Haihuwa Da Hanji Page 15 Hausa Novel
Ta ɓangaren Afeefah Dr. Na tafiya ta janyo wayan, number Dr. Sulaiman shi ne number na biyu da ya shiga wayanta murmushi ta ɗan yi bayan ta buɗe sakon Saleem. Kusan saƙon shin na ashirin da wani abu kenan a ranar.”Ya jikin? Kin ji sauƙi? Kin ci abinci? Don Allah kar ki zauna da yunwa ki ci ko kaɗan ne, ko akwai abin da kike so in sa a kawo miki?”Saƙonnin kenan masu dauke da kulawa. A yanzu ma emphasizing yake akan ta ci wani abu cike da damuwa ƙarara a kalaman nashi duk ya damu, rubutu ta fara a hankali”Na Ci abinci kuma na ji sauƙi sossai ka kwantar da hankalinka ka ji Ya Saleem?”Numfashi mai nauyi ya sauƙe a sadda saƙon ya riskeshi matsalar shi ko ya baro Maiduguri ya dawo Kaduna a yau bashi da damar bata kulawa yadda ya dace hakan na damun zuciyarshi ƙwarai da gaske.”Alhamdulillah! Yanzu ni ma zan iya saka wani abu a baki na, na gode Afeefah. Ki kular min da kan ki sossai in akwai wani damuwa kar ki yi ƙasa a gwiwa wurin sanar min”Hawaye ne suka cika idanunta, me yasa zuciyarta ba za ta karye a kan saleem ba? Shi ne mutum na biyu da ya karɓe ta a yadda take, bai damu da maganganun mutane ba, ya ba ta kariya daga cutarwa ya ɗauko ta ɗaga kan titi ya kawo ta gidan su, yana iya ƙoƙarin shi wurin ganin bata zubar da hawaye ba, bata san da me za ta saka mishi ba bata ma da abin saka mishin da ya wuce Adu’a, har ranta take jin duk abin da mahaifiyarshi da ƙannenshi za su yi mata in har akwai hakkinta ta yafe musu ba za ta taɓa rike su ba saboda salim ya wuce wannan gaɓa a rayuwarta.”Ka ci sossai har da sauran kaso na, sai da safe”Tana kai nan ta kife wayar tare da kwanciya don da Talatuwa ta shigo ɗazu ta roƙe ta ta kawo mata ruwan dumi tayi alwala, da alwalar tayi ta sallolinta daga zauna saboda jiri da baya barin ta ta tashi.Ta ɓangaren Sameera wani tsanar Afeefar ya sake cika zuciyarta, tunanin matakin da za ta ɗauka a kanta take yi, ko ta je tayiwa Afeefar gargaɗi akan kula Dr ne? Wani zuciyar yace yanzu duk abin da fushi ya dibe ki kika yi mata tsautsayi ya faɗa kanki a bata da lafiyan nan ai kin kaɗe, gwara ta warke first a haka dai da nauyin zuciya ta kwanta tana ta juye-juye cike da haushi da tsanar Afeefah da tayi sanadiyar kasa baccinta a daren.Kaman yadda Dr. Sulaiman ya yi alƙawari bayan ya tashi aiki da safen wanka kawai yayi ko hutawa bai yi ba ya ɗauki Baaba jummai don yana so ta yini wa Afeefar kila jikin ya sake ƙarfi idan ta ga mutum kusa da ita, sam baya so abin da ya faru jiya ya faru yau hakan ma ya sa yayiwa Baaban umurnin shirya mata duk wani abu da ta san bakin marar lafiya zai so da basket mai girma suka nufi gidan, ba su wani nemi iso ba suka zagaya zuwa sashen Boys quaters ɗin ya bar Baaba ta soma shiga.Afeefar ta ji ƙarfin jikin nata sossai musamman da ta samu baccin dare mai nauyin gaske, ta samu ta lallaɓa ta watsa ruwa ta ɗan kimtsa ɗakin tana sanye da peach abaya ta ɗaura gyalen a kanta, ganin Baaba ya sa farin cikinta bayyanuwa ainun, Baaba ma tana murmushi take cewa “Ah jiki ya yi kyau Alhamdulillah””Sannu da zuwa Baaba””Sannu Afeefah, ya jikin dai? Kin ga kan gaisuwar nan bari na shigo da Alhj ƙarami ya miki alluranki yana sauri zai je ya kwanta idan ba haka ba yanzu za ki ga ya kama ciwon kai da baya ƙarewa ta daaɗi”Afeefah murmushi kawai tayi Baaba ta fice seconds kaɗan sai ga su, Afeefar ta warware gyalen ta ta yafa bisa kanta, babu hula a kan hakan ya sa tsantsin gashinta ke ta zamar da gyalen tana gyarawa, gaishe shi ta shiga yi yana amsawa idanunshi na a kanta yana yaba yadda jikin ya fara kyau, Alluran ya haɗa yayi mata yau kam ma rakin ya fi na jiya, don akwai pcm kuma babu ruwan diluting hakan ya sa yayi mata a hankali yana yi mata sannu don zafin shi.Bai jima sossai ba ya tafi ya bar su da Baaba da ta zage ta ƙarasa gyaran ɗakin ya fita fess ta bata abinci tana ci suna ‘yar hira bayan ta gama ma ta miƙe kwance suna cigaba da hirarsu tun tana amsawa baaban har bacci yayi awon gaba da ita.Shi Sulaiman yana isa gida ya ga Abbanshi tsaye suna magana da mai gadi, idanunshi ya ɗan runtse gabanshi na ɗan faɗuwa yau dai Abba ya kama shi, bai so ya dawo ya haɗu da Abban ba Dukda Umma ta gayamishi Abban na son ganinshi ya dai san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki kuma shi kaman har yanzu bai shirya ba, haka dai ya sauƙa yana ɗan shafa kai ya matso su suka sake gaisawa da mai gadin a lokacin sun gama magana da Abban ya juya ya wuce.”Za ka shafa kai ai Sulaiman, wai Hausawa suka ce in kere na yawo zabo na yawo watarana dole a haɗu””Barka da safiya Abba”Yayi gaisuwan a kunyace yana yar dariyar maganan Abban.”Barka dai Sulaiman ya aikin?””Alhamdulillah Abba””Toh ina magananmu ta kwana? Ka dai san na gama ɗaga maka ƙafa ko? Na fa gaji da ciyar da tuzuru don ka fi ƙarfin gauro”Abban na murmushi ya ƙarasa magananSulaiman Dariya yayi yace “Soon Abba in shaa Allah””bari na gaji da Soon ɗin nan naka za ka sha mamaki, dama akwai yaran abokai da dangi da duk na yarda na kuma gamsu da nasaba da tarbiyar su sai dai ka ji an saka maka rana, kar ka ga ina murmushi Sulaiman wannan ne last chance ɗinka, wai kai ko kunya baka ji? Kannenka duk sun tara ‘ya’ya maza da mata kana zaune abin ka?”Har lokacin murmushi yake, ya matukar sanin mahaifinshi Alhj Abdulrasheed mutum ne mai saukin kai da sauƙin hali Dukda tarin kudin da Allah ya bashi, ɗan kasuwa ne da har yanzu bai daina nema ba daga shi har yaranshi suna da sauƙin hali da kyautata mu’amala da duk wanda hakan ya haɗa su.”In shaa Allahu Abba za ka ji alkhairi i promise””I hope so, yanzu kake dawowa daga aikin kenan?””A’a Abba, na dawo da wuri na ɗan je na duba wata patient ɗina ne a gida na ba ta medication””Toh yayi kyau, a je a huta Allah ya taimaka”Ya amsa da Ameen yana jera wa mahaifin nashi adu’ar ƙara girma da lafiya ya wuce ɗaki, haka kawai yake tsintar fuskar Afeefah a idanunshi idanunta, murmushinta da ma sassanyar muryarta na dawo mishi kaman a yanzu take yi mishi, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya…Kaman wasa fa