Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 26 Complete Novel

 

🐅MATAR* *DAMISA🐅
(The Wife Of Tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma’u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّه الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ——-> 73 & 74 <——-

🗣️🗣️ Knocking Mommy take tana ambatar sunayensu amma shuru ko motsi babu,
“Junaid ko baka ɗakin ne..?
Ayushh kizo ki buɗe mana ina muku magana…”
Jin shurun yayi yawa yasa Mommy ta tura ɗakin tana faɗin ko ba mutane ne aciki….” kafin ta rufe baki idonta ya sauƙa akan Junaid da Ayush suna manne da juna ko motsi babu, hakan ma a ƙasin ɗakin ba’a kan gado ba.

“kutt wani irin iskanci ne haka ai ko baccin mutuwa kuke yaci ace kun ji ƙiran da nake muku,
wai ma abun nakun yakai hakane daman? ku rasa a yanda zaku kwanta sai a ƙasa?…”
Jin ko motsi basu yi ba, gaban Mommy ne ya yi wani irin bugawa a wahalce ta haɗiyi yawu tana zazzaro ido waje, ta nufi gurin su tana bubbugan bayan Ayush dake itace a saman Junaid! ganin bata motsa ba tasa hannu ta ɗago Ayush gani tayi wuyanta a karye ta faɗa jikin Mommy, a tsorace Mommy tace “Innalillahi nashiga uku, meya faru da ku?..”
Kwantar da Ayush gefe tayi tana ƙoƙarin cacumar Junaid shima jin jikinsa tayi ya sake,
a firgice Mommy taja da baya zuciyar ta na tafarfasa kasa cewa komai tayi tsabar yanda numfashin ta yake hargutsuwa sama-sama take jan numfashi, daƙer ta iya tashi ta nufi hanyar fita hajijiya na ɗibar ta, da gudu take sauƙa downstair har ƙafarta ya sulale ta faɗi tana gangarawa daga saman benin tana zuwa ƙarshe goshin ta ya bugu da ƙasin tiles a wannan lokacin ne Mommy tayi ƙara tana dafe da kayinta domin ba ƙaramin buguwa tayi ba har gurin sai da ya fashe,
duk da hakan bata yi ƙasa a gwiwa ba ta nufi ɗakinta tana ɗingishi alamun taji ciwo a ƙafar,
wayarta ta ɗauko a saman gado tana laluman number hospital cikin sa’a taci karo da shi ta yi dialing call cikin ƙanƙanin lokaci ta kara a kunne murya a disashe take faɗin “Ambulance! Am bu lance!!…” daƙer take fitar da numfashi, daga nan tasau wayar ƙasi ta dafe ƙirjinta ta kafa gwiwowin ta a ƙasi ta fashe da wani irin matsanancin kuka ga jini duk ya wanke mata fuska, goshinta ba ƙaramin buguwa tayi ba, gashi tana buƙatar taimakon gaggawa domin ciwonta ne yake shirin tashi..
tana cikin wannan halin taji yo jiniyar Ambulance har sun iso….

Wasu ma’aikata ne masu fararen kaya suka fito da gudu suka shige gidan,
fararen likitoci ne daka gansu kasan ba ƴan nan ƙasar bane,
bayan sun shige falo raba hanya sukayi wasu suka haura upstairs wasu kuma suka nufi ɗakin Mommy kamar wanda aka sanar musu a yanda majinyatan suke,
haka suka firfito dasu duk aka shigar dasu cikin motar,
direct hospital aka nufa dasu,
tin a cikin motar suka sanyawa Mommy Oxygen kafin ta fita hayyacin ta…

******

“Maimoon wai meya sameki ne kin shugo gida kina kuka kamar wata ƙaramar yarinya…”

“Ammy babu komai”
Mahaifiyar Maimoon ce ta zuba mata ido sannan tace “karya kike Maimuna, akwai abunda ke damunki kuma kike ɓoye mun, ban sanki da ƙarya ba”
tayi ajiyar zuciya sannan ta dafa Maimoon ta kuma cewa “i known because of Hasheem koh..?”

