Hausa novels

Halysaah Page 90 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 90…Bayan Khaleesat ta shimfida tabarmin da Babanta yasa ta shimfida ta koma parlor ta nufi kujera zata zauna har a lokacin hankalinta ya kasa kwanciya duk da irin approach din deputy toward her dad but she was so tense and confused, gashi ita bata ma san ko su waye ba, Nenne na kallonta har ta zauna kan kujera sannan tace “Yanxu baki lallabasa kun shigo gidan tare ba kika bar sa zaune bakin gate? Haka rayuwa zata ci gaba yana zaman kofar gida kamar Mai gadi kenan?” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, she was trying all possible best to keep calm at this moment, Nenne ta kyabe baki ta dau remote ta danna inda Islam ta nuna mata ana dannawa idan za a canza tashan kallo, tana canza tashar duk yaran dake zazzaune parlon suka juyo suna kallonta, ta tsuke fuska, Mikewa Khaleesat tayi ta bar parlon ta tafi dakin Ummanta ta sameta zaune tare da Aunty Farida sai Mama Shatu dake zaune daga kusa da kofar dakin a zuwan ta shigo hira da Umma, tunda Khaleesat ta shigo Umma ke kallonta, ganin Mama Shatu kawai Khaleesat ta juya ta tafi dakinta, Aunty Farida ma ta bi ta da kallo, bayan kusan minti biyar sai ga Umma ta shiga dakin nata tana kallonta tace “Lafiya Khaleesat?” Khaleesat ta sauke idonta har Umma ta karaso ta zauna gefen gado tana kallonta, sai ga Aunty Farida ma ta shigo dakin tana tambayarta me ya faru? Da kyar Khaleesat tace “Baba ne yayi baki a motoci ban san daga ina suke ba” Umma ta kasa daina kallonta ita ma a dan tsorace tace A motoci kuma? Ke wa ya gaya maki?” Khaleesat tace “Muna zaune tare a waje sai ga su a motocin” Hankali tashe Umma tace “Yanxu yana ina Malam din?” Khaleesat tace “Ya ce in shimfida masu tabarma a tsakar gida, har ma sun gaisa da bakin” Juyawa Aunty Farida tayi ta fita daga dakin, ta tafi can compound ita ma dai hankalinta a tashe, ai ko ta hangosu zazzaune saman tabarma su hudu sai Malam Ali na biyar da ya sinne kai ko me suke gaya masa oho, ta juya ta koma cikin gida. Karfe goma saura na daren Khaleesat ta shigo parlon Babanta tare da Aunty Farida, Umma ma na zaune parlon sai Nenne, Nenne ta gyara zama tace”To yanxu Ali ko don wannan girmama ka da yan unguwan nan suka yi suka shigo har gidan nan suka zazzauna a tabarma suna gabatar maka da kansu ya kamata ka rufa mana asiri kar ka sake zama bakin gate kamar Mai gadi, baka ji dadin da naji ba wallahi ganinka a tsakankanin manyan mutane a tsakar gida” Malam Ali dai kallonta kawai yake, can yace “Yanxu Baaba wa yace maki yan unguwan nan ne?” Nenne ta saki baki tace “Ba yan unguwan nan bane? To yan unguwan dake gaba da namu ne ko wanda ke bayan namu?” Malam Ali yace “Ni bakin da suka zo gidan nan bama su da alaka da unguwan nan gaba dayan ta” Nenne ta zaro ido tana kallonsa tace “Kai haba dai? To a ina ka samo su Ali? Su waye?”Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace “Dalilin tara ku a nan da nayi kenan Baaba, duk za ku ji waye su da kuma me ya kawo su gidan nan” Nenne ta gwalo ido tace “Wani laifin kuma ka sake yi Ali? Mun shiga uku mun lalace, abun arziki bai amshe mu ba, ko kwace gidan suka yi?” Malam Ali ya kara sauke wata ajiyar zuciyar cikin nutsuwa ya fara koro masu bayanin su waye mutanen da suka zo da kuma dalilin zuwan nasu gidan, tunda ya fara magana Khaleesat ke kallonsa babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, haka ma Umma da Aunty Farida that look speechless, Sai da Nenne ta jira ya kai har karshe sannan tayi mitsi mitsi da ido tace “Amma ka ban mamaki kuma ka ban tsoro da baka masu koran kare ba Ali, anya kuwa ba a canza min kai a daki na je wankan jegon ka a bandaki ba kuwa tunda gidan yawa ne kuma mu uku muka haihu ba wani tazara tsakaninmu??? Ali yanxu kana nufin baka kore su ba ka zauna ka sauraresu har karshe?” Malam Ali yace “In kore su kuma Baaba…. Nenne tace “Amma daga Awdul din har iyayensa Allah Ubangiji ya tsine masu albarka daga su har wanda ya basu shawaran turo maka manyan mutane su baka hakuri, kai kuma da yake gantalalle ne kai baka san ciwon er ka ba maimakon kace masu ai an sa mata rana biki saura sati daya yanxu haka shine ka zauna da wata safarka a kafa kamar dan bigilantee a tsakankaninsu kana sauraronsa, to wallahi idan ban kai karar su kotu ba Allah ya tsine min, ko Awdul ne kadai namiji da ya rage a duniya idan na kara basa auren jikata a kirani tsohuwar banza tsohuwar hofi, haba fisabililahi, sannan shi yaron nan da ya siya mana gidan nan kanin ubanmu ne shi ko na uwarmu da zai siya mana katon gida haka idan har ba sonta da aure yake ba, sai ya fito ya gaya mana yana sonta mu wani irin kwakwalwa gare mu da baza mu gane ba? ai ni ba yarinya bace nasan abinda nake, wallahi sonta yake so kuma na aure, haka kawai ka biye barayin gwamnati su saka ka a tsakiya don su tsorata ka ka sake daukar er ka ka bada a karo na biyu? Ko dai baka da lafiya ne Ali?” Malam Ali dake ta kallonta cikin nutsuwa yace “Yanxu fa Baaba baki saurareni na kai karshen bayani na ba…. A fusace tace “To ina jin ka maza maza tafi karshe Malam Ali yace “Ni nace masu bazan ma Jiddah dole ba, duk abinda take so shi zan mata kuma shi nake so, in ma shi Abdul din tace take son komawa ni bazan hanata ba sai dai in bi ta da fatan alkhairi, in kuwa tace bata so to hakan ya zauna don bazan mata auren dole a karo na biyu ba” Nenne tace “To maza tun basu yĆ­ nisa sun isa gida ba ka bi su kace ai babu wannan zancen ko makamancin sa, yarinya tace bata sonsa ta tsanesa, in kuma wannan karan da karfin mulki za su yi amfani da shi wajen auren nata kamar yanda suka yi da kudi watannin baya to sai su yi mu gani, maza su gaya ma dan su ya cire shegun idonsa akan Khaleesah bata sonsa kuma tafi karfinsa nesa ba kusa ba wallahi” Hawaye ne kawai ke zuba idon Khaleesat tana shessheka tana jin wani zafi a ranta, ta jinginar da kanta jikin Aunty Farida cause she is beginning to loose her control, Sosai Aunty Farida ke jin dadin maganganun Nenne don ita ma banda tafarfasa babu abinda zuciyarta yake a inda take zaune, Umma kuwa dafe kanta da yayi mata nauyi sosai tayi, Nenne tace “Ka ji me nace maka ko baka ji ba Ali?? Tun gari bai waye ba ka san yanda zaka yi ka sanar masu babu wannan maganar da suka zo da shi don har an saka ma Khaleesah rana da wanda take so kuma ranan jama’ar nan daurin aure” Malam Ali yace “Shikenan Baaba, su a yanda suka zo ma suna tunanin bayan sun gabatar da bukatarsu nauyin su da ganin girmansu zai sa in amince lokaci guda babu ja in ja, amma wallahi ban yi haka ba, nuna masu nayi ni bani da ta cewa sai abinda ‘ya ta tace shine magana don bazan kara mata dole ba, yanxu zuwa gobe suna saurarata su ji ya ake ciki, don haka bazan boye masu komai ba in sha Allah, zance su yi hakuri