sabo ya fara shiga tsakaninsu da Dr. Sulaiman kachokan yake bata dukkan kulawar shi ya kan zo kullum sau biyo har saida duka alluran ta suka ƙare, kuma bai taɓa shigowa hannu banza ba har ta kan rasa waye ya fi wani damuwa da ita tsakanin shi da saleem da bai taɓa hutawa da yi mata saƙo ba, ko da ta samu sauƙi ta komawa aikinta sai Sulaiman ya cigaba da ƙiran ta tun suna gaisawa kawai su yi sallama ya fara jan ta da hira da wasa.Yau tun safe jikinta ke a matuƙar mace, saƙon saleem ya shigar da ita rudani da damuwa marar misaltuwa Dukda ta tsammaci hakan sai dai ya daketa fiye da zato.Sallar asuba ta farka tana buɗe idanunta ta sauƙa tayi alwala ta zo ta gabatar da shafa’i da wutiri kan ta miƙa sallah, tana idarwa ta janyo wayan don karatu yadda ta saba sai ta ga pending message, buɗewa tayi ta ga ƙarfe 2 da ‘yan mintuna gabanta ne ya ɗan faɗi me yasa saleem zai mata saƙo tsakiyar dare? Composing kanta tayi ta buɗe tana karantawa hawaye na silalo mata “Afeefah na san a lokacin da za ki ga wannan duniyarki za ta sake shiga rudani fiye da yadda take ciki a yanzu, na san tsoro zai mamaye zuciyarki, na san za ki yi tunanin anya saleem na cikin hankalinshi kuwa ya turo wannan saƙo? Toh duk lafiya ta ƙalau kuma ina cikin hayyacina hasali ma tunani da matsuwar zuciya akan fallasa sirrin ta su suka hana ni bacci har kawo wannan lokaci, Afeefah na kasa hana zuciyata ƙaunarki… Zuciyata ta kamu da Soyayyar ki ba na wasa ba, wallahi Soyayyata a gareki gaskiya ce, kuma ta ginu ne daga tushen tausayi Afeefah ina ƙaunarki fiye da yadda zan furta miki”Kuka kawai ta fashe dashi tana haɗa kanta da gwiwa, wani sabon al’amari ne kuma ke shirin shigowa rayuwarta? A sadda take karanta sakon Saleem duk wani tsika na jikinta sai da ya tashi, zuciyarta kaman zai Faso kirjinta ya fito Dukda ta jima da tsammatar hakan sai dai bata kawo hakan kusa ba, ba tsoron ta soyayyar shi ba tsoronta danginshi ta ina za ta fara son saleem? Ta yaya?Ta san saleem duk inda mace take neman nagartaccen namiji ya kai har ma ya wuce abin tambayar mahaifiyarshi da ‘yan uwanshi za su karɓi uzurinshi? Ta Tabbatar muddin suka ji cewa salim na son ta zamanta a gidan ya zo ƙarshe kenan to in sun kore ta ina zata je? Ko da ta koshi da kukan ta fito ta ƙarewa gidan kallo sai taji ma har wacece ita da namiji kaman saleem zai so ta? Har wacece ita da za ta yi mafarkin rayuwa da saleem? Ai ko da girgiza kanya ta fi magarya zaƙi.Jiki a sabule ta gama dukkanin ayyukan ta, ko da ta dawo ɗakin ta sake samun sabon saƙon saleem.”Afeefah na san na saka ki a rudani sai dai nima na rasa mafita ne, wallahi ban san sadda soyayyar ki ta samu matsuguni haka a zuciyata ba, ba ni da iko da ita bare har in hana ta. Don Allah kar ki yi kuka kuma kar ki firgita idan ba kya so ba zan tilasta ki ba don wallahi na fi kaunar farin cikinki da nawa farin cikin, kar wannan dalili ya sa ki ja baya da ni kawai na sauƙe wani nauyi ne da nake jin ya zame min dole na sauƙe, ina sake sanar da ke cewa Na so ki jiya, na so ki