Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 23 Complete Novel

*ASM Bk2023*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………bin Kawu Amadu kawai take da ido da alama tayi mutuwar zaune abun kaman a mafarki take jin shi wai ita za’a ma Aure kuma ma a garinsu, shima Kawu Amadun zugudum yay yana kallonta can ta yunk’ura da k’yar ta mik’e hannunta ruk’e da jakarta ta fita daga d’akin ta nufi d’akinta har wani Jiri Jiri take ji a haka ta isa tana shiga ta aje jakarta a gefe ta nufi bakin gado ta zauna sai zare ido take sam tama rasa tunanin da zata yi can zuciyarta ta fara tunano mata da Mutumin wato wanda ta iske a fadar Ard’o har ya rink’a mata tambayoyi da turanci ashe da biyu yayi mata hakan kenan,wai d’anshi Dr Khalid za’a aura mata! haka ta dingi maimaita sunan a cikin ranta tana haka wayarta dake cikin jakar islamiyya ta fara ringing da k’yar ta yunk’ura ta nufi jakar ta fiddo wayar kafin ta koma bakin gadon sai lokacin ta kalli screen d’in taga mai kiran nata, My Lovely Dad shine sunan da ta gani wato Baffan ta ne kenan, d’an jimm tayi cike da fargaba kafin hannu na rawa ta d’aga kiran ta kara a kunne kafin tayi Magana daga can yace “Inna wuro” har saida gabanta ya d’an fad’i kafin a hankali tace “ah Baffa”,
“Kin dawo daga Makarantar kenan Amadu ya fad’a man kina can” wani abu ta had’iya jin muryar shi ta canza sosae a hankali tace mashi eh ta dawo ta gaida shi ya amsa, shiru ya biyo baya daga ji yana son mata magana ne amman ya kasa, can tay k’arfin halin cewa “Baffa wai da gaske an bada ni za’a man Aure?” D’an jimm yay kafin ya fara Magana “Wallahi tallahi inna wuro wannan duk aikin Ard’o ne ni sam bansan da Maganar wai ya bada ki ba sai wata guda da ya wuce lokacin kuna cikin yin jarabawa shine ya kira ni yake sanar dani wai in fad’a maku ya bada ke ga yaron chairman kuma ya sanar mashi kun kusa k’are karatun naki don haka kuna gamawa in zo in d’aukko ki, Wllh inna wuro ranar banyi bacci ba Saboda tashin hankali ban k’ara shiga damuwa ba sai bayan da kuka gaman ya kira ni yace ai Chairman ya fad’a mashi kun k’are don haka in zo in d’aukko ki ranar gwuiwa na a k’asa na rokeshi da a kyale ki karatu kike son yi in kika yi za’a amfana sosae amman da bud’ar bakin shi sai cewa yay ina kokarin nuna mashi iko da ke abunda wani bai ta6a yi mashi ba, duk yadda na so in fahimtar dashi abun ya gagara don ce man yay ba don Alhaji Lawal d’in ya ce a barki ki k’are karatun ba ai da tun lokacin da ya nuna yana son a bawa yaron nashi za’ai maku auren yanzu kuma ba abunda zai fasu don har sadaki ya amsa yana wurin shi, tun ranar inna wuro banda cikakkar lpy wllh nasan kina son karatu sosae kuma muma duk muna so hakan yasa na kasa ma kira in sanar daku don wannan Auren dole ne…..” D’an dakatawa yay yana maida numfashi dama tunda suka fara Magana ta fahimci canji a muryarshi, ci gaba da magana yay “bayan sati guda da yay man Magana ya ga ban zo na taho dake d’in ba shine ya tara yan gidan yana masu kukan na nuna mashi iko da d’iyata ina son bashi kunya to kowa ya shaida in dae na hana Auren bashi ba ni, nan abun ya zama abun Magana gaba d’aya aka tsangwame mu ni da iyali na ana ta maganganu dama suna jin haushi yadda Ardon ke d’aura ni akan komae nashi nan aka samu wasu suka zugeshi yace bai son in k’ara sa mashi hannu a