Juyowa Maimoon tayi tana kallon Mamanta ido yayi jawur tsabar kuka tace “Ammy mutuwa zanyi, rayuwata bata da wani amfani, Doctor Hasheem ya yaudareni……” ta fashe da matsanancin kuka.

Ammy ce ta jawo Maimoon jikinta tana rarrashin ta tareda faɗin “bazaki mutu ba ɗiyata,
nima na lura da yanayin Hasheem ba ƙira a waya sannan ya daɗe baizo gidan nan ba, Maimoon tinda har ya nuna miki haka wata ƙil yanzu baya sonki ne kawai ki rabu da shi….”

A razane Maimoon ta tashi daga kan Ammy ta miƙe tsaye tana faɗin
“what..? mekike faɗa ne haka? Ammy cewa fa kika yi na rabu da my Doctor, kenam duk tsawon shekara da shekarun da naɗau ina kiwon soyayyarsa ya tashi a banza? impossible i can’t leave him because he is my life and my spirit…” ta ƙarasa maganar tana kuka,

Ammy tana zaune a bakin gadon Maimoon ta zuba mata ido cike da mamakin yanda ɗiyarta ta saka soyayya a cikin zuciyarta har tana iƙirarin zata mutu,

“Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, Maimoon karfa ki manta ke fa malama ce kuma mahaddaciyar alqur’ani, kiyi imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, mutuwa ma takan iya raba ɗa da uwa ko uba, sannan ta raba masoya biyu kuma ba yanda kika iya, meyasa da iliminki kuma kin sani amma kike so ki taɓe…”
ajiyar zuciya Ammy taja sannan ta miƙe ta nufi gurin da Maimoon take tsaye ta kamo hannayenta biyu ta kuma cewa “ƴata kuma Aminiyata kinaso kiga hawaye a idon Mahaifiyarki? nasan duk duniyan nan ba wanda kike so fiye da ni da kuma Mahaifinki kada kice zaki nuna mun kinfi son saurayi fiye da iyayenki..”

Jikin Maimoon ne yayi sanyi ganin hawaye kwance saman fuskar Ammy, da sauri ta kai hannu tana goge mata hawayen tace “Ammy ki daina kuka dan Allah zaki raunana mun zuciya..”
Ammy tace “toh kema ki daina shiga damuwa nima sai na daina kukan, rashin ganin walwalarki yakan jefa ni cikin matsala Bintu na.”
Maimoon rungumar Ammy tayi tana faɗin “shikenam Ammy nayi miki alƙawari bazan sake barin hawaye ya zuba mun ba indai a gabanki nake, sai dai idan na farin ciki ne..”

itama Ammy rungumar Maimoon tayi tana faɗin “shukran Bintu..”

******

*WASHE GARI*
Tinda Asuba Doctor Hasheem yake bubbuga ɗakin Laila amma taƙi buɗewa ba irin magiyar da baiyi mata ba har ya koma yana mata barazanar idan ya ɓalla ƙofar zai ɗauki mataki a kanta duk da hakan Laila bata zo ta buɗe ba,
har zuwa ƙarfe 11 na safe Hasheem ya kuma dawowa yana ƙoƙarin ɓalle ƙofar ɗakin amma ya kasa, shi tsoronsa kar yaje ta mutu domin jiya yayi mafarkin mutuwa,

“ke Laila ina miki magana bakya ji ko? dan Allah ki buɗe mana Autar mu bansanki da fushi ba, kuma na baki hakuri ai, insha Allahu bazan ƙara dukanki ba nayi miki alƙawari, wannan ma tsautsayi ne, in har baki buɗe ba yau ba zuwa hospital,”
shuru Laila taƙi buɗe wa….

tin jiya ta rufe kanta a ɗaki take ta sharar kuka,
abun ya bata mamaki “wai Bros ne zai mareta akan budurwa??”
tana jin kiran da yake mata amma ta share,
Laila tana da zuciyar masifa, sai ta iya kwana uku bata ci komai ba saboda zuciya irin tata, ita fushin ta ma yana shafar abincin da zata ci!
Dalilin da yasa Doctor Hasheem yake damuwa sosai akanta indai tayi fushi domin yasan halin ta, tin jiya bata ci komai ba kuma haka zata cigaba da fushi indai ba lallamanta akayi ba..

