Novel Document

Uwani Yar Kashin Gwiywa Complete Hausa Novel

Description/Story:

Uwani Yar Kashin Gwiywa Complete Hausa Novel

Written By Ameera Adam

 

Description

Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye suka fara ‘yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. “Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku.” Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali.

Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin.
“Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne.” Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka.

“Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami.”

Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce.

“Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture…” Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta.

“Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?” Lami ta sake taɓe baki ta furta. “Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa.”

Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. “Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa.” Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce.

“Wai ina Lami take?” Da sauri Lami ta amsa. “Ga ni mana.”

“A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya.” Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. “Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki.” Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. “Uwar garke fa…”

“Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?” Baba Isuhu ya katse ta da sauri.

“Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa’a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan.” Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes.

“Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo.” Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya.

“Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke ‘yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki…” Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, “Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi.” Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. “Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna…” Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta.

“Ke ‘yar nan da gaske?” Lami ta gyaɗa kai tana murmushe.

“Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arziƙi, ko ni ƙanwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwaɗayi, duk wurin da ake samun mai maiƙo-maiƙo a nan na fi ƙarfi.” Lami ta yi gaba tana tafiya cikin ƙwambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matuƙar aka wayi gari da an yi mata ƙauri da tinkiya ta san daraja da ƙimarta ta ƙaru a idanun facalolinta.

 

CIKIN DARE

 

A hankali Uwani ta buɗe idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada.

“Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji.” Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. “Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi haƙƙin tashina tsakiyar dare da kike yi…”

“Dada kamar kukan uwar garke nake ji.” Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da ɗan nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. “Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su…”

“Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama ‘yan matan ƙafafuwanki ki yi gaba.” Jin takaicin abin da Dada ta faɗa ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje.

Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin sanɗa yana waige har ya ƙarasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace maƙogaro ya maƙe murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. “Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa.” Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya ɗago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya ƙarasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya ɗan fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A ɓangare ɗaya ƙirjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana raɓe a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya leƙa ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa.

“Haba Isuhu tun ɗazu ɗauko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan.” Baba Isuhu ya yi ƙasa da murya ya ce. “Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ƙofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicciɓo maka ita.” Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar garke da ke cin dusa, ya tattaro iya ƙarfinsa ya ɗago ta sai ji kake ɓaaaarrrrrrr wata uwar tusa ta ƙwace masa. Uwani da kawo kanta kenan ta saki murmushi ta ce.

“Kai da jin wannan tusar ka san su uwar garke bacci ya yi daɗi.” Har za ta gota sai ta leƙa garkensu, sai dai haskarwar da ta yi babu uwar garke babu alamunta. Da sauri ta juyo tana shirin fasa ihu ta hango Baba Isuhu rungume da uwar garke, ita kuma uwar garke jin matsar da Baba Isuhu ya yi mata ya sa ta ware baki ta ce.

“Meeeeeeeeehhh.”

Uwani Yar Kashin Gwiywa Complete Hausa Novel txt

File Name   Uwani Yar Kashin Gwiywa… Hausa Novel Doc.
Title   Uwani Yar Kashin Gwiywa Complete Hausa Novel
Author    Ameera Adam
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    23/10/2024
File Size    350KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦800
Phone No   07062062624
Download Uwani Yar Kashin Gwiywa Complete Hausa Novel By Ameera Adam

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog

Back to top button