Hausa novels

Halysaah Page 25 By Khaleesat Haydar

HALYSAH 25…

Khaleesat felt so much relieve after leaving AJ’s room, tana biye da Jay ta koma dakin da take, ba tare da Jay ya kalleta ba bayan ya ajiye laptop dinta dake hannunsa yace “Kin ji sanda aka bude kofa da asuba ne?” Khaleesat na kallonsa ta girgiza kai tace “I am not sure, may be ina bacci sannan, banyi bacci da wuri ba” Yace “Ohk” Tace “Why are you asking?” Ya juyo yana kallonta, ya ɗan mata murmushi yace “Nothing” Tace “But ai frnd din ka yana shigowa ya dau stuffs dinsa wani lkcn” Jay yace “Ohk” Har ya juya sai kuma ya sake dawowa yace “Kince baki yi bacci da wuri, ciwon kan ke damunki har yanzu?” Ta girgiza kai tace “A’a, kawai baccin ne dai bai zo ba” Yace “Ohk” Khaleesat ta bi sa da ido har ya fita daga dakin sannan ta zauna gefen gado a hankali, har cikin ranta take jin kamar ta jawo ranan talata, she is so tired tana bukatar kawai ta ganta kusa da Ummanta, she need her Mom’s hug, Jay na fita ya kira ma’aikatan gidan su gyara ma AJ dakinsa, Jay made sure the workers left nothing untouched a dakin duk da babu abinda dakin yayi, amma irin gyaran da aka ma dakin da bandakin ba na wasa bane, sai da ko ina ya dawo yana sparkling tsabar gyara sannan Jay ya koma downstairs, amma still a ranan ma AJ bai kwana dakin ba, yayi kwanciyarsa a parlor kan kujera. Washegari which was monday AJ na zaune usual spot dinsa a compound da Coke din gwangwani a gabansa, har a sannan yaki ce ma Jay komai a gidan, not even Jay hatta ma’aikatan gidan duk ba wanda yake yi ma magana he is just keeping straight face, Jay ya fito daga cikin gida ya karasa har inda yake zaune, ko kallon direction dinsa AJ bai yi ba yana juya counter din hannunsa, Jay na kallonsa yace “Abba wants to speak to you” Yana fadin haka yace “Abba gashi nan” Ya ajiye wayar gaban AJ, Calmly Abba yace “How are you doing Junaid” AJ ya sauke idonsa ya gaida Abba, Abba ya amsa yace “You didn’t call to know if we arrived safely” AJ yace “Ayi hakuri” Abba yace “It’s fine, yaushe za ku dawo hutu” AJ yace “Ran Thursday zan dawo in sha Allah” Abba yace “What about Jawwad” A takaice AJ yace “I don’t know” Abba yace “Hand the phone over to him” Jay ya dau wayarsa sitting in one of the chairs beside AJ yace “Na’am ina ji Abba” Abba yace “Kai yaushe zaka dawo” Jay ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Probably next week in sha Allah” Abba yace “Ohk Allah ya kai mu, earlier today you said you have something to tell me unfortunately ina tare da baƙi a lkcn, so what is it Jawwad” Jay ya ɗan shafa kansa thinking of where to start, can dai yace “Abba dama it’s about the girl u saw yesterday” Abba yayi shiru at first, sai kuma “Ohk, what about her?” Jay yace “Abba ni ne na kawota gidan ba AJ ba, she is a student of John Hopkins also, she is having issue with House rent and she’s writing exam, so shine kawai na kawota gidan nan zuwa sanda zata gama jarabawan….” Abba ya dakatar da shi yace “Did you and Junaid birth me or i birth you both?” Jay ya girgiza kai da sauri yace “Billah Abba i am not cooking up stories, believe me, all what i am saying is the truth ai kasan bana maka karya Abba, kawai dai ni na kai ta dakin AJ ne without even his knowledge cause Aunty will definitely see her in the house, part din AJ ne kawai nasan bazata shiga ba, kuma because of this… AJ parlor ya dawo yake kwana, wallahi babu komai tsakaninmu da ita kawai taimako ne, you can even speak to her to confirm ranka ya dade” Abba yace “If she is