Uncategorized

Hira Da Matattu Part 5 (True Life Story) By Jamila Umar Tanko

 HIRA DA MATATTU….5 ( TRUE STORY)

Mun isa gidan Nanah kowacce kanta ya daure amma abin mamaki ba su razana da yawa ba, kamar yadda na razana dan ba sa ganin abinda nake gani. 

Sun yarda da cewa ni ce ban fahimta ba amma Sharifah bata mutu ba kuma ma bata qasar tunda ga gidan nan alama ta nuna an dade babu kowa. Wataqila kanin nan na ta ne kadai a gidan da suka gani qofar gidan wato Bello shi kuma baya kula da tsaftar gidan shine kawai.

Na tabbatar da zarar na ci gaba da yin musu zasu dauke ni zautatcciya, dan haka yin shiru ya fiye min alkhairi.

Bayan an jajanta sai kowacce ta fara shirin komawa gida dan magruba ta yi. Mun fi kusa da Maryam Alqali ta tambaye ni ko zan tafi ta rage min hanya?

Ina tsoron komawa gidanmu dan zan hadu da fushin mahaifiyata da yayyayena ga mijina baya gari. Na manta ranar ma da ya ce min zai dawo. 

Na bar wayata a gida dan haka sai na amshi wayar Nanah na kira number Mamana. Tana jin murya ta yi ajiyar zuciyar jin dadi, gami da sauke haushin da ta dade tana ji, ta balbale ni da fada. 

Ta ce ina na tafi ga mijina ya dawo a gari tunda rana, na bar waya na fita ba da izinin kowa ba. 

Na fara yi mata bayani akan rasuwar Sharifah, daman kalmar da take so ta ji kenan na kira wato aljana sharifar da na yi gamo da ita. Mama ta manta gaba daya da babbar qawata Sharifah ita a dole aljana ce mai suna Sharifah ta shige ni. 

Ai kuwa ta hada da ni da aljanna Sharifar ta cukuikuya ta nannarka mana zagi. Ta ce ko in dawo gida ko ta zo gidan Nanah ta suburbude ni. 

Hawaye ya cika min ido na ce “shikenan Mama tunda kin ce haka Allah Ya sa ki ga abinda nake gani za ki daina zagina.”

Ta ce ” babu ruwana da wata Sharifah, ko na ganta ubanta zan ci ni.”

Jikina a sanyaye na tashi tsaye, hannuna na rawa na daura dankwalina da mayafi na fito tsaf kamar mai hankali na bi maryam Alqali ta sauke ni a gida.

Tun daga qofar gida nake cin karo da hararar yayyaena.  Na yi sum-sum-sum na shige gida. Anan  na ci karo da fadan Mama. 

Maganar gaskiya da wannan tashin hankalin na gidanmu gara in tafi gidana ko ni kadai ce in zauna saboda zan fi samun ‘yanci ihu da guje-guje. Amma anan da me zan ji ga zagi ga harara ga rukiyya. 

Na harhada komatsaina zan nufi qofar gida, Mama ta ce “ga mukullin motarki fa.”

 Na ce “ina ruwan gawa da tuqi kuma? Mama ki dauki motar na bar miki.”

Eh tabbas komai ya bayyana sai Mama ta sa qannena su riqo ni, domin ta tabbatar babu lafiya. 

Na ga an zo an cicvibe ni an dawo dani falo, kan ka ce kwabo an fara yi min karatu da tofi. 

Maganar gaskiya gara ma in daina nunawa kowa halin da nake ciki dan ba zasu fahimta ba sai dai ma in sake jawowa kaina ukuba.

Aka kira mijina a waya aka sanar masa ya zo ya tafi da ni, sannan ya ji bayanai akan ciwona.

Nayi-nayi kada su fada masa komai ni lafiyata kalau dan na san kawai ajina zasu zubar a gaban mijin, wanda yake ganina wayayyi kuma mai ilimi. Idan ya ji ina maganar fatalwa ba ma aljanu da aka fi yarda da su ba tabbas ajina ma zai zube.

Ya zo a gigice abin mamaki sai suka ga na warware na tare shi da murna na ce mu tafi gida daman motata ce ta sami matsala nake so ya zo ya tafi da ni. 

Mama in zata yi magana sai in yi sauri in katse ta, nan da nan na ja shi da sauri muka fita. 

Mu na fita ina jiyo muryar Mama ta barke da kuka ta na cewa ” babu sauran Samha.  Samhata ta zare.”

Mun isa gidana tare mijina Aliyu, amma yana ta jero min tambayoyi akan yadda na fita ba tare da na fadawa kowa ba. Ya san ba halina ba ne. 

Nan fa na dinga tsara shi har ya amince dan shi ya yarda da tarbiyya da riqon addina. 

Babu walwala a tare da ni sai dai ina ta boyewa, daga na tuna Sharifa da muqarrbabanta sai in ji duniyar ta koma min up-side down.

Bayan na yi wanka na nutsu, Aliyu ya fita ya siyo mana abinci kala-kala. Bawan Allah tunda ya ga ban dafa abinci  ba ya tabbatar bani da lafiya. 

Ga yunwa ina ji kwanana biyu ban ci abincin kirki ba kuwa. Na samu na danqari kazar nan sosai na qoshi. 

Sai na fara dawowa daidai. Amma duk da haka bana gane wasu daga cikin hirarrakinsa. Daman shi mutum ne mai yawan tunawa da mutuwa da maganar kowa ya shirya duniya ba matabbata ba ce.

