Gargadar So Chapter 115 By M Shakur
Ammi tace “kin manta takura da cin mutunci da tijaran da ubanki yake miki akan rashin aure both acikin gida da kofar gida? Are you trying your go back to that life eh?” Hawwa tai shiru tana kallon Ammi tana share fuskanta hawaye sun kasa daina zuba, ran Ammi yabaci iya baci tace “you want to risk everything ki kara komawa gidan ubanki kiyi another 30yrs babu miji ko” Hawwa ta kalleta asanyaye Ammi tace “yesss! Bakida farin jinin maza kowa tsoronki yake sabida ke yar sanda ce this same hali da dabi’u dakikema Ibrahim yasa sauran maza sukaki aurenki, Hawwa kinaso ki kashe auren nan and live the rest of your life ba miji ko? Tayaya zaki dinga baccin dare? Ko maza zaki farabi kifara karuwanci?” Dasauri takalli Ammi, Ammi ranta yabaci yau ba boye boye tace “an gayamiki I don’t know your problem? Hawwa sabida ke wawiya ce kodan wannan matsalan bazakija bakinki kiyi shiru ba kin dauka zaki iya rayuwa babu d’a namiji ne?”Hawwa tai shiru sai goge fuska take, Ammi ta dafe kanta tai shiru, chan tace “Hawwa jikina yayi sanyi da lamarinki, wlh, wlh da banma kanwata alkawari zan rikeki ba da wlh yau na yafeki Hawwa duniya da lahira, Hawwa kowa dakike gani yanama Allah laifi, wasu shaye shaye, wasu gidan boka, wasu zina, wasu kisan kai, wasu ta’addanci, wasu kidnapping, my point is nobody is perfect! Yaron nan kalli gidan daya taso, kalli yanayin sa, shi kadai iyayensa suka haifa, Allah kadai yasan jarabawan rayuwa dasuka gani kafin su sameshi, yanda aka taso dake ba haka yataso ba, but yana sonki, yace zai chanza saiki jawosa jiki, da kulawa da kyautata ma juna harya chanza, change is not easy, it takes patient, but Hawwa kalli kalan halin dakikeyi, Hawwa zagi harda mari, harda mari Ya Allah!”Kai abun nama Ammi wani kalan ciwo da baxama ta iya bayani ba, she can’t believe Hawwa can do all this abubuwa to this poor boy, sabida taga yaron ajebota ne ko menene, dan talaka ai da yanzu an kirasu ance suzo su dauki gawanta dan wlh saiyaci uban ubanta ta mareshi, Ammi ta shiga share hawaye, noooo she can’t forgive Hawwa just yet, wlh bazata iya yafema yarinyar nan yanzu ba, amman tadaure tace “mahaifinshi na sonki but wlh yaji abinda kikema dansa ko yaji kinkaimai d’a kotu he will hate you for life Hawwa! Hawwa da kotu har gwara kisa mu iyaye mu karban miki saki ba kisa mutum a kotu ba! Duba da kalan gidansu, da mukamin Baban sa dayake dan siyasa kuma dan kasuwa!” Ammi tabuga kirjinta crying sosai tana kallon Hawwa tace “jinake kaman ni kikama abubuwan dakikama Khaleel Hawwa, it will take time kafin na yafe miki Hawwa, wlh kuwa I can’t forgive you just now sabida kin nunamin I’m not your mother and bankai mother awajen ki ba” kuka Hawwa keyi mai tsuma jiki Ammi ta fuzar da iska tace “jiya mijinki na asibiti tun safe baida lafiya!” Dasauri Hawwa takalli Ammi, Ammi tace “I am sure idan cancer bata kashesa ba kece babban cancer dazata kasheshi but ba komi kinma kanki, Alhamdulillah kin nemi saki kafin ki kashe dan mutane yarabu dake, anyways Babanki shine ke tareda mijinki a hospital tun jiya yauma sun koma sai anjima” Ammi ta sunkuci jakanta tai kofa dasauri Hawwa tarike Ammi tace “Ammi meya sami mijina eh Ammi”? fizge hannunta Ammi tayi azuciye tace “cikani kafin zuciya ta debeni namiki jina jina wlh shegiya mai kan kwakwa, yarinyar sai taurin kai kaman daga zamanin fir’auna tazo sakeni!” Ammi tamata tsawa dayasa Hawwa tasaketa da gudu Ammi tafice fuuuuu ranta abace.Kirjin Hawwa wani kalan bugawa yake Khaleel was sick? Har Baba natare dashi a asibiti? Innalillahi wani asibiti? Which hospital is he using? Tunanin hospital nasu yasa tafara hawa staircase taje sama