Hausa novels

Mejo Najeeb Page 46 By Autar Alheri

“Maryama. Wani irin faɗuwa gaban Ammi yayi arazane yaɗago tana kallon ma mallakin Muryar kamin tabuɗe baki arikice tace *ABBAN JAZLAN* sehawaye sharr a idonta suka wanke mata fuska…amugun rikice Abba yaƙarasa gareta tare da riƙo hannunta, sekai yasaki kuka yana faɗar “itace wlh Alhaji Abubakar zokaga Maryama ce bagizone takemun ba wlh Allah Maryama ce, sekuma yasake rushewa da kuka. “, Subhanallah Alhaji wai mike faruwane? Wacce Maryama kake nufi? Badai Ammin najeeb ba?? Yatambaya cikin mamaki. “itace Alhaji wlh Ammin najeeb ce itace dai Maryamata ya Allahh.Duk wanda ke wurin mutuwar tsaye yayi daga su mejo harsu ummi da isseta dakuma innar halima, hakama mama bintu mlm Musa kowa kallon ikon Allah yakeyi. “Ikon Allah dan Allah bawan Allah kuzauna seku mana bayanin suwaye ku yafi wannan tsayuwar duk kun sakamu a duhu, cewar innar halima datake ƙoƙarin yimusu shimfiɗa. “Hakane kam gaskiya kuzo muzauna aikuma bazancen tafiya yanzu Alhaji Abubakar yafaɗa yana ƙoƙarin zama.. dukkansu zama sukayi amma daƙyar Alhaji Abubakar yasamu Abba yasaki hannu Ammin isseta. Kowa yayi jugun anrasa me magana se can Alhaji Abubakar yace “Alhaji khamis nifa kaɗauremun kai a iya sanina Maryama tarasu kamar yadda kagayamin aranar sunan ummi sekuma yanzu kace gata miyake faruwane hakan? Wani sabon kukane yazowa Alhaji khamis me taɓa zuciya cikin kukan yace “Maryama bata mutuba Alhaji ɓata tayi Bara kaji yadda muka rasa Maryama.Mukoma baya kaɗan Alokacinda Alhaji Idris ya aurawa Khamis ƴar shi awannan lukacin ne shikuwa abdussalam ya auri Hajiya Hannah idan baku mantaba bayan rasuwar Alhaji Idris khamis yabar Niger garin maraɗi yakoma Nigeria mukace abisa wani al’amari megirma daya faru, wannan al’amarin bakomai bane face ɓatan matarshi Maryama yar Alhaji Idris daya aura Mishi kuma ƙanwar Alhaji abdussalam. Bayan rasuwar Alhaji Idris wata ranar Laraba sun kwanta lafiya qalau shida Maryama da jinjirin ɗansu najeebullah amma koda garin Allah yawaye basu tashi da Maryama ba batagidan annemeta sama da ƙasa anrasa kumaga jinjirin ɗa tabari. Wannan ɓacewar ta Maryama baƙaramin tada hankalin mijinta da alahalinta yayiba sunyi neman duniya ba’asametaba. Bayan shekara ɗaya da ɓatan Maryama Alhaji khamis ya ɓullo da zancen auren jamila ƙawar Maryama, hakan yace abdussalam yace idan kuwa ya’auri Jamila tobaze yadda tariƙe najeeb ba domin kuwa tun ɓatan Maryama Safiyya ke kula dashi wadda takasance ƙanwace a gun Maryama cousin sister ɗinta ce sabida hakan baze kwace shi agareta ba yabashi….jin hakan yasa khamis cewar to ze auresu su biyu inyaso Safiyya tacigabada renon nejeeb har Allah ya bayyana mahaifiyarshi. Daga hakan kuwa aka aurawa Alhaji khamis Jamila da Safiyya suka zauna anan gidanshi dake tare da na abdussalam Safiyya nacigabada kula da najeeb…kwatsam wata rana Alhaji khamis yacewa Alhaji abdussalam zekoma Nigeria dