💛 HAJAR 💛
By Feenerh_feeche
{4…}
Biyar da rabi na yamma ya sayyadi Nura ya shigo ajin yi musu kiran suna, idonsa akan Hajar ya fara sauka wacca ta sunkuyar da kanta tana duba abinda babu a jaka, Addu’a ya fara yi musu kana ya fara kiran suna, duk wanda aka kira sunansa sai ya tashi ya tafi gida idan kuma kasan kayi fashi sai ka jira ai maka hukuncii, ajin ya ɗaɗe ya rage daga Hajar sai ya sayyadi Nura, register ya rufe ya maida hankalinsa gareta, a hankali yace “Hajara mai yasa jiya kika yi fashi”, Hajar ta haɗiyi wani yawu ba tare da ta kallesa ba tana wasa da hannunta cikin hijab tace “ya sayyadi online registration naje na NECO kuma ban dawo da wuri ba”, ya sauke ajiyar zuciya yace “toh saiki dage da karatu kinji??”, tace “Insha Allah”, yace “har yanzu dai Nursing ɗin kike son karanta”, a karo na farko da ta ɗago fararen idanunta sai kuma tayi sauri ta mayar dasu ƙasa tace “Eh”, yace “toh shknn, indai kin ɓaro marks Insha Allah zaki tafi Nursing School”, tace “insha Allah zanyi ƙoƙari”, ya ringa kallonta sai kuma ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yace “lokaci nake jira na nemi izini wajen Baba na ringa zuwa wajenki a gida, iya ganin da nake miki a makaranta yayimin kaɗan gaskiya, ace kullum idona baya ci ya ƙoshi”, ta janyo hijab ɗinta ta rufe fuska murya can ƙasan maƙoshi tace “ni gida zan tafi”, yayi murmushi mai sauti yace “toh taso ki tafi”, a hankali ta tashi ta ɗauki jakarta ta fita a ajin ba tare da ta bari ta kalli wajen da yake ba. a gate ta tarar da zainab da take jiranta suka rankaya suka tafi gida. da daddare Hajar na zaune akan tabarma tana cin tuwo, umma ta fito daga ɗaki da mafici a hannunta itama ta samu guri ta zauna tace “kai gaskiya yau akwai zafi inajin hadari ne a garin”, Hajar tace “ɗazu ma naga ana walƙiya, ina sabra ita bazata fito tasha iska ba sai sanƙarau ya kamata?”, umma tace “tayi bacci kinsan daga anyi sallar isha’i take kwanciya”. Maama tana daga can ƙofar ɗakinta tare da Maimuna wacca ta kawo mata ƙorafi akan Naseer. garin zafi ake shiyasa suka firfito tsakar gida shan iska, Hajar ta miƙe ta kai kwanon da ta gama cin abinci wajen wanke-wanke ta ɗebi ruwa tana wanke hannunta, Sallamar Baba ta janyo hankalin kowa garesa, Hajar tace “sannu da zuwa Baba”, ya amsa yana miƙa mata ɗaya daga cikin ledar da ya shigo dasu, Maimuna tana ganin ya miƙawa Hajar leda ta miƙe zaune daga kan cinyar Maama tace “Baba sannu da zuwa”, yace “yawwa zoki karɓar muku naku”, Maimuna ta taso da sauri ya bata leda ɗaya ya wuce ɗakinsa da guda tinda ledojin uku ne. Hajar ta kaiwa umma ledar ta samu guri ta zauna ta tanƙwashe ƙafa, Umma ta buɗe leda, karfashe ne mai zafi ga kuma yaji a gefe, umma tace “kai Allah ya saka da alkhairy ya ƙara buɗi, sako hannu muce Hajara”, a hankali Hajar take ƙurmushe karfashen saboda tana sonshi. Maimuna kam tana buɗe ledar ta kalli Maama tace “Chaɓ, daman tinda naji ƙarni nasan wannan abun ne”, Maama ta warce ledar tace “idan bazaki ci ba ki barshi” ta ɗauki guda ɗaya ta luƙa a baki ta ƙurmushe, Nabilah ta fito daga ɗaki da fitilar wayarta rakani toilet ta haska kifin hannun Maama tace “me kuke ci ne naji ƙayau ƙayau ana tauna?”, Maama tace “karfashe ne idan zaki ci, yanzu babanku ya shigo dashi”, Nabilah ta taɓe baki tace “ni kam bazan ci ya farfasan baki ba, kina ganin abu sai kace ƙanzo, Sa’adatu nake jira nasan bazata shigo gidan nan hannu rabbana ba”, Maimuna tace “wallahi nima ita nake jira”, Maimuna tana rufe baki saiga sallamar Sa’adatu, hannunta riƙi-riƙi da ledoji, da sauri Maimuna ta tarota ta amso ledojin, Sa’adatu ta zauna kan tabarma ta fige ɗankwalin kanta tace “wash nagaji, Maama yau kam ai banyi dare ba ko??”, Maama ta kawar da ledar karfashen da take ci ta suɗe hannu tace “Eh yau ba kiyi dare ba ƴar albarka”, Sa’adatu ta warce ledojin hannun Maimuna tace “cewa nayi ki buɗe, ai kya bari na buɗe da kaina”, Sa’adatu ta ciro takardar tsire da ƙatuwar robar ice cream tace “Maama ga naki”, ta