Hausa novels

Kurkukun Kaddara Chapter 2 By Boss Bature Complete Novel

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Boss Bature ✍️*

dedicated to Aunty kubra😘

*E2*

The Begining Of The Story,(Farkon Labari)

ƙasa ƙasa Cikin baccinsa ya soma Jin sautin kukan Jariri acikin kunnuwan shi, tun abun bai damun shi har kukan Ya fara addabar shi, ya hana shi sakat wanda Hakan Yayi silar farkawar shi daga bacci, a hankali ya ɗan ware manyan idanuwan shi masu ɗauke da Bacci don da alama bai gaji da baccin ba, Ceilling Ya ƙurawa ido kamar mai karanto wani abu, a ƙoƙarin shi naya tariyo abunda kunnuwanshi ke jiyo mashi wanda Yayi silar farkawar sa daga Bacci,

Yana ƙoƙarin tunanowa Kwatsam Yaji kukan Jaririn Inya inya, mai sautin gaske, Zumbur ya ƙarasa Janye Blacket ɗin daya Lullu6a dashi Yayi wurgi dashi gefe ɗaya, kayan Bacci ne Ajikinshi Brown Colour Riga da wando, yayi mamakin ganin babu ita asaman gadon, ko ina taje ne? sauko da ƙafafun shi ya yi ƙasa ya yi, Cike da fargaba Ya miƙe yana mai tunanin Inda aka samu Kukan Jariri Acikin Gidansa, Shi dai A iya sanin shi Matar shi bata haihu ba,duk da cikinta nata yakai wata tara,

Gaba ɗaya ya ruɗe Yama rasa Ta ina zai ga Jinjirin dake kuka, Domin kuwa sautin ya karaɗe Ɗakin nashi,zukunnawa Ya yi tare da leƙa ƙarƙashin gado, wayam baiga komai ba miƙe wa ya yi da sauri ya nufi wardrobe Ya buɗe ya zazzago da kayan dake acikinta, duk a ƙoƙarin shi naya gano inda aka samu kukan Jariri aɗakinsa, Tuni ya haɗa uban gumi ajikinshi, aran shi harya fara tunanin kodai Aljanune!? abu kamar wasa idan jaririn yayi kuka sai ya lafa ƙasa ƙasa,wannan karan Yanayin kukan tamkar Ana zare Ranshi ne, har wani jan kukan akeyi inyaaaaaaa,

“Ka duba toilet”?zuciyar shi ce tayi mashi tambayar, shiru ya ɗanyi kamar me tunanin wani abu,tun da yake arayuwar shi wani abu bai ta6a tsorata shi ba irin na yau, kukan jaririn duk ya firgitar da shi,har wani gumi ya haɗa,

Ja da baya da baya yayi a hanzar ce Ya juya gaban Faskeken Madubin ɗakin, Wayar shi ya ɗauko yana dannawa Call logs Ya shiga, missed calls Ya tarar Na Uzair, babban amininsa

Calling Layin yayi tana fara ringing, uzair ya ɗaga kiran ko sallama baiyi ba ya soma magana”Uzair Akwai matsala Cikin gidan nan fa!” muryarshi na kerma yayi maganar,

On the other hand Uzair yace”Wata irin matsala kenan?
“Kukan jariri ne Ya tashe ni daga bacci,Bansan a ina aka samo kukan ba, kuma na tashi banga benazir ba”

“Ka kwantar da hankalin ka, Gani nan zuwa”
“Yawwa,dan Allah kayi sauri” rejecting call ɗin yayi kafin Ya ajiye wayar saman bedside drawer,

Walking Slowly Ya nufi hanyar toilet ɗin Cike da fargabar abunda zai taras, cikin sanɗa yake yin tafiyar, jikinshi na kerma,a hankali ya ruƙe Handle ɗin ƙopar ya buɗeta

