Hausa novels

Abban Sojoji Book 2 Chapter 72 End

CIGABAN LABARI

 

Abu ba ƙaramar wahala tasha ba a hannun Ya sayyadi,daga ita har yaran bai raga masu ba,tun yana 6oye mata mugayen halayenshi,har ya fara bayyana mata su,babban tashin hankalin da ta fara fuskanta a wurinshi shine shigo mata da Manyan Alhazan da yake yi acikin gidansu,in suka shiga ɗaki sai suyi fiye da 6hrs basu fito ba,wani sa’in har gurnani take ji ya cika gidan tamkar namun dawa na yaƙi,wannan abun ba ƙaramin razanar da ita yake yi ba,kuma duk in ta tambayeshi me suke zuwa yi a wurinshi sai yace mata *Wala tajassasu*kuma ta tsaya a iya matsayinta kar tace zatayi mashi shisshigi irin na mahaifinta,tarasa uban me sukeyi acikin ɗakin,abun ba ƙaramin damunta yake yi ba,tun tana iya jurewa har dae wata rana ta yi masu la6e a window ɗin ɗakin shi,a ranar abu taga tashin hankalin da bata ta6a gani ba da idonta tunda uwarta ta haife ta,wani irin yunƙurin amai ne yazo mata da gudun gaske tabar leƙen sun da takeyi ta koma bakin fanfo tana kwarara amai tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito,agaban fanfon ta zuƙunna tare da fashewa da kuka,ta dafe kanta da hannunta saboda raɗaɗin da yake yi mata,gaba ɗaya rayuwarta ta shiga ƙunci taji ta tsani kanta,kamar ta kashe kanta haka ta dinga ji a lokacin,

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

ta jima abakin fanfon kafin ta koma cikin ɗakinta,a lokacin triplets ɗinta suna kwance sae sharar bacci sukeyi,komawa tayi daga gefen gadon ta zauna tare da ɗan russinawa dai dai saitin fuskokinsu tana kallonsu,yadda suke sharar baccin su zai tabbatar maka da cewar suna cikin kwanciyar hankali,tasa su gaba tayi tana faman shessheƙar kuka muryarta na rawa ta dinga cewa”Na cuci kaina!Kuma nacuci rayuwar ƴa’ƴana,Haƙƙin mahaifina kadae bazai ƙyale ni ba,na bijire mashi na ƙuntata mashi duk don saboda in auri sayyadi,haƙiƙa na tafka babban kuskuren da bazan ta6a gyarashi ba,Ni duk a zato na kowane mutun daya iya jan ayar kur’ani ya fassarata kuma yayi wa’azi abainar jama’a,mutumin kirki ne bai aikata zunubi tsarkakakke ne shi,ashe ba haka bane,ko acikin malaman akwai nagari akwai kuma na banza,wanda suke amfani da iliminsu na addini don su cutar da mutane,Mommy saida ta gargaɗe ni akan hakan amma na bijire mata saboda na makance akan soyayyar sayyadi,Ni ban tsaya nayi bincike akan rayuwarshi ba,kawai natashi na aure shi,kuma na ƙuntata ma mahaifina duk don saboda shi,na kuma ƙuntatama Mijina mai sona da gaskiya,wlh na cuci rayuwata….!kaicona…….’

 

Sosai abu ke shassheƙar kukan,sautin kukan da takeyi ne ya farkar da Sehrish sai faman mutsustsuka idanunta takeyi da hannayenta,hannu abu takai tare da ɗauko ta,ta zaunar da ita asaman cinyoyinta,shafa fuskarta tayi tare da cewa”Rishina kin farka?kina jin yunwa ne”?

Also Download Ɗaudar Gora Page 8 By Billyn Abdul

A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskar mahaifiyarsu,koda taga hawaye na zuba a idanun oumman tasu,sae ta sanya tafin hannunta tana share mata su tana cewa”oum ki daina,banasho,nima inyi kuka,’tayi maganar da hausarta ta ƴan koyon magana,hada ta6e la66anta zatayi kuka,

Hakan da tayi yasa abu ta fashe da dariyar karfin hali tana kallonta,kwantar da kanta tayi asaman ƙirjinta tana shafa sumar kanta tace”na tambayeki kina jin yunwa baki faɗa mun ba,’

Cikin shagwa6a tace”inaji,amma tare dashu usana da johad anci.  ‘

Abu tace”shikenan,bari mu jira su farka daga baccin sai in dafa maku ko indomie ce kuci,bayan kun gama ci sai inyi maku wanka,in shafa maku mai in canza maku kaya sannan in kaiku gidan maman sadeeq ku tayata fira,kina son zuwa ko?

Inasho,ta bata amsa,

Suna cikin yin fira da ita sai ga sayyadi ya faɗo cikin ɗakin nata,tana ganinshi gabanta ya faɗi rass don yanzu yafi yi mata kama da ibliss,

Yadda ya nufo ta a fusace yasa tayi saurin sauke sehrish daga jikinta ta miƙe tsaye tana kallonshi fuskarta da alamun tsoro,

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Nuna ta yayi da hannunshi yana huci yace”Abu!uban me ya kaiki yin la6e aɗakin can!angaya maki banganki bane?duk wani motsin ki acikin gidan nan,acikin kunne na nake jinshi,basai da na faɗa maki cewa kada ki tsananta bincike akaina ba!

duk da tsoranshi da take ji hakan bai hanata tanka mashi ba,

“Saboda baka da gaskiya shiyasa ka hana inyi bincike akanka!yau naga komai da idanuna ashe kai ba sayyadi bane!baƙin shaiɗan ne wanda ke 6oye mugayen halayansa!wlh nayi danasanin auranka sayyadi yafi sau aƙirga,banta6a sanin cewa kai dabba bane sae yau!wlh sai ka sake ni don bazan iya cigaba da zama da fasiƙin mutun irinka ba……’

Tunkan ta ƙarasa maganar sayyad ya fashe da dariya hada dafe cikinshi,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,shiru tayi tana kallonshi,

Sai da ya gama tiƙar dariyarshi sannan ya sassauta muryarshi tamkar zai lallashe ta yace”My wife,yau da bakinki kike jifana da waɗannan munanan kalaman?nifa ne sayyadin nan naki da kika kwallafa rai akai,ban wani canza ba,’tundaga kan yadda yake yi mata magana ta gane cewa ba karamin gogaggen ɗan bariki ba ne,ya kware wurin iya sarrafa harshe dama da irin kalaman nan nashi ya yaudareta tun farko,in yazo zance ya tsareta da idanunshi yana yi mata nasiha,

daƙyar ta iya haɗiye miyan dake bakinta,cikin sanyin murya tace”Kaji tsoran Allah!meyasa kayi amfani da ilmin da kake dashi na addini wurin cutar da rayuwata?saboda kasan cewa inason malamin addini mahaddacin al’qur’ani shiyasa ka biyomin ta wannan sigar don ka yaudare ni,laifin me nayi maka da har na cancanci hakan a wurinka”?