nayi mata miji” A fusace Nenne ta nufi kofa tana cewa “In Alhaji Musa bai yi hankali ba zan taka har gidan nasa in ci masa mutunci wallahi, tun da saboda shegen dan sa aka halitto Khaleesah ba sai ya zo ya sake daura auren ba mu gani, wato ya zo maka da manyan mutanen garin nan yanda zaka yi masu biyayya ga ka dan banza ko? To mu zuba da su” Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Umma ma ta mike ta bi bayanta don bakin ciki ma bazai bari tace komai ba, shi dai Malam Ali kallon Khaleesat kawai yake, a hankali yace “Kiyi hakuri Jiddah, babu me maki dole in sha Allah, ki kwantar da hankalinki” Ita dai Khaleesat hawaye kawai take ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace “Amma Malam tun farko bai kamata ma ka zauna ka ci gaba da sauraransu ba bayan kaji dalilin zuwan su, kamar yanda Nenne tace da kawai sai kace masu ai an saka mata rana kawai” Malam Ali yace “To tunanin nan bai zo min ba wallahi, amma ba komai in sha Allahu zan kira na kusa da Deputy din gobe in gaya masa yanda ake ciki don ya bani numbersa suna sauraran kirana gobe” Aunty Farida tace “Allah ya kyauta” Mikewa tayi ta dago Khaleesat suka fita daga parlon. Daren ranan nan Khaleesat kasa baccin kirki tayi, she was so disturb, ta rasa menene zai sa Abdul ya hakura da ita ya cire ransa a kanta cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, dama kullum a ranta tana jin ba fa hakura yayi ba, he is definitely coming back amma bata san ta wannan salon zai sake dawowa ba, ko kadan bata yi mamakin gano sabon gidan nasu da suka yi ba ba don ko dubu biyu suka ba wani a Mariri tsaf zai kawo su tunda kusan kowa yasan inda suka dawo yanxu, sai kusan karfe hudu da rabi ta tashi daga saman darduman da take zaune bayan ta idar da sallolin da tayi sannan ta kwanta…. Da asuba bayan ta idar da Sallah tayi azkar ta tafi dakin Umma ta gaisheta, Umma dake zaune kan darduma har lokacin ta dinga kallonta don tana ganin idanuwanta ta gane bata yi bacci ba daren jiya kuma tayi kuka, Khaleesat ta zauna kusa da ita ta gaisheta cikin sanyin murya, Umma ta jawo ta jikinta a hankali tace “Bana son ki tada hankalin ki Khaleesah, in sha Allahu babu wani abu da zai sake hadaki da Abdul ina nan ina maki addu’a kema ki dage da addu’a kinji?” Hawaye ya cika idon Khaleesat ta gyada ma Umma kai kawai… Aunty Farida na zaune dakin Nenne tana kallonta tana ta koro mata jawabi, Nenne ta kare jawabinta da cewa “Don haka kema ki hada kayanki kala uku ko hudu zuwa nan da gobe mu kama hanya kawai, sam ban ga ta zama ba wallahi Parida, dole ko nawa ne in bada a min addu’a a dauke hankalin tsinannen yaron nan akan jikata ya rabu da ita na har abada, zuwa anjima kuma ki kira min Murja in sanar mata gamu nan zuwa Bauchi gobe, dama ina ta cewa zan je kwanan nan to ga babban dalili zai kai ni yanxu, ke ina ga ma har da Khaleesar za mu tafi don gwara mu je da ita aga warce za ayi ma addu’aido da ido, in akwai wani taimako da za a bata tayi amfani da shi sai a bata in tsareta tayi, banda Ali dan banza ne da wani idon yake son mu kalli yaron nan dake ta mata hidima saboda soyayya, ai sonta yake Ahamad din, to kanin ubanmu ne shi zai mallaka mana kantamemen gidan nan haka babu dalili? Don haka maza mu shirya gobe mu tafi Bauchi mu samo mafita, farkon zuwan Ali furson ai can naje kishiyar Murjan ta rakani gun babanta ya bani taimako, babban bawan Allah