having rent issue don menene baza ku bata kudin hayan ta biya ba ko kuma ni ku min magana, na menene sai kun kawota nan gida cikin ku ta zauna? Is that ur home training? Dama addininku ya yarje maku da haka?” Jay ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace “Kayi hakuri ka gafarce mu Abba, she will be rounding up her exam on Tuesday, and she will leave in sha Allah” Abba yace “Kaga da ba don nasan baza ka min karya ba Ahmad i won’t listen to you, da Junaid ne ya tsaya mun wannan bayani bazan yarda da shi ba, and my plan was to start making arrangement na samar masa mace da zan aura masa a kai masa ita can ƙasar, tunda ka min wannan bayanin naji na kuma yarda amma daga kai har shi sati biyar na baku kacal ku gabatar min da macen da za ku aura, ita kuma i will send you some money to sort out her House rent” AJ ya daga kai yana kallon Jay bayan yaji abinda Abbansa yace, sai kuma ya mike kamar zai tashi sama ya bar wajen, shi dai Jay was speechless this was the least thing he was expecting to hear from Abba, jin Abba ya katse wayar ya zuba ma screen din ido, ya basu 5 weeks?? jay ya fi minti goma zaune a wajen kafin daga karshe ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya dau wayarsa ya shiga cikin gida. The next day Khaleesat suka gama jarabawansu na karshe and she was so happy amma kuma da ta tuna wasu abubuwa kawai sai mood dinta ya canza, suna zaune tare da Safiyyah a cikin makarantar ganin yanayinta da yanda ta sauya lokaci daya tayi shiru, Safiyyah ta kalleta tace “Why are you like this Khaleesat?” Khaleesat ta daga kai ta kalleta, a hankali tace “I don’t have the means of going back to Nigeria Sophie, the burden i am placing on my Housemate is too much ba shi ya kawo ni kasar nan karatu ba, he knows nothing about me, don me zan yi ta dora masa nauyina har haka?” Safiyyah tace “To ya za kiyi Khaleesat, tunda ba ke kika rokesa ya maki ba ai kawai addu’a zaki masa Allah ya saka masa da alkhairi, he is ur God sent Angel, ba gashi with or without Abdul kin gama jarabawanki lafiya ba” Khaleesat ta sauke idonta jin hawaye ya ciko mata, Safiyyah ta hade rai tace “To meye na kuka kuma?” Muryarta na rawa tace “Ni dai bana son yace zai sake kashe min kudi masu yawa in koma Nigeria, i am feeling guilty” Safiyyah ta wani kalleta, can tace “Kya rube a kasar nan kuwa, ke kina da hanyar komawa ne? Ko kuma aikatau zaki nema a kasar ki tara kudin komawa Nigeria? In ba dai kudaden Abdul dake account dinki zaki yi using ki biya kudin jirgi ba” Safiyyah na kai wa nan ta kyalkyale da dariya tace “Ko ya kwashe en kudaden nasa ne?” Ita dai Khaleesat tayi shiru taki ce mata komai, Safiyyah tayi dariyarta me isarta sannan tace “Allah ba batun wasa ba, ya kwashe kudaden nasa ne?” Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace “Suna nan” Safiyyah tace “Miliyan nawa ne ma?” Khaleesat ta sauke idonta tace “Almost 9.5 Million” Safiyyah tace “To kawai ki siya Ticket abunki tunda dai yasan ba uban wani gareki a kasar ba da zai baki kudin komawa Nigeria ba, bayan shi kawo ki, in nice ke ma har shopping sai nayi na komawa Nigeria a cikin kudin wallahi, ai bazai san kin taɓa ba tunda ba shi ke ganin alert ba” Safiyyah na dariya ta kare maganar, ita dai Khaleesat bata tanka ta ba, Safiyya tace “Naji kinyi shiru ko baza ki taɓa ba? Wallahi yanzun nan in raka ki shopping mu fatattake kudin” Khaleesat tace “Ai ba nawa bane da zan fatattake su” Safiyyah ta kwashe da dariya tace “To ai sai kiyi ta zama a kasar, dama gulma ce yasa kika