Hausa novels

Gargadar So Chapter 124 By M Shakur

Wuraren 12:30 na rana Mom ta farka daga baccin safiyan datayi ta watsa ruwa tafito tana sanye da waya mahaukaciyan lace tazuba gwalagwalai da 2friends nata zasuzo ta tsaya turus ganin Hawwa a falo ita kadai zaune akan kujera takife kanta a hannun kujera bacci yadan kwasheta mamaki abin yabama Mom badai tun safen nan yarinyar nan tana nan bata koma side nata taje ta kwanta tayi bacci tahuta ba.Wucewa dakin ma’aikatanta tayi suna ganinta duk suka tashi zaune tace “an gama girke girken danace ayi?” Babban Chef nata tace “Mrs Khaleel cooked everything Ma, she asked us to rest” baki Mom tasaki saikuma ranta abace tafito tawuce dinning tashiga bude warmers ya Allah! Lafiyayyen biryani Mandi, gizzard dodo, pepper chicken, kofta, samosas, moimoi, salad, sai juice na fresh juice zobo da cucumber juice Hawwa tayi, sannan ta yankama Mom fruits in very very fine shapes cus taga Mom na shan fruits dazu, Mom bata taba ganin irin fine shapes na slices din nan ba sai kawai tajuyo takalli Hawwa daidai PA na zuwa wajen da suit tace “yanzun nan tai baccin Ma” Dasauri Mom tace “ba dole ba ta daurama kanta aiki kaman jaka ga masu aiki duk suna nan” dan murmushi PA tayi tace “the food is delicious Ma tazubamana namu all of us ate” kallon PA Mom tayi saikuma ya harareta ba yabo ba fallasa tace “wake her up taje ta kwanta ta huta please” tana maganan tawuce sabida wayanta dake ringing PA tai wajen Hawwa ahankali tayi taping chair dasauri Hawwa tabude idanu PA tace “Ma tace kije side dinki ki kwanta ki huta” dasauri taceBangaji ba daidai bakin Mom na parking motocinsu PA tawuceta tai gaba Hawwa tawuce dinning tana gyara komi tana kara gyara mayafinta Mom tafito zatai magana pA na shigowa da bakin wasu matan ministers ne dasauri Mom tai wajen su suka rungume juna tace “welcome Hajiya Hajara, Welcome Hajiya Shema” suka shiga gaishe gaishe ahankali Hawwa tazo wajen tadan duka cikeda girmamawa tace “sannunku da zuwa ina yininku” murmushi dukansu sukama Hawwa sukace “your daughter Inlaw ko wow she’s so beautiful kinsan lokacin bikin ina Qatar ban samu nazo ba” Hajiya shema tafadi tana kallon Hawwa, ahankali Mom tace “muje muyi lunch first before anything”Ma’aikatan Mom da uniform suka fito zasuyi serving Hawwa tace “don’t worry I will do it” Hawwa tazo wajen anatse tana bude komi takalli kawayen Mom tace “Anty wat do you want me to serve you”? Hajiya Hajara tace “wow your daughter Inlaw is so homely and cultured” dan murmushi kadan Mom tayi, Shema’u tace “serve me Mandi da kofta salad dai this cucumber juice” zuba musu Hawwa tayi sannan takalli Mom data mata wani shegen kallo but bata damuna, cikeda girmamawa tace “Mommy mezan zuba miki ko kinason wani abu daban na dafa miki “? Atare duka kawayen Mom sukace “wowwww Hajiya Zee we want daughter in law like this oo” dan murmushi kadan Mom tayi tace “samin moimoi da sauce” Hawwa tadau plate mai kyau tasama Mom da nama ta ijiye gabanta tasamata spoon tace “Mommy zakici fruits na yanka miki naga kinason avocado harda shi” sosai Mom ke kallon Hawwa saikuma tace “give me small” sama Mom tayi sannan tabar wajen sai kawai ta shiga kitchen ta zauna kan kujera dake island din batasan wani daki zata shiga baKawayen suna fara yaban abincin Hawwa Mom ba yanda