Haihuwa Da Hanji Page 23 Hausa Novel
“Ba ki da hankali ne nace!”Ya sake faɗa da ɗan ƙarfi, in za ta iya tunawa kalaman shi na farko kenan a gareta, kila to bata da hankalin ne don yanzu ma rikice wa tayi ta rasa me zata ce Bakinta ya kasa furta ko A sai baya baya da tayi da sauri idanunta da suka firfito farare tass a kanshi.Ganin Hararar da ya watsa mata yana cewa “Daina kallona!”Ya sa tayi saurin ɗauke idon, Mammi ce ta ceceta “Haba Saraki! Bata san kana wurin bane za ka tasa ta gaba kana zazzare mata ido, kayi haƙuri”Mammi yake kallo, itama Afeefah jin abinda Mammi tace ya sa tayi ƙoƙarin har haɗa kalaman haƙuri tace”Ka..yi haƙuri”Tsaki ya ja ya wuce ta ya barta da fitinannen kamshin shi, kitchen ta wuce ta ɗauko lunch box ɗin mai kyau dashi ta fito a sanyaye tacewa Mammi”Mun tafi Mammi”Daga haka ta fice a parlorn da sassarfa don tana fitowa ya zuba mata ido, tsaki ya ja bayan fitan ta ya dubi Mammi “Meyasa kuka sakata makarantar da ba’a sa hijab kamar ba musulma ba?”Mammi ta kalleshi “Yanzu menene aibun uniform din nan?”Sky blue shirt ne da navy blue blazer da skirt Dukda a gwiwa ne sai dai ta saka socks da ya haura mata har cinya, cover shoe Black ne kafafunta sai navy blue cap da ta rufe kanta kirip dashi, neck tie ne me layi layi sky nd navy blue sun yi mata kyau kayan kuma babu inda ke bude jikinta banda hannayenta da fuskarta.Baki ya taɓe bai sake cewa komai ba, abin kari mammi ta kira aka kawo mishi ya fara karyawa a hankali, bayan ya gama ya dube ta “Mammi auren salim next week friday””toooh aure haka kwatsam babu sanarwa babu shiri?””Nima jiya ne yake faɗa min””Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya sa da mu za’a yi”Ya amsa da Ameen.Daga nan wani hirar ta shiga yi mishi yana bata amsa a hankali hankali har suka gama ya miƙe ya bar gidan.Ƙarfe biyu sai ga ‘yan makaranta an shigo, bata samu Mammi a babban parlor ba kawai sai ta shige ɗakinta tayi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga Abaya onion colour mai kyau, hula ta saka ta fito ta nufi ɗakin Mammi jinta take very fresh nd healthy, wani sa’in ta kan tuna salim da halin da yake ciki sai kuma tace kila ma ya manta da ita, Sulaiman ma kan zo mata rai ko yaya yake oho bata sani ba.Da sallama ta tura parlorn Mammi ta shiga ta sameta zaune gabanta abinci ne, farin shinkafa ce basmati aka dafa amma dibawa aka yi kaman na jinjiri da alama ma da measurement cup aka gwada don ba zai wuce 1/2 cup ba, sai wani wake green, akwai salad ɗan kaɗan shi ma daga lettuce sai cucumber da lemon tsami, kaza ce gasashiya ‘yar kaɗan itama a gefe sai ruwa.Murmushi Mammi ke yi tana amsa sallamar “Barka ‘yan makaranta an dawo?””Eh Mammi mun dawo, ya jikin?””Alhamdulillah, Ki karɓi abinci ki ci sai ki huta ko?””Toh Mammi”Abincin Mammin ta zubawa idanu sama da seconds biyu kan tace “Mammi idan ba damuwa zan iya tambayar me yake damun ki?”Mammi tayi murmushi tace “Babu damuwa Afeefah, ciwo biyu ne ke damuna an haifeni da diabetes na gado don tun ina shekara biyu aka gane cewa na gaji ɓangaren mahaifina ne da ciwonsu na sugar, matsalar ciwon