Doctor Hasheem yana zaune a falo yayi tagumi Laila ba ƙaramin ƙona masa rai tayi ba,
sallama yaji anyi ya ɗago da kansa yana faɗin “Haydar ka dawo ne..??”
“wallahi kuwa Bros mun kammala exam, amma Bros ya na ganka a gida baka je hospital ba?”
Ajiyar zuciya ya yi sannan yace “na rasa yanda zanyi da Laila, tin jiya ta kulle kanta a ɗaki har yanzu taƙi buɗe wa..”

“Amma Bros mekayi mata ne..?”
Haydar yayi tambayar yana kallon Bros ɗin shi..
Shafa fuskarsa yayi da hannayensa biyu yana hura iskar bakinsa yace “Laifi tayi mun na mareta…”

zaro ido Haydar yayi sannan ya miƙe tsaye yana faɗin “shikenam yau Abinci ya huta, daman ita take cinye mana abincin gidan!
yau kam abinci inci in ƙara inci in ƙara, yana magana yana haɗawa da rawa..

Daman Haydar da Laila basa jituwa kullum a cikin faɗa suke, daman fifikon wa da ƙanwa ne a tsakaninsu,
ya wuce kitchen ya ciko plate da abinci ya dawo falo ya zauna yana ci yana kallon plasman ana showing MAZA A YAU acikin shirin Arewa 24, sai da yaci iya cinsa tukun ya ture plate ɗin gefe bai iya cinye abincin ba,
duk abunda yake yi kuwa Doctor na kallonsa sai daga baya yace “Haydar ya za’ayi Laila ta fito ne ?”
Haydar yace “kaima Bros kasan halin ta, kawai shareta taga an damu da itane shiyasa..
Amma abu ɗaya zanyi mata ta fito”

Dr ya zabura yace “please Haydar ka taimaka kasa ta fito..”

Yace “toh shikenam ina zuwa”
Haydar ya tashi ya nufi wajen ɗakin Laila yana faɗin “Ah Oyoyo Oga Junaid your welcome, ya kwana biyu…..”
kafin ya ƙarasa maganar sai ga Laila ta fito da gudu tana washe baki tare da faɗin “yana ina?.”
Jin yanda Haydar ya kwashe da dariya yana nunata da yatsa tareda faɗin “ƴar wahala ta fito, so shame wallahi..” ya na cigaba da dariyar sa….

Ɗaure fuska tayi tana hararar sa taja dogon tsuka zata koma ciki Doctor yayi saurin tare ta….

******

Mommy ce take zaune a bakin gadon Ayush, kanta ɗaure da bandeji ita yau ta samu sauƙi domin ba ƙaramin kulawa tasha ba.
ita kuma Ayush tana kwance ido a rufe ita tanada sauran numfashin ta, daga suma ta wuce da yin bacci sakamakon allurai data sha ga kuma an ɗaura mata drink na ruwa,
sai ji kake tana ƙiran Yaya Junaid, tana motsa lips ɗinta a hankali “Yaya Junaid! kar ka mutu ka barni, nima zan bika mu tafi tare…”
Mommy ce ta kira sunan ta “Ayushert.”
a cikin baccin ta amsa da “na’am..”
Mommy ta kuma cewa “meya faru daku ne” still idon Ayush a rufe domin bata cikin hayyacinta tace “Abba na ne, Ab ba na, Abbana ya kashe shi kuma zamu tafi tare da Yaya Junaiddd…”

