Novel Document

Wani Rabo Complete Hausa Novel

Description/Story:

Wani Rabo… Complete Hausa Novel Document Written By Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)

Description

PROLOGUE
Fadin irin halinda nake ciki abune mai matuqar wahala domin dimauta damuwa qunci da baqinciki wasu yanayi ne wainda nake ciki a daidai wannan lokaci duhu kadai nake gani yayinda na rigada na sare da tunani ko fata a rayuwa
In zaka tambayeni tunanin me nakeyi toh ko tantama bazan iya gaya maka ba gayawa kaina nake yi bazanyi kuka ba saidai a hankali naji duk wani kwarin gwuiwa da nake dashi yana guduwa hayyacina kam ya dade da qaura daga gareni

Wani irin daci nakeji a harshena yadda kasan nasha madaci na daure iya daurewa amma naji kamar hakan ya na so yafi qarfina waishin anya ina da rabon farin ciki kuwa? Anya Ina cikin mutane masu saar farinciki kuwa which is very unlike me tunda nake ban taba loosing hope ba amma a wannan lokacin na tabbatar banda wani hope da ya rage gareni qirjina na dafe jin zuciya tana shirin tsaqa kirjina ta dako tsalle ta fito
Dukda wannan bashine karo na farko ba amma wannan din yafi na baya zafi da ciwo gareni na rasa me yasa haka din tambayar kaina nayi ” u never saw it coming right? Toh dama me kike expecting bayan wannan meyasa baki shiryawa wannan ranar ba humm lallai FAHEEMAH kar ki zama me manta baya mana ………ko kin shiga sahun mata masu saurin mantuwa ne…?”

“Hajiya hajiya ina zamuje ne ?” Tambayar da ta katse mun dunqulallen tunanin da nake kenan ajiyar zuciya na sauke tareda kallon mai maganar drivern napep din da ya dauko ni ne a hankali nace “hayin banki zaka kaini malam ” wani kallon wulaqanci yayi min tareda jan wani fusataccen tsaki ” haba hajiya ya zaayi ki dauko mutum tun dazu muke ta yawace gari baki sanarmin da kinda zan kaiki ba sai yanzu kice mun wani hayin banki ” ya qarashe maganar da tsaki
Batason doguwar magana ko wani abu dan haka tace “malam kayi haquri dan allah ” a masife ya tare min numfashi “babu wani hakuri da zaki bani malama wlh bazaa cuce ni sannan ace inyi hakuri ba ehee dan haka zaki biya 1500 kudin man da na qona a banza sannan kuma 1000 na tafiyar da mukayi da wanda zan kaiki gida”
Kallonshi nayi cikeda mamaki domin abinda yake tambaya baiyi kamada hankali ba kallon banza ya watsamin tareda cewa “idan bai miki ba ki bada dubu biyu saiki nemi wani keken ki koma gida ” kallon inda muke nayi kirjina yana bugu can kasan kigo road ne daga wurin zuwa main road ba qaramin tafiya bane ni bansan ma mai yasa muka biyo tanan ba
A halin da nake ciki ban buk’atar k’arin damuwa dan haka nace mai “muje malam Allah ya tsare ” jan kekenshi yayi ya nufi hanyar titi dani mundan jima kafin muka hau kan titin sai a lokacin ne hankalina ya dan kwanta U-turn yayi ya dauki hanyar da zata sada mu da kawo har muka iso baka jin sautin komai sai na ababen hawa da kuma masu tallah da conductors suna neman fasinjoji har kofar zahra clinic dake bayan gidanmu ya saukeni biyanshi abinda ya nema nayi sannan na nufi kofar gidan namu
Koda na isa a wangale naga gate din abin ya bani mamaki matuqa musamman da naga motar mamie a parke a gefe ga kuma wata murya tana tasowa daga parlorn mu a guje na qarasa sakamakon sheda muryan da nayi Areepah ce take magana amma kuma bansan da wa takeyi ba ina murda handle na jiyo tana cewa
“……..In dai babu abinda kike boyewa toh kiyi magana ki bude baki kiyi magana wai halin da muka shiga a baya bai isheki kiyi magana bane sai kinga mun fadi munbar miki duniyar tukunna ? In dai bakiyi magana ba toh hakan na nufin abinda mutane suke fadi gaskiya ne so u left us with no choice than to believe what the society are saying about you……….” A firgice na shigo parlorn sakamakon gane da wanda take magana da nayi
Bansan sanda na tsinke ta da mari ba “bakida hankali ashe Mamie’n ne kikewa irin wannan maganar ina hankalin ki ya tafi ne areepah sai me in abunda mutane suke fadi gaskiya ne me hakan ya rage mu dashi kinsan balain da kalamanki zasu haifar kuwa innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya Allah ka tausaya min wannan abin yafi qarfin zuciyata da kwakalwata……………” Taga taga nayi zan fadi fadeel da yake shigowa ya tareni daga nan kuma komai ya dauke min diffff ………..