yau, zan cigaba kuma da son ki har zuwa gobe sannan zan cigaba da son ki kowace rana”Numfashi mai nauyi ta sauƙe hannunta har rawa yake, hawaye kuwa ya fi pampo zuba a fuskanta, ita dai da bad luck aka halliceta mugun tabo da shaidar ta zai cigaba da bibiyar ta har abada, a yau anan ba wani ne ya mutu ba amma tambarinta shi ya ja mata tsanar da ba zai taɓa sanyawa mommy ta amince da ita a matsayin surka ba ko tana mutuwa tana farkawa kuwa.Bata san yadda yake ji a ranshi ba amma ta san abin da zai hana shi sukuni haka babba ne, ba za ta bari salim yayi kuka saboda ita ba don haka a hankali ta rubuta”Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi”Lumshe ido yayi daga ɓangaren shi, shi karan kanshi tsoron yake ji, amma ya zai yi? Kalamai ya cigaba da mata na kwantar da hankali gabaɗaya yinin, ganin ya damu sai ta danne nata damuwar ta nuna mishi bata da matsalar komai kuma a shirye take da duk abin da zai je ya dawo, ta san bata da wannan ƙwarin gwiwar amma da shi kila komai ya zo da sauƙi.Washegari da yamma tana zaune tana karatun alqur’ani kawai ta ga saƙon shi “Hey dear zan dawo gobe, me kike so na taho miki da shi?”Ta karanta text message ɗin ya fi sau uku zuciyarta haka kawai ya shiga bugawa amma ta dake ta rubuta “Ka fi kowa sanin abin da ya fi cacanta da ni, duk abin da ka kawo ba zan ƙi farin ciki ba”Murmushi mai kyau ya saki, yana Fatan kasantuwar alaƙarsu na har Abada yana fata da Adu’a akan muddin ya fito fili komai ya zo mishi da sauƙi don babu yadda ya iya da abin da zuciya take so.A Washegarin duk iyalan gidan suka shiga shirin tarbar breadwinner ɗin su, hidima kawai ake don a wannan karo ya ɗan jima bai zo ba, dab la’asar ta gama wanke-wanke tana shirin shiga wanka ta ji wayanta na ringing, ta san Sulaiman ne don shi kaɗai yake kiran ta sai kuma saleem da yake mata text message, dagawa tayi tare da sallama ta shiga gaishe shi, ya amsa cike da wasa kaman yadda yake mata tamkar ‘yar baby ya ɗauke ta.”Yau dai haka kawai na ji ina son ganinki har mafarkinki na yi fa da na yi baccin rana, zan tafi office da yamman nan idan kin ba ni dama in biyo in kalle ki ko kaɗan?”Ta ɗan sauke numfashi a ɓoye a hankali tace “Ni na isa hana ka?”Da ɗan murmushi yace “A’a ai na zaci za’a yi min rowan wannan beautiful and innocent face ɗin ne”Tace hmmm, wani zuciyar na ce mata kila fa shima in da ya san wacece ita ba zai raɓeta ba.”Sai ka zo, a gaisar min da Baaba please””Banda ummana?”Yayi maganan a hankali, tayi murmushi “har da ita fa Dr. Da ma kowa da kowa””Toh wa zan ce mata tana gaisheta?””Afeefah mana?”Ta faɗa tana ‘yar dariya murya a karye, shi ma murmushi kawai yayi ya yanke call ɗin.Wankanta ta shiga a gaban madubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, sossai ta ƙara ganin chanzawarta ba’a tsawo ba don dama chan ita ɗin doguwar mace ce, sai dai ta ɗan kara kauri saɓanin da da take lange-lange kuma fatar ta ya kara wani irin kyau da sheki, mutane dayawa su kan yabi kyaun fatarta musamman a zamanta da Aunty zee amma