kawo maganar ba wani abu ba don nasan Jay kike saka ran ya biya maki ticket” Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take ta kasa ce mata komai, amma ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta, Safiyyah tace “In kuma in ma Ya Musty magana to, don dai Economy class ticket da zai siya mana bazai ce ya gagaresa ba” Da sauri Khaleesat tace “A’a, zan yi amfani da kudin account dina” Safiyyah tace “Atoh dai” Khaleesat ta gaya mata haka ne kawai don bata son taje ta ma Ya Musty magana…. Jay ne ya zo daukansu a schl din as usual, sai da ya fara dropping din Safiyyah sannan ya kama hanyar gida da Khaleesat, daxun nan yaga Abba ya sako masa dala dubu goma wai na House rent dinta, da ya gaya ma AJ sai cewa yayi ya masa transfer din Dala dubu biyar shi ma ya rike dubu biyar din tunda ba su suka kawota kasar ba, shi da Jay bai tankasa ba, Jay dake driving ya ɗan kalli Khaleesat jin shirun yayi yawa, yaga alamar tayi nisa tunanin da take, sai a sannan ya kula da idonta da yayi ja, a hankali yace “Halysaah” Juyawa tayi ta kallesa trying to look alright ta ɗan yi murmushi tace “Na’am” Yace “Are you okay?” Tayi yake tace “Na gaji ne kawai” Jay yayi shiru, bai sake ce mata komai ba amma yasan ba gaskiya ta fada masa ba, a ɗan few months din da yayi da ita har ya gama studying dinta gaba daya, he knows when she is happy, sad, bored, disturbed, and even tired, wannan karan yaga damuwa ne karara a fuskarta, ya dai ci gaba da driving dinsa har suka isa gida, bayan yayi parking ya juya yana kallonta, a hankali yace “Me ke damunki Halysaah?” Duk kokarinta na ganin ta nuna masa ba komai hakan yaci tura, don kawai ita ma gani tayi kuka ya taho mata, Jay ya jinginar da kansa da kujeran motar bai ce mata komai ba, kwana biyu ya huta da kukanta don a sanda ya dawo da ita gidan rana daddaya ne bata kuka don ma Safiyyah na taka mata burki kuma ya ga tana ɗan jin maganar Safiyyar wani lokaci, sai da tayi kukanta me isanta sannan yace “Sauka mu shiga ciki to” Ba musu ta bude motar ta sauka tana goge idonta, shi ma ya sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin gidan. Khaleesat na kwance da yamma ta shiga Hisnul Muslim dake wayar Jay sai ga kira ya shigo wayar, a hankali ta mike zaune tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren taji yace “Kin tashi?” Tace “Uhm” Yace “Kin yi sallah?” Tace “Nayi” yace “Ohk will you mind going out to the park with me?” Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace “Ohk, thank you” Yace “You are welcome, i will be waiting for you at the parlor downstairs” Tace “Ohk” After almost 15 mins Khaleesat ta sauko downstairs cikin shiri, sosai kayan jikinta yayi mata kyau sai dai ta rame sosai, shi kadai ne zaune parlon yana jiranta, tun da suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya mike ya jira har ta iso parlon yana kallonta, a tare suka fita zuwa parking space din gidan ya bude mata motar, ta ɗan kallesa tayi murmushi tace “Thank you” Ya bude ido yace “No thanks” bayan ta shiga ya kulle motar sannan ya zaga ya shiga driver seat, one of the best park na state din ya kai ta and she love everything about the park, the view was so fascinating and breathe taking, she felt so refresh and relieve taji kamar bata da wani damuwa a lkcn, Jay ya siya masu Wraps da fresh lemonade, wannan karan bata ji kunyar cin abinci gabansa ba, lkci lkci yake daga kai ya kalleta, ita dai ta dinga kallon feral horses dake park din from a far distance, can ta kallesa tace “Su ba a