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

shu’umin murmushin nan nashi ya saki kafin yace”Ae malaman ma suna muka tara!abu kinyi kuskuren yadda da cewar kowane malamin addini mutumin kirki ne,wasu malam ne nagaske wasu kuma suna yin amfani da maluntar tasu da wata manufa don su Cimma burinsu kamar ni kenan!saboda kawai kin ganni malami ina yin shigar mutunci in yi wa’azi in janyo aya in fassara gani kuma mahaddacin kur’ani sai akace maki ni mutumin kirki ne?An rubuta a goshi na ne?me yasa kuke yin believing da abunda idanuwanku suka gwada maku ne?duk wani ɗan adam da kika sani aduniyar nan bai da tabbas!duk yadda kikaso ki gane mutun na gari kona banza abun zaiyi matuƙar wuya agare ki,saboda akwai masu fuska biyu,zaki ga mutumin banza yana aikata abunda yaga dama agaban kowa baijin kunyar kowa zai aikata zina zaiyi sata,zai zalunci wani zai sha giya,zai yi kaza yayi kaza,kinga shi wannan ya bayyana asalin suffarshi,wani kuwa zaki ganshi babban malami ne mahaddacin al’qur’ani wanda ya saba wa’azi agaban dubban jama’a yana faɗakar dasu cewa suji tsoran Allah kar suyi kaza idan sukayi kaza zasu shiga wuta idan sukayi kaza kuma zasu shiga Aljanna,idan kika bincika kuma wannan malamin ɗabi’unsa da halayansa iri ɗaya ne dana wannan mutumin dana fara kwatanta maki!amma shi bai bayyana suffarshi ta asali ba,yazo da sigar maluntaka don ya cimma wata manufa tashi ta hanyar yin amfani da ilmin addinin da yake dashi,wani kuma zaki ga malamin ne nagaske akwai ilmin addinin Akanshi amma baki ta6a ganewa, kamar dae Abusufyan yaron kirki,abusufyan tun yana da shekara sha wani abu aduniya ya haddace al’qur’ani mai girma tare da manya manyan littattafai na addini,amma ya ɗabi’unsa da halayansa suke?babu mai iya gane cewa yana da ilmin addini akanshi indae ba anyi mu’amala dashi ba,saboda irin rayuwar daya taso yanayi,abota da mata da kuma rashin kunya baijin kunyar furta kalami abakinsa ko gaban wanene 6arota kawai yake yi,kowa zaiyi tunanin cewa shi jahilin addini ne ashe ba haka bane,yasan me yakeyi kuma yana da kyakkyawar zuciya ba kamar sayyadi ba,

*dawa zamu yadda aduniyar nan?lalube kawai mukeyi acikin duhu,musamman zamanin nan da muke ciki,Zaiyi wuya ka gane mutun na gari dana banza,shiyasa da yawa mata muke shan wahala wurin neman miji na gari da zamuyi rayuwa dashi,tunda bamu da tabbas akansu Mazan!haka matan ma bamu da tabbas mu kanmu,da mazan da matan wahala kowa ke sha wurin neman righteous life partners,A ƙarshe nidae shawarar da zan ba mutun shine ya dage da addu’a kawai,sannan ya gyara rayuwarshi in ma akwai wani kuskuren da yake aikatawa ko min ƙankantarshi,saboda da yawa wasu abubuwan wlh mu muke ja ma kanmu batare da mun sani ba,muyi ta ganin ba dai dai ba arayuwarmu,dole sai mun gyara sannan zamu ga dai dai mu kanmu,Allah yasa mu dace,Amin.

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Haƙiƙa su Sehrish sunga rayuwa fiye da tunanin mai tunani,uƙuba babu irin wadda basu sha ba a hannun mutumin nan,tun kafin su mallaki hankalinsu suke jin wannan sautin abun da mahaifinsu ke aikata shi da manyan alhazawan nan dake kawo mashi ziyara,abun ba ƙaramin tsoratar dasu yake yi ba,duk subi su gigice,babu yadda abu batayi ba akan ya daina shigo mata dasu cikin gidan amma ko ajikinshi,in ma ta takura mashi sai ya kwatseta da cewa ae gidan bana Ubanta bane,da kuɗinshi ya siyi gidan,

Abu har ya fara affecting ɗinsu sehrish daga sunji gurnanin nan sai subi su gigice su firgice suna yi mata kuka suna cewa Oumma dodo,dodo,ta rasa yadda zatayi dasu baiwar Allah,ƙarshe ta dinga kaisu gidan makwabciyarta suna yini acan wani sa’en ma har kwana suke yi agidanta,

Lokacin da Sayyadi ya gane hakan,ba ƙaramin faɗa yayi mata ba akan tadaina kai mashi ƴa’ƴanshi gidan makwabtansu,dama basu shiri da Mijin maman sadeeq,shima malamine sosai amma malamin gaske ba irin sayyadi ba,shiyasa ya tsane shi,saboda ya sanya mashi ido sosai akan lamurran rayuwarshi duk da bai ta6a tarar shi da sunan zaiyi mashi magana ba,babu wanda ke tanka ma wani acikinsu,ƙaryace ta haɗu da gaskiya,kuma a makarantar islamiyya ɗaya suke koyarwa,tun lokacin da sayyadi ke tarayya da abu,sae da ya ta6a kiranta ya gargaɗeta akan ta daina kulashi,su kansu basu san asalinshi ba,kuma basu yadda dashi ba acikin malaman makarantar amma abu taƙi jin maganarshi saboda ta makance akan son shi,maganin marasa jin maganar malamansu kenan da kuma iyayensu kai harma da mazajansu,babu wanda acikinsu bai ja mata kunne ba amma tayi kunnan uwar shaggu dasu ita ga Juliet,yanzu dae ga romeo nan yana ta gasa mata aya a hannu,duk da dae akwai aikin sihiri,Allah ya kara karemu da kariyarsa,Amin

 

A kwana a tashi babu wuya wurin Allah su Sehrish suka kai shekara 5 a duniya,daga lokacin ne fa sayyadi ya fara sanya masu ido saboda kyawunsu dake fusgarshi,nan fa ya fara saƙa wani abu aranshi,

 

Wani sabon salo ya 6ullo mata dashi,na horon yunwa kwata kwata yadaina kawo masu abinci acikin gidan,yaran suyita fama da yunwa,wani lokacin kamar zasu rasa ransu in suka fara billayi suna kuka,hankalinta yabi ya tashi ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi,gashi bata da kuɗi bata da hanyar da zata same su balle tace zata ɗauki nauyin ciyar dasu,kamar maroƙiya haka ta koma bi gida gida na makwabtansu akansu ƴan mata abinci taba yaranta,tun tana samu suna ɗan mata har aka fara tseguminta abayan idonta,tun suna gulmarta a6oye har aka farayi agabanta,ƙarshe ma da zarar su sehrish sun leƙa kopar gida za’a fara gulmarsu ana cewa ga ƴa’ƴan abu almajira nan sun fito,haka zasu koma sunayi mata kuka,saboda tsokanarsu da akeyi,har jan gashin kansu akeyi ayita dungurin goshinsu,gaba daya mutane suka ɗauki karan tsana suka ɗaurama yaran,duk irin kyan dake garesu,kowa ya daina taimakonsu,bakomai yafi ɗaga ma abu hankali ba face yadda mutane suka tsani ƴa’ƴanta,babu damar su fita waje da sunan zasuyi wasa cikin ƴan uwansu yara sai ta gansu sun watso da gudu cikin gidan suna kuka,haka zata haɗasu a ƙirjinta ta rungumesu tana kuka,duk wannan abun dake faruwa sayyadi yana sane saboda shine silar komai dake faruwa dasu,

 

Gaba ɗaya kowa ya ɗauki karan tsana ya ɗaura masu,mutun biyu ne kaɗae suke tausayin rayuwarsu,Maman sadeeq da kuma Mijinta,kullum cikin tausaya masu sukeyi,a kullum su hosana suka shiga gidan yunwa ta koro su,ita ke zama ta girka masu abinci,har ta kaiga in zatayi girki tare dasu take auna abincin don tasan zasu zo nema ne,ita kaɗae ce take kwantar ma abu da hankali,

Also Download Hira Da Matattu Page 1 By Jamila Umar Tanko

A ƙarshe dae da abun ya fara yi mata yawa da kanta ta tunkari sayyadi a ɗakinshi lokacin yana a gida baije aiki ba,tunda ta shigo ɗakin ya ɗaure fuskarshi yana daga kishingiɗe saman gadonshi,

Wuri tasamu daga gefe ta zauna ta gaishe shi daƙyar ya amsa mata ma,yadda kasan auren ƙiyayya sukayi dashi,

“Meyasa kake barin mu da yunwa baka ajiye mana abinci acikin gidan nan yanzu?

ta6e bakinshi yayi tare da cewa”Yaushe rabon da kiban haƙƙina na aure?hakanan zan zauna ina ciyar dake da ƴa’ƴanki ne saboda haihuwata kukayi?