Mommy cikin rashin fahimta tace “wazai fahimci wannan maganar ki Ayush, ki buɗe baki kiyi mun bayani Dalla-dalla…” suna cikin wannan halin sai ga Doctor samuel ya shugo duba jikin Ayush yace “Doctor ki barta yanzu tunaninta yake fara dawo mata kwakwalwa, bata cikin hayyacinta zuwa anjuma kaɗan zata farka.” duk wannan maganganun daya yi su acikin harshen turanci ya yi…

Mommy tace “okay what about Junaid??”

Doctor Samuel yace “yes abunda nazo sanar miki kenam, munyi iya ƙoƙarin mu kuma ya farfaɗo,
sai dai kwakwalwarsa ta juye sai wani gwalatu yake tayi!.. but Hajia kamar dai ya haukace…”

Mommy a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin “what?? yarona ya rasa tunanin sa, taya hakan zai faru.” da gudu Mommy ta ratsa ta gefen Doctor ta fice, kai tsaye room ɗin Junaid ta nufa! tana shiga kuwa ta sameshi ya fisge jinin da ake ƙara masa ya zauna a tsakiyar gado ya naɗe sawayensa kamar mai cin tuwo yanata gwalatu kamar haka “ǧ’rēæñçüčæǰǰǰǰǰǰǰǰæ”rëžñœøœöøœæç…”
(Asmeetah ta baza kunnuwa domin taji meyake faɗi amma ta kasa 🤔🤔)

Subhanallahi Junaid fa ba mutuwa yayi ba haukatar da shi akayi,
Mommy ce ta nufi gurinsa da gudu tana faɗin “Nashiga uku Junaid ka haukace ne? ta ƙarisa tana kuka..

shi kuwa ganin tayo kansa yasa ya ƙanƙame jikin gini yana ihu, yana kukan jarirai tare da gwalatu wanda ba jin abunda yake faɗa ake ji ba,

Mommy tana rarumo shi, shi kuwa yana guduwa mata yana wannan kukan luɗa
“Innƴyaaa 😭! Innƴyaa😭!! Innƴyaaaa😭😭 !!!…
Duk wanda yaji wannan kalar kukan sai ayi tunanin haihuwa akayi a ɗakin saboda kuka tsakk irin ta jarirai yake yi..
bai daina kukan jarirai ba har saida Mommy ta tashi daga bakin gadon ta ɗan ja da baya tukun yayi shuru yana ajiyar zuciya irin yanda yara idan sunyi kuka suke ajiyar zuciya haka shima yayi ya ɗauki babbar yatsar sa ya zura a baki yana tsotsa, ga hawaye a saman fuskar sa sai tsotsar yatsa yake ta yi…

Kuka Mommy take sosai bazata iya ganin wannan takaici ba, haka yasa ta bar ɗakin da gudu tana kuka,

Oga Junaid dai haka ya zauna a cikin ɗakin yana tsotsar yatsa da zaran wani ya shugo ɗakin kuma sai ya fara kukan jariri,
cikin dare kuwa haka ya hana mutanen asibiti yin bacci ya damesu da kuka, da haka likitocin suke shiga suyi mata treatment amma abu ba sauƙi,
a cikin daren kuwa Ayush ta farka tana Kalle-kalle a hankali take motsawa ta tashi zaune daƙer, idon ta suka sauƙa akan Mommy tana kan sallaya ta ɗaga hannu sama tana ta Addu’o’i.
Kwatsam kunnuwanta suka jiyo mata kukan Jariri yana ta ihu, ɗaga kanta sama tayi tana kallon fanka dake juyawa iska ta ko ina ga na A.C haske ta ko ina amma a wannan lokacin ƙarfe 2 na dare ne…

jin kukan jaririn yayi yawa yasa ta sauƙar da ƙafarta ƙasi, tana tafiya a hankali ko takalmi babu a ƙafarta ta fice daga ɗakin,
ita kuwa Mommy bata sani ba.