ciro wata takardar da kuma robar ice cream ta miƙawa Nabilah tace “keda Maimu”. ta kwashi ragowar ledojin ta shiga ɗaki. hannu baka hannu kwarya sai kace mayatattu suke cin tsiren nan suna yaɓa ice cream a baki, Maama sai habaici take zubawa faɗi take “haihuwa tayi min rana, ina zaune akawomin tsire da ƙanƙara mai madara na more, wasu kam sunyi asara kullum saidai a kawo musu takarda ace anyi ƙoƙari a jarabawa”, Nabilah ta danna tsire a baki tace “yo daman shege yanada wani amfani ne, ai amfanin shege bai wuce baƙin fenti ba”. Hajar ta miƙe ta zazzagi omo ta wanke hannunta ta shiga ɗaki, muddin ta zauna a tsakar gidan nan to kwa tabbas za a iya tashin hankali domin kwa ba haƙuri ne da ita ba musamman ma aka taɓo mata uwa. Washe gari da wuri Hajar ta dawo daga school saboda ranar juma’a ce, umma ta tarar tayi shirin fita, Hajar ta ajiye jakarta tace “Umma fita zakiyi ne??”, Umma tace “ta dole ce Hajara, gidan Jamila zanje na duba jikin Hafsa, kar abin ya zama shiririta na shiga wata sabgar ban dubata ba”, Hajar tace “to bari nayi sauri na shirya saimu tafi tare”, Umma ta girgiza kai tace “da ke nayi niyyar zuwa amma hakan bazai yiwu ba, inada ragowar kulele da ban siyar ba wajen ta dubu, daman ranar juma’a sai bayan masallaci akafi ciniki, ga Sabra nan ta tayaki zama bazan daɗe ba Insha Allah”, Umma ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace “Hajara karki biyewa kowa ayi tashin hankali dake kinji”, Hajar ta jinjina kai tace “Allah ya tsare sai kin dawo..”. Hajar tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa roba-roba, ta dasa kujera a tsagar gida tana yankewa Sabra farce, Sabra ta zille ƙafa tace “dan Allah Adda karki yanke ni”, Hajar ta ɓalla mata harara ta fuzgo ƙafar tace “da can da nake yanke miki na taɓa yankar ki ne??”. wani yaro ne yayi sallama siyar kulele, Sabra taje ta amso kuɗin Hajar ta zuba masa a kwanon da ya kawo, Hajar ta shiga ɗaki ta ɗakko canji ta bata ta kai masa tare da kulelen, saida yaron ya tafi ta tina cewa bata zuba masa yaji ba, tasan aiken iliya mai awo ne tinda taga kwanonsa ne, indai shine sai ya dawo yace a zuba masa yaji, ta zauna ta ƙarasawa Sabra yankar farcenta, tana gama mata ta fita wasa ita kuma ta shiga bayi, tana toilet ta jiyo yaron ya dawo yanata ɓurari wai a zuba yaji a kulele. Sa’adatu ta fito tsakar gida da kayanta haɗin bauta, zani jaka a tsaye sai wata tsohuwar riga Tshirt duk ta jeme, gyatsine tayi ta mulmulo ashar tace “kai me za a baka kake mana ihu??”, yaron yace “yaji za’a zuba min a kulele”, Sa’adatu taja wani dogon tsaki tamkar tsohuwar tsaka tace “kawo na zuba maka”, ya miƙa mata kwanon, ta buɗe tana kallon kulelen da aka shanana masa manja gwanin sha’awa, ta taɓe baki ta tsugunna ta duntsi ƙasa cikin hannu ta barbaɗe kulelen da ita tas, ta rufe ta miƙa masa tace “jeka an zuba yajin”, yaro yayi kasaƙe yana kallonta da mamaki, taja tsaki ta fara kwashe kayan shanyarta akan igiya, Hajar ta fito daga bayi taga yaro tsaye da kwano a hannunsa tace “yaji za’a zuba ko??”, ya nuna Sa’adatu da hannu yace “waccan ce ta zuba ƙasa a ciki”, Hajar ta zaro ido waje tace “ƙasa?” ta karɓi kwanon ta buɗe, ai kam dai kulelen nan bazata ciyu ba saboda tasha ƙasa harda tsakuwa, wani ƙululu ne ya tsaya mata a maƙoshi gashi umma ta mata gargaɗi, dole ta hakura ta zubo masa wata sabuwar kulelen ta juye waccan, ta koma kan kujera ta cigaba da yanke farce, gani tai bazata iya yin shiru ba kawai anyiwa baabarta asara ta ɗari biyu, ta kalli Sa’adatu da take kwashe kaya jikin igiya tana bigesu saita linke ta ɗora a kai tace “Sama fanta ƙasa coca cola, fuska fara ƙafa baƙa”, Sa’adatu ta ƙyalƙyale da dariya amma a zuciyarta ji take kamar ana zuba mata dalma, Hajar kam kamar ta sani harma kamar waƙa take haka ta cigaba da cewa “Sama fanta ƙasa coca cola, fuska fara ƙafa baƙa”, Sa’adatu da haushi ya gama turnuƙeta gashi Hajar ko kallonta ba tay ballantana tace da ita take ta shiga ɗaki tamkar zata tashi sama.