sugar idan yayi tsanani yana iya affecting koda to wannan dalilin ne ya janyo na samu damuwa da koda shekaru tara zuwa goma baya, an ma yi min aiki an chanza duka ba’a dace ba Afeefah har ma an ba ni wa’adin wata uku shine ƙarshen rayuwata sai kuma gashi da yardar ubangiji na shekara bakwai bayan nan”Afeefah damuwa ne sossai ya nuna a fuskarta tace “Toh Mammi shi ciwon ƙodar yaya yake? Ba’a warkewa ne?””Allah ya halicci mutane da koda biyu, wani halitta ne kaman wake akwai wasu ma da suke da ɗaya jal kuma suke iya rayuwa amma kowa biyu Allah yayi mu da su, waennan kodar amfaninsu kuma su tace jininmu ne idan ruwa yayi yawa su cire ta ta hanyar fitsari, suna taimakawa wurin hana jini ya hau sannan suna kuma sake wasu kwayoyin halitta na hormones su hana ƙarancin jini suna kuma haɗa vitamin D dake ƙara karfin ƙashi. Akwai abubuwan da suke kashe koda ba sai ciwon sugar ba wani ma abu mai sauƙi kan iya janyoshi kaman rashin shan isashen ruwa, riƙe fitsari ki ga mutum yana jin fitsari ya matse shi sai lokacin da ya maka tukuna zaka tafi da gudu, yawaitar shan pain killers baya na ɗan ciwo a sha diclofenac, wani yatsa ma na ciwo ki ga an apka feldin yawaitar shan su akai akai to su suna zuwa ne su rufe jijiyar da yake kaiwa koda jini, a cikin jikin mu kuma koda na daga cikin organs da suka fi kowanne bukatar jini, Sai kuma hawan jini ya fi yawa ma a ƙasar mu yana taimakawa sossai wurin kashe koda waennan dalilan bayan ciwon sugar su kan iya haifar da ciwon ƙoda, a kan iya chanzawa a dace amma ni an chanza min duk biyu ba’a dace ba yanzu haka ina zuwa dialysis ko wani wata.”Tamkar Afeefah za ta zubar da hawaye take juya maganganun Mammin “Mammi Allah ya baki lafiya ya sa kaffara ce duk kika yi ta yi”Mammi tayi murmushi tace “Ameen, kila Allah ya ajiyeni ne don ƙaddarar haɗuwarmu kila alkhairi zai haifar, bana fita kwata-kwata sai da Saraki ranar kawai na ji ina son fita ashe da rabon mu haɗu ne”Afeefah tace “Na ga Yaya…”Sai ta kasa cewa Rayyan a hankali tace “Ya Saraki! Ya damu sossai da rashin lafiyar naki”Mammi ta ɗan murmusa Allah ya sa kar Rayyan ya ji tana ce mishi Saraki don baya so, shiyasa ko su Abeeha ma Ya Rayyan su ke cewa “Afeefah ba zan iya misalta miki yadda hankalin Saraki ke tashi a kan ciwo na ba, ko kin san hatta me dafa min abinci ta karantu ne sossai akan cimar masu ciwon mu? Saraki ya tafi yayi courses akan likitanci ne bayan ciwon sugar na ya haifar min da wannan ciwon ƙodar in ba haka ba burin shi ya zama soja ne kawai ba Army medic ba, duk don ya san irin taimakon da zai bani a cikin gida ba sai mun yi ta zarya asibiti ba sanin bana so”Jinjina irin kaunar da yake mata take yi, lallai Rayyan na son mahaifiyarshi.Cigaba da mata hirar irin gudumawar da Rayyan yake bayarwa a rayuwarta take yi. A yadda dai ta gansu kaman babu wani namiji a gidan bayan Rayyan to mahaifinsu rasuwa yayi? Bata da wannan amsar sai dai ta san idan har tana gidan za ta sani ne.Abeeha ce ta shigo “‘yan makaranta ashe an dawo?”Tayi maganan tana zama hannun kujerar da Afeefah take “Na dawo Adda Abeeha, makarantar akwai daaɗi