*ASM Bk2011*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……Tunda ya fito daga Section d’in na su ya rasa tunanin da zaiyi game da inda Zaraah ta tafi a cikin halin ciwo,Wayarshi dake ajiye gefe ya kai hannu ya d’auka ya fara tunanin k’ara kiran Kawu Amadu ya tambayeshi ko ta dawo daidai lokacin ya fito daga Main Gate d’in Makarantar, yana k’okarin kara wayar a kunne kaman ance ya waiga gefe ya hango kaman wata a cikin Bus Stop dake a 6angaren hagu, cire wayar yayi ya katse kiran kafin ya taka burki a hankali ya fara yin reverse har yazo daidai Bus Stop d’in ya sauke glass d’in kopar, k’ura ido yay yana kallon cikin bus stop d’in, wata ce zaune ta d’age k’afafunta sama ta kifa kanta saidae ba lalle a gane ko d’aliba bace don hijabinta ya sauka ta lullube jikinta gaba d’aya kuma kalan hijab d’in ba irin ta sauran d’alibai bace, sanin Fatun irin hijab d’in take sawa don ita prefect ce yasa ya bud’e Motar ya fita ba tare da ya rufe kopar ba ya nufi Bus Stop d’in saidae tun kafin ya k’arasa ya shaida itace sakamakon takalmanta dake ajiye a gefe wanda shine ya k’ara siyo mata su wani zuwa da yay Lagos, tsaye yay bakin wurin yana k’are mata kallo fuskarshi a yamutse sam baiji dad’in ganinta a wurin ba don ba komae a ciki sai uban dirty,
“ZARAAH” ya kirata da wata irin murya shiru bata d’ago ba har saida ya d’an k’ara d’aga Murya ya sake kiranta sannan ta fara kokarin fiddo kanta daga cikin hijab d’in, koda tay arba dashi a firgice ta mik’e tsaye tana kallonshi shima kallonta yake sam fuskarshi ba walwala ganin yadda duk ta canja ga idanunta sun yi ja sun d’an k’ank’ance, kasa jure ma kallon nashi tay ta sadda kai idanunta cike tab da kwalla k’irjinta na bugawa da sauri da sauri,
“Follow me” ya fad’a had’i da juyawa, har ya tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yana mata wani kallo ganin bata motsa ba,a sanyaye ta duk’a tasa takalmanta kafin ta nufe shi da kanshi ya zagaya ya bud’e mata kopar ta shiga ya rufe shima ya zagaya ya shige, jin bai ja Motar ba kuma taji ya shigo yasa ta d’aga kai a hankali ta kalleshi suka had’a ido da sauri ta mayar da kanta k’asa dama tunda ta shigo haka yake, tsit kake ji cikin Motar sai Ac dake ta aiki,
“Zaraah” bayan wani lokaci taji ya kira sunanta, a hankali ta amsa mashi,
“Look at me!” d’an cije baki tay da k’yar ta d’aga ido ta kalleshi sai kuma tasa hannu guda tana d’an murza idanun don bata iya jure ma kallon nashi,
Gently yace “Zaraah what’s ur problem??” cikin disasshiyar murya tace “ba komae” d’an ta6e baki yay kafin yace “in ba komae mi zaisa ki zauna a skul ke kadae after closing hours and kince ma Haulat baki lafiya bazaki attending Practical class ba ta dawo bata iske ki ba ina kika je da baki tsaya kun tafi gida tare ba?” d’an runtse ido tay jin yadda sautin muryarshi ke fita yaushe rabon data ji Maganarshi haka,to miyasa ma yake nemanta da har yaje wurin haulat ta ayyana a ranta, tana cikin haka taji yace ba Magana yake mata ba, d’aga kai tay ta kalleshi kaman zata sa kuka tace “naje Clinic ne ina can aka tashi lokacin dana dawo class kuma banga kowa ba shine na kwanta daga baya kuma na fito na zauna anan” duk da ta d’ago bata kallon idanunshi take Maganar, sigh yay idonshi akanta ya tambayeta mi yake damunta ne saida tay d’an jim kafin tace cikinta ke ciwo,shiru yay yana nazarinta sai faman sussune kai take,
“Why kika daina zuwa gidan Hajiya??” har saida gabanta ya fad’i jin tambayar da yay mata d’an d’agowa tay tana yamutsa fuska tace “ai yanzu wani lokacin har yamma muke kai wa saboda lesson da ake to wani lokacin dana koma nike tafiya islamiyya Weekend ma ina islamiyya” yace “ranar da ba islamiyyan fa ba zaki iya zuwa ba?”