CHAPTER ONE ( The day)

A cikin ranaku masu muhimmanci a rayuwar dan adam babu rana kamar ranar auren sa , Ranar aure rana ce da babu tamkar ta a tarihin rayuwar halitta, akan yi mata lak’ani da rana d’aya tamkar ya dubu Rana ce mai dauke da dunk’ulallen farin ciki da annasuwa mara misaltawa
Nima a gareni hakan take wani yanayi nake ciki mai tattare da farinciki da nishad’i musamman idan na juya na kalli friends dina a zagaye dani sanye da atamfa wacce sukai ankon ta wai fa duk sun taru ne domin ni, domin su tayani murna da fatan alkhairi murmushi na sauke ina mai kallon bestie wacce ita ma kallo na take yi murmushi tayi min sannan ta furta “Masha Allah”
Sanye nake cikin wata Emerald colored bridal gown wacce aka tanade ta domin ranar nan fuskata dauke da wani kwalliya wanda wata kwararriyar make up artist tayi min ga wani annuri da yake fita daga fuskata hannaye na dauke da wani hadadden lalle da zubona ‘yan hannu da wristwatch da ya k’ara k’awata hannun kafata kuma sanye da wani takalmi wacce muka yo ordern shi daga dubai tare da clutch din kana gani na ka ga amarya kuma yar gata wacce aka dade ana jiran zuwar ranar aurenta
Dukda tsantsan farinciki da nake ciki hakan bai hana ni jin wani bahagon yanayi yana lullub’e ni ba wani irin bugu naji kirjina yana yi dafe kirjin nayi sannan na kishingida kadan ina maimaita “la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimiin” babu adadi yi nake ina maimaitawa har na dan ji saukin yanayin da nake ciki duk da dai bai tafi gabadaya ba amma da sauki
Areefah ce ta shigo dakin da karadin ta tsayawa tayi a kaina a daidai lokacin da tayi arba dani “wow Addah amarya fatabarakallah Masha Allah na rasa mai zance wannan haduwa haka , abeg tashi zaune in miki pics kafin angon nan ya ga wannan haduwar ” hararar ta nayi jin ko miyau bata bari ta hadiye take ta zuba haka
Turo baki tayi ” please Addah ki zauna ” d’an muskutawa nayi na zauna tareda jingina da Allon gadon da muke zazzaune nan kowa ya fara ciro wayarshi zai dauke ni hotuna aka fara yi kujera na koma na zauna ana cigaba da daukan hotuna karar wayata dake hannun Areefah ne ya katse hoton da ake yi
Rufe baki tayi tareda cewa “laaa na manta fa tun dazu uncle Masud yake ta kiranki fa wlh shi ne ma ya aiko wai in kawo miki wayar ” gabadaya yan matan suka hada baki wurin cewa “Awnnnn see love!!” Niko hararar areepha nayi tareda cewa “silly girl amma kin shigo baki fada min ba sai shiririta kika tsaya yi ” rufe baki tayi tana shirin dariya na jin abinda na fada “sorry Addah na manta ne wallahi ”
Wayar na amsa tana shirin katsewa cikin siririyar murya nace ” Assalamu alaika angon FAHEEMAH gwarzon jarimi basarake ” shewa suka kara saki yayinda Areepha da Noosrah suka turo kunnuwan su dan jin mai zai ce wata murya mai cike da damuwa ce ta amsa sallamar “I’m Sorry FAHEEMAH I’m really sorry ki gafarce ni wlh an fi karfina ne there’s nothing I can do about it forgive me please….”
