Description/Story:
Kayar Ruwa Book 1 Complete Hausa Novel Document Written By Nana Halima
Description
_A wasu lokutan da bamu tsammaci rikicewar al’amura ba, sai ya zamana al’amuran sun runcaɓe mana babu zato babu tsammani. rayuwa kan canja tayi juyayi da mutum, wasu ta juya da su duniyar rikicewa, firgicewa da tashin hankali har mutum kanji tamkar shi kaɗai aka tsana, yayin da a gefen wasu juyin rayuwa kansa su mance da baƙin ciki, haushi, da damuwa, su dulmiya a jin daɗin rayuwa. babu abin da bai da farko, babu abin da bai da asali, haka babu abin da bai da tushe, kazalika babu abin da bai da ƙarshe, sai dai yarda da Allah kan tafiyar da komai cikin daidaito._
_kamar dai yanda darasi ya ke a matsayin koyarwa da miƙa saƙo, hakan yasa a yau zan rubuta labarin rayuwarmu, sunana Sa’ida Salman, kuma wannan shi ne labarin ƘAYAR RUWA…
________________________________
Kwance na ke akan makeken italian royal bed a cikin tamfatsetsen ɗakin barcina. Wayata ƙirar S22 na gefena ina sauraren karatun alqur’ani mai girma cikin ƙira’ar Muhmood Hosary, idanuwana a lumshe suke tamkar mai bacci, sanyin acn da ke busawa na bin dukkan ƙofofin gashin jikina, yayin da gefe guda hancina yake shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren wutar da na kunna a burner wanda ba ya ko ƙaurin kamawa saboda irin salon yanda nake bi wajen sanya shi.
Sanye na ke cikin doguwar rigar material mara nauyi, rigar na ɗaya daga cikin sutturun da nake so sosai a kayana duk da material ɗin ba wai mai tsada ba ne, fuskata fayau babu kwalliya ko ɗiso, sai hakan ya ƙara fito da ramar fuskata.
Gaba ɗaya yau jina nake yi kamar mara lafiya kuma kaman an yi min mutuwa, sai dai babu ko ɗaya a ciki, tun safe da na tashi bakina babu ɗanɗanon komai ga tsananin faɗuwar gaba na damuna, hakan yasa tun lokacin nake ta adu’oi da tasbihi, kuma karatun ƙur’anin da na kunna ina saurare ina bi shi yake d’ebe min kewa, to amma dai duk da hakan ina ji a jikina cewar akwai wani babban al’amari da zai girgiza duniyata nan kusa, ina jin kamar nan kusan zata zamar min ƙarshen komai na rayuwata ne.
Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi, na juya kwanciyar da nayi inda a yanzu na ke fuskantar bakin ƙofar shigowa, cikin zuciyata ina roƙon ubangiji da yasa komai zai faru ya zama alkhairi, ya kuma ba ni ikon cinye kowacce kalar jarabawa da iya ɗaukan ƙaddara.
zoben azurfar da ke hannuna na ke ta kallo ina jin wani abu mai girman gaske na tsarga min, yayin da tunanin wasu shekaru yasa fuskata ƙwacewa da murmushi mai faɗi, murmushin da za’a kira shi da na yaƙe.
Wayata na ɗauka don duba lokaci, ƙarfe biyar da mintina na yamma ya nuna min, zaune na miƙe da mamakin gudun lokacin a cikin raina na furta “har biyar?, Lallai duniya na gudu, Allah kasa mu cika da imani”.
Da azama na zuro ƙafafuna ƙasa ina gyara ɗaurin ɗan kwalina, ji nake kamar zan faɗi saboda rashin ƙwarin jiki, kaman wadda ta sha zawo ya zabgar da ita a yini ɗaya. Tsayuwa nayi gaban tafkeken madubin ɗakin na tsaya ina ɗaukar tissue in shiga goge kwantsar ciki saboda ciwon idon da nake fama da shi daga shekaran jiya zuwa yau.
Kallon kaina na tsaya yi a cikin madubin, lallai in har akwai rayuwa da shekaru to tabbas akwai sauyi, gaba ɗayana kamar ba ni ba, kallo ɗaya da zaka min ba sai ka ƙara na biyu ba zaka ga zallar ƙuruciyar da ke kan fuskata, wanda zai bayyana maka cewar shekaruna ba su da yawa. Sai dai kuma in har kayi min farin sani a baya, to a yanzu zaka ce na sauya, ba wai sauyi na ɗabi’a da halayya ba, a’a sauyi na halittar jiki. A baya ni ɗin ƴar duma duma ce mai kyawun dirin jiki tubarakallah, ina da irin jikin nan da babu kalar damuwa balle yunwa, saɓanin yanzu da ko’ina a jikina ƙashi da jijiyoyi ne suke magana, ido kuwa ramar da ta fito da shi waje yanda kasan na mujiya, gefen kumatuna duk ya zurma ciki, shi kansa uban hasken da nayi ba na komai ba ne sai na shegiyar ramar da nayi, albarkatun ƙirjina kuwa duk sun kwanta shalaf kamar wacce ta shayar da ƴaƴa ɗari, duk na zama wata babu kyan gani kai baka ce me tashen ƙuruciya ba shekaru ashirin da huɗu a duniya.
Lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawaye, sai dai basu sami nasarar zubowa ba, cikin yanayi na bala’in tausayin kaina na sunkuyar da kaina ƙasa ina jin wani dunƙulallan abu na tsaya min a maƙogoro yaƙi wucewa, hakan sai ya zama famin ciwo a gare ni, wanda da zan samu in korashi da yawun bakina ko kuma ya wuce da kansa wataƙila da na sami sassauci. Cikin ƙarfin halin da na saba na ɗago kaina ina mayar da tarin ƙwallar da ta cika min ido, ɗakin kawai nake bi da kallo, ko a iyaka shi aka bar bawa rayuwa ya ishe shi jin daɗi da more rayuwa, damuwarsa ta gushe, ballantana kuma ace rayuwa kake yi a cikin tamfatsesen gidan nan da yake sai kace a ƙasashen turawa, lumtsum nake a cikin daula, duk wanda yazo gidana ba ya son tafiya, iya dukiya dai an narkata wajen ginin gidan, zaka rantse da Allah ba duniyar da talakawa ke rayuwa ba ne, idan ba Allah ya soka da rahma ba sheɗan sai ya shagaltar da kai da yin ibada.
Sau tari ƙawayena da ƴan uwana kan ce min ke kam Sa’ida kin more, ba ki da saurin baƙin ciki da takaicin duniya domin Allah ya kashe ya ba ki, arziƙi ta ko’ina, kalli gidan da kike ciki kamar ba za’a mutu ba, irin motocin da ake fita da ke a cikinsu zamansu kaɗai yasa kiyi ƙiba ki fresh, abinci kullum da nama, ke kam ba ki da sauran damuwa, ba su san da cewa ba anan take ba wai abin da yawa mutuwa taje kasuwa, sai da kwanciyar hankali ake jin daɗin.
Madubin da ke gabana na kalla da kyau, na sauke babbar ajiyar zuciya tare da yin murmushi mai ciwo, ina mamakin masu faɗa min irin wannan zantukan, ban sani ba ko iyaka daular da Allah ya ajiye ni a ciki kawai suke kallo shiyasa ba su taɓa lura da cewar akwai ƙalubale mai wahala a gefe, bana jin daɗin gidan, bana farin ciki sam, su ka kasa ganin irin lalacewar da nai, su ka kasa fahimtar gwara ma rayuwata ta baya akan ta yanzu, su ka kasa fahimtar ina da buƙatar taimakonsu. Su na ganin cewa zan iya yi musu komai tun da su na kiran wannan ƙaton gidan da gidan Sa’ida, ba su san cewar babu abin da zan iya, domin ba ni da komai, tun da komai ɗin da su ke kallo ba mallakina ba ne ba taƙamata ba ne.
Ƙwarai kuɗi da rai da lafiya rahma ne, kuɗi komai ne bayan lafiya, babu abin da yafi ace yau kafi ƙarfin komai, ace yau kai ne kake ɗauka ka bayar ba wai a ɗauka a baka ba, kaci mai kyau kasha mai kyau ka kwanta a mai kyau kasa sutturu masu kyau da tsada, ka hau jirgi ka keta hazo zuwa in da kake so, ka ɗiba ka kashe babu mai ƙayyade maka, kayi mu’amala da mutanen da su ka fika. To amma me?, duk da irin tarin dukiyar da kake da ita, da irin daular da kake rayuwa a ciki, muddin babu kwanciyar hankali to babu farin ciki da jin daɗi. Ni a wurina gwara in rayu cikin talauci akan ace ga tarin dukiyar amma babu zaman lafiya babu kwanciyar hankali balle na sami natsuwar zuciya…
File Name | Kayar Ruwa Bk 1 Hausa Novel Doc. |
Title | Kayar Ruwa… |
Author | Nana Halima |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | True Life Story |
Published Date | 24/01/2024 |
File Size | 445Kb |
Format Size | TXT |
Phone No | 09030398006 |
Download Kayar Ruwa Complete Novel Document By Nana Halima
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.