“Allah ya kiyaye in ƙara haɗa shimfiɗa dakai sayyad!rashin sani ne yasa ko lokacin baya nake baka haɗin kai,amma yanzu nagane ko kai wanene…. ‘

Murmushi ya saki yana kallonta batare da ya ƙara tanka mata ba,

Cigaba da magana tayi”bai kamata laifina ya shafe su ba,su fa ƴa’ƴanka ne jininka ne!meyasa zakayi masu horon yunwa saboda laifin da nina maka?haba sayyad sai kace ba ƴa’ƴanka ba?akan idonka ake wulaƙantasu amma ko ajikinka,narasa gane wannan abun………’takaici ne yasa ta kasa ƙarasa maganar ta fashe mashi da kuka,cikin shessheƙar kuka taci gaba da cewa”tun da na haifi yaran baka ta6a nuna masu soyayya irin ta mahaifi ba,tun satin farko da suka zo duniya,ko ɗaukarsu bakason yi,me yasa dan Allah?kayan sawar su ma duk sun tsufa sunyi masu kaɗan,amma baka ta6a ɗaukar ko fallan atampha ba wannan kace gashi a ɗinka masu,wai kai wani irin mutun ne!?

Da buɗar bakinshi sai cewa yayi”Dabba!”

Shiru abu tayi tana kallonshi kamar ta rufe shi da duka haka take ji,

“Ko kin manta munanan kalaman da kika jefe ni dasu ne?da bakinki fa kika kirani da sunan dabba,”

“Dan Allah to kayi hakuri komai ya wuce,ni so nake kawai ka daina yi mana horon yunwa ko dan saboda yaran nan,koda ace ni ba zaka bani ba,su yara ne basu san komai ba,ba zasu iya jurar yunwa ba,sannan kuma ya kamata ka sanyasu makaranta tunda bakinsu yafara buɗewa sosai suna magana,”ba don taso ba haka ta dinga lallashi akan ya taimaki yaran,

Sai da ya mula ya sha iska sannan yace”ni bazan iya ɗaukar nauyin karatunsu ba,saboda ni ban fito gidan arziƙi ba kamar Abusufyan,kinsan cewa Ni malamin makaranta ne,makarantar ma ta islamiyya,salary ɗina bai wuci 20k ba,idan har kinason kula da yaranki ki tashi tsaye ki nemi kuɗinki mana,’

Fuskarta ɗauke da damuwa tace”Meyasa zakayi mun haka sayyad!idan kasan cewa ba zaka iya ɗaukar nauyin su ba,meyasa ka bari na haifesu….   ‘

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

Yunƙurawa yayi tare da miƙewa yabar mata ɗakin yana faman buga tsoki,ta jima zaune jugum aɗakin nashi,kafin ta miƙe ta koma bedroom ɗinta,zirga zirga tashiga yi tana neman mafitar yadda zata samu kuɗi don ta tallafama rayuwarsu,bakowa bane ya faɗo mata aranta ba face Ya haris,tana da tabbacin cewa in yaji halin da take ciki zasu iya taimaka mata duk da tana jin kunyar tunkararsu amman bata da wata mafitar data wuce wnn,addu’a ta shiga yi Allah yasa har yanzu da number shi data sani yake amfani,

 

Da wayar makwabciyarta tayi amfani wurin kiran Haris,cikin sa’a ta shiga,lokacin daya ɗaga kiran taji muryarshi sai ta fashe mashi da kuka,nan fa hankalinshi ya tashi ya shiga tambayarta ko lpy,bata 6oye mashi komai ba,game da halin rayuwar da suke ciki ita da ya’yanta,haris yayi mata al’ƙawarin zai taimaka masu,su bashi lokaci,

 

Bayan wasu ƴan kwanaki haris yayi mata aiken kuɗi masu yawa,dasu tayi amfani wurin nema masu makarantar boko da kuma islamiyya,wani lokacin har zama takeyi da kanta ta koya masu karatu,sun ɗan samu sauƙi a wannan lokacin kafin sayyadi ya sake ƙunsa masu wani baƙin cikin,ya kwashe mata Sehrish da jahad 6at aka neme su aka rasa,kamar abu zata yi hauka wurin nemansu,ashe zuwa yayi ya saida ma ƙungiyarsu yaran don suyi amfani dasu,shi kuma suka bashi makudan kuɗi,Mijin maman sadeeq ne ya tona mashi asiri a wurinta,saboda yaga lokacin daya gudu da yaran a 6oye ya tafi dasu,ranar kaca kaca sukayi dashi har bugunta sai da yayi saboda shaƙo kwalar rigarshi da tayi tana jifanshi da munanan kalamai,a ƙarshe tace zata haɗa shi da Allah in bai dawo mata da ƴa’ƴanta ba,tun daga ranar ta fara sallar dare tana kai kukanta wurin Allah,duk yadda sayyadi yaso ya juye mata tunani akan ta daina ibadar nan amma abun yaci tura,ko yayi nufin yi mata asiri babu abunda ke yin tasiri ajikinta,

Also Download Idon Naira Chapter 1 By Mamuhgee

A ƙarshe dae sae gashi a tsakar dare aka dawo mata dasu sun fita hayyacinsu sunyi jaga-jaga dasu,kamar an jefosu haka ta gansu sun faɗo ɗakinta,sae kuka sukeyi ko sutura babu ajikinsu,ga miyau na zalala abakunansu,hankalin abu ba ƙaramin tashi yayi ba,sai lokacin taƙara sanin wanene sayyadi,kuma ta fara kokwanton cewa Anya ƴa’ƴanshi ne,gaba ɗaya kuɗinta sae da suka ƙare wurin nema masu magani don tunda suka dawo ciwon kai,ciwon ido,ciwon ciki,ciwuka iri-iri haka suka dinga fama dasu,har gadon asibiti aka kwantar dasu sukayi jinya duk ita ke faman ɗawainiya dasu tare da Maman sadeeq,har mijin ta yana zuwa dubasu a asibitin sannan ya taimaka masu da wani abun hadi da addu’oi,amma Sayyadi kuwa ko leƙo asibitin baiyi ba,koda aka sallame su suka dawo gidama basu same shi ba,haka abu taci gaba da shan wahalar rayuwa,ko makarantarma acikin sati bai wuci sau biyu suke zuwa ba,saboda rashin lafiyar da suke ta fama da ita,kuma duk in sukaje makarantar da kuka suke dawowa,saboda yara dake tsokanarsu akan cewa mahaifinsu ɗan mafiya ne mai yankar kawunan mutane,wannan abun ba ƙaramin cutar da rayuwarsu yake yi ba,shiyasa duk suka tsani zuwa makarantar,

 

Akwai wani lokaci da Sehrish ta fito waje cikin unguwarsu ta miƙi hanya tana tafiya tana kuka abun duniya yayi mata,kwata kwata basu jin daɗin rayuwarsu ta ko’ina a ƙuntace suke,a daidai wannan lokacin Wata danƙareriyar mota tayi parking a gefenta,cikin sauri matashin dake cikin motar ya buɗe ya fito ya tunkareta,sam bata lura da shi ba har sae da ya ruƙo hannunta,a firgice ta juyo tana kallonshi da idanunta waɗanda sukayi jawur saboda kukan da tasha,ga majina duk fuskarta ta 6aci,zuƙunnawa yayi agabanta yana kallonta,gwanin ban tausayi ƴar ƙaramar yarinya ko kallabi babu akanta balle takalma,ga kayan jikinta duk sun 6aci,

Kamar yadda yake kallonta haka itama take kallonshi,ɗan gayu dashi yasha wankan suit ajikinshi,

Cikin sanyin murya yace”Ya sunanki”?