they are all nice to me basu yi min dariya ba””Ai na faɗa miki babu mai miki dariya, wasu da girman da suka fi naki ma suke zuwa suyi karatu bare ke da jikinki ba nuna girman yake yi sossai ba””Aikam na gani kuma na ji daaɗi, ga malaman sun iya karantarwa komai fa fahimta nake kaman na sani tun da chan”Mammi da Abeeha suka murmusa, za ta sake magana kenan Ya shigo parlorn da sallamar da shi kaɗai yake sanin yayi kayanshi.Kai tsaye kusa da Mammi yaje ya zauna, da ita da Abeeha suka haɗa bakin ce mishi”Sannu da dawowa”Kai ya ɗan gyaɗa bai kalli kowaccensu ba, mammi ma ta mishi sannu da dawowa yake tambayarta ya jikinta ta amsa da da sauƙi.”Yauwa Mammi ɗazu na haɗu da Samha a school ashe auren ya salim wani sati?”Abeeha Tayi maganan da ɗan mamaki, Dukda da ta kalli Samha sai da ta tuna abubuwan da suka yi wa Afeefah kuma haushin su take ji har ranta ko da samhar tayi mata magana da kyar ta daure ta amsa, wurin kokarin janta da hira ne take sanar mata auren salim ɗin kuma suna gayyatarta.Wani irin faɗuwa gaban Afeefah yayi “Aure Ya Saleem zai yi?”Bata san a fili tayi maganan ba sai da ta ɗago idanunta suka faɗa cikin nashi da a lokacin ya ɗago ya kalleta jin furucinta, da sauri ta ɗauke ido gabanta na dokawa sam bata son suna haɗa ido bata san me yasa ba, sai dai yanzu maganar auren saleem ɗin sai ta ji shi wani iri duk ta ji babu daaɗi, Abeeha ma sai da tayi maganan kan ta tuna da Afeefar.Mammi ce tace “Eh aure zai yi Afeefah wani sati, kar ki wani sa damuwa a ranki in shaa Allahu Allah zai musanya miki da abin da ya fi alkhairi”Kunya ne ya rufe ta sai ta duƙar da kai tana kallon yatsun ta sautin tsakin shi ne ya shiga kunnenta, Mammi ta fara mishi faɗa akan yawan tsakin kaman wani tsaka, Abeeha ce ganin yanayinta ta ja Afeefar akan su je su ci abinci suka fice daga parlorn.****Hidima fa ya kankama ɓangaren Amarya sai shiri ake wane, tun saura sati aka fara bikin ‘yan karya don Mommy sossai ta ajiye musu kuɗi Dukda ma angon ya ja mata gargadi akan duk abin da za su yi kar su sake su saka shi, bai ma je gidan ba ko sau ɗaya sai ranar da suka yi kauyawa bayan Magrib yana zaune harabar gidan su da dangi suka cika, shiru kawai sam ba ya jin daaɗin komai kuma komai ba ya burgeshi kaman daga sama ya ji Muryar Mommy.”Saleem yanzu ka rantse sai ka nunawa duniya duka ba ka son auren nan dole na maka ko?”.Shi bai san me yayi ba, kaman zai yi kuka yace “Me nayi kuma mommy?””Ko sau daya ka je kofar gidan su Sabrina da sunan zance? Ko ita ba mutum ba ce? Ka hana ta saka ka cikin duk hidimar ta da kyar ma na bugi cikinta ta nuna min kai ne baka so ba ba bata sanar da kai bane, baka bata komai ba haka ake yi?””Amma mommy ni nace tayi wani hidima ne?””Au in kai kana ƙunci da baƙin hali a kan wata chan da na tabbatar yanzu ta rabarwa maza kanta sai aka ce ita ma ta biye ka kuyi ƙuncin tare?”Runtse ido yayi ya buɗe tuni suka sauya Meyasa mahaifiyarshi ke yin abu kaman bata je islamiyya bane? Ya subhallah maganar da ta faɗa ya mugun ƙona mishi rai amma ya zai yi ne? Uwa uwa ce.”Zan je, zan ba ta kuɗin”Abin da kawai ya iya faɗa