsafta don in Mutum bai kula da ya je kusa da Mutane za’a ji yana wari, ki rink’a yin wanka akai akai, kina saka turare amman ba wai in zaki fita ba don ba kyau a jikinki zaki d’an rinka fesawa ki shafa na shafawa…..” katseta Fatuu tay da fad’in “harda can wurin da yake zubowar?” girgiza kai tay a’a sai bayan kin kimtsa kin rufe sai ki shafa, kuma ba ta6a Al’qurani har sai kin samu tsarki….”
“To harda Hadisai ba’a ta6awa?” kai ta girgiza mata alamar a’a, haka taci gaba da fad’i mata Abubuwan da ya kamata tayi da wanda bai kamata ba, koda Haulat taje islamiyyar bata ga Fatun ba hakan yasa da yamma ta biyo mata lokacin gwaggo bata nan tace mata ita bata lafiya bazata ba taje kawae koda ta tambayeta miya sameta bata fad’i mata ba tace ita dae bata lafiya kawae taje haulat d’in tay tunanin ko bata son zuwa ne kawae tay tafiyarta sai bayan Magrib gwaggon ta dawo tayo mata siyayyar su pads da panties duk da tana da su harda turare, Washe gari kuma da ciwon ciki ta farka ta d’ingi bullayi duk da ba wani ciwo bane na tashin hankali amman ta dingi raki har tana ce ma gwaggon ita dae in haka zata ci gaba to gwara ya d’auke kawae ta huta gwaggon dae tay banza da ita iyakar sannu kawae take mata da kyar bacci ya d’auketa bayan gwaggon ta bata Magani, Washe gari kuma data tashi ba ciwon har ta tafi Makaranta, sai ga Fatuu ta zama kamar kwad’o bunu bunu sai ta tafi tayo wanka ita don kar aji tana wari haka ta dingi 6arnar pads sai da gwaggo ta ankare ta tambayeta yadda akai tace ai sau biyar take wanka har saida taba gwaggon dariya tace wannan ai sai sanyi ya kamata tace mata sau ukku zata rink’a yi Safe da Rana da Dare tace to, sati d’aya tayi tana yi kafin tayi wankan tsarki don an koya masu a islamiyya ta iya kuma gaba d’aya da tana jinin bata je islamiyyar ba, sai da ya k’ara dawo mata ne wani watan lokacin suna Makarantar boko ta fara ciwon Haulat ta kaita Clinic anan tasan Fatun ta fara period d’in bayan sun fito ta fara mata tsiya tana ashe su Fatuu girma yazo shiyasa aka k’ara hankali ita dae banza ta mata tana ta kanta, ko su Hajiya sai da Azumi ya zo ne suka san ta fara Period d’in sosae ta ja bakinta tay shiru saboda Abunda gwaggo tace mata.Wannan kenan game da yadda Fatuu ta fara Menstruation.