hawansu ne?” Yayi murmushi ya girgiza mata kai yace “Ba a hawa” Tace “And nobody is controlling them?” Yace “Sort of, they are just on their own with no supervision, ko kina son in kai ki inda zaki hau doki ne?” Er dariya tayi ta girgiza masa kai kawai, ya ɗan kalleta, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki a lokacin, ta kalli wraps dinsa da bai karasa ci ba tace “You are not eating?” Yace “Za ki ci ne?” Tayi murmushi tace “A’a, na koshi, kawai naga baka ci da yawa bane” Yace “Na ci abinci daxu ne, i am full” Ta kalli lemonade din gabansa tace “To in dauka?” Yace “A karo maki wani kenan?” Ta girgiza kai da sauri tace “Aa fa, i just don’t want it to waste ne” Ya dauki sauran lemonade din nasa ya ajiye mata a gabanta yana kallonta, ta dau straw din ta fara shan lemonade din a hankali, dauke ido yayi daga kallonta, wayarsa ya fara ring yana dubawa yaga AJ ne ke kiransa, yayi picking ya kai kunne, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, after few seconds Jay yace “Ni sai next week probably, ban gama abinda nake ba, do not book with me” Ajiye wayar yayi bayan AJ ya katse, ya kalli Khaleesat yace “Zaki jira har next week mu tafi Nigeria, or you will leave before then?” Khaleesat tayi shiru at first, a hankali ta sauke idonta tace “Yanda kace” Yana murmushi yace “Ko zaki bi AJ, he is leaving soon, yanzu ma ticket zai yi booking” Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, sai kuma tace “He that dislikes me shi ne zan bi sa?” Jay yayi dariya yace “How will you say he dislikes you Halysaah? He dislikes you shi ne yaje har apartment dinki yayi rescuing dinki? Ke ce dai baki ganesa ba har yanzu, AJ is nice just that yana da son girma ne kuma baya son raini, which i understand him because that’s our heritage, kinga ke ko gaishesa baki yi” Tana wasa da straw din lemonade din gabanta tace “To ai nasan ko na gaishesa bazai amsa ba, saboda na taɓa gaishesa bai amsa min ba” Jay dai yayi murmushi yace “In kin ci gaba da gaishesa ae zae amsa” Tace “Ur frnd doesn’t like me at all, he prefer my frnd” Jay yace “Who told you he is my frnd? AJ is my cousin bro Halysaah” Khaleesat ta daga kai ta kallesa tace “Da gaske?” Yayi murmushi yace “Ba ma kama ne?” Khaleesat ta buda hannu tace “Ni ban wani san yanda fuskarsa yake ba ai, ban taɓa kallonsa sosai ba” Jay yayi dariya, a hankali yace “To cousin brother dina ne, His dad is my father’s junior bro” Khaleesat tace “To amma dai ka girmesa ko?” Jay na murmushi yace “Not at all, just 3 months ne tsakaninmu, we will clock 34 next year” Khaleesat tace “Shi ne yace ya haifeni?” Jay bai san sanda yayi dariya ba sosai, sai kuma yace “Zolayarki fa yake, but how old are you?” Ta sauke idonta kasa kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace “I am 20” Jay ya wara ido yace “Waw, you are still a Baby Halysaah” ta wani kallesa, yana murmushi yace “To ai in AJ mace ne kuma an masa auren wuri ya isa ya haifeki” Yana dariya ya kare maganar, Khaleesat dai taki cewa komai still playing with the straw in front of her, a hankali Jay yace “Are you angry?” Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tayi murmushi ta girgiza masa kai still looking at him, Jay ya kwantar da murya yace “U misunderstood AJ, yana da kirki sosai, kuma yana da tausayi, just that he is a no nonsense kuma baya son raini, sannan truly yana da girman kai na sani, but that doesn’t make him bad, kuma da kinsan wanene shi zaki san yana ma da saukin kai” Khaleesat ta karasa shan lemonade din gabanta taki ce ma Jay komai, Jay ya kalli agogon wrist dinsa yace “Let go for horseback riding before it gets late” Khaleesat ta zaro ido tace “A’a ni dai bazan hau doki ba” Yana murmushi yace “To mu je dai” Shi ya fara tashi sannan ita ma ta mike suna tafiya a tare, satan kallonsa tayi suka hada ido ya ciro wayarsa yace “Let’s take some pictures with this beautiful view” A hankali tace “Ok” Tana tsaye kusa da shi yayi masu hoton da wayarsa, yana kallon hoton da yayi masu ya taɓa hancinsa yace “Ya naga hancinki yafi nawa tsayi, ya naga kamar kin fi ni kyau” duk lokaci daya ya jero tambayar yana sake kallon hoton da kyau, ita dai Khaleesat tayi murmushi tace “Uhm is that an irony?” Jay yayi dariya yace “I am serious Halysaah” Wata er Africa ce ta zo wucewa ya mika mata wayarsa politely yace ta masu hoto pls, yarinyar ta amshi wayar zata masu hoton, yanda Khaleesat taji ta uncomfortable kusa da shi, shi ma dai kamar hakan ne cause he left a little gap between them, yarinyar ta masu hotuna masu kyau kuwa, ita kanta yarinyar sai kallon hoton take kafin ta mika ma jay wayarsa tana kallon Khaleesat admiringly tana murmushi tace “You are so Beautiful” Khaleesat ta sauke idonta tace “Thank you” Yarinyar ta daga masu hannu ta bar wajen, bayan Jay yayi mata godiya, kallo daya yayi ma hotunan ya mayar da wayar cikin aljihunsa yace “Let go for horseback riding Housemate” Wani park din ya kai su daban da ake hawa doki, duk yanda yayi da Khaleesat ta hau doki bayan ya biya masu kudi taki wai ita bata iya ba tsoro take ji, daga karshe ta marairaice tace “Ni dai kawai ka bani wayarka in dinga maka video sai kai ka je ka hau” Yayi murmushi kawai ya mika mata wayarsa yace “To ai shikenan” Khaleesat was so impressed with his horse riding skills kamar irin dama ya saba din nan, sai murmushi take masa, mutanen wajen ma suna ta kallonsa, Khaleesat’s eyes were glued to him all through, tana yi tana masa video, sai after 7 suka bar wajen, tana kallonsa kafin su shiga mota tace “Where did you learn to ride horse confidently?” Yayi dariya yace “Back home” Tana murmushi tace “To ka taɓa zuwa nan ne?” Jay yace “Tab ai nan wajen zuwan AJ ne, kawai dai of recent ne muka dena zuwa” Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, sai da ya fara biyawa African Restaurant ya siya mata abinci, ganin leda daya ya mika mata yace “This is for you” Tace “Kai fa?” Yace “No, i am taking tea and bread this night” A hankali tace “Ohk, thank you” Bayan sun isa gida yayi parking, ta juya tana kallonsa a hankali tace “Thank you so much, Allah ya saka maka da alkhairi, i appreciate you” Without looking at her yace “Amma nace ki dena min godiya ko Housemate?” Tayi shiru, ya bude motar ya sauka sannan ita ma ta sauka, yana gaba tana biye da shi har suka shiga gidan, AJay na zaune parlor yana shan fruit salad yana kallon kwallo, ya juya ya kalleta don shi bai ma san bata gidan ba, suna hada ido abinda Jay yace mata daxu ya fado mata, ta sunkuyar da kai, kamar munafuka tace masa “Good evening” AJ ya gyara zama yana kallonta yace “Kin saba gaisheni ne zaki ce min Good evening??” Khaleesat ta ɗan kalli Jay da ya karasa cikin parlon, Jay yace “Good night Halysaah, if you need anything you call my line” A hankali tace “Thank you” Daga haka ta wuce sama, Jay na kallon AJ yace “Ba don na mata magana ba kana tunanin zata gaisheka ne dama? Ni ne nan na saka ta, sai me kuma in baka amsa ba?” AJ yace “Zamana take a gidan da zata gaisheni” Jay dai yaki tanka masa.

*

Back to top button