Haɗadɗen toilet ne Ko’ina Na Cikinshi Fari ƙal atsaftace ba ƙazanta, kamar ance Ya kalli ƙasan tiles,Ba zato ba tsammani Yaga ɗigon jini, Gaban shi ne Yayi wani irin mugun bugu ji kake daram! a firgice Ya ɗago da idanuwan shi yana kallon Cikin toilet ɗin,Wani irin tsoro ne Ya kama shi lokacin daya hango Jikin Bathtub(kwamin wanka) jaga jaga da Jini kamar an yanka ɗan akuya, a ruɗe ya soma ambaton Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un, kamkar a mafarki yake kallon Lamarin, Cike da fargaba ya ƙarasa shiga cikin toilet ɗin don ya gane wa idanuwanshi, a dai dai bakin kwamin wankan Ya tsara turus, Yana Kallon Jinjirin dake Acikinsa kwance,duk jini Ya wanke jikinshi Sai tsanyara kuka Yake yi,
Lokaci guda gabanshi Ya faɗi rass tunawa da wasu maganganu da suka tsaya mashi aranshi tun shekaran jiya

Tuni ya karaya hakan na nufin a daren Jiya ta haihu acikin toilet, saboda ƙarfin hali irin nata har ta iya haihuwa da kanta ta kuma Gudu duk da irin Jinin da ta Zubar, abun yayi mugun ɗaure mashi kai, ga wani irin ƙunci da yake Ji acan ƙasan Zuciyarshi, Tuni hawaye sun wanke fuskarshi, sam bazai juri ganin jaririn shi a cikin mawuyacin hali ba, sosai ya fashe da kuka tare da kai hannayenshi cikin bathtub ɗin Ya ɗauko Jaririn, bai damu da kayanshi su 6ace ba ahaka ya ƙanƙameshi ajikinshi yana shar6ar hawaye,

“Taj!taj!! muryar amininsa ce da alama sun shigo cikin gidan, Atare suka faɗo Cikin ɗakin nashi a fujajen, Su Biyu ne shida Matarshi wadda ke sanye Cikin Jallabiya baƙa, Ta yafa mayafi akanta, farace tass doguwa,Shi kuma Uxair din, Jallabiyace ajikinshi brown color

Shigarsu keda Wuya Sai gashi Ya fito rungume da jaririn a ƙirjinshi,

Aruɗe suke kallonshi, murya na kerma Aneelarh tace”Ta haihu ne”?
Tunkafin ta rufe baki Uzair ya kar6e da cewa”Meya ke faruwane taj?wannan Jaririn fa?Kodai ta sauka ne”?
Daƙyar ya iya daidaita natsuwarshi ya soma magana”Ita ce tabar mun shi, nima bansan meya faru ba, kawai naji kukan jariri, shine ma Ya tashe ni daga bacci,a toilet na sameshi cikin bathtub”
Atare suka haɗa baki suna salati, Kafin Aneelarh ta kar6i Jinjirin Tabi ta gefenshi ta nufi toilet don ta gyara mashi jikinshi,

Uzair kuma Yaja Hannun Taj suka fito falo, tsayawa Sukayi suna fuskantar Juna, ran kowannan su a6ace,
“Amma dai matar nan anyi ƴar akuya, dama can Ni bata kwantamun araina ba, In banda daƙiƙanci taya laifin ka zai shafi abunda ke cikinta”?

tun kafin yakai ƙarshen maganar taj ya katseshi da cewa”Laifin me nayi mata Uzair!? meyasa wasu mutanan basu da tunani ne?sun ɗauki duniya wurin zama,Suna manta cewa wata rana dole su koma Ga Allah, kuma zasu yi bayanin duk wani abu da suka aikata mai kyau ko mara kyau,” dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yaja numfashi kafin yaci gaba da magana,.
“Benazir Ta ƙona mun rai, bazan ta6a yafe mata ba, Allah ya isa tsakanina da ita,Ta nuna mun rashin imaninta ƙarara akan Jariri na, In sha Allah Zata ga Sakayyar hakan……”kafin Uzair Ya kuma Furta wani abu, Sae ga Aneelarh Ta fito hannunta ɗauke da jaririn cikin lallausan towel fari, wani irin farin Cikine akan fuskarta,tunkafin ta ƙaraso wurinsu ta soma ambaton”Tabarakallahu Ahsanul kaliqin, Tunda nake amsar haihuwa a asibitin mu ban ta6a Cin karo da kyakkyawar Jinjira ba, Irin wannan Hurul ainin dake a hannuna ba….

A sukwane Uzair da Taj suka kalli juna kafin suka mayar da idanuwansu kanta,
“Am just Speechless wlh, Ka gode ma Allah, Da Benazir bata yi tunanin kashe maka itaba, da kuwa munyi Babbar asara,”takai ƙarshen maganar adai dai lokacin ta ƙaraso gabansu,.