..cikin shessheƙar kuka tace”dan Allah ni ka rabu dani,ka ƙyale ni in tafiyana,’

Abun yaso ya bashi dariya,shafo fuskarta yayi tare da cewa”Faɗamun me yasa kike kuka?idan kika faɗa mun zan taimake ki,’

A ƙule tace”Nidai ka ƙyale ni dan Allah,kawai ka rabu dani,kona faɗa maka babu abunda zaka iyayi mana saboda babu mai sonmu Allah ne kawai ke son mu,’

Tuni yaji hawaye sun cicciko mashi acikin idanunshi,Haris dake zaune cikin mota yana hangensu ta glass ɗin motar ba ƙaramin tausayi yarinyar ta bashi ba,

lallashinta ya shiga yi yana cewa”kiyi haƙuri kinji?bakowa ne baisonku ba,Nima gani kuma ina sonku sosai,ashirye nake dana taimake ku indae kunaso,zan ɗauke ku mu gudu mu bar ƙasar nan,in tafi tare daku can wani wuri mai daɗi kuyi rayuwarku ko baki so?

“dagaske kake”?muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,

ɗaga mata kai yayi alamar eh,tare da cewa”yanzu ki biyoni mu tafi batare da kowa ya ganmu ba,”

Karanta>>> Yadda Zaki Kara Girman Kugu (Hips)

Girgiza mashi kai tayi tare da cewa”Su hosana fa?su bazaka tafi tare dasu ba?Oummanmu fa?itama anan zaka barta,

“Kada ki damu suma duk zanzo in ɗaukesu daga baya,”

Maƙe mashi kafaɗa tayi tace”a’a ni bazan bika ba,sae dae inje in kirasu Johad da hosana,mu tafi atare,”

“Shikenan zan jiraki ki kirasu,kada ki faɗa ma kowa babu wanda zai san mun tafi,”

Amsa mashi tayi da toh sannan jiki na rawa ta juya da gudu ta koma gidan,

Sai lokacin haris ya fito daga cikin motar jikinshi a sanyaye ya ƙarasa inda abusufyan yake zuƙunne,hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarshi yace”Yanzu ka tabbatar da abunda nake faɗa maka ko?

Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace”Haris yaran nan fa ƴa’ƴana ne!ina ji ajikina,hatta kamannin fuskarsu ma irin nawa ne,bansan ya akai hakan ya faru ba,mutumin nan baida Imani dama na jima ina zarginshi,kuma zanyi bincike akanshi,bazan ƙyaleshi ba haris,ni babban abunda yafi damuna yadda yake tafiyar da rayuwar yaran,kamar sunfi kowa rashin gata aduniya,ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan har tasan cewa kowa baison su,tama rasa ina zata tsoma ranta saboda ƙuncin da take ji,so yake su kamu da ciwon zuciya tunda ƙuruciyarsu,” ƙarasa maganar yayi tare da miƙewa tsaye yana share kwallar data zubo mashi,

“Akwai matsala fa,muddin rayuwar yaran nan taci gaba da tafiya ahaka,yakamata muyi gaggawar sanar da Abbanku domin ashawo kan matsalar tun kafin ka rasa yaran nan!amma inaso yanzu idan suka zo mu fara biyawa asibiti domin ayi masu gwajin jini don mu tabbatar da cewar ƴa’ƴanka ne,”

Yana kai ƙarshen maganar tashi,sae ga Sehrish ruƙe da hannun Hosana da jahad,ta ruƙo hannun kowannansu sun fito daga gidan,ko abu batasan da fitar su ba,saboda ta shiga makwabtansu wurin maman sadeeq don ta samo masu abincin da zasu ci,

 

Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar abusufyan lokacin da yayi arba dasu,ruƙe da hannun juna,kamar jira yake yi su ƙaraso wurinshi,ya zuƙunna tare da haɗasu duka ya rungumesu a ƙirjinshi,ya jima dasu a haka kafin ya raba jikinshi da nasu,anan ne yayi masu hoto da wayarshi,ya ɗaukesu a yadda suke kaca kaca dasu da niyyar ya nuna ma gwaggon katsina don taga halin da yaran suke,ko zasu nemi mafita,

Akan idon mijin maman sadeeq mlm nura,abusufyan ya sanya su sehrish acikin motarshi,a back seat suka zauna,haris kuma shike driving ɗinsu,

Shi kanshi yayi mamakin yadda yaran suka amince suka biyo shi,ko mahaifiyarsu basu nema ba,duk irin shaƙuwar dake tsakaninsu da ita wannan zai tabbatar maka da cewar ta kansu sukeyi,sun gaji da komai,

 

A katafaren gidan nan nasu inda sukayi rayuwa shi da abu,tare dasu hajiya Ameena anan yakai yaran,cikin gidan ya shiga tare dasu,ya rage kayan jikinshi,sannan ya bisu ɗaya bayan ɗaya da kanshi yayi masu wanka acikin toilet,ya wankesu tass ya kuma wanke masu gashin kansu da shampoo,bayan ya kammala yi masu wankan,anan bedroom ɗinshi,ya shafe masu jikinsu da mai,ya gyara masu sumar kansu,sai da yabi kowaccensu yayi mata kalaba guda biyu akanta,ba ƙaramin kyau sukayi ba,bayan ya gama yi masu kitson ya hau saman gadon tare dasu ya kunna masu cartoon awayarshi na tom and jerry suna kallo,

Karanta>>> Maganin Sanyi Ko Wane Iri Ne Da In Sha Allahu

Shigowa haris yayi cikin ɗakin hannunshi ɗauke da manyan ledoji guda biyu,lokacin daya samu abusufyan kwance saman gadon tare da ƴan ukunnan duk sun manne mashi suna kallo,abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba,sae yaji aranshi dama a wurin abusufyan yaran suka taso,da sun ji daɗin rayuwarsu,

Ƙarasawa yayi tare da miƙa mashi ledar kayan,ya taso ya kar6a,kayan sawa ne daya siyo masu,sai kuma ledar abincin da yayi masu take away a restaurant,

Bayan haris ya fito daga ɗakin ya fito falo yana jiran Abusufyan ya kammala shirya yaran su tafi asibitin,

Sanya masu kayan abusufyan yayi,sannan ya fiddo masu da take away ɗin abincin suka zauna suna ta turawa a bakunansu,zuba masu ido yayi yana kallonsu,ganin ya kura masu ido yasa Hosana ta ɗebo abincin a hannunta takai mashi abakinshi don yaci shima,

Murmushi abusufyan yayi ya buɗe bakinshi ta sanya mashi abincin,a haka har suka kammala cin abincin,

 

Yayin da suke nan,Abu nacan tana haukan neman ƴa’ƴanta,gida gida haka ta dinga bi tana neman su hosana,har sai da Allah ya haɗa ta da Mijin maman sadeeq shi ne yake sanar da ita cewa wani matashin saurayi ne mai kama da yaran yazo ya ɗaukesu,tunda taji hakan ranta ya bata cewar Abusufyan ne,jiki asanyaye ta koma cikin gidan,gefen gadonta ta zauna addu’a tashiga yi Allah yasa shine,in ma dagaske shinen Allah yasa karya dawo mata dasu hosana ya tafi dasu kawai duk inda zaije,tabar mashi su,

 