“Ai wani lokacin in na koman na gaji ne amman ko ranar nan naje Hajiyan bata nan sai Aunty Saude kadae na iske kai kuma lokacin baka nan” tana k’arasa Maganar ta dukar da kanta don tasan k’arya ta shirga mashi bata son ya gane kuma tasan bazai ta6a zuwa wurin Saude da sunan ya tambayeta game da abunda ta fad’a ba shiyasa tace mashi haka,shiru yay na d’an lokaci still kallonta yake,
“About coming to skul in d morning miyasa kike tahowa, in baki so ina kawo ki ne u should tell me sai in bari ba kisa inata zuwa kullum ba” d’an runtse ido tay ashe bai jin dad’in hakan, dama kawu Amadu kullum sai ya gaya mata yazo ran Alhamis har yana ce mata kodae ta daure yaci gaba da kai su tunda yak’i daina zuwa kar yaga kaman ana wulakanta shi tace ita dae a’a bata so, jin tunda yay Maganar bai kuma cewa komae ba yasa ta d’aga idanu ta kalleshi ashe kallonta yake nan take idanunsu suka had’u kasa saukesu tay a hankali tace “da..dama an fara yi mana lesson da wuri ne shiyasa muke tahowa amman kayi hakuri” kawae sai taga yay d’an guntun Murmushin gefe ya jingina kanshi jikin headrest, yana daga cikin abunda ke burgeshi da ita wato bada hakuri da ta yi mashi ba daidai ba, a da yayi tunanin harda tsoron yarjejeniyar dake tsakaninsu yasa take saurin bashi hakurin amman daga baya ya fahimci bashi yasa ba kawae haka take, ganin bai ce komae ba yasa tay tunanin baiyi hak’urin ba a hankali ta k’ara cewa “kayi hakuri Ya Handsome” daga yadda yake ya k’ura mata ido itama kallon nashi take tana d’an motsa baki,
“Ya Handsome yayi hak’urin” yay Maganar had’i da lumshe ido da sauri ta kauda fuskarta gefe ita kanta bata ma san Ya Handsome d’in ta ambata ba tuni take son ta daina kiranshi da hakan amman ta kasa saboda ta saba bata ta6a kiranshi da sunanshi ba tunda suke, shiru ya biyo baya kowa da abunda yake sak’awa a ranshi haisam ya d’an d’age kanshi sama gaba d’aya ya yarda da abunda ta fad’a don yasan bata mashi k’arya hakan yasa ya d’an ji sauk’in damuwar da yake ji game da halin da take ciki wani sashe na zuciyarshi kuma na izashi akan ya tambayeta dangane da Maganar da Abbas yay saidae bai san ta ina zai fara ba sai kawae yace mata ance kina sona? ya tambayi kanshi the question sound so silly, juyawa yay ya kalleta ta juyar da kanta gefe tana kallon waje, hannu ya kai ya fara kokarin jan Motar ta juya ta kalleshi sai kuma ta sake kauda kan gefe ta d’an ja hijab d’inta ta rufe Fuskarta, tunda suka hau hanya ba wanda ya k’ara tanka ma wani shi idonshi na akan hanya ita kuma ta rufe fuskar, jin ya tsaya da Motar yasa ta d’an cire hijab d’in tana kallon inda suke don taji sunyi saurin isowa in dai gida suka zo, idasa cire hijab d’in tay tana k’are ma harabar da suke kallo lokaci guda ta fahimci inda ya kawota wato Wani babban private Hospital ne har saida kirjinta ya buga ta juya da sauri ta kalleshi suka had’a ido yace mata ta fito ya bud’e kopar Motar ya fita, ba yadda ta iya jiki a mace ta bud’e itama ta fita ya tunkari main entrance na Asibitin ta bi bayanshi walking slowly, yana shiga reception inda Medical records suke ya nufa dama suna da Family card a Asibitin nan Hajiya ke ganin likita bayan ya masu bayani an shigar da sunan Fatun suka ce ya