Slowly Taj da Uzair suka ɗaura Idanuwan su kan Jaririyar, Saboda tsabar Kyanta har Razana saida Suka ɗanyi, Babu wanda yayi tsammanin ganin jaririyar haka, farko ma sun yi tunanin Namiji ne saboda hankalinsu ba’a kwance yake ba, ashe ta maca ce,

Fara ce Sol har wani shining skin ɗinta take yi saboda tsabar haske, Natural Beauty ce, Bakomai yafi jan hankalin su ba, face Ƙwayar idonta (vivi gray) mai launin ruwan Toka ash Colour, ta ciza har ƙyalli take Yi, Sumar kanta Brown Colour ce Curly mai nannaɗa, har saman goshinta wani kwantaccen gashi ne, kuma kan nata acike yake da yalwataccen gashi, ga dogon hanci Allah ya bata, ga kuma Ƙaramin baki, mai ɗauke da siraran la66a Pink colour kamar an shafa mata jan baki,

Saboda tsabar farin Ciki,taj Ya kalli gabas Yay sujjada Yana kuka Yana Gode ma Allah.

“Ka fara tsarka ke jikinka mana,”Uzair ne yayi mgnr.

Murmushi suka saki gaba ɗayansu a ya yin da suke Kallon shi,
“Ina taya mu farin Ciki sosai, Aneelarh Wannan kyautar Allah ce agaremu, Naji dadi da Benazir batayi tunanin kashe jaririyar ba,
Murmushi aneelerh ta ɗanyi”Ji nake kamar nafi mahaifin Yarinyar Farin Ciki, yau Rana ce me cike da tarihi, Ranar da Taj Ya zama Uba,
Murmushi suka kuma saki atare,A lokacin Taj ya ɗago daga sujjadar, hawaye sharkaf akan fuskarshi, Bazai iya misalta irin farin cikin da yake Ciki ba,

Miƙewa Yayi tsaye Ya koma gabansu, hannu ya miƙa ma aneelerh ta bashi babyn, maƙe mashi kafaɗa tayi, tare da yi mashi nuni da idanuwanta, sai lokacin ya tuna da yadda jikinshi ya ke, duk ya 6ace da jinin babyn sa daya ɗauke ta ɗa zu, Mirmishi ya sa ki da sauri Ya kama hanya zuwa bedroom ɗin sa, within mins sai gashi ya dawo jikinshi sanye da jallabiya, ya gyara jikinshi miƙa mata hannu ya yi batare da musu ba ta miƙa mashi ƴarshi, Yasa hannu biyu ya kar6e abunshi, sosai ya ƙanƙameta, Ya tsare ta da idanuwashi yana kallonta, Sae faman mutsu mutsu take Yi, ta tura yatsanta ɗaya acikin baki sai tsotsa take Yi,

Ba komai ya fi ɗaure ma shi kai ba a game da yarinyar face kwayar idonta, kaf dangin su babu mai irin launin ƙwayar idonta, sai dai ko acikin dangin mahaifiyarta,

Cikin sanyin murya ya soma magana Yana kallonta”ke kyautace agare Ni, Inasonki Sosai, Allah ya raya mun ke bisa tafarkin addinin islama, Allah Ya bani ikon kula dake Alfarmar annabi muhammad (SAW) Allah ya tsare mun ke, Allah kuma yasa ki xama silar farin Cikinmu,” haka ya dinga Jero addu’o’i, Suna uxair suna amsa mashi Ameen ameen