*** **** *****
Ranar Monday da wuri ya fara shirin zuwa aiki before k’arfe bakawae na Safe ya shirya tsaf ya fito ko part d’in Hajiya bai je ba don yasan ba lalle in ta tashi ba, Parking Space ya nufa ya hau Mota ya fice daga gidan su Officer na mashi a dawo lpy, daidai gaban gidansu Fatuu ya parker motar lokacin k’arfe bakwae tay daidai ya danna horn sai da yay kusan sau hud’u sannan saiga Amadu ya fito da alama ma daga bacci ya taso yana isowa bakin Motar ya sauke glass da Murmushi Amadu ya gaishe dashi ya amsa yace ya kira mashi Zaraah yace to ya juya don yasan bata tafi ba tunda bata yi mashi sallama ba, lokacin daya je d’akinta ta gama shirinta tsaf zata tafi yace “ke kije ga Romeo d’inki can yazo” wani kallo tay mashi cikin rashin fahimta tace waye romeo yace mata Ya Haisam yana jiranta a waje daga haka ya juya, sototo tay ita sam bata yi tunanin daya tambayeta time d’in da suke tafiya zuwa zai yi ba, tura baki tay ta d’auki jakarta taje tay ma Gwaggo sallama kafin ta nufi hanyar wajen kaman an mata dole, lokacin data fita ya rufe glass d’in side d’inshi hakan yasa ta zagaya ta bud’e gaban ta shiga kafin ta rufe,d’an juyawa tay ba yabo ba fallasa ta gaishe dashi ya amsa fuskarshi a d’an sake kafin yace mata ya jiki tace mashi da sauk’i daga haka ya ja Motar suka tafi, lokacin da taje gidansu Haulat bayan ya tsaya fuskarta kaman zata yi kuka Haulat ta tambayeta lafiya tace ba Ya Handsome ne bal yazo zai kaisu,
“To shine na d’aure Fuska haka keda Ya Handsome d’inki” wani kallo ta jefa mata kaman zata kai mata bugu Haulat d’in tay yar dariya tace “yi hakuri wasa nike maki amman yakamata ki saki ranki don Allah”
“To nifa nace banson ganinshi sai ciwon yay ta k’aruwa kuma ni so nike in daina jin abunda nike ji” tay Maganar kaman zata saka kuka,
“Kar ki damu zaki daina ji ki dawo kamar da bada jimawa ba, da kin daina ganinshi in ya tafi” shiru kawae tay sam bata son kuma jin zancen tafiyar nashi, bayan sun koma wurinshi suna shiga Motar Haulat ta gaidashi ya amsa kafin yaja suka tafi kaman dae kullum Fatun bata Magana sai ma juyar da kanta da tay gefe,bayan sun isa tana shirin fita ya tambayeta lokacin da zasu tashi tace sai da la’asar ya bata kud’i tay kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa tay mashi godiya ta fita lokacin Haulat ta fita tana jiranta suka wuce aji. Da la’asar kuwa sai gashi ya dawo d’aukarsu har saida Haulat taji hakanan ya bata tausayi, Washe gari talata ma da wuri ya shirya yaje d’aukarta yana yin horn biyu sai ga Amadu ya fito bayan ya gaishe shi yace “aikuwa wai ta tafi” shiru yay yana kallonshi kafin yace “U mean ta tafi skul en?” Amadu yace mashi eh yanzu da yaji horn yaje d’akinta don yayi mata Magana ya iske bata nan shine ya tambayi gwaggo tace ta tafi,jinjina mashi kai yay yace mashi “thanks” Amadun yay mashi a dawo lpy ya juyo ya koma gida, zaune yay baija Motar ba yasa hannu guda ya ruk’e ha6arshi yana d’an bugun bakinshi da index finger dinshi wondering why Zaraah ta canja ne lokaci guda, nan take zuciyarshi ta bashi amsa da she loves u dat’s why,d’age kanshi yay sama ya runtse idanunshi tunanin Maganganun Abbas ya shiga yi ga kuma Maganar Dr Habeeb na bp d’inta da ya d’anyi high hakan na nufin he’s responsible for everything, sigh yay ya bud’e idanun a hankali ya kai hannu ya ja Motar ya tafi abun nata mashi yawo a Zuciya, lokaci guda