Lokacin da sukaje asibitin akayi masu gwajin jini,result ɗin ya nuna cewa yaransa ne,nan fa suka shiga murna shi da haris,duk da sunyi mamakin taya akai yaran suka kasance nashi!hakan na nufin da cikinshi abu tayi aure,

Haris ne ya bashi shawarar su ɗauke yaran kawai karsu maidasu gidan nan,Abusufyan shima ya amince da hakan,bai maida su sehrish ba ya koma dasu gidansu,kusan kwana uku su sehrish sukayi awurin Shi,acikin waɗannan kwanakin sun samu kyakkywar kulawa a wurinshi,kullum sai sunce mashi yaje ya ɗauko oummansu itama ta dawo gidan,sai yace masu su ƙara haƙuri zai kawo masu ita,

 

Ana haka sayyadi yadawo tun bayan da aka sallami su sehrish da jahad daga asibiti bai ƙara leƙo gidan ba sae a wannan lokacin yayi ma abu zuwan bazata,tun aranar ya soma tambayarta ina ƴa’ƴanshi suke,banza takeyi mashi bata bashi amsa,jinjina kanshi yayi tare da cewa duk ma inda takai su zasu dawo ne da ƙafafunsu,

 

Aranar da yayi maganar,tsakar dare suna kwance abusufyan ne tsakiyarsu,hosana da jahad suna gefe da gefenshi,Sehrish kuma na kwance saman jikinshi duka ya sanya hannunshi ya dafe su,

 

Kwatsam yaji kukansu acikin kunnuwanshi,a firgice ya farka nan fa yaga tashin hankalin da bai ta6a gani ba,sai birgima sukeyi idanunsu sun canza launi,kowacce ta dafe kunnanta sae ihu takeyi,saboda sunansu da ake ambata da wani irin sauti mara daɗin ji,hankalin abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kar yaran su mutu,wata irin zufa ce ke tsastsafowa daga jikinsu,sharkaf suka jiƙe,

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

Faɗowa cikin ɗakin haris yayi jikinshi na kerma,abusufyan na ganinshi muryarshi na rawa yace”Haris kalli yaran nan ka gani wlh bansan me ya same su ba,ko zamu kai su asibiti ne”?

Girgiza kai haris yayi tare da cewa”Ko mun kaisu asibiti babu abunda zasu iya yi masu!yanzun nan sayyadi ya kirani awaya ya sanar dani cewa mu dawo mashi da ƴa’ƴanshi in ba haka ba zasu mutu a hannun mu ne,kuma zaiyi shari’a damu akan laifin mun kashe mashi ƴa’ƴanshi,ina da tabbacin cewar duk shirinshi ne wannan,”

Jiki na rawa abusufyan ya sauko daga saman gadon ya ɗauko hosana da jahad a hannnunshi,haris kuma ya ɗauko sehrish,

Cikin mota suka sanyasu,sannan haris yaja motar suka nufi gidan Ya sayyadi,wuraren ƙarfe sha biyu kenan na dare,tun kan su ƙarasa ƙopar gidan suka hango sayyadi atsaye jikinshi sanye da jallabiya,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,

 

Parking ɗin Motar sukayi,da sauri suka ɗauko mashi yaran suka kai mashi,abun mamaki suna ƙarasawa inda yake sai gashi sun dawo cikin hayyacinsu,tun daga nan kowa yasha jinin jikinshi,

koda suka saukesu ƙasa,suna ta faman murza idanunsu,suna yin arba da sayyadi,jikinsu na kerma suka ƙanƙame abusufyan suka manne mashi tamkar zasu koma jikinshi,

 

Hasken fitilar kwan dake a kopar gidajensu da kuma hasken motar su abusufyan dake ajiye,shi ya taimaka masu wurin ganin junansu da kyau,

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Sayyad da kuma Abusufyan,maƙiya sun haɗu,

Haris ne yace”kaji tsoran Allah,laifin me abu tayi maka ita da yaranta da har kake son cutar da rayuwarta?

Murmushi kawai sayyadi yayi yana kallonsu yace”nagode sosai,da irin kulawar da kuka ba ƴa’ƴana,naga an canza masu kaya,an kuma saya masu takalma,abu yayi kyau,kaga masu Ji da naira,ba kamar mu ba ƴa’ƴan malam shehu…….’

. afusace abusufyan ya katse shi da cewa”Kai malam!ka faɗamun taya akai ka auri abu da ciki na!don bincike ya nuna cewa yaran nan ƴa’ƴana ne!ba naka ba!dama najima ina zarginka wlh!kai ba mutumin kirki bane!”

shu’umin murmushin nan nashi ya saki tare da cewa”Oh kanaso kasan yadda akai na auri abu da cikin ka”?

Har suna haɗa baki shi da haris wurin cewa Eh,

Dariya sayyad yayi kafin ya matso dab da Abusufyan suna fuskantar juna ido cikin ido yace”tabbas Ƴan ukun nan ba ƴa’ƴana bane!naka ne halak malak,tun lokacin da kuka rabu da abu ta sanar dani cewa tana jin tashin zuciya,anan nagane cewa tana ɗauke da cikinka,shine na kwantar da cikin ta hanyar yin amfani da sihiri na,babu wanda yasan cewa tana da ciki har na aureta,sannan na bayyanar da cikin a jikinta,don su taso amatsayin ƴa’ƴana…….’

Katse shi haris yayi da cewa”meyasa kayi hakan toh”?

Sayyadi yace”bana faɗin dalili sai dae kawai in bada amsa,’

Jiki asanyaye abusufyan yakai idanunshi kansu hosana dake manne ajikinshi sun ƙankameshi,alamar basu so yabarsu anan,tuni yaji hawaye sun cicciko mashi a idanunshi aranshi yace ashe dae dagaske jini na ne su,

“Amma meyasa ka auri abu?yanzu nake kokwanton cewa anya don kana sonta ka aure ta”?

sayyad yace”ina fa?ni sam mace bata gabana!namiji kawai,da maza nake mu’amalata,Na auri abu ne duk don saboda in samu hanyar da zan shiga rayuwarka,kuma na samu,’yayi maganar yana nuna su sehrish dake ƙankame da jikinshi,

Karanta>>> Amfanin Ƴaƴan Gwanda Musamman Ga Mata

Rae a6ace haris ya cakumi wuyan rigar sayyadi yana cewa”wlh bazamu ƙyaleka ba,mugu azzalumi!zamuyi ƙararka kotu akan yaran nan,’

Dariya yayi tare da cewa”nafi ƙarfin kotu haris!babu abunda zasu iyayi mun,’

“”Idan ka fi ƙarfin kotu ae baka fi ƙarfin Allah ba,zamu kai ƙararka wurinshi,kuma insha Allahu sayyad ba zakayi kyakkywan ƙarshe ba,sae kayi mummunan mutuwa kamar yadda mahaifinku kakah yayi……’

Buge hannun haris yayi daga cakumar wuyan rigarshi da yayi,cike da mamaki yace”Oh ashe ka gane ni!”

jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa”bangane kaba,amma tunda ka ambaci cewa kana son shiga rayuwata na gane cewa kai daga family ɗinsu kakah kake,Azzaluman mutane,mugaye waɗanda suka mayar da zalunci hanyar cin abincinsu,masu tada ƙayar baya a ƙasarmu,asannu asirinka zai tonu kamar yadda na ubanku ya tonu kuma insha Allah,Abbana da kuma yayana Hussein,kai bama su kaɗae ba nayi maka alƙawarin cewa a hannun ɗaya daga cikin jikokin Amminmu zaka Mutu,mummunar mutuwa kuma a wulaƙance kamar dabba haka zakayi ta,idan Allah ya nuna mun wannan ranar ni kuma zan tuna maka waɗannan kalaman da nayi maka,