Miyau na hadiye sannan nace “wai me yake faruwa Mas’ud kayi min maganar da zan fahimta mana what’s all this? ” ajiyar zuciya ya sauke kafin yace ” I’m not getting married to u !! I’m not marrying gabadaya! ba yin kaina bane karfi na aka fi but wallahi I love you !! I really do,ki yafe ni FAHEEMAH” kallon Noosrah nayi inajin wani hawaye yana fara taruwa a idanuwa na a hankali cike da dauriya na ce “OK Allah ya bawa kowa RABONshi mafi alkhairi Nagode ” tareda katse kiran gabadaya
Noosrah ce ta girgiza min kai ganin Ina shirin fashewa kallon mutanen dakin wainda suke bina da kallon son sanin me yake faruwa nayi rik’e hannuna Noosrah tayi tareda dagani mikewa nayi cikeda sanyin jiki fita mukayi izuwa parlor inda abokan arziki suke zaune suna ganin mu suka Sakin gud’a “Masha Allah……. ga amarya…….amarya an sha kyau………Allah ya sa gidan zamanki ne …….Allah ya bada zaman lafiya……. ” maganganun da yake fitowa daga bakunan su kenan wanda suke sawa hawaye na kara zubowa
Da’kin ba’ki dake tsakar gidan muka nufa ba kowa a ciki sai katifa sai kuma doguwar kujera a share yake a gyare saboda biki kan katifar na kwanta tareda sakin kukan da nake bukatar yi kukan nakeyi kamar rai na zai fice daga jikina ji nake kamar karshen duniyar kenan shikenan kuma tawa ta kare kila ma mutuwa zanyi Noosrah ce ta riqoni ta na lallashi rungume ta nayi na sa wani kukan itama rungume ni tayi muka dukufa kukan
“Wannan wani irin sakarci ne ke kunzo kun dukufa kuka ke da ya kamata ki rarrashe ta amma kin sata a gaba har da tayata ” Ammi ce ta fada tana mai shigowa dakin da muke bamu saurare ta ba muka cigaba da kukan gwara Noosrah ma ta dan rage nata niko wani sautin na k’ara janye ta Ammi tayi sannan ta rungume ni a jikinta tana mai rarrashi na akan k’addara tace ” haba daughter kuka ba shi zai yi maganin matsalar nan ba kedin ba matar Masud bace rabon ki yana gaba addua ya kamata kiyi akan Allah ya kawo miki naki RABON nan kusa kuma yasa shine alkhairin ki, take heart dear ”
Ta cigaba da rarrashi na tana kawo min misalai na rayuwa tun Ina kukan har ya dauk’e sai ajiyar zuciya kawai nake yi Areefah ce ta shigo da kaya a hannunta ammi ce tace in cire kayan jikina in chanja body con ce baka karba nayi nasa sannan tasa wipes ta goge min fuskata da ta cude nan mascara can lipstick tas ta goge sannan ta umurce ni inje in wanke fuskar toilet din dakin na shiga na wanko fuska na sannan na dawo dakin
wani zazzabi ne ya fara rufe ni nan na fara rawar sanyi fita Areefah tayi sai gasu da Anty Sa’adah abokiyar aikin Mamie dubani tayi sannan tayi min allura cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ni a wurin…………..

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button