yaji yana son ya tambayeta game da hakan saidae tunaninshi in da gaske Zaraah son shi take ya zaiyi?? A haka har ya isa wurin aiki ba tare da ya samu solution akan hakan ba. Da La’asar Fatuu ta dawo saida taci Abinci sannan ta shiga wanka bayan ta fito ta fara shirin islamiya hakan yasa ta d’an Makara, sanye cikin Uniform ta fito lokacin shagon kawu Amadu a rufe yake don shima yana Makaranta bai dawo ba, saura kad’an ta isa bakin lungun gidan Hajiya da zata karya kwana sai ga Haisam ya taho a kan bike d’inshi zaije gym hakan yasa ta ja ta tsaya shima tsayawar yay lokacin har ya d’an wuce ta don ma ba gudu yake sosae ba, baya yayo da bike d’in ya dawo gabanta suka fara kallon kallo duk da fuskarshi na acikin Helmet amman tana ganin idanunshi lokaci guda taji ta tsargu da kallon da yake mata a hankali ta kai hannu d’aya ta d’an kama gefen hijab d’inta tana d’an matsawa yadda zata hau kan kwanar sosae nan take ya gane abunda take shirin yi wato guduwa har saida ya d’anyi guntun Murmushin mamaki ta ciki ba tare data gani ba wato dae ita bata da ranar girma, hannu ya kai ya cire Helmet d’in daga kanshi hakan yasa ta tsaya tana kallon fuskarshi ba ko k’yaftawa shima kallonta yake a kausashe yace “kina ruguwa zan biki in take ki!!” zaro idanu tay da alama ba k’aramar razana tay da jin abunda ya fad’an ba don bata ta6a tunanin zaice zai mata hakan ba, still idanunsu na kallon juna k’irjinta na bugawa da sauri da sauri yayin da shi kuma yake nazarinta, can ta kasa jurewa ta duk’ar da kanta ba zato kawae sai ganin kwalla yay na d’iga kan hijab d’inta hakan kuma ya k’ara tabbatar mashi da abunda yake son ganewa hakanan ba yadda za’ai don yana kallonta ta kama yin kuka gashi sam a can baya bata jin nauyin had’a ido dashi yarinyar dake mashi k’uri da ido,
“U can go” taji cool voice d’inshi ta fad’a,aikuwa ko kallonshi bata yi ba ta juya da sauri ta tafi saida ta d’anyi nisa ta waigo yana nan bai tafi ba juyawa tay taci gaba da tafiya ba tare da ta sake juyowa ba har sai da ta kai k’arshen lungun ta sake waiwayowa still he’s there da sauri tasha kwana ta shige sai lokacin ya maida Helmet d’in ya ja bike d’in ya tafi,koda taje islamiyyar tunaninshi kawae take duk in ta ganshi sai zuciyarta ta k’ara rikice mata komae ya dawo mata sabo Haulat na lura da ita don ta rigata zuwa saidae yanzu har ma ta saba da ganin Fatun cikin irin halin don tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k’ok’i.
Bayan sallar isha lokacin da Haisam ya dawo ya tsaya bakin shagon Amadu yana ganinshi ya fito yaje wurinshi ya gaishe dashi bayan ya amsa yace yaje yace ma Zarah yana nemanta yanzu a part d’inshi ya amsa mashi da toh ya juya da sauri, lokacin da ya shiga tana parlor ita da gwaggo ta tasa Abinci a gaba tana d’an tsakurarshi, a bakin kopar parlon ya tsaya yace “Ke kije Ya haisam na kiranki ya wuce yace ki iske shi a part d’inshi yanzu” daga haka ya juya ya koma, lokaci guda gabanta yay wani irin bugu ta fara tunanin miyasa zai kirata a cikin ranta,ganin bata da niyyar tashi yasa gwaggo cewa “to ki tashi ko kyaje ki dawo dare nayi in kin dawo kya ci Abincin ki sauri” ido tabi gwaggon dashi lokacin ta mayar da idonta kan TV dama kallo take, a sanyaye ta mik’e ta fita hannunta ruk’e da plate d’in Abincin ta mayar kicin kafin ta koma d’akinta ta daukko mayafi ta d’aura akanta ta tafi, tunda ta tunkari gidan zuciyarta