bata taɓa yarda fatar mai kyau bane kaman yanzu, ta buɗe sossai daga ƙasa sai dai saman babu wani auki tsarin jikin sai ya bata wannan figuren da ake cewa coca-cola, a sadda take Dutsen-wai bata taɓa kawo ko a mafarki za ta auru ba amma da ta dawo Anchau Dukda jita-jitar da ake yadawa a kanta hakan bai hana wasu tararta da sunan So ba amsar ta dai karatu ne a gabanta, ta kuma san ko ta amince da wuya ne a haifi da mai ido musamman ga ‘yan uwa da abokan arzikin wanda za ta amincewar, a yanzu kuwa da babu halin karatun muddin ta cigaba da zama a gidan tana jin za ta so matsawa wani environment ɗin inda za ta samu so a yadda take kuma a bata rayuwa ingantacciya, amma Saleem shi ne namijin da zuciyarta ta fara aminta dashi don ya yi mata abin da kuɗi ko godiya ba za su taɓa biyan shi ba.Tana wanka haka kawai tana hawaye, tana ji a ranta matuƙar komai ya bayyana kwaɓarsu za ta yi ruwa ba na wasa ba, kuma wa’adin zamanta a gidan ya ƙare, amma in ta saurari Sulaiman fa? Sulaiman bai san asalin ta ba, bai san tarihi da mugun tabon ta ba idan ya sani kila shi ma iyayenshi ba za su taɓa karɓar ta ba. Da wannan tunani da damuwar ta fito daga wankan.Man shafawar da Sulaiman ne ya kawo mata haɗe da wasu dogayen riguna inda yake ce mata babu abin da ke karbarta kaman dogayen riguna ko don bai taɓa ganinta da lace ko atampha bane amma tana matukar tafiya da tunanin shi in ta saka su shi ta shafa, ta ɗauki wani maroon Abaya da ya sake fito da kyaun skin ɗinta cikinsu ta saka, ta ɗan fesa turare tare da man leɓe kaɗan, mayafi ta yafa daidai Sulaiman na ƙara kiranta a kan ya zo.Shi kuwa Sulaiman a sadda ya gama shiryawa ya fito parlorn ya ci karo da mahaifiyarshi da ƙannenshi.”Sai ina Ya Sulaiman?”Ɗayar ta faɗa.”Ina ruwan ki? Sa ido….”Ya faɗa yana hararanta.Wacce suke tsananin kama da wacce suka yi maganan da farko tace “Sana’ar banza ba, ai yaya ka fita sabgar fa’iza ta cika saka ido. In zo in raka ka ne?””Kema bana so gulmatu”Dariya suka sheke da shi ganin yadda ya ke hararinsu. Tsaki ya ja “Umma na tafi””A gaishe min da surkar tawa”Narkewa yayi “umma wai har da ke a biye wa waennan yaran?”Ta Yi dariya tana cewa “Sai dai ka dawo”Ya fice abin shi a jikin mota ya tsaya yana kokarin shiga sai ga Fauza ta miƙa mishi wani leda wai in ji Umma ya kai mata, yayi murmushi ya karɓa kawai bai ce komai ba.Gidansu akwai sauƙin hali da haɗin kai shi ne babba, yana da imediate kanwa da tayi aure sai wani namiji kafin twins ɗin nan mata biyu, mahaifinshi fitaccen ɗan kasuwa ne inda mahaifiyarshi ke aiki da federal government, ba su taɓa raina talaka ko ya yake musamman Sulaiman da shi ko na kasa da shi ya kan girmama, babu mai cewa ga wani tambari nashi ko hali marar kyau Dukda kowani mutum tara yake bai cika goma ba.Sai da ya biya ya kara mata sayayya akan na Umma kaman koyaushe matukar zai je wurinta bai taɓa zuwa hannu banza ba ya nufi gidan, bayan yayi parking ya ƙira ta, Bata kai ga fitowa ba aka wangale Gate ɗin gidan Motar Ryan ta kutso kai ciki a hankali…