ne mutumin a kauyen, kuma gun iyaye da kakanni ya gaji wannan baiwa tasa, in muka ce za mu biye Zahra’u da Ali to fa Khaleesah na cikin gararin rayuwa, miji wawa mata wawiya ga su matsoratan banza, don haka gwara mu rufa ma kan mu asiri Farida kar a mana dariya, naga ke da wayewar ki kuma kina da wayo, sannan hankalina bai kwanta ma ace mu tafi ba Khaleesah ba kar shegen yaron ya sake lallabowa ya dauketa tunda ba addini ne da shi ba, gwara mu mu je da ita kawai ayi abinda za ayi” Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace “To Allah ya kai mu goben Nenne” Nenne tace “Allah ya maki albarka, ku hada kayanku a akwati daya ke da Khaleesar, Ni kuma zan zuba ko a bacco bag ne mu kama hanya” Alhaji Musa ne zaune parlon sa ajen karfe sha dayan safe yana waya, Momy dake zaune ta hakikance kan kujera sai kallonsa take har ya idar da wayar ya ajiye, rai bace tace “Yanxu suna nufin su ce uban yaki amincewa kenan Alhaji??” Alhaji Musa ya sauke ajiyar zuciya yace “Gashi kuwa kina jin yanda muka yi a waya da Deputy, ban taba tunanin zai yi turning down din maganar nan ba duba da irin mutanen da suka je har gida suka samesa, idan Abdallah zai yi hakuri ya saka ma ransa salama ina ga zai fi alkhairi, this was the only option I tot will work” Momy tayi mitsi mitsi da ido tace “Amma wannan muturni anyi tsinannen talaka, ko duba girman mutanen da suka je har gabansa suka zauna bai yi ba, banda Abdul ya nace har yana neman yi ma kansa illa ya ja min asara don Allah yaushe za mu zubar da girman mu da mutuncin mu haka a gaban talaka fakiri?” Alhaji Musa ya sauke ajiyar zuciya yace “Yanxu ke a matsayin ki na uwarsa babu hanyar da zaki bi ki masa magana ya saka ma ransa salama ya mance wannan yarinya ya hakura?” Cike da damuwa Momy tace “Wallahi Alhaji nayi, ba irin yanda ban bi da shi ba a matsayina na uwarsa amma abun yaci tura, ko baccin kirki Alhaji bana iya yi saboda halin nan da Abdul ya jefa kansa kan wannan er talakawan, ace mutum bazai ci abinci ba kullum gashi nan gashi nan dai ne kamar wanda ya fara samun matsala a kwakwalwa to ina lafiya a nan Alhaji? Kar wani abu ya samesa fa mu shiga uku shi Kenan garemu a duniya, shi yasa na kawo maka shawaran ka hada kan manyan abokanka abokanka ka nemi alfarman su je maka su samu matsiyacin uban yarinyar amma daga karshe dubi abinda yayi ma masu, nasan su kansu za su ga sun zubda mutuncinsu gaban mutumin da bai wuce drebansu ba” Alhaji Musa dai girgiza kafa kawai yake don shi kansa halin da Abdul ke kokarin jefa kansa ciki ba karamin damunsa yake ba, ya kira Malam Ali yayi sau uku tun ma lamarin Abdul din bai yi worst haka ba amma bai daga kiransa ba bai kuma biyo sa ba, har yayi zuciya ya goge numbersa, da ya ga dai Abdul bazai taba hakura ba yasa ya hada kan manyan abokansa ya turasu kamar yanda Momy ta basa shawara amma duk da haka babu wani fruitful result, mikewa Momy tayi ta fita daga dakin ranta a dagule ta tafi dakin Meemah, cike da damuwa tana kallonta tace “Meemah yanxu menene shawaranki akan wannan hali da dan uwanki ke kokarin jefa kansa? Yanxu haka fa tun jiya da safe yaki bude daki, ba ci ba sha, ban san wani hali yake ciki ba, tsorona kada wani abu ya samesa fa in shiga uku Meemah shikenan gare ni a duniyar nan” Sai kuma ta zauna gefen gado ta dafe kai ta fashe da kuka sosai, Meemah ta sauke ajiyar zuciya, ita fa ko kadan halin da Abdul ya