ke harbawa ji take kaman ta rusa ihu, lokacin data k’arasa part d’in nashi a hankali tasa hannu kan handle din ta d’an turo kopar ta leka ganin bai ciki yasa ta idasa shiga ta tsaya bakin kopar tana kallon cikin falon yaushe rabon da ta shigo,rasa yadda zatayi ta sanar dashi tazo tay hakan yasa tayi tsaye ta kasa k’arasawa ciki balle taje bakin Corridor kaman yadda take mashi a da,tanata tsaye ba tare data zauna ba can taji fitowarshi da sauri ta kai idanunta kanshi da alama wanka yayo yana sanye da jallabiya Maroon mai gajeran hannu ganin ya nufo cikin falon yasa ta sunna kanta kasa,kan L-shape yaje ya zauna idonshi a kanta ganin tak’i kallonshi yasa yace taje ta Zauna yana nuna mata bangaren da armchairs suke kaman bazata ba sai kuma ta nufi ciki kaman wadda kwai ya fashe mawa a ciki, kujera ta biyu taje ta zauna ta yadda suna da d’an nisa dashi shiru ya biyo baya kanta na k’asa tana wasa da yatsunta shi kuma ya zuba mata ido yana kallonta ya ma rasa ta ina zai fara mata Magana don yasan ba lalle ma ta fad’i mashi gaskiya ba kaman sauran lokutta,can ya tuna da bata ta6a yi mashi Maganar auren da zaiyi ba nan take ya samu ta inda zai fara,
“Zaraah” taji muryarshi ta sauka a kunnanta a hankali ta amsa ba tare da ta d’ago ba, ya k’ara cewa “Zaraah look at me” jimm ta d’anyi kafin slowly ta d’ago idanun ta sauke su akan fuskarshi,
“Dama ina son tambayanki ne baki san zanyi Aure ba?” motsa baki ta fara yanayin fuskarta ya canja amman ta kasa cewa komae har saida yace bata ji mi yace bane sannan kaman zata yi kuka tace ta sani,
“Ok, ain’t u happy for me shiyasa baki nuna man kina taya ni murna ba?” kaman zata saka kuka tace a’a tana taya shi murna,
“k’arya kike Zaraah baki tayani farinciki zan yi Aure!” taji ya fad’a da d’an d’aga murya, girgiza kai ta fara idanunta har sun ciko da kwalla ta fara rantsuwar tana tayashi farinciki sai kuma tasa mashi Kuka, d’an guntun Murmushin gefe yay still kallonta yake Wannan yawan kukan kawae ya isa ya bayyana akwae abunda take 6oyewa,
gently yace “Zaraah tell me what’s ur problem mike damunki ne”? Cikin sigar lallashi yay mata Maganar, kallonshi tay fuskarta shabe shabe da hawaye tace ” ba komai Ya Ha….” bata samu damar k’arasawa ba sakamakon buga hannun kujerar da yake zaune yace “U’r not telling me d truth Zaraah! Enough of all these lies kinsan bana son k’arya just tell me why u been acting strange! Ba haka nasanki ba, u are not d Zaraah i ave known!” zare ido tay tana kallonshi yana Maganar a harzuke sak kaman ranar da yayi ma Farha fad’a da tayi mata gori yanzu ma da gani ranshi a 6ace yake yay mata Maganar,
“Am all ears Zaraah, mike damunki?” ya sake tambaya bayan ya d’an sassauta muryarshi ta rasa yadda zatayi sai kokonto take a cikin zuciyarta na ta gaya mashi ko karta gaya mashi, ganin ya kafeta da ido yasa ta fara motsa baki a hankali cikin Muryar kuka tace” Ba abunda ke damuna” yaraf ya maida bayanshi ya jingina da kujerar yana cigaba da kallonta ya kankance idanu ita kuma tana ta faman sussuna kai da gani yasan ba gaskiya ta fad’i mashi ba sigh yay calmly ya furta “u can go” aikuwa da sauri ta mik’e ta nufi hanyar fita saidae tana kaiwa bakin kopar sai ta kasa bud’ewa ta fice sakamakon ganin 6acin rai k’arara da tayi akan fuskarshi, kamar an zare mata laka ta juya ta kalleshi ya d’age kanshi sama idanunshi a rufe, slowly ta juyo ta dawo