*SHIN WANENE ZAHEER TAJUDDEEN?*

Tajuddeen ɗan asalin Wani ƙauye ne da ake kira Buzaye wanda ke a ƙarƙashin ƙaramar hukuman ɗanja dake a jahar katsina, Haifaffen ɗan garin ne, nan ne tushen shi, anan dangin su suke,mahaifin shi da mahaifiyarshi Auran Zumunci ne, Ƴa’ƴan wa da ƙanine, Malam Zahiru shine sunan mahaifinshi, Mahaifiyar shi kuma Yahanasu, tun da su ka yi auren Allah bai ba su haihuwa ba, abun tun bai damun su harya fara damunsu, mutanan garin har sun fara yi masu surutu kan rashin haihuwa, haka dangin su ma, sun fara tanka masu akan Haihuwa, musamman Deeje Mahaifiyar malam zahiru, kullum mitar rashin haihuwar matarshi take yi, Ita dai burin ta a haifa mata Jikoki, sun shiga mawuyacin hali,Har shirin zuwa asibiti su ka yi don a duba lafiyar su a gano inda matsalar take, A wannan Lokacin basu da babban asibiti A yankin sai da su ka yi tafiya zuwa cikin jihar katsina, Suka sauka agidan balaraba ƙanwar Yahanasu da ke aure anan Cikin garin, sun samu kyakkyawar tarba a wurinta,haka mijinta ma, ya yi farin Ciki da zuwansu, domin kuwa malam zahiru Abokin shi ne ta silar shi Ya haɗu da balaraba, Kwanan su ɗaya a gidan ta, a washe garin ranar Suka je asibiti aka duba su, A ƙarshe dai Likita ya tabbatar masu da cewa Lafiyarsu qalou Lokacin haihuwarsu ne baiyi ba, Su Cigaba da addu’a kawai in dai suna da rabon haihuwa aduniya to zasu ga jininsu duk mun daren da ɗewa, kwanansu Uku a katsina suka dawo nan buzaye, Koba komai hankalin su Ya ɗan kwanta,tunda an tabbatar masu da cewa basu da matsalar Haihuwa,

Bayan tsawon Lokaci Da yin aurensu, Kusan shekera ashirin da biyar kenan, A wannan Lokacin Allah Ya kawo ƙarshen koken rashin haihuwarsu, wato Yahanasu ta samu Ciki, saboda tsabar farin Ciki har ƴar ƙwarya ƙwaryar walima suka shirya aka kira masu kiɗan kwarya, Aka ci aka sha,

A kwana a tashi, yahanasu ta haifi kyakkyawan jaririnta wanda yaci sunan shi Tajuddeen sunan Mahaifin Malam Zahiru, Tun yana yaro suka ƙwallafa rai akanshi, Kowa son shi yake yi, kuma tun daga shi Allah bai ƙara basu haihuwa ba har suka tsufa, a lokacin da taj ya fara girma, kawun shi ƙanin mahaifinshi Ya kwallafa rai akan subar mashi Yaron tunda basu da hali, Yanaso ya ɗauki nauyin karatunshi, acan inda yake aiki Jihar Jos, a lokacin ƙin yadda su ka yi saboda shi kaɗai ne ɗansu wanda suke kallo suji daɗi a duniyar nan, sunfi son ko da yaushe Ya kasance atare dasu, Babu yadda Uncle ɗin nashi ya iya dole yabar masu abunsu, Amma duk da haka sai da ya taimaka masu da abunda zasu kula dashi, don kafin tafiyarshi,Sai da ya tabbatar sun sanya shi makarantar Boko da islamiyya, tukunna Ya tafi,

Tajudeen tunda ya taso Yaro ne mai hankali da natsuwa akwai na annabawa wato haƙuri mutun ne maison Jama’a, ga son Ibada,ga tsafta sam baida wata damuwa a rayuwarshi, ga kyautata ma iyayen shi, tun yana ɗan shekara Goma shabiyar aduniya yake ƙoƙarin ɗaukar nauyin iyayen shi,Wasu aiyukan na mata duk ya iya su, Share share wanke wanke,wankin kayan su da guga, Ɗebo ruwa a rijiya,Hatta girki Mafi yawan lokutta indai ba makaranta, shi yake zama ya girka masu abinci, shiyasa a kullum iyayen shi suke ƙara sonshi, kullum Cikin sanya mashi albarka su ke yi.

Bayan Tajudden Ya kammala Secondry school, Wannan uncle ɗin nashi dake a Jos Ya ƙara kawo masu ziyara, Ai tunda Yayi arba da tajuddeen yaga Yadda ya sauya, Ɗan kyakkyawan matashi, nan fa ya ƙara sa naci akan subar mashi yaron Ya tafi dashi Can Ya sanya shi Jami’a dama yana da ɗa ɗaya Tilo mai suna Uzair burin shi ya haɗasu Wuri ɗaya su yi karatu atare, Nan ma suka ƙi amince mashi, haka shima Tahujudeen ya kafe akan baison zuwa yafi son zama da iyayenshi,

Babu yadda Uncle ɗin bai yi dasu ba, Amma suka ƙi yadda,a karshe Ya yanke shawarar zuwa wurin mahaifiyarsu deeje,