Hannu Abusufyan yasa tare da dafa kawunansu sehrish dake manne da jikinshi yace”idan Allah yasa su kayi tsawancin kwana basu mutu a hannunka ba,A gabansu za’ayi komai,”

Fashewa da dariya sayyadi yayi hada dafe cikinshi,lokaci guda kuma ya tamke fuskarshi tamkar bai ta6a yin dariya ba yace”kai fa ƙaramin ɗan iska ne mai kwana da wando,har yanzu bakasan wanene sayyadi ba,labarina kawai kake ji,nafi ƙarfin duk wanda kake tunanin zai iya ɗaukar fansa akaina!danginku gaba ɗaga babu wanda zai iya ɗaga mun yatsa,kuma inaso na sanar maka cewa muna nan muna shirin tarwatsa farin cikin zuri’arku,muna nan muna shirya maku maƙarƙashiya,bani kaɗae bane yawa gare mu kuma muna nan kewaye daku,’

Kallon juna haris da Abusufyan sukayi kafin su mayar da idanunsu kan Sayyadi,

“Daga rana irin ta yau!ina mai gargaɗinka da cewa kada ka kuskura ka ƙara yunƙurin zuwa ɗaukar yaran nan!wlh in har ka ƙara takowa kazo inda suke!ko kuma ka turo wani naka da niyyar ya taimakesu!koma wanene sai ya Mutu!!!!na sanya katanga a tsakaninku dasu,zaku iya tafiya,”

Karanta>>>Maganin Rage Kiba Da Tumbi Cikin Kankanin Lokaci In Sha Allahu

Ya ƙarasa maganar tare da nuna masu hanyar inda motarsu take da hannunshi,hannu abusufyan ya sanya yana ƙoƙarin raba su hosana da jikinshi kuka suka fashe dashi suna roƙonshi akan karya tafi yabarsu a hannun wannan mutumin basu son zama dashi……..’wata irin tsawa ya sayyadi ya daka masu a gigice suka raba jikinsu dana abusufyan suka shige gida da gudu suna kuka,ashe Abu tana a la6e a zauren gidan tana sauraronsu,tun lokacin da abusufyan yazo da su hosana,tasha kuka kamar taje ta rungumoshi ajikinta haka ta dinga ji,kamar ta zauce tayi hauka,su hosana na shigowa ta haɗasu duka ta wuce dasu ɗakinta,anan suka zauna suna ta sharar kwalla,

 

Jiki asanyaye abusufyan da haris suka shige cikin motarsu,tun daga wannan lokacin ne abusufyan yabar Nigeria ya koma Turkey gaba ɗaya,bai ƙara leƙo nigeria ba,ya nesanta kanshi da kowa ne saboda bazai juri zuwa nigeria ba,yayin da ƴa’ƴanshi suke rayuwa awulakance baida ikon taimakonsu ko ya sanya a taimakesu,sai dae Addu’a da yake binsu da ita.

 

Haka su sehrish suka ci gaba da shan wahalar rayuwa a hannun mutumin nan,wani tashin hankalinma sayyadi  ya fara kwaɗaita dasu,ya dinga nemansu a 6oye abu bata sani ba,duk in tayi kuskuren fita ta barsu acikin gidan yazo ya same su haka zai ƙumshe su aɗakin yana tsoratar dasu akan susha mashi gabanshi,duk abu bata ankare ba,sae wata rana da ta ta6a dawowa ta same su suna ta kwarara amai wani irin abu mai yauƙi yauƙi yana fitowa abakinsu,tsare su tayi da tambaya akan me suka sha ne ya 6ata masu ciki,ƙin faɗa mata sukayi saboda tsoran kada Abbansu ya kasheta kamar yadda yayi masu barazana in suka faɗa mata,ganin sunƙi faɗa mata yasa ta ɗauko wuƙa a kitchen ta nuna su da ita tana cewa”Ko ku faɗa mun ko in kashe ku a wurin nan,”gaba daya suka tsorata,sehrish ce ta buɗe baki ta sanar da ita abunda mahaifinsu ke sanyasu suna yi mashi,saboda tashin hankali nan take ta yanke jiki ta faɗi asume,

Kukan da suka fashe dashi ne yasa makwabciyarsu shigowa gidan don taga meke faruwa ne,anan ta samu abu a sume ruwa ta ɗebo ta yayyafa mata ta farka,miƙewa tayi zaune tare da sanya hannu ta dafe saitin zuciyarta tana ambaton Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!ya Allah ka ɗauki raina tun kafin baƙin cikin mutumin nan ya kashe ni,Sayyadi ka cuci rayuwata ka gama dani nashiga uku! Wayyo Allah na!

Tasha kuka kamar ta zauce,daƙyar maman sadeeq ta lallashe ta bayan ta tsagaita da yin kukan take tambayarta meya faru,bata 6oye mata komai ba ta kwashe ta sanar mata,a lokacin maman sadeeq har hawaye sai da ta zubar masu saboda tsabar tausayin yaran,ranar yini sukayi suna jimamin abunda ya faru atare kuma suka duba yaran don su tabbatar in bai lalata su ba,duk da sun tambayesu ko ya masu wani abu a wurin sunce a’a,bayan tafiyar maman sadeeq ta koma gida mijinta ta samu tayi mashi magana akan Yayi ma sayyadi magana akan abunda yake aikatawa saboda abun yayi yawa,yana cutar da rayuwar yaran, nan gaba zai iya lalata masu rayuwarsu gaba ɗaya har ma yayi silar Rasa ransu,

Karanta>>> Dalilan Dake Zawo Rashin Sha’awa Ga Mata

Jinjina kai Malam yayi tare da cewa”Hmmmm taya zan tunkari mutumin nan?me zan iya yi mashi?Mutumin da kana ja mashi aya yana fassarata!taya zai fahimci cewa badai dai yake aikatawa ba?bayan yasani kuma yake take sanin!Tabbas na tausaya ma rayuwarsu amma babu ta yadda zan iya taimakon rayuwarsu sae dae na bisu da addu’a kawai,Allah shine zaiyi maganinshi”shi kanshi Abban sadeeq sae da ya zubar masu da kwalla,ya tausaya ma rayuwar yaran,tabbas suna cikin masifa,

 

Bari in taƙaice maku labarin,sayyadi shine yayi sanadiyar ta6in hankalin hosana,a tsakar dare suna bacci ya ɗauketa batare da sanin kowa ba,ya kaita gidan wani Babban ɗan siyasa kamar yadda suka tsara dashi akan cewa zai kai mashi ita yayi amfani da ita don cin nasarar za6en shi,sam batasan ya ɗaukota ba sae dae kawai ta ganta asaman gadon mutumin,fasa ihu tayi da sauri ta diro daga saman gadon tana ƙanƙame jikinta,mutumin nan babu kunya babu tsoran Allah ya shiga tu6e kayan jikinshi agabanta,a tsorace tace mashi fitsari take ji,ya nuna mata hanyar toilet taje tayi fitsarin yana jiranta,

Jiki na rawa ta shige cikin toilet ɗin ta rufo ƙopar,Kunna fanfo tayi don kar yaji ƙarar abunda zatayi,zagaye tashiga yi acikin toilet din tana neman abunda zata fasa window ɗin kewayen,annan ƙasa ta samu wasu ƙarafuna masu ɗan tsayi kamar an ta6ayin gyaran wani abu a toilet ɗin aka ajesu nan,