kaita Nurses room za’a d’auki BP nata sai a tura su wurin likita ya amsa da Ok, juyowa yay yayi mata alamar ta biyo shi da hannu suka nufi window d’in da a samanta aka rubuta Nurses room d’in yana tsayawa kafin yay Magana yaji daga gefenshi an ce “H,Zakee d latest ango to be” juyawa yay ya kalli mai Magana da fara’a ya furta “Dr habeeb” yana k’araso ya mik’a mashi hannu suka gaisa da fara’a yace “to ya shirye shirye, ai Abbas ya tura mana iv in sha Allahu damu za’a d’aura Auren” da Murmushi kan fuskarshi ya amsa da Allah ya yarda,
“Amman miya kawo ka Asibiti ko kana fever d’in angwancewa ne” yar dariya yayi ya nuna mashi Fatuu yace sis d’inshi ya kawo,ya kai idonshi kanta kafin ya juya kan haisam yace “an tura ta wurin Dr ne?” yace “No yanzu za’a tura” jinjina kai yay ya lek’a ta windown yace ma Sister d’in dake zaune tay taking BP nata ta tura mashi ita yanzu ta amsa da “Ok Dr”, kallon Fatuu ya sake yi yace ta zagaya ta shiga ciki ta amsa da to bayan ta gaidashi ta tafi sukuku da ita ta shiga shi kuma suka cigaba da Magana da Haisam yana mashi complaining kan rashin Network mai kyau da suke fuskanta sai ana cikin aiki ya yanke Haisam d’in ya fara suggesting abunda yakamata suyi suna cikin haka Fatuu ta fito yace ma Haisam su tafi consultation room yace Ok, bayan sun shiga Dr d’in ya nuna ma Haisam kujeran dake gaban desk ita kuma Fatuu ta gefenshi yace ta zauna ya fara lallatsa Computer d’in dake sama kafin ya d’ago da d’an Murmushi yace ” yauwa sis mike damunki ne?” shiru ta d’anyi sai taji dama bata ce ma Haisam ciwon ciki take ba yanzu ba daman ta canja ciwo, a hankali tace,
“Ciwon ciki ne”
“Ok ciwon ciki wane iri, kina period ne?” damm gabanta ya d’an fad’i duk sai taji nauyin tambayar shima Haisam dake latsa waya cak ya tsaya hakanan yaji yana son jin amsar da zata ba likitan,
“Ok yaushe kika fara ne?” saidae kawae haisam yaji wannan tambayar ta likita don da kai Fatuu ta bashi amsar tana yi d’in,
“Shekara biyu” ta fad’a k’asa k’asa,
“To dama duk in zaki kina ciwon ciki ne?” kai ta d’aga mashi alamar eh ya sake cewa “Yanzu shine ya saki ciwon cikin ko kuwa wani ciwon cikinne daban?” a hankali tace mashi shine duk da k’arya take ba period d’in take ba yanzu, tambayarta yanayin yadda take jin ciwon yay ta bashi amsa ya jinjina kai kafin yaci gaba da rubutu a Computer d’in can ya sake kallonta yace bayan wannan ba abunda ke damunta tace eh, Jama’a ina Haisam? da alama ya k’ame a inda yake saboda tsabar mamakin jin wai Zaraah na period for good 2 years now abunda bai ta6a zato ba duk da yasan ya ta6a yi mata fad’a kan sakin baki tana fad’in abu irin haka amman bai yi zaton zata iya rikewa ba tsawon shekara biyu ba tare da ya sani ba, kallonta likita yay bayan ya gama rubutun yace ta jirasu a waje don ya lura duk bata sake ba ta mik’e sumimi sumimi ta fice, Doctor ya kalli haisam yace mashi ba wata matsala bace menstrual pain ne ai yaji ma ya d’aga mashi kai kawae yace yanzu ya tura Magani zasu je pharmacy a amsar mata ya amsa da Ok yana kokarin mik’ewa Doctor ya dakatar dashi ta hanyar cewa”amm H,Zakee, sis d’in nan naka ba wani abu dake damunta banda wannan ciwon?” komawa yay ya zauna yana kallon doc d’in yace akwae matsala ne,