harkokin shi, jiya naga tashin hankali inna wuro cewa yay in tattara in bar masa gida ya yafe ni kuma in har ban bari anyi auren ba Allah ya isan shi bai yafe man ba……” Karyewa muryarshi tay ya fashe da kuka, wani irin zaro ido Fatuu tay jin Mahaifin nata na kuka abunda bata ta6a gani ba ko ji da Hankalinta da sauri cikin rawar murya tace “Baffana kuka kake!!” Had’iye kukan yay yace “inna wuro har ga Allah ban son abun nan ban so wllh na fi so kiyi karatun ki zai amfanemu gaba d’aya in kika gama ko kuma kina cikin yi Allah yasa kina da wanda kike so ku ka daidaita sai ki yi auren ki amman ba ai maki dole ba, yanzu bansan ya zanyi ba” sosae jikin Fatuu yay wani irin mugun sanyi wani irin tausayin Mahaifin nata ne ya kamata lokaci guda taji ranta ya 6aci da abunda ake masa wani irin kwarin gwiwa ta ji ta samu tace “Baffana ka daina damuwa na yarda ayi man auren kazo ka d’auke ni!” murya na rawa yace “Inna wuro kin yarda kenan kin hak’ura da karatun?”d’an murmushin takaici tay kafin tace “Eh Baffa in dae hakan zai fitar da kai cikin halin da kake ciki to na hak’ura in Allah ya sa ina da rabo ko ba yanzu ba zanyi in kuma bani da rabon yi ko ba ai man auren ba bazan yi ba” sosae ya shiga yi mata godiya yana fad’in “Nagode, Nagode inna wuro yadda kika sadaukar da farin cikin ki Saboda nawa farincikin in sha Allahu ko ba yanzu ba kema zaki dawwama cikin farin ciki har k’arshen rayuwarki, Nagode Allah ya jik’an Mahaifiyar ki dama Aysha Alkhairi ce a gurina gashi nan har bayan ranta ina ganin Alkhairin ta…” Shesshekar kukan shi kawae take ji hakan yasa itama kwalla suka zubo mata sharrr saidae bata bari kukan yayi sauti ba don kar ya ji cikin breaking voice tace mashi don Allah ya daina kuka bata jin dad’in hakan da sauri yace to ya bari, can taji yace “yanzu ita gwaggon ki fa naga ta d’auki zafi da Maganar sosae” damm gaban Fatuu ya fad’i tunowa da yanayin da ta riski gwaggo tabbas ba k’aramin 6aci ran ta yay ba sai kuma ta ayyana k’ilan in ta nuna ta amince zata saukko hakan yasa tace mashi kar ya damu zata fad’i mata ta amince tasan zata saukko, sosae ya shiga yi mata godiya yana saka mata Albarka da harshen fulatanci tana Amsawa kafin ta tambaye shi yaushe zai zo d’aukan ta d’in yace zai sanar da ita ta fara shiri dae sannan zai tura na Amadu kud’i in akwae abunda zata siya na amfanin kitchen tunda yaga a birni jere ake mashi ta amsa mashi da to kafin suka yi sallama, k’ura ma wayar ido tay bayan ta cire ta daga kunnanta sai lokacin kuma ta fara tunanin anya bata yi gangancin saurin Amincewa ba kuwa, tasan waye za’a aura mata? tsuru tay tana ta faman zare idanu can kuma ta yanke koma waye zata aureshi ko don ta fitar da Mahaifinta daga halin da yake ciki don tasan dama can ana bak’in cikin yadda Ardo yafi ji dashi yanzu in ta k’iya sun samu abun da suke so, shiru tay tana