Hannu tasa ta ɗauka jiki na rawa ta haye saman toilet seat ɗin dake a rufe,ta faffasa windown da sauri da sauri duk mutumin nan baijiyota ba,sai da ta fasa glass din ya tarwatse sannan ta biyo ta windown duk batayi tunanin cewa bayan yana da tsayi ba,kawai ta  afka,gaba ɗaya ta bugi floor ɗin da ƙarfi kanta ya fashe,hancinta da bakinta duk suka bugu ga sauran kananun glass da suka yayyanketa ta,gigitacciyar ƙara ta saki saboda azabar da tasha,amma hakan bai hanata yunƙurawa ta miƙe da gudun gaske ta nufi hanyar fita daga gidan,mai gadin gidan na sallar dare ta samu ta fice da gudu ta karamar kopa tana kuka ta miƙi hanya gashi dare ne,

 

Acan kuwa tsakar dare Oummansu na bacci ta jiyo muryar jahad tana cewa”oumma ki tashi,hosana bata a gida fa,banganta ba,har kewaye na duba amma babu ita bansan ina taje ba,hankali atashe abu ta farka,a lokacin itama sehrish ta tashi,gaba daya suka shiga nemanta,duk sayyadi na ɗakinshi yana jiyo hayaniyarsu bai tanka masu ba,da suka duba ko ina basu ganta ba,anan fa hankalinsu ya ƙara tashi,fitowa sukayi suna bi gidaje suna tambayarta wasu a amsa masu da bata nan,wasu gidajenma ba mai zuwa balle ya basu amsa,kai tsaye suka miƙi hanya suna duddubawa ko wani mummunan abu ya faru da ita ne,lokacin da suka hau gefen titi suna tafiya……..

Adai dai time ɗin Hosana ta shigo kan hanyar da gudu tana kuka hannunta dafe da kanta dake ta zubar da jini,tana ambaton oumma, oumma,

a gigice suka kai idanunsu wurinta,da gudun gaske suka tunkareta,abu na ƙoƙarin dakatar da ita akan ta kauce daga saman titin amma sam bata a cikin hayyacinta,wata mota ce ta bugeta da ƙarfin gaske gaba ɗaya ta kife ƙasa,mai motar na bugeta yaja motar da gudu yabar wurin alamar cewa da gangan ya bugeta,ashe ɗan siyasan nan ne yabiyo ta,bayan ya jima yana jiranta ta fito daga toilet bata fito ba,kawai ya afka ciki anan ya samu ta fasa glass ta gudu,yana huci ya fito ya mayar da kayanshi,ya bi bayanta cikin motarshi,don karta tona mashi asiri yasa yayi mata haka don ta mutu,

Karanta>>> Dalilan Dake Sawa Nonuwa Suke Zama Kanana

Zubewa sukayi agabanta suna ta kuka suna ta faman jijjigata a ƙarshe Abu ta sanya hannu ta ɗauketa,a ƙafa suka taka da sauri da sauri saboda babu abun hawa,gashi sae bleeding takeyi,suna cikin tafiyar nan sai ga Mijin maman sadeeq cikin napep,ashe tun lokacin da suka je gidan neman Hosana,bayan tafiyarsu ya gaza samun natsuwa shine ya biyo bayansu,napep ɗin ma bata shi bace arota yayi,saboda mashin ɗinshi babu mai,

Adai dai inda suke ya tsayar da abun hawan nashi,tunda yaga halin da hosana ke ciki bai tsaya tambayar ba’asi ba yace su shiga ciki,

A daren ranar suka kaita asibiti,likitoci suka shiga duba ta,tun nan aka sanar dasu cewa Sai anyi mata aiki,ana buƙatar kuɗi miliyan ɗaya da rabi,nan fa hankalinsu ya tashi,saboda ko sisi basu da ita,

Har washe garin ranar ana kan abu ɗaya,andai samu an fara treating ɗin raunukan jikin nata,aikin dai ne ya gagara,sun jima a asibitin nan ana neman taimakon kuɗin da za’ayi mata aiki amma ba’a samu ba,sayyadi ko leƙo asibitin baiyi ba,bayan shine silar komai don ubanshi,

 

Sanadin haukacewar mahaifiyarsu kuwa,lokacin anata neman yarda za’a harhaɗa kuɗin aikin hosanan,duk wani abu mai dan amfani tasa an sayar dama ba wasu abun kirki suka rage mata ba,don duk ta siyar da kayayyakinta wurin kula dasu Sehrish,a lokacin abu duk ta gama fita hayyacinta ta kode ta rame,duk da dae kyawunta na nan,amman inka ganta zaka yi tunanin ta girmi shekarunta saboda wahalar rayuwa,

ta yanke shawarar zuwa gidan ta duba taga idan sayyadi yana nan jin shiru bai neme su ba,ko labarin kwanciyar hosana asibiti baije mashi bane,

Tana sa ƙafarta tsakar gidan nanfa ta dinga jin wannan gurnanin abunda sukeyi mara daɗin ji,ranta yayi mugun 6aci,kitchen ta nufa ta ɗauko tukunya ta zubo ruwa a fanfo kusan rabin tukunyar mai fadi,bayan ta ɗaura ruwan sai da ta jira ruwan ya tafasa sosai yana huci sannan ta sauke shi,tsumma ta ɗauko ta ruƙo tukunyar dashi,ta nufi ɗakin nashi,cikin sa’a sun bar ƙopar a buɗe dama da yawan lokutta basa rufe ƙopa turo ta kawai sukeyi,

Karanta>>> Ingantaccen Matsi  Da Bashi Da Illah

Faɗawa cikin ɗakin abu tayi,mutun shida ta samu kamar wasu mayu manne da juna,aikuwa tana ƙarasawa wurin gadon,ta ɗaga tukunyar gaba ɗaya ta maka masu ruwan zafin ajikinsu,wa’iyazubillah,agigice suka rabe da junasu,wata irin gigitacciyar ƙara suka shiga saki ta azabar radaɗin tafasasshen ruwan zafin nan da abu ta watsa musu,ihu suka dinga yi suna birgima,fatar jikinsu duk ta ɗame ta lalace,

Duk atunaninta hada sayyadi acikinsu ashe yana acikin toilet,razananniyar ƙarar daya jiyo daga cikin bedroom ɗinshi ne yasa shi fitowa daga cikin toilet din,Waro ido waje Sayyadi yayi tare da aza hannunshi akai yana ambaton”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!Abu baki da hankali ne!!kinsan ko me kika aikata?

Idanunta jawur ta kalleshi rai amatuƙar 6ace tace”Na sani,kuma ina cikin hayyacina,wlh naso ace hada kai acikinsu na haɗa na ƙona,uban kowa ya huta da wannan masifar…..’

Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya kifa mata mari zazzafan gaske har sae da gefen bakinta ya fashe,

Ɗagowa tayi da idanunta dake zubar da hawaye tace”Banji zafin marin da kayi mun ba!ada inajin shakkarka amma yanzu bana jin tsoranka acikin zuciyata,Wlh saina tona maku asiri duniya tasan me kuke aikatawa,daga nan in na fita gidan radio zanje in yaɗa duk wani mugun abunda kuke aikatawa,’

Wani irin huci ya shiga yi zufa na gangarowa daga jikinshi sae tsuma yake yi,hannu yakai tare da shaƙo wuyanta ya bugata jikin wardrobe ɗin dakin,

Sannan ya soma magana da wata irin murya mara daɗin ji yace”Ke daƙiƙiyace har yanzu bakisan ciwon kanki ba!kina tunanin cewa zan bari ki tona mun asiri ne!!kafin na juya maki tunaninki,inaso nasanar dake cewa Hosana jahad da sehrish ba ƴa’ƴa na bane!Da cikin abusufyan na aure ki!kuma nine na kashe mahaifinki baba buzu,saboda yana ƙoƙarin hanani auranki!’

 

Wasu irin hawaye ne masu zafin gaske suka shiga gangarowa a fuskarta,tsabar baƙin ciki da takaici yasa ta gaza magana,saboda wani irin ƙululun baƙin ciki daya tokare mata maƙoshinta,

ƴa’ƴan naki ma bazan barsu ba!ɗaya bayan ɗaya saina kashe su!’