Lokacin daya je wurinta, Sosai ya Tunzurata, Ya nuna mata irin Albarkar da zasu samu da yaron idan ya tafi dashi birni,A ƙarshe dai hada Cin hanci Yaba uwar tasu, da yake tsohuwa deeje akwai shegen son kuɗi, Shiyasa Ko tsakaninshi da malam zahiru, tafi ji da shi saboda duk in zaizo Buzaye sai ya haɗo mata sha tara na arziƙi, haka idan zai tafi ma,

Babu Yadda Yahanasu da malam zahiru suka Iya, Ba da son ran su ba, A wannan lokacin suka rabu da tajuddeen, Suna kuka yana kuka, gwanin ban tausayi duk da Uncle ɗin ya yi masu alƙawarin duk In suka samu hutun makaranta zai turo masu shi, hada mai aiki ya ajiye masu agidan wadda za ta ci gaba da kula dasu kamar yadda tajuddeen yake yi masu, hatta Ginin gidansu sai daya sabunta masu shi,

Bayan tafiyarsu Jos, Rayuwar Tajuddeen ta canza sosai, Yana samun kyakkyawar kulawa a wurin Uncle ɗinshi da kuma matarshi Hajiya Adama, ga kuma aboki daya samu ɗan uwan shi Uzair, wata irin shaƙuwace a tsakaninsu, kullum suna atare, dare da rana a tare Uncle abdallah ya sanyasu A university kuma Course ɗaya suke karanta 6angaren jarida, da yake ra’ayinsu yazo ɗaya, duk in lokacin hutu ya yi Sukan shirya shi da Uzair su tafi Buzaye wurin danginsu, Har hutunsu ya ƙare tunkunna suke dawowa gida,

Bayan Wani Lokaci, Tajuddeen da Uzair Su ka kammala degree ɗinsu, dama kuma tunkafin Su yi graduation, kowannan su yana da budurwar shi wadda yake da burin aure, Taj dai Wata ɗiyar hamshaƙin mai kuɗice ɗan siyasa Allah Ya haɗa shi da ita, Kyakkyawar gaske Asalinta ma half cast ce,mahaifiyarta balarabiyar Egyp ce, mahaifinta kuma Bahaushe ne gaba da baya, Sunanta Benazir Sam bata da sauƙin kai, maca ce mai matuƙar Ji da kanta, Sam bata mu’amala Da mutun idan har mahaifin shi ba shahararren mai kuɗi bane kamar mahaifinta, kuma ba’a ta6a ta a zauna Lafiya, shiyasa kowa ke shakkar shiga gonarta, ƙawarta ɗaya kwallin kwal wadda Jinin su ya haɗu da ita, amma kuma halinsu yasha banban, Aneelerh maca ce mai sauƙin kai, ita kanta ƴar masu kuɗi ce amma bata ɗauki duniya da zafi ba, Tana bin komai asannu, Ga tarin ilmin addini da take dashi, Dukkanninsu kowa da Course ɗin da ya karanta,Ita Benazir Business administration ta karanta, Aneerlerh kuwa Medicine ta karanta, tunkafin ma ta kammala karatu mahaifinta Ya gina mata Privet hospital mallakin ta, atare su ka yi karatunsu ƙasar germany ita da aneelerh, farkon haduwar su A cikin jirgi ne suka fara sanin juna, A lokacin zasu tafi Germany ƙaro karatu, sun zauna a seat ɗaya cikin jirgin, kasancewar aneelerh bata cika shariya ba, ko batasan mutun ba, takan gaida shi harma taja shi da fira, ita ta fara yi ma benazir magana suka fara fira sama sama, tana ta shan ƙamshi, sai ga shi daga baya da suka isa ƙasar germany sun kuma haduwa a University ɗaya, Sunyi mamaki daganan kuma suka ƙulla zumunci,