tunanin yadda zata tunkaro gwaggo don wata irin shakkarta ce ta kamata can ta yanke bari ta bari sai Anjima lokacin tasan ta d’an huce, tana haka aka fara kiran sallar Azahar ta mik’e don yin salla lokacin data fito suka yi kacibus da gwaggon ta yo Alwala zata koma d’aki fuskarta sam ba walwala ko kallon Fatun bata yi ba ta wuce d’aki hakan ba k’aramin k’ara ma jikin Fatuu sanyi Yay ba, bayan ta gama sallar zaune tay a d’aki tana ta sak’e sak’e a ranta gaba d’aya gidan yayi tsit kai kace sakon Mutuwa aka fad’a masu kowa yana d’aki ko Abinci ba wanda ya nema kuma tuni gwaggon ta gama don lokacin data gama tana kitchen ne Amadu ya kai mata wayar, mik’ewa Fatuu tay ta fito ta nufi kicin ta zubo ma Kawu Amadu da shima tunda ya dawo daga Masallaci yana d’aki, lokacin da ta shiga ya d’an kishingida kan Katifar shi da alama tunani yake jin sallamar Fatun yasa shi kai idanunshi kopar shigowar, a bakin katifar ta aje plate d’in Abincin da d’an murmushi tace “Kawu Amadu ga Abincin ka” tashi yay zaune yana mata kallon mamaki ganin ta ba wata damuwa sosae a tattare da ita don ya d’auka zuwa yanzu tana can tasha uban kuka koma tana cikin yi, ganin kallon da yake Matan ne yasa tace “Baffa na ya kira ni yayi man bayanin komae kuma nace mashi na amince da auren” bud’a ido Amadu yay yana kallonta wit surprise written boldly all over his face don bai ta6a tunanin hakan ba ta cikin sauki surprisingly yace “yanzu kenan kin yadda ayi maki auren kin hak’ura da karatun?” D’an guntun murmushin takaici tay kafin cikin karewar murya tace “to Kawu Amadu ya zanyi Baffana na cikin matsala kuma zai k’ara shiga wata in har ban Amince ba don Ard’o yace ya bar mashi gida in dae bai zo ya d’aukko ni an Mani auren ba kuma wai bai yafe mashi ba….” Sai lokacin tasa kuka ba k’aramin sanyi jikin Amadu yay ba dama yasan ba yadda za’ai Baffanta ya goyi bayan hakan cikin sauk’i don kuwa duk Abunda Fatun ke so shima shi yake so, rarrashinta ya shiga yi yace ta daina kukan, sam bai son Al’amarin don bai dace ayi mata hakan ba ba kamar da Kamalu yayi mashi bayanin wanda za’a aura Matan d’azun da ya kira shi don jin Karin bayani, sauke nannauyar ajiyar zuciya yay kafin yace mata Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi tace Amin, tambayarta yay ita ta ci Abincin tace a’a yace to suci tare, bayan sun gama yace ta k’aro masu farko tace ta k’oshi yace bai yarda ba dole ta k’aro suka ci bayan sun gama ta d’auke plate d’in ta maida kitchen har zata shiga d’akinta ta dakata tana kallon kopar d’akin gwaggo a ranta tana tunanin anya ma gwaggon ta ci Abincin don bata ga alamun ta d’iba ba can ta juya ta koma kicin d’in ta zubo mata ta nufi d’akinta lokacin data shiga tana zaune kan dardumar salla da alamu tunda ta gama sallar bata mik’e ba, amsa sallamar da Fatun tay ba tare data kalleta ba ta nufi gefenta ta duk’a ta aje plate d’in Abincin a sanyaye tace “Gwaggo ga Abinci ki ci” jimm tay kafin ta juyo ta kalleta har saida gaban Fatun ya d’an fad’i ganin yadda idanunta suka sauya kaman itama kuka tayi, ganin yadda fatun ke kallonta yasa