jefa kansa ba wani damunta yayi ba in dai akan er talakawan can ce, ace duk class da girman kai irin nasa amma kan er matsiyata ya nemi maida kansa kamar mahaukaci zautattace, Cikin rawan murya Momy tace “Wallahi kwanaki da naga abun nasa yaki ci yaki cinyewa har kudi na bada a min aikin da zai maido hankalin yarinyar kansa amma a banza Meemah, in ba dai zuwa zan yi in tone abinda nace maki an bani na binne a garden ba in kone su” Meemah ta wani kalleta, can tace “Kema dai wallahi Momy, ki tone me kuma? Don Allah ki rabu da Abdul zai dawo dai dai nasani, lallai ne sai mutum ya samu abinda ya kwallafa rai dama in ba don yaga kuna biyesa ke da Daddy ba, ai abun nasa har da iskanci, ita kadai ce mace a duniya bayan ga mata wa enda ma suka fita komai” Wani tsawa Momy tayi mata tace “Tun ba yau ba nasan baki da imani baki da tausayi Meemah, kuma mugun nufinki akan Abdul sai dai ya kare maki wallahi, in dai dawowar yarinyar garesa ne zai dawo masa da farin cikinsa to ina maraba da hakan wallahi, da nasan wannan abun ne zai biyo baya yaushe har zan raba su ta karfi da yaji?? Ai da sai dai in ta gana mata azaba a gidan nan, amma ina neman rasa yarona akan mace kice kar in damu, to wallahi zan je in tono layun in Kona, sannan in har sato ta ne kadai mafita ni da kaina zan basa shawaran yayi hakan, dama wancan karan ma ai sato ta din yayi daga Lagos, ko ba a daura auren ba ya tafi duk inda zai tafi da ita kawai, yanxu ai jin kan ta take budurwa shi yasa zata yi ta iskanci tana rawan kai, kawai na cuci da na a banza a hofi saboda dalilina mara tushe” Tana kai wa nan ta fice daga dakin, Meemah ta wani kyabe baki tana ci gaba da danna wayarta, da wuka Momy ta tafi garden din kamar dai zata yanko vegetables, tayi bake bake ta tona ramin da ta binne layun ta ciro tana kare masu kallo, sannan ta tafi kitchen zata konasa saman gas… Tun da Khaleesat ta sanar ma Jay mutanen da mahaifin Abdul ya aiko wajen Babanta hankalinsa bai sake kwanciya ba kamar yanda nata hankalin ke a tashe tun daren jiya, gaba daya yaji zaman Abujan ma kamar a kaya yake, at first bata ma gaya masa ba sai da suna waya da yaji mood dinta da yanda take responding sai ya tambayeta abinda ke damunta shine har ta gaya masa, bayan la’asar Ajay ya shigo daki rike da Glass cup na Smoothie da Ammi tayi masu, ya ajiye ma Jay nasa yana kallonsa yace “Anything?” Jay ya kallesa kamar bazai ce komai ba, after a while kawai ya gaya nasa abinda Khaleesat ta sanar masa, Ajay yayi shiru na kusan minti daya after listening to Jay, can ya kallesa yace “I think kawai ka samu Mai martaba da maganar, since Mami ta nuna maka she is fine with ur choice, gobe da safe sai mu koma Bauchi ka gaya masa ta amince…. But i will advise you duk yanda ku ka yi da Mai martaba kar ka gaya ma Mami, don nasan shi idan ya tashi zartar da ko wani hukunci sai ya gama zartarwa yake sanar da kowa” Jay dake kallonsa yace “Amma me yasa kace kar in gaya ma Mami yanda muka yi da Mai martaba?” Ajay yace “Just an advice, Ina ga kamar in baka gaya mata ba process din zai fi tafiya smoothly kuma da sauri, baza a tsaya wasu sirfa ba or anything of such, You know our mothers and exaggerating of things” Jay dai yayi shiru bai ce komai ba, Ajay ya dan yi murmushi yace “Dama nasan gayen nan bazai hakura ba, and he can do anything silly, I don’t even think she is safe in kano….”

Back to top button