dakinta tashiga ta kwabe hijabi ta wanke fuskanta tafito tashiga closet atampa tasaka diguwan riga tadauki veils da handbag kirjinta harwani bugawa yakeyi tana kiran sunayen Allah hankalinta yayi mummunan tashi no wonder jiya taga baya iyacin abinci sosai tadauka fadan dasukeyi.Fitowa tayi diguwan rigan yamata kyau tayi kofa tafice tawuce wajen mota tashiga taja tabar gidan.Khaleel na zaune cikin mota he’s very weak they just drop Baba agida suka dauko hanyar gidansu wayanshi ya shiga ringing ganin Mom ne saida yadanji wani iri he hopes batasan baida lafiya ba ahankali yace “Salman did you tell Mom banda lpy?” Dasauri yace “nooo” daukan wayan yayi kafin yayi magana Mom tace “My Baby na kana ina banganka both jiya da yau ba though jiya nasan bamanan muma where are you?” Ahankali yace “gani ahanya zan dawo gida”Dasauri Mom tace “tom idan kazo i want to see you be fast” murya cha. Kasa yace “okay” gıda suka shiga around 5 yana kallon motan da babu da yasan Hawwa batanan kenan wani kalan ijiyan zuciya yasauke aka budemai mota yafito yana tsayawa da kyau ganin Mom tsaye gaban study nata tana kallonshi wucewa yayi yashiga lift yayi sama yana ganinta yace “ina Noor?”Ahankali tace “tana tareda lesson tutor nata come” Mom takama hannunshi suka shiga office nata Khaleel yaga wani security wanda bai sani ba sanye da suit yadauke kai ya zauna Mom itama ta zauna kan kujeran dake facing nashi tace “Leely na I want to tell you something but inaso ka fahimce ni” tadan sauke ijiyan zuciya tace “dazaka auri Hawwa I forced Salman yagayamin everything he knows about Hawwa, and nima on my own nai finding info akanta cus I want to know wace zaka aura this is wat I always do nasan who is coming into my Son’s life” Khaleel yayi shiru yana kallon Mom yana hade fuska gani maganan is about Hawwa, yace “okay naji and? Why did you call me here Mom”? Dan ijiyan zuciya Mom ta sauke tace “2days ago ko 3days ne ma naga Hawwa tafita in the night sanye da uniform this guy is my private security agent, he works for me privately ganin is late I had to call him yabi Hawwa duk inda zata just for her safety, so yabita yakuma biyoku har kuka dawo gida so ni I forget to tell him he should discontinue the mission, so this is abinda yakawomin just now” Momy tadauki some pictures dake kan table nata that are close tamikama Khaleel ahankali ya karba yana kallo Baban Yasser yagani tsaye jikin motanshi da Hawwa ta dauka tafita dashi jiya ita Hawwa na cikin motan zaune, ga pictures din dahar glass na motan yarike yana leka Hawwa, numfashin Khaleel hargitsewa yashigayi yanabin hotunan yana dubawa one by one Mom cikeda makirci tace “I know very well ance mutumin chan tsohon saurayinta ne I know everything my question is what is she doing with him a Shari’a court? Although nasan ita yar sanda ne but metaje yi a shari’a court? Khaleel duk matan dazan auro maka suka shigo gidan nan basa kara fita saika sakesu to avoid sumaje su hada jiki da wasu mazan, is Hawwa cheating on you da aurent……..” “Mommmmmm!” Khaleel yayi ihu yana buga table na Mommy yanunata da yatsa yace “I know who my wife is! Don’t presume anything akan matana! My wife is special! My wife is a woman that guide her chastity! My wife is decent! She’s not a bad wild girls kalan wanda kike auromin! Hawwa can never do this! Idan ma sun hadu and so?” Yayi shiru cikin fushi yace “kada ki karasawa wani yabi matana ko abincika min mata I don’t appreciate that Mom! And I condemn such behavior! I trust my wife Mom okay!” Yayi maganan yana yaga hotunan ya watsar akasan wajen yawuce yafita daga office din Mom yawuce kasa numfashinsa baya fitowa da kyau yawuce flat dinsu dasauri……