ta durkusa a gabanshi cikin muryar kuka tace “Don Allah YA HAISAM kayi hakurii…..” kawae sai ta fashe da matsanancin kuka ta duk’ar da kanta k’asa,yana daga yadda yake yay wani guntun murmushi jin sunan data kirashi dashi wato HAISAM wanda tunda suke bai ta6a jin ta kirashi da hakan ba,shiru bai dago ba still idanunshi a rufe suke yana sauraran sautin kukan da take yi , sosae take kuka harda sheshsheka her tears trickling down, a hankali ya d’ago da kanshi yana kallon kanta da rabinshi ke a bud’e sakamakon zamewa da gyalen yay cikin wata kalan murya da bata sanshi da ita ba ya kira sunanta ba tare data kalleshi ba cikin kuka ta amsa yace “Look into my eyes Zaraah” a hankali ta d’ago idanunta sunyi jawur ta kalleshi still kukan take saidae ta d’an rage sautinshi, tunda yake bai ta6a jin zullumin a fad’a mashi wata Magana ba kamar yanzu saidae ya za6i yaji koma miye da ganinta cikin halin damuwa haka, shi Mutum ne mai damuwa da damuwar wani ba kuma kamar ita da yake ganin shine silar damuwartata in hasashen da suke ya tabbata,
“Ki fad’a man abunda ke damunki Zaraah, why the sudden change?” bin shi da ido kawae take tana d’an motsa baki had’i da had’iyar yawu, yaci gaba da cewa “am not Happy seeing u like dis, am not at all” yay Maganar yana d’an girgiza kai alamar tabbatar mata da bai jin dad’in ganinta cikin wannan halin,tsam ya mik’e ya bi ta gefenta ya wuce, tissue box ya d’aukko ya dawo inda ya tashi tana ta dai kallonshi ya yago mai d’an yawa ya mik’a mata ta amsa ta fara goge fuskarta ya aje box d’in a hannun kujerar kafin ya juyo fuskarshi a sake cikin muryar lallashi yace “now tell me, kina da damuwa ko??” tsayawa tay da goge fuskar ta d’an bud’a baki a hankali ta jinjina mashi kai alamar eh, sauke boyayyar ajiyar zuciya yay ya d’an gyara zamanshi ya nuna mata close to him yace tazo ta zauna har saida ta kalleshi da sauri ganin wurin da ya nuna matan ya d’an lumshe mata ido ganin hakan yasa ta mik’e ta nufi Kujerar saidae bata zauna gab da shi d’in ba ta d’an matsa kad’an,juyowa yay ta yadda zai facing d’inta sosae ya fara bin ta da wani kalan kallo da sauri ta sadda kanta k’asa ba zato ba tsammani kawae taga ya kawo hannuwanshi ya kama nata hannuwan, da sauri ta runtse idanuwanta tana jin wani abu nayi mata yawo a duk ilahirin jikinta kafin a hankali kuma ta ware su kan santala santalan hannuwanshi farare tas masu d’auke da zara zaran yatsu ga gashi liya liya kwance luff,tunda take dashi tsawon lokaci bai ta6a sa hannu ya ta6a jikinta ba sai yau itace dae ada kan ta girma sosae take ta6a shi shima bazai wuce a kirga ba kaman lokacin da su goga suka so yin raping d’inta da ya zo ta kankameshi sai lokacin da zai masu hoto a park da kuma ranar salla shima da zai masu hoto….tana cikin tunanin taji ya kira sunanta a sanyaye, slowly ta d’aga idanuwanta da suka kankance ta kalleshi cikin ido kaman yadda shima yake kallonta lokaci guda kirjinta ya hau bugawa da mugun k’arfi shi kanshi k’irjin nashi bugawar yake amman ya daure Calmly yace “tell me what’s it??” k’uri tay mashi ko kyaftawa batayi ya lumshe mata ido alamar ta fad’i mashin, A hankali ta fara motsa baki alamar zata yi Magana amman ta rasa ta ina zata fara, jinjina mata kai yay idanunsu cikin na juna ta sake bud’e baki _”Ya Haisam I luv u, I want u to Marry me pls………………..
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.