“No,ba wata matsala bace babba just bp d’inta ya d’anyi high gaskiya so bansan ko wani abun na damunta bane amman zai iya yuwuwa ciwon da take yasa shi hawan is possible” ya k’arasa yana jinjina kai, shiru Haisam ya d’anyi doc Habib yace kar ya damu zai iya yuwuwa ciwonne amman zai iya tambayarta yaji in wata damuwarce kar abun yay yawa ya amsa mashi da to suka mik’e tare suka fita lokacin tana zaune kan dogon bencin dake kallon d’akin ganin likitan suna fitowa ta had’a ido da Haisam da sauri ta juyar da kanta gefe don yanzu sai taji tana kunyar had’a ido dashi ganin yasan abunda tasan bai sani ba, shima d’auke kan yay ya bi Doctor suka je
pharmacy d’in aka bata magungunan, lokacin da suka fito bata sani ba saida suka zo saitin inda take zaune ta d’ago yay mata alamar su je da kanshi ta mik’e da sauri tay gaba, suna fitowa harabar Asibitin Haisam yace ma doc ya koma shi dake cikin aiki suka yi sallama yay mashi godiya kafin kowa ya juya ai tana ganin ya nufo Motar ta bud’e da sauri ta shige, lokacin da ya bud’e Motan ya shiga ta juyar da kanta ta rufe face d’inta da hijab kaman yadda tay da zasu zo, idonshi akan hanya bayan sun fito yana ta driving bai tanka mata ba saidae can k’asan zuciyarsa he was totally surprise,sai yan tunane tunane yake lokaci bayan lokaci yake d’aga ido ya kalleta ta cikin Mirror, a daidai gaban wata babbar Super Market ya parker Motar gefen hanya tana jin sun tsaya ta cire hijab d’in tana kallon inda suke jin ya bud’e Motar yasa ta waiga ta kalleshi lokacin ya fita daga cikin Motar ya zagayo ta side d’in da take ya nufi cikin wurin tana ta kallon bayanshi har ya shige ciki taci gaba da kallon wurin, bada jimawa sosae ba ya fito hannunshi ruk’e da babbar shopping bag mai d’auke da tambarin wurin tana ganin ya taho da sauri ta k’ara rufe fuskar, back door ya bud’e ya ajiye ledan kafin ya zagaya ya shiga ya ja suka tafi, yana driving yana cigaba da kallonta ta mirror ba komae yafi tsaya mashi ba face hirar su da Abbas ga kuma Abunda Doctor Habeeb yace game da BP d’inta,suna shiga layin gidansu ta bud’e fuskar tana kallon gefenta har suka k’araso kopar gidansu a hankali ta juya ta kalleshi tace mashi ta gode yay nodding kanshi tana niyyar bud’e Motar taji yace “da yaushe kuke zuwa skul din?” d’an kyakkyafta idanu tay ta d’an d’age baki tace “da wuri dae muke tafiya wani lokacin k’arfe bakwae ko da yan mintuna” calmly ya furta “Ok” ta bud’e Motar ta fita ganin tana niyyar nufar gida ya sauke glass d’in ya kirata ta juya tana kallonshi yace ta d’auki kayan baya nata ne kai kawae ta d’aga mashi ta bud’e ta d’aukko ledar ta lek’a ta gaban tace mashi ta gode, bin ta da ido kawae yay ta janye kan sai kuma ta kasa tafiya tana ta kallonshi ya ja Motar ba tare da ya rufe glass d’in ba tabi bayan Motar da kallo, sai lokacin hankalinta ya kai kan wak’ar dake tashi daga cikin shagon kawu Amadu ta Hamisu breaker wato so dangin Mutuwa,natsuwa tay tana saurarar baitinkan wak’ar kamar haka,
_🎼🎼🎻So dangin Mutuwa ne shi don baya duba rarrashi so guba ne kama da Madara yake, shi Masoyi yana da gaggawa buri nay ya yi wa so k’awa shi kuma so kama da kura yake🎼_
_So bai san wata kara ba,bazai ragawa kowa ba,kullum tanadin kushewa yake_🎼