Na gyara zama na fara jeho masa tambayoyi akan MATATTU da kuma yadda rayuwa bayan mutuwa take. A dukkan bayanansa babu in da ya ce matattacce yana dawowa duniya ayi ta artabu da shi kamar yadda nake fama da Sharifah. 

Na ce masa meya sani game da fatalwa? Ya tabbatar min akwai aljanu da su kan iya yin shigar mamaci dan su tsorata bil’adama. 

Na yi shiru ina kallon talabijin tabbas ko a cikin talabijin din idanuwana na nuna min mai kama da Sharifah.

Na zabura na ce “Aliyu mayar min da wannan tashar ta larabawa ko turawa.”

Ya dube ni ya ce ” Hausa fim ne fa, series dinki da kike bi.” 

Na tashi da sauri na shige daki dan ni na san abinda na gani, kafin in fara baza hali a gabansa har ya fahimta toh gara in matsa.

Biro da littafi na dauko na rubuta kakaf masu bi na bashi da wadanda nake bi  bashi. Da wadannan na munana na nemi su yafe min. 

Sannan na basu labarin ciwon ajalin da zai kashe ni kada su ji na mutu su zaci mutuwar fuju’a na yi, A ‘a sam na yi jinya mai wuyar gaske wato artabu da fatalwa, da irin wannan jinyar ai gara cutar qanjamau.

“Me kike rubutawa ne?” Aliyu ne ya tambaya.

Ya yi mamaki da ya ga na zabura na wargaje biro da littafi kowanne ya kama gabansa, alhali a hankali yayi magana. 

Na yi sauri na dauke littafin na boye, yayi-yayi in bashi ya gani na ce lissafina ne na masu pre-order kaya.

Ya nemi ya ji yaya muka yi da alqalin da Yaya Anas ya hada ni da shi, wacce shawara ya bayar?

Oho na ma manta komai kuma na rasa amsar da zan bashi. 

Duk hirar da ya dauko sai ya ga hankalina baya kai, ya ce in sha panadol in kwanta ko zazzabin ne. Na bar shi a daki na fito falo dan dauko maganin da yace in sha .

Wayata ce a caji kasancewar a silent take ashe ana ta kira.

Na duba da sauri na ga bakuwar lamba ce bani da ita a cikin garin sunayen mutanena. Na amsa da sauri bana tantama na san daya daga cikin qawayena ne suke kira dan su na so su ji yaya na isa gida, kuma yaya jikina.

Wata murya na ji wacce ta yi min kama da muryar da ta fi kowacce murya a doron qasa munin sauraronta, wato muryar Sharifah.

Tabbas bayan na yi sallama aka amsa sai na dafe qirji tun kafin ta gabatar min da kanta.

Muryar ta ce ”  Samha Sunana Sharifah Nasir,  ina so ki rufa min asiri ki…….”

Daga wannan kalmar na fita hayyacina na saki wayar ta fadi ta fashe yayin da nima na fadi na fashe a gefe daya.  Ina kyautata zaton suma ne..

Na ganni akan kujera maimakon a qasa sannan kuma Aliyu yana yi min firgita yana yayyafa min ruwa.

Ina farkawa na yi salati na tambaya na ce “ina Sharifah?”

 Ya ce “wacece haka?” 

Na sake cewa “ina wayata?” Ya nuna min ita a qasa gami da cewa ” wayar ta fashe.”

Na ce ” Alhamdulullah gara da ta fashe dan na hakura da riqe waya har abada.”

Ya tambaya “me yasa?” 

Na ce “baa amfani da a waya a lahira ai.”

Ya gyada kai ya ce ” tabbas amma ke a duniya kike ai.”

Na fashe da kuka mai tsanani.

Wannan karon Aliyu ya sake shiga damuwa, ya shiga tambayata in fada masa yanayin ciwon nawa dan ya san asibitin da zai kaini. 

Na ce “idan akwai garin da idan mutum ya mutu kafin ya isa lahira yake rayuwa bayan mutuwa can zaa a kai ni. Wannan karon da sauri ya miqe ya ja da baya yana kallona. 

Ya fada a bayyane “ya kamata in kira Mama na fara tunanin daman akwai abinda Mama take so ta fada min amma kika hana.”

Dan haka ya jawo wayarsa da sauri zai kira Mama na zabura na fusge wayar na hana shi. Na tabbatar masa da lafiyata kalau.

Haka muka kwana ina zabura ina haurawa daga gefen hannunsa hagu in dawo gefensa na dama.

Maganar Sharifah ke dawo min a kunnuwana da ta ce  in rufa mata asiri. Asirin me take so in rufa mata ne? Amma ni ta tona min nawa asirin. Ina zamana lafiya ada yanzu gashi ta haukata ni.

Aliyu dai duk inda na haura sai ya yi addu’a ya toho min, ya ci gaba da barci dan ya gaji.

Barci barawo sai da ya sace ni amma fa mafarkin dai na ta ne, da ita da alqalinta. Wannan karon har da qanjnta Bello. 

Hasbunal lahu wa ni’imal wakil. Na ganni a tsakiyarsu ana walima. Wannan wacce irin masifa ce walima da matattu???

Madalla da ALQALAMIN JUT

To be continued….

Hira Da Matattu Part 4 (True Life Story)  By Jamila Umar Tanko


Also Download: Hira Da Matattu 1 to 10 complete

Back to top button