★Zaune take cikin wani jugunannen palour wanda ya ƙure lambar haɗuwa, hannunta riƙe da wani tsadadden bowl tana shan fruit salad, damɓasheshiyar Tvn palour sai aikinta take, wata ƴar budurwa ce ta sakko daga kan stairs ɗin da ya kewaye makeken palour, ta zauna kan sofa tace “Mami yaya Nurain bai dawo ba har yanzu??”, Mami ta shanye fruit ɗin bakinta tace “Eh bai dawo ba”, Noor ta taƙune fuska ta kalli agogo sai kuma ta jingina da kujera ta fara latsa tsaleliyar wayarta, Mami ta kalleta tace “is there any problem dear??”, Noor ta ajiye wayar tace “No Mami”, Mami tace “ohk” ta cigaba da shan fruit salad ɗinta tana kallon Tv, few Minutes after that wani sassanyar ƙamshi ya fara karaɗe palourn da yake ƙamshin breath taking freshner, Noor ta kalli door jin ƙamshin na yayanta ne, ai kam dai shi ɗin ne, yayi sallama ya tako a hankali hannunsa riƙe da briefcase, Mami ta ajiye bowl ɗin hannunta a hannun kujera bayan ta amsa sallamarsa, a kan soft carpet ɗin dake malale a palourn ya zauna yace “Mami barka da gida”, Mami tayi murmushi tace “An dawo lafiya Nurain”, yace “lafiya alhmdllh” ya koma kan kujera ya zauna. Noor tace “yaya sannu da dawowa”, ya kalleta yace “yawwa Lil sis”, Mami tace “a kawo maka abinci ko sai anjima”, yace “amm yanzu zanci, Noor ta shirya min kafin na dawo”, ya ɗauki briefcase ɗinsa yabi stairs, saida yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya ƴan ubansu sannan ya sakko down stairs, already Noor ta gama shirya masa lunch, zama yayi yana ci peacefully, Mami tace “yauma kayi surgery ne Nurain??”, ya ajiye spoon ɗin hannusa yace “yeah Mami, amma banje hospital da nufin yin surgery ba, wata patient aka kawo emergency tana buƙatar aiki in not less than 24hours, a rayuwar nan ta yanzu nothing goes without money, gashi asibiti sun buƙaci su kawo kuɗi mai yawa kuma basu da hali ga surgeon ɗin da zaiyi aikin yace sai an biya sa, ni kuma naga aikin is inside my field shine nayi surgeryn free”, Mami ta jinjina kai tace “Allah ya saka maka da alkhairy, i know baka zama likita saboda neman kuɗi ba sai don temakon al’umma”. yace “Mami akwai rashin temako a ƙasar mu sosai, masu temako basu da yawa”. Mami tace “idan ka temaki wani Allah zai temake ka, Nurain Allah kaima ya dafa ma cikin lammuranka”, yace “Ameen”. glass cup ya ɗauka da lemon kwali, har zai buɗe lemon sai kuma ya fasa ya kalli Noor yace “plxx change it with chivita orange”, ta miƙe ta amsa ta shiga kitchen ta buɗe damfareren fridge ta ɗakko masa chivita orange, ta dawo ta ajiye masa a gabansa sai kuma ta tsaya tana kallon rigar jikinsa fara tass, tsuke ido tayi tana nuna rigar tace “yaya wai rigar nan ta rannan da ka shafo taɓo ajiki yauma itace ka saka??”, Nurain ya kalli rigar jikinsa yace “hey get out” ya saita mata hanya……..✍️
Download Hajar Hausa Novel Document By Nafeesa Yusuf Nagoda
Click the below green button to read the novel online
READ HAJAR PAGE 5 COMPLETE NOVEL
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.