_……..So baza ya kyale tsoffi ba, kuma bai tsallake MAKWABCI BA nagane shi illatarwa yake🎼_
Tana jin wannan baitin ta juya da gudu ta shige gida sam shi kawu Amadu bai ma san da ita a wurin ba yana can yana sauraren wakarshi, tana shiga d’akinta ta nufa ta haye gado tana ta6e baki kwalla suka fara gangarowa kan cheeks d’inta don sai taji kamar don ita akai wakar can ta jawo jakar da ta shiga da ita ta zazzago abunda ke ciki, k’amewa tay baki bud’e tana kallon uwar Pads d’in da ya siyo mata dasu turarurruka kawae sai ta idasa fashewa da kuka, dole ma tay kuka wllh rasa Haisam matsayin Miji ba k’aramar Asara bace yanzu da bata had’a komae dashi ba ji uwar hidimar da yake da ita ina ga kuma ace shi Mijinta ne, Mutum ne shi da yasan yakamata wanda ba tantama zai kare hakkokin Matarshi sosae, haka ta d’ingi riskar kuka har ta gaji don kanta ta tashi duk da kanta na mata wani irin ciwo ta cire Uniform d’in jikinta ta d’aura towel ta nufi toilet don yin wanka, bayan ta gama shiryawa ta kabbara sallar Azahar da bata yi ba tana gamawa tabi da La’asar da aka yi bada jimawa ba, bayan ta gama sosae tayi Addu’oi tana zubar da kwalla ta rok’i Allah in Haisam rabonta ne Allah ya batashi matsayin miji in ba rabonta bane kuma yasa ta hak’ura dashi,bayan ta shafa ta mik’e jin kanta nayi mata ciwo ta fita taje d’akin gwaggo ta d’aukko Magani bayan ta sha ta koma kan gado ta kwanta ta fad’a duniyar tunane tunane ita kanta ta san mawuyacin abu ne ta Auri Haisam ba kamar da ta ji da bakinshi yace baida ra’ayin mata biyu kawae zuciyarta ce ke takura mata da soyayyarshi, yunk’urawa tay ta tashi zaune a fusace ta fara buga katifa tana Fad’in “Ki daina takura man don Allah, bai sona, bai sona miyasa kike azabtar dani da son shi ne!!!” ta k’arasa tana ta huci ta kumbura baki, a hankali kuma ta koma ta kwanta tana cigaba da hucin da alama zuciyarta ta kaita mak’ura a haka bacci 6arawo yay awon gaba da ita………
_Dandano Daga Next Page_
…….Da sauri ta runtse idanuwanta tana jin wani abu nayi mata yawo a duk ilahirin jikinta kafin a hankali kuma ta ware su kan santala santalan hannuwanshi farare tas masu d’auke da zara zaran yatsu ga gashi liya liya kwance luff,tunda take dashi tsawon lokaci bai ta6a sa hannu ya ta6a jikinta ba sai yau itace dae ada kan ta girma sosae take ta6a shi shima bazai wuce a kirga ba kaman lokacin da su goga suka so yin raping d’inta da ya zo ta kankameshi sai lokacin da zai masu hoto a park da kuma ranar salla shima da zai masu hoto….tana cikin tunanin taji ya kira sunanta a sanyaye, slowly ta d’aga idanuwanta da suka kankance ta kalleshi cikin ido kaman yadda shima yake kallonta lokaci guda kirjinta ya hau bugawa da mugun k’arfi shi kanshi k’irjin nashi bugawar yake amman ya daure Calmly yace “tell me what’s it??” k’uri tay mashi ko kyaftawa batayi ya lumshe mata ido alamar ta fad’i mashin, A hankali ta fara motsa baki alamar zata yi Magana tace”………..TILL MONDAY IN ALLAH YA KAI MAMU RAI.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :Â Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :Â @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:Â Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.