Yana faɗin hakan ya saki wuyanta,da gudun gaske abu ta fito daga cikin ɗakin nashi tana kuka,a ƙopar gidan ta tsaya tana faman ambaton sunan baba buzu tana cewa babana ka kashe mun ka raba shi da ranshi,ka kashe mun babana ko,kuma zaka rabani da ƴa’ƴana suma ka kashe su ko……’haka ta dinga sambatu ita kaɗae,

Tun daga wannan lokacin abu ta haukace ta miƙi santa tana faman sambatu,

 

Wannan shine silar rabuwarsu da mahaifiyarsu basu ƙara sanin inda take ba,

 

Abunda kuma yayi silar komawarsu katsina,labarin neman da mahaifinsu yake yi masu don ya kashe su kamar yadda ya fada ma abu,ya isar masu maman sadeeq,ko aikin ba’ayi ma hosana ba,amma ta miƙe saidae babu hankali ko kaɗan,da taimakon Mijin maman sadeeq ya sanyasu a mota tare da damka ma direban amanarsu,bayan yasa anyi ma hosana allurar bacci ya bama Sehrish address ɗin gidan tsohuwar nan,wadda ta kasance kishiyar mahaifiyarshi ce anan suke zaune,tsohuwa mai kirki koda yayi mata bayanin halin da yaran suke ciki ta tausaya masu sosae ta kuma ce zata rike su da tsakani da Allah,shima kuma yayi alkawarin zai rinka turo da dan abunda Allah ya hore,

Da daddare suka isa unguwar ba tare da sanin kowa ba,sai da aka taimaka masu kafin aka samu suka shiga da hosana gidan,a ɗaki ake rufeta saboda haukan da takeyi,na bugun mutane da jefe jefe,tsaf zata iya kashe mutun,

Wannan shine silar komawarsu gidan tsohuwar nan,tayi masu halarci arayuwa,ita ta dinga nema masu tallafi don a maida hosana asibiti ayi mata aiki,haka sehrish ma bata zauna ba,har wankau suke yi suyi guga itada jahad suna tara kuɗin da za’a kai hosana aiki,kafin tsotsai ya ritsa da jahad,

Akwai wani lokaci da suka je gidan wani ɗan majalissa jin labarin cewa yana taimaka ma marasa lafiya waɗanda ake buƙatar kuɗin da za’ayi masu aiki,tsohuwa da sehrish suka je gidan mutumin,yayin da suka bar jahad a gida tana aikin wanki,

Tana cikin yin wankin nan ta dinga jin kukan hosana gwanin ban tausayi tana cewa dan Allah su buɗe mata ƙopa su taimaki rayuwarta mutuwa za tayi,tana son ganin ƴan uwanta,me yasa kullum suke ƙumsheta a ɗaki,zafi ya isheta,itafa tana da hankalinta,ba mahaukaciya ce ita ba,tana da hankalinta,

Natsuwa jahad tayi tana sauraranta,yanayin yadda hosana ke kalamanta yasa tayi tunanin cewa kodai ta samu lafiya ne,tun tana tsoran buɗe mata ƙopar har dae tausayinta ya kamata sosai,da sauri taje ta buɗe mata ƙopar,

Karanta>>> Rigakafin Zubewar Nono, Lalacewa Da Kuma Yadda Mike

Kamar jira take a buɗe da ƙarfi ta damƙi wuyan jahad da hannunta,ta janyota cikin ɗakin,tana cewa”dama kece kika sace ni ko?kika rufe ni acikin ɗakin nan kina cutar dani!yau Allah ya kamaki!wlh saina rama,

Duk yadda jahad taso ta kwaci kanta a hannun hosana abun yaci tura saboda wani irin mahaukacin ƙarfi ne ke gareta,buga kan jahad tashiga yi ajikin bango,jahad ta fasa ihu saboda azabar da taji,nan take jini ya shiga bulbulowa daga goshinta,kuma hakan baisa hosana ta daina bugunta ba,har saida taga jahad ta daina motsi sannan ta saketa,

Adai dai lokacin tsohuwa da sehrish suka dawo cikin gidan,da gudu suka faɗo ɗakin da hosana take ganinshi a buɗe nan suka samu jahad wanwar ƙasa jini na zuba,itama hosanar tana baje ƙasa sai faman mirgina-mirgina takeyi numfashinta na fita sama sama,

Wannan shine silar da aka kwantar da hosana da jahad asibiti,har akayi ma jahad ƙarin jini,ita za ayi mata aiki,

Inda Allah ya taimakesu asibitin suna da wata ƙungiya wadda manyan masu kuɗi ke tallafawa marasa lafiyan da za’ayi ma aiki da wani parcentage,sun samu kuɗin amma akwai cikon da zasu yi dubu ɗari tara likitocin suka buƙata a wurinsu,

Sehrish tasha wahala sosai wurin neman cikon kuɗin nan,duk inda taje neman taimako sae an nemi ta bada kanta sannan abata kuɗin,anan ne wata mata dake jinyar wata a ward din da aka kwantar dasu hosana take ba sehrish labarin hajjaju dake ɗaukar ƴan aiki tana samo masu aikatau suna yi kuma suna samun alheri dayawa,saboda gidajen manyan masu kuɗi take samo masu aiki,matar tace in taci sa’a ma,aranar da tafara zuwa aiki sai tace ma masu gidan su bata kuɗin aikinta na shekera ko biyu ne,in aka dace zasu bata kuɗin,bayan matar ta bata address din gidan,tun daga ranar sehrish kullum sai taje ƙopar gidan hajjaju nemanta,har Allah yasa ta samu ganinta,

 

Atakaice tarihin su sehrish hosana da jahad kenan,duk da bakomai aka fayyace ba, amma mutun zai gane inda aka dosa,

 

💋Boss Bature💋

 

Jikin kowa yayi mugun sanyi,masu raunin zuciya acikinsu tuni sun soma zubar da hawaye,hatta jahan dake da taurin kai sai da ya matse kwalla,Abusufyan kuwa tuni ya fashe da kuka,haka gwaggon katsina kamar ƙaramar yarinya haka ta dinga kuka tana fadin”Allah ka tsine ma Sayyadi da duk zuri’arshi!Allah ya wulaƙanta rayuwarshi kamar yadda ya wulakanta rayuwar ƴa’ƴan abusufyan ɗina,

 

Hatta Abbansu sae da ya matse kwalla shi da Abbas da su fawan,kowa ya harzuƙa ransu yayi mugun 6aci,tsananin tausayin su Jahad hosana da sehrish ne ya kamasu,marshal Omar kuwa sunnar da kanshi ƙasa yayi idanunshi sunyi jawur jikinshi sai kerma yake yi,zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi saboda tsabar 6acin rai,

Sehrish kuwa lokacin da Jahad ta kammala bada labarin tasa kuka ita da Hosana,

Nan take ta miƙe daga jikin Sgr,hankali a matuƙar tashe take kallonsu yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi,kowa zuba mata ido yayi yana kallonta ganin yadda jikinta ke rawa tana kallonsu hosana da jahad,

Muryarta na rawa ta ambaci sunansu”Hosana jahad kune………’tana faɗin hakan ta yanke jiki ta faɗi asume,

Da sauri abusufyan da hajiya azeema sukayo kanta hada su jahad ɗin,

Sam Sgr bazai iya jurewa ba,yunƙurawa yayi azafafe ya juya tare da nufar upstairs ya koma bedroom ɗinshi,agaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi wadda take daure tamau,gaba daya jikinshi sae kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,wata irin zufa ce tashiga gangaro mashi daga gefe da gefen fuskarshi,tabbas idonshi Idon Sayyadi………………………….

Back to top button