kenan ba tare da ya kalli mahaifiyar tashi ba, sai da ta wuce ya bita da kallo yana jan Astagfirullah don yana tsoro, ‘ya’ya mata ne garesu yana tsoron Allah ya hukunta mahaifiyar tasu da daya daga cikin yaranta, yana tsoro ta fahimci kuskurenta in a Hard way.A lokacin ya miƙe ya nufi mota kan ya shiga aka wangale Gate, motar Rayyan ne ya shigo cikin gidan dole ya fasa tafiyar sai ya nufi wurin Rayyan ɗin suka gaisa.”Fita za ka yi ne?””Eh wai zan je ne in ba Sabrina kudaɗen da ya kamata su yi hidimar bikin”Kai Rayyan ya gyaɗa yana furta “zagayo mu tafi”Zagayawa yayi ya shiga motar, shiru yayi dama shi ne mai hirar muddin suna tare da Rayyan to shi ma baya cikin yanayin hiran, hakan kuma sai yake sa Rayyan ke jin wani iri sai ya ga kaman bai kyauta mishi ba ɓoye mishi da yayi Afeefah na gidan su amma zaman lafiyanshi kenan tunda mahaifiyarshi ba amincewa zata yi ba ko ya faɗa mishi ɗin.Har suka isa unguwar da saleem ne ke ta mishi kwatance hira ba sossai ya hada su ba, a cikin Layin aka yi kauyawan ana ta shirye-shiryen kiran sallahn isha su kam suna nan suna chasewa ‘yan mata sai zuba rawa suke, Rayyan ya samu wuri yayi parking yana kallon arean da abin da suke yi a ranshi ya ja tsaki yayi dubu, auren saleem ne ake yi ake wannan haukan? Babu natsuwa a lamarin nasu babu kama kai, ba’a hana hidima ba amma sai a yi shi da tsari ba irin wannan ba ko daga rawar da ake ka san an zubar da mutunci.Wayanta ya shiga kira ringing na karshe ta ɗaga “Hello Ya Saleem”Ta faɗa da ɗan ƙarfi saboda kida dake tashi”Ki zo ina daga bayanku kaɗan”Babbar kawarta ta janyo jiki na tsuma suka nufi motar, baya suka bude suka shiga suna gaishe su.”Amma mun yi fushi sai yau abokanan ango ke neman mu?”Ci kan ku Rayyan bai ce ba, arzikin kallo ma basu samu ba yana wurin ne kawai saboda Saleem ne da wani ne waennan ɗin sun mishi kaɗan ya haɗa numfashi da su a mota guda.Bundles na ‘yan dubu dubu guda uku ya buɗe dashboard ya fiddo ya ajiyewa saleem a kan kafafunshi dole ya ɗauka ya juya ya miƙa mata “Ku yi hidima.”Jiki na rawa suka karɓa sai kamshi kudin ma ke fitarwa na sabunta.”Akwai wani abu?”Ya tambaya saboda kawai mommy ta mishi dole”A’a ya saleem wannan ma ya isa mun gode sossai”Daga nan suka fice don shi maganan soyayya ma ba wai hada su yake da ita ba.”Ka ga abin da mommy ta ja min ko Rayyan?”Saleem ya faɗa bayan sun fice daga unguwar.Hakika shima ya ga wautar mommy, da ya ga yarinyar sai ya hasko Afeefah a idanunshi ko a kusa bata da abin da za’a haɗa ta da Afeefah bai ce komai ba dai har ya mayar da saleem gida.Su Gaje sun yi shiri matuƙa na wannan aure, yayinda amarya tayi shagali sossai kuma ta kullaci kannen angon da babu wanda ta gani a hidimar ta har aka ɗaura aure ranar Juma’a, Dukda aure ne da babu wani sanarwa ko hidima saleem ya ga mutane kwarai an mishi kara, saboda shi ma na jama’a ne Rayyan na a gefenshi yana yi ne kuma saboda saleem ne don baya son harkar hidima da hayaniya har aka ci bikin aka watse, amarya dai ta tare a sashen saleem na gidan inda duk mommy ce ta tsara hakan sai fatan Allah ya basu zaman lafiya.



