Uncategorized

Kawa Ta Aure Saurayin Kawarta Nan Take Bayan Ita Kawar Ta Ce Ba Ta Son Saurayin A Yayin Da Ake Cikin Addu’ar Daurin Aure

 A ranar Asabar ne wani abin mamaki ya faru a Unguwar Katsinawa dake garin Mararrabar/Nyaya, inda wata budurwa ta ce a dakatar da shagalin aurenta da ake kan yi, saboda ba ta son saurayin da yake shirin auren nata.

Wani abin mamaki da ya auku shine ana tsaka da mamakin danyen hukuncin da yarinyar ta yi, nan take sai daya daga cikin kawayenta ta fito ta bayyana cewa ta amince a daura auren da ita idan har shi saurayin ya amince.

         KARANTA WASU LABARAN

Ana zargin wani kwastoma da kashe wata Karuwa a jihar Jigawa.

Da gaske Mai shadda zai auri Aisha Tsamiya ?/ jaruma ta koma kurkuku/rigimar yan tiktok da 13×13

Zafin Kishi ya sanya wata mata caccaka wa mijinta wuka har sai da yace ga garinku nan

Farashin Burodi Ka iya tashi a Nijeriya Saboda Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.

Nan take shi ma saurayin ya ce ya amince ba tare da wata-wata ba aka daura masu auren.

Amincewar bazatan da sabuwar Amaryar ta yi domin a daura mata aure ba tare da ta shirya ba, ya sanya ta sha ruwan addu’o’in fatan alkairi daga jama’ar unguwa, inda ita kuma wadda ta fasa auren ake ta yin Allah wadai da abinda ta yi.

Saidai a safiyar yau Lahadi RARIYA ta samu labarin cewa budurwar da ta ki amincewa a daura mata auren ta yanke jiki ta fadi, inda aka garzaya da ita asibiti, inda kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu tabbacin ko an sallamo ta.

Wasu dai na dangata sumar tata da nadamar kin amincewa a daura mata auren da ta yi, saboda kin amincewa tata bai sa an soke auren ba, sannan kuma hidimar bikin ya karu fiye da yadda aka tsara tun a farko.

Back to top button