tafiya take ita kaɗai tana bin yanda take jiyo kukan yaro,
ga gashin kanta a baje ya rufe mata gadon baya, itama kamar wata Aljana da blue riga a jikinta na asibiti zuwa gwiwar ta, sai ta tazo dab da ɗakin da take jin kukan tasa hannu zata buɗe taji a dafata ta baya har sai data tsorita ta waiwaya da sauri, wani Doctor ne wanda yake night duty ya kamo hannun ta yana faɗin “meya fidda ke a wannan daren, kije ki kwanta ki huta kinji ko..” ya kaita har ɗakinta, daiden lokacin Mommy ta idar da salla ita ma ta nufo gurin Ayush tana faɗin “Ayush ina kika je kuma? bansan kin farka a baccin ba ai” ta kamo hannun ta sannan ta zaunar da ita a kan gado…

Ayush ce ta buɗi baki tace “Mommy wacece ta haihu ina jin kukan jariri, kodai bashi da lafiya ne inaso inje na duba jaririn…”

Hawaye na gangaro wa Mommy tace “Ayush ki kwanta ki nutsu kinga baki da lafiya”
Ayush ce ta katse Mommy da cewa “Ina Yaya Junaid? ya mutu koh? daman na sani sun kashe shi, nima kuwa mutuwa zanyi…” ta fashe da matsanancin kuka,
Mommy ta jawo ta jikinta tana rarrashin ta, itadai Mommy Allah ne kaɗai yasan irin baƙin ciki dake zuciyarta…

*WASHE GARI*

wata mata ne take zaune da yaronta a kusa da room ɗin Junaid, kwatsam sai suka jiyo kukan jariri, daman ita awu tazo yi tanada tsohon ciki, yaron ta yace “mama an haifi jariri yana kuka a ɗakin can..”
ganin uwar bata kula shi ba yasa yaro ya nufi ɗakin yana zuwa ya buɗe ya shige ciki,
Yaro kam yaga Junaid a kan gado zaune sai kukan jaririn yake tayi, a tsorace yaro ya jefar da fidar hannunsa ya gudu yana faɗin “Mama ƙatoto ne yake kukan jariri, babba ne kuma yana kukan yaroro ƙarami…” uwar bata fahimci mai yaron yake cewa ba kawai ta fisgi hannun yaro suka tafi….

Doctor Hasheem ne ya shugo ɗakin Junaid ganin Junaid a wannan halin ya firgita shi,
daman kafin yazo an bashi labari! shine yanzun yazo ya tabbatar, gashi kuwa har yanzun bai daina kukan ba
Shi kuma Junaid ƙara volume kukan luɗan yake idan ya kalli Doctor Hasheem sai kuma ya kalli fidar da yaron nan ya jefar, Doctor Hasheem ne kawai ya fahimci kukan yunwa yake yi kuma bazai iya sauƙa daga kan gadon ba,

Hannu Doctor ya kai kan fidar dake yashe a ƙasi ya ɗauka gashi kuwa cike yake da madara, zuwa gabansa Doctor yayi sannan ya miƙa masa fidar..
Dariya Junaid ya farayi yana mimmiƙo hannayensa, yana ƙara irinta yara masu wasa ga kuma yawun da ke zuba a bakin sa irin mai yauƙin nan na yara, kafa baki yayi akan fidar yana zuƙan madarar cikin, ya rirriƙe da hannu biyu yana lumshe ido,
Doctor Hasheem ne ya taimaka masa ya kwantar da shi yana shan madarar fidar a kwance har bacci ya ɗauke shi…

Tsabar takaici da tausayi haka Doctor Hasheem ya fice daga ɗakin yana hawaye….

 

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

 

*MASHA ALLAH*

(Kuga fah jaririn aljani aka turowa Junaid😭😭🤣🤣🤣 )

 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

Back to top button