ta d’an k’ak’alo murmushin yak’e tace mata ta gode Fatun ta mik’e ta bita da kallo har ta fita wani irin tausayin yarinyar ne ya kamata don duk a tunanninta Fatun bata san abunda ke faruwa ba, k’ara dawowa tayi ta kawo mata ruwa ganin bata ko ta6a Abincin ba yasa a marairaice tace “Don Allah gwaggo ki ci” fuskarta a sake ta d’aga mata kai alamar to, har ta juya taji tana tambayarta ita taci Abincin ne tace mata eh sun ci da Kawu Amadu kai ta k’ara d’aga mata Fatun ta fita ta koma d’aki ta zauna a bakin gado tana wasi wasin ko in ta gama taje tayi mata Maganar tana ta sak’e sak’enta ta d’an kwanta har bata san bacci ya kwashe ta ba saida akayi la’asar gwaggo tazo ta tada ita tace bazata islamiyya bane, ba 6ata lokaci ta shirya ta canja wasu Uniform d’in ta tafi, Bayan sallan isha lokacin Fatuu ta gama cin Abinci ta maida plate d’in kitchen bayan ta fito tay tsaye bakin kopar d’akin gwaggo tana sak’e sak’e can dae tay shahada ta shiga da sallama lokacin gwaggon na zaune kan sallaya hannunta ruk’e da cazbaha ta jingina bayanta da jikin gado tana lazimi, daga can gefe Fatun ta duk’a idon gwaggo a kanta ita kuma sai sussuna kai take ganin haka yasa gwaggo d’aga hannuwa ta shafa Addu’a kafin tace mata da wani abu ne, farko Fatun shiru tay ganin yadda gwaggon ta zuba mata ido yasa cikin rawar murya ta fara Magana “d..dama d’azun Baffana ya kira ni ya sanar dani abunda ke faruwa wai Ard’o ya bada ni za’a man Aure….” Wani murmushin takaici mai d’an sauti gwaggon tayi kafin a harzuk’e tace “ki k’yale ni da shi zan nuna masa nima ina da iko dake ba Ard’o ba ko lamid’o ne shi sai inda k’arfi na ya k’are wllh don ina ji ina gani bazan k’yale a lalata maki rayuwa ba har wani ne d’an chairman can” ta k’arasa tana huci ba k’aramin tashi hankalin Fatuu yay ba murya na rawa kaman zata sa kuka tace “A’a gwaggo don Allah ki yi hak’uri ki k’yale shi ni na Amince ayi man Auren…..” Bata k’arasa sakamakon wata gigitacciyar tsawa da gwaggon ta daka mata tace “dum hetsi!!!” ba k’aramin firgita Fatuu tay ba har saida ta dan goce daga zaune jikinta ya hau kerma tana zare ido, a fusace gwaggon tace “a wodi hakkilo! tashi ki fita ki ban wuri!!” Fashewa Fatuu tay da matsanancin kuka ta hau bata Hakuri tana mata magiya akan ta Amince in ba haka ba Baffanta na cikin matsala Ardo tsine mashi zai yi, haka ta shiga fad’i mata halin da baffanta ya fad’i mata yana ciki gwaggon tay banza da ita kanta a k’asa can ta d’ago idanunta cike da tsantsar 6acin rai a kausashe tace “iyakata zaki nuna man Fatuu??? Da sauri ta girgiza mata kai tace “a’a don Allah gwaggo kar kice haka kawae ina son na fitar da Mahaifina daga halin da yake ciki idan aka hana Ard’o yin yadda yake so zai tsine masa ne kuma yace ya bar masa gida ma don Allah ki bari ayi man Auren kawae ni na hak’ura da karatun kuma dama kwanaki ba kince in ina cikin karatun ma na samu miji ba aurar dani zaki na idasa karatun acan gidanshi to ki barni don Allah gwaggo in da rabo sai in yi acan d’in” duk abun nan idanun gwaggo na akanta ta d’an kya6e baki can tay wani guntun murmushin