Bayan sunyi degree suka dawo Nigeria, Sati ɗaya da dawowar su suka shirya zuwa Shopping Mall domin yin siyayya, anan Allah ya haɗa su da Su tajuddeen suma ranar sunje yin siyayya, basu sha wahala ba, wurin samun amincewa daga wurinsu, In a short time soyayya mai ƙarfi ta kullu atsakaninsu, har takaisu ga yin aure, Wannan shine farkon haɗuwarsu, Taj bai tashi sanin wacece Benazir ba, Sai bayan da aka shafa fatihar auransu, Aka kaita Gidanshi, ta hana abokan ango shugowa Siyen baki, dama Ko time ɗin da aka kaita gidan, Family ɗinta ne zalla babu ƙawaye don bata Hulɗa da mutane, Aneelerh ce kawai Aminiyarta da akayi masu aure rana ɗaya, Sati ɗaya su ka yi suna shan soyayya, Ta iya tarairayar miji da bashi hakkin shi akan lokaci, sai dai bata Iya girki ba, kuma bata iya Gyaran gida ba, dai dai da gyaran gado wannan batasan Ya zata yi shi ba, saboda tsabar sangartata da akayi, ranar da ya yi mata complain kan cewa Tayi mashi girki sai cewa tayi, ba’a halicci Hannayen ta donsu girka ma ƙato abinci ba, tsabar 6acin rai kamar Ya rufeta da bugu bata iya komai ba, sai danne dannen waya ko salla sai taga dama take yinta don wani lokacin Sai dare take hada sallar Azahar da isha’e da magrib duk tayi su a lokaci ɗaya.Salatul fajr kuwa, Sai ƙarfe goma na safe take Yinta, idan ya yi mata nasiha sai tace “Ae ba a ƙabari ɗaya za’a binne mu ba, mommy ta sanar dani cewa in yi sharholiya ta son raina Aljanna tamai rabo ce,”

Bawan Allah taj, da yake yana sonta, haka yaci gaba da zaman haƙuri da ita, kullum shi ne Zarya zuwa restaurant Cin abin, daga bisani ne da abun ya dameshi, ya samu Uxair Ya kwashe komai game da zamanshi da Benazir Ya sanar mashi, Ba ƙaramin tausayin shi Yaji ba, a ƙarshe Yace mashi Ya daina zuwa restaurant Cin abinci, Ya dinga zuwa gidanshi suna ci, idan ma bai iya zuwa kullum zai dinga kawo mashi,

Tun daga ranar duk in Aneelerh zata Yi girki hada Taj take haɗawa, daga baya kuma Aneelerh ta fara zuwa aiki, hakan yasa suka nemi ƴar aikin da zata dinga yi masu aikin cikin gida kada abun yayi mata yawa, koda uzair ya sanarma Mahaifiyarshi hajiya adama game da neman masu aikin da zasu dinga yi masu aiki a gidanshi dana Tajuddeen, Cikin sa’a Hajiya adama tayi ma mai aikinta Esther magana akan ta nemo masu masu aiki mutun biyu, Batare da 6ata lokaci ba, Esther ta samo masu ƙannanta dake cikin buƙatar aikin yi, dama su ukune Kuma marayu, suna a Cikin buƙatar abunda zasu tallafi rayuwarsu dashi, Sai gashi Allah ya kawo masu aikin yi, Sunan ƙannan nata Ana da Janet Ana itace take aiki agidan Uzair janet kuma agidan tajuddeen,

Rayuwar Janet a gidan Tajuddeen,Ta aikatu kamar jaka a wurin benazir, Gashi abu kaɗan saita rufeta da bugu saboda tsabar Zalunci, haka ta jure zama da ita, kodan saboda albashin da take samu mai tsoka awurin Taj, Yana ji da ita mutunne mai kirkin gaske,

Tun bayan auransu da Sati biyu dai dai da rana ɗaya Taj bai ta6a jin dadin zama da benazir ba saboda baƙin halinta mahaifinta kanshi kuka yake da ita, duk Cikin ya’yanshi babu mai irin halinta, ga shegen yawon tsiya,da auranshi haka take fita Night club kuma ba yadda zaiyi da ita kusan kullum sai sunyi sa’insa da ita, hatta Cikinshi data ɗauka, ba irin maganin da bata shaba don ta zubar dashi amma Abun ya faskara, Allah ya riga daya ƙaddara zuwanshi duniya, ita fa duk duniya ba wanda ya isa yayi mata faɗa taji, wata irin bauɗaɗɗiyar macace, mai wuyar sha’ani hatta Aneelerh ta sha yi mata nasiha akan tagyara rayuwarta a karshe ma saita yaki ce aneelerh daga rayuwarta, ta ɗauki gaba da ita ko magana bata haɗa su, lokacin da Cikinta ya soma Girma kamar tayi hauka saboda ba ta san Ganin shi ajikinta, kamar ta sanya hannu ta danna shi ya baje haka take ji, Taj yasha kamata tana kokarin shan maganin don ta zubar dashi,Wanda hakan yayi silar da har su ka yi faɗa da ita kaca kaca, kuma Tace mashi koda ta haihu kada yayi tunanin zata shayar mashi da abunda ke acikinta, ashe dama jira take ta haihu tabar gidan, Shine ta tafi tabar mashi jaririya cikin kwamin wanka, dama kuma tunkafin tafiyarta, Ta kori mai aikin gidansu Janet, Batare da saninshi ba wannan kenan………