zatayi tana kai moimoi bakinta Ya Allah! Saida taji kunnenta yayi motsi sabida dadi this girl can cook like this? She has chef oo but akwai wani homely and love taste da abincin Hawwa kedashi tass ta cinye ta kara saida tacı moimoi uku kawayenta sunci sukai nak Hajiya Hajara tace “Hajiya Zeenatu anya bazan kawo matar d’ana Muhammadu tazo wajen matar danki ta koyi girki ba kuwa? Kinga har cooking school na sata but duk abanxa gaskiya matar danki ta iya girki wat! Please can I package this kofta naje dashi gida with this fresh juice” murmushi sosai Mom tayi tace “sure sure haba” sunci abinci sosai Mom was just feeling herself suka dawo falo suna hira saiga Hawwa tafito rike da tray na Bowl of ice cream da brownie Hajiya Shema tace “anya kinaso mu koma gidanmu kuwa Hajiya Zeenatu diyarki ta karyamin wait loss see standard dessert ice cream da brownie” suka daddauka Hawwa taja stool ta ijiye gaban Mommy tawuce kitchen Mom ta kalli kawayenta tace ina zuwaKitchen tabiyo Hawwa tana rufe kofa dasauri Hawwa ta juyo cikeda masifa Mom tace “so kike ace na maida matar d’ana yar aiki na?” Kan Hawwa na kasa Mom tadan dafa goshinta tace “wat are you still doing in my side eh? Wuce kitafi nagaji da ganinki wlh” Mom tana maganan tafito tana murmushi.Kofan kitchen Hawwa tayi tayi alwala anan pampo baya tashigo tafito tashiga dakin masu aiki tayi salla aciki tanaji kawayen Momy na tambayanta Mom na cewa ta kwanta taji sunce agaisheta please, tana nan cikin dakin kusan 10min saiga PA tazo dakin tace “Madam tace nakiraki” tashi Hawwa tayi tafito kanta akasa Mom ta kalleta so take tarufeta da masifa but saitaji kuma takasa ba yabo ba fallasa tace “kinci abinci?” Girgiza mata kai Hawwa tayi, cikeda masifa Mom tace “wuce kije kidiba kibarmin flat dina kitafi naki” batai musu ba saitaje dinning din dahar an gyara tadauki karamin plate ta debi abinci kadan tasa spoon ta zauna takai bakinta wlh takasa ci, damuwa yamata yawa da bata iyacin abinci Mom takai kusan 3min tana kallonta, tadan sauke ijiyan zuciya tace “jiranki nake ki cinye abincin nan kitashi ki bar bargarena” dasauri tashiga cusama kanta abincin, sai kawai ta kware tafara tari dasauri Mom tace “give her water PA” wucewa wajen PA tayi da sauri tasama Hawwa ruwa a cup tabata da sauri ta karba tasha Mom duktana kallonta, ita kawai tabarmata flat cus bamataso ganinta tazo tafara tausayinta danta farajin wani iri iri game da yarinyar itakuma tasan batason Hawwa ta tsaneta sabida abinda tama danta, ijiye cup din Hawwa tayi ta karasa dannama kanta abincin sannan tadauki plate din Mom tace “bama PA na plate din zatakai kitchen wuce kitafi” ahankali Hawwa tabata ta taho tana tafiya kaman bataso tawuce kofa Mom na hararanta saikuma ta tsaya wajen kofan tadan juyo ta kalli Mom dasauri Mom tadauke kai tana tabe baki hakan yasa Hawwa tabude kofan tafita daidai Motan Noor na shigowa gidan tadawo daga school tun kafin ayi parking tafara ihu Hawwa ta tsaya Noor tafito ana parking tazo da gudun bala’i kaman tai shekara bataga Hawwa ba tace “Mommy FAA” Hawwa tabude mata hannu tawani rungumeta kawai Mom tabude kofa tace “saken mini yarinya, Princess come here” sakin Noor Hawwa tayi Mom ta dauketa suka wuce ciki Noor nama Hawwa bye, Hawwa tawuce flat nata ahankali zuciyanta ba dadi.

Back to top button