takaici irin mai nuni da yaro yaro ne kafin cikin raunatacciyar murya tace “ki je kiyi duk yadda ranki ke so!” Tana niyyar sake cewa wani abun gwaggon ta mik’e a fusace tayi kanta tana fad’in “ki fita ki ban wuri shashasha….” Kasa k’arasawa tay sakamakon muryarta da ta karye kawae sai tasa kuka tana fad’in “ni ai da yake bani na haife ki ba shiyasa baki damu da damuwata ba” da gudu Fatuu ta nufi d’akinta ta fad’a kan gado tana wani irin kuka mai cin rae to itama dae gwaggo kukan tasa tay zaune a gefen gado ana cikin haka Amadu ya shigo gidan yana jiyo kukan Fatuu ya nufi d’akinta ko sallama bai yi ba ya kutsa kai jin yadda take kuka hankali a tashe ya shiga tambayarta abunda ke faruwa amman abu d’aya take fad’i shine “Gwaggo ce….” Cikin rashin fahimta yake tambayarta mi gwaggon tayi mata ganin bata da niyyar bashi amsa yasa shi fita ya nufi d’akin gwaggon sai dae ba shiri yay turus bayan ya shiga d’akin ganinta zaune tana ta matsar k’walla jiki a mace ya k’arasa gabanta ya duk’a bisa gwiwowinshi idanunshi har sun kawo kwalla, dafa knees d’inta yay cikin rawar murya yace “gwaggota Mike faruwa kike kuka” shiru bata bashi amsa ba bata kuma kalleshi ba, hawayen idonshi ne suka fara sauka ya fara mata magiyar ta fad’i mashi abunda ke damunta can ta kalleshi cikin muryar kuka tace “ni Fatuu zata watsa ma k’asa a ido ina k’ok’arin kwatar mata yancinta amman ta nuna man iyakata duk irin kokarin da nike akanta amman ta kasa bani goyon baya Saboda ni bata damu da farin ciki na ba…” Sosae tasa mashi kuka ya mik’e da sauri ya janyota jikinshi ya shiga lallashinta yana bata baki had’i da yi mata Nasiha da k’yar ya samu ta d’an saukko tace “Shikenan taje Allah ya taimaka na cire hannuna daga kan ta tayi duk Abunda yafi mata” da sauri Amadu ya girgiza kai yace “a’a Don Allah gwaggo kar kice hakan…” Katse shi tay da fad’in “To mi kake so in ce, zan ci gaba da damuwa da ita ne bacin ta nuna man iyakata, ko da yake dama nima ce da katsaladan da nike kokarin shiga tsakanin uba da yar sa”
“Gwaggo kema ai kaman matsayin uwa kike a wurinta iya Abunda Mahaifiya zata ma d’iyarta kike mata” girgiza mashi kai tay cike da 6acin rai tace “a’a Amadu ni ba matsayin uwa nike ba a wurinta tunda gashi ta nuna” duk Maganganun da suke Fatun na la6e tana sauraran su ta rufe bakinta da tafin hannunta jin Maganar Gwaggon ta k’arshe yasa ta watsa da gudu d’aki tana cigaba da rizgar kuka, sosae Amadu ya shiga kwatanta ma gwaggo dalilin Fatun na amincewa da Auren yana rok’on ta akan tayi hak’uri kar tai fushi da ita in sha Allahu komae zai daidaita, to a Daren ranar dai tsakanin gwaggo da Fatuu ba wanda ya runtsa shi kan shi Amadun baccin shi Sama sama ne ya ma rasa tunanin da zai yi don samun mafita shin zai ce ma Fatuu kar ta yi ma Mahaifinta biyayya tayi ma Mahaifiyarshi ko ya ya? Itama Fatun sak’e sak’e kawae take in wata zuciyar ta nuna ta yi ma gwaggo biyayya sai wata zuciyar kuma ta ce kenan ta Amince mahaifinta ya shiga mawuyacin hali akanta duk da zata iya taimaka mashi???
.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.