Uncategorized

N-Power: Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power

Sadiya Umar-Farouq, ministar harkokin jin kai, magance bala’o’i da ci gaban al’umma, a ranar Laraba, ta bayyana wani shiri da gwamnatin tarayya ta yi na kiran karin matasa 400,000 a karkashin shirin N-power.

Ministan wadda ta yi magana a Kano a wajen rufe taron N-Knowledge Training Batch C1, ta ce adadin na cikin wadanda suka ci gajiyar shirin na N-Power miliyan daya da shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shi.

 Ta yi bayanin cewa “Muna aiwatar da shirin ne a hankali inda rukunin C1 ke daukar jimillar masu cin gajiyar 510,000 kuma rukunin C2 zai fara aiki nan ba da jimawa ba.”

 Hajiya Umar-Farouq ta bayyana cewa shirin na N-Knowledge ya mayar da hankali ne wajen baiwa matasa ‘yan Najeriya sana’o’in hannu da kuma ba da takardar shaida domin su zama kwararrun ma’aikata, masu kirkire-kirkire da ’yan kasuwa da aka shirya don kasuwanci a cikin gida da ma duniya baki daya.

 Ministan wadda ta samu wakilcin mataimakin daraktan kudi da asusu na ma’aikatar Muhammad Sambo ya bayyana cewa sama da matasa 3,000 daga shiyyar Arewa maso Yamma sun samu horon sanin makamar software da na’ura mai kwakwalwa a karkashin rukunin C1 na sashen N-Knowledge na ma’aikatar.  Shirin N-Power.

Karanta:

✓ Sabbin Hotunan Momee Gombe, Maryam Booth da Hadiza Gano.

✓ An baiwa mawaƙi Umar M. Shareef jakada a gidan television.

✓  Cikin fushi Umme Zeezee ta mayar wa da wani saurayi da martani akan cewa ita ba jaruma ba ce

✓  Hukuncin Abincin Kirsimeti Ga Musulmi Fita ta farko 

 Ta bayyana cewa, “Sannan ne cewa shirin N-Power wani muhimmin bangare ne na Shirye-shiryen Zuba Jari na Jama’a na kasa da ke zaune a Ma’aikatar Agajin Gaggawa, Gudanar da Bala’i da ci gaban jama’a ta Tarayya, inda ta kara da cewa shirin zai taimaka wa matasan Najeriya  a fannin kasuwannin cikin gida da na duniya baki daya.

 Ministan ya ce “Shirin N-Knowledge ya yi niyya ne don inganta wa matasan Najeriya 20,000 rayuwa ta hanyar gogar da su a ɓangaren ayyuka masu daraja a duniya da abubuwan da ke cikin ƙere-ƙere da fasahar sadarwa.  Za a cike gibin da ya samu na kusan 7,000 da wuri don cimma burin daukar ma’aikata 20,000 kamar yadda aka kebe domin wannan kashin.”

Back to top button