*Boss Bature*

Cigaban Labari

Bayan sun samu natsuwa, Aneelerh ta basu shawarar su ta fi asibiti don ta duba lafiyar babyn, Ta kuma Yi mata injections ɗin da ake yiwa kowani yaro da zarar an haifeshi, domin bashi kariya

Atare suka tafi asibitin wanda Ya kasance Mallakin Aneelerh ne, Ƙaramin privet hospital acan aka duba Lafiyar babyn, tana da ƙoshin Lafiya bayan dawowarsu gida Aneelarh taso ta shayar da babyn Amma Taj ya hana saboda gudun kada Ya haramtawa ƴarshi auren ɗansu,wanda burinsu ne shi da Uzair, su haɗa Ya’yan su aure, duk da ita aneelerhn har yanzu shiru,

A ƙarshe sai dai ƙanwar maigadin gidansa ce Inna kuluwa Take shayar da ita, dama Tana Cikin shayar da jikanta da mahaifiyarshi ta rasu tabar mata, watan shi shida a duniya shima yabi mahaifiyarshi, baba maigadi ne ya bashi shawarar ya bata Babyn ta shayar da ita, baiyi gaddama ba ya amince, a ranar tazo daga ƙauyen su, Sai da aneelarh taje da ita asibitin su aka duba lafiyar jikinta tukunna aka bata Rainon Babyn, Acikin gidan taj ya ware mata haɗaɗɗen bedroon ɗin da zata zauna,

Ranar suna Yarinya taci sunanta *UNAISAH* shine sunan da mahaifinta ya naɗa mata Amma Yana kiranta da *ANGEL* a matsayin Nickname dinta, Bayan kammala sallar juma’a akayi naɗin sunan,

Tun ana saura kwana Biyu suna, Mutanan Buzaye suka zo, daga Ciki hada Mahaifiyar tajuddeen Yahanasu ta tsufa tukuf tare da mahaifinshi malam zahiru, hada kakarsu deeeje suka zo, tare da wasu daga Cikin danginshi, a daren ranar da suka ƙaraso, kowa Ya soma tunanin ina Uwar yarinyar take ne, sai a lokacin yake sanar dasu game da guduwar benazir da ta tafi tabarshi da yarinyar, Ran danginshi ba ƙaramin 6aci yayi ba, sunji haushin Abunda Matarshi tayi, dama tun fil azal basu so ya auri bare ba, sun so ace cikin dangi ya samu mata ya aura, don ba yadda zasuyi ne ƙaddara ta riga fata,

A 6angaren Taj kuwa yaso ace uncle abdallah ƙanin mahaifinshi, yana nan a ka yi sunan sai dai kash, tunda jimawa sukayi tafiya zuwa South korea, da ya ke acen kasuwancinshi yafi ƙarfi, duk da haka Sunyi waya dashi, Har video call suka kira shi don ya nuna masu babynsu, aikuwa sunsha ruwan mamakin ganin kyakkyawar ɗiyar tajuddeen, Don ita Hajiya Adama matar Uncle din, cewa tayi da zarar sun dawo nigeria zata ɗauke ɗiyarta, saboda ta raineta ko alokacin Taj bai sanar da su game da Abunda ya faru tsakaninshi da benazir ba, don baiso ya tashi hankalinsu ya bari ne sai Sun dawo tukunna Suji komai,

Alhamdulillah An kammala taron suna Lafiya, ƴan uwa da abokanan arziki sunci sun sha sun shaida Zuwan *UNAISA* duniya, aranar Tajuddeen kamar yayi hauka saboda tsabar farin ciki, domin kuwa ya samu alheri sosai awurin abokananshi, da kuma masoyanshi don hada key ɗin mota ya samu, ga kuma kayayyakin da suka dinga haɗawa ƴarsa, manya manyan akwatina na kayan baby, shi kanshi ya samu kyautar shaddoji a daren ranar sunan Tare da Uzair suka shiga ɗakinshi suna ƙirga kyaututtukan daya samu, A kalla ya samu kuɗi Sama da 3m, baya ga kayayyakin da ya samu har hawaye saida taj ya zubar, dama shanun da aka yanka ranar sunan bai ƙarasa biyan kuɗinshi ba, bashinsa yaci har uzair na gargaɗin shi akan karya ɗauki abunda yafi ƙarfinshi Ya siya masu rago kawai ya wadatar, Amma yace ina ƴar shi tafi ƙarfin rago sai dai sa.sai gashi Allah Ya rufa mashi asiri,

Sai da su Deeje sukayi Wata ɗaya Cuf tukunna suka shirya komawa Buzaye, Sunyi tunanin taj zai bar masu yarinyar ne su tafi da ita can ƙauyansu buzaye kafin Ya samu matar aure, Amma ina koda Su ka zo mashi da maganar tafiya da babynshi, Sai ya juya masu ƙeya, alamar bazai bayar ba,don dole suka haƙura, dama deejen ce ta matsa su tafi da ita,amma mahaifiyarshi Yahanasu sam bata ayyana hakan aranta ba, musamman da ta ga yadda Inna kuluwa ƙanwar baba maigadi take kula da ita Sai hankalinta ya kwanta,

Ba ƙaramin alheri taj yayi masu ba lokacin da zasu tafi, kusan abunda ya samu ya kasa uku, ya basu kashi ɗaya,Kashi ɗaya kuma yaba Uzair amininsa, Amma yaƙi kar6a saima ya ƙara mashi sunyi rabuwar arziƙi da iyayenshi Sunata sanya mashi albarka har kwalla saidaya zubar bayan tafiyarsu Allah sarki rayuwa kenan

A 6angaren inna kuluwa kuwa babyn Tana samun kyakkyawan kulawa a wurinta, duk da ba’a tare suke yini ba kuma ba a tare suke kwana ba, saboda taj da kullum yana manne da ita, sai dai fa duk lokacin da tafara tsala kukan yunwa, dakan shi yake daukar ta yakai ma inna kulu aɗakinta, Yaƙi yarda yabar mata Yarinyar Saboda ya mutu akan sonta, kona seconds baisan rabuwa da ita zuwa aikine kawai yayi mashi cikas, ba ƙaramin abu ke rabashi da babynshi ba, ko aiki yaje yana dawowa jiki na rawa ya ke zuwa ɗakin inna kuluwa ya ɗauketa, idan dare yayi kuwa dama atare da ita yake kwana, Saman kirjinshi yake kwantar da ita Su sha baccinsu,

A daren ranar wata Alhamis ne Yana zaune saman Sofa Yana danne danne acikin Laptop ɗinshi, Ya jiyo sautin dirar motoci a lokacin angel tana a hannun inna kulu, bai kaiga zuwa ya ɗaukota ba, Yana jira ya kammala aikinsa ne kafin ya Amsota don su kwanta,

Zugudum yayi yana jiran ganin wanene Ya kawo mashi ziyara a irin wannan Lokacin Kusan ƙarfe 9 na dare,

Daga wajen Falon yaji anyi mashi sallama, muryar babban mutum,

Da sauri ya kalli agogon dake manne a bango, kusan ƙarfe tara na dare, duk a tunaninshi uzairne don bai ɗauki murya ba,

hakan yasa shi ɗan ɗaga murya tare da cewa”Come In”

Turo ƙopar akayi, a hankali Ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,

Da mamaki akan fuskar taj yake kallonshi,

Babban mutunne yana sanye Cikin kaya na mutunci na hausawa, Shadda tare da malun malun mutun mai cikar kamala,
fuskarshi ɗauke da murmushi,

Bakowa bane face Alhaji Ubaid Mahaifin Benazir Kaka Ga Angel,

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

Mu haɗu a next page, saoda wadanda su ka ce bai buɗe ba yasa na rage yawan page ɗin, kar a manta da comment like and share

Domin neman ƙarin bayani ayi mana magana ta whatsapp
*08103884440*

*08169856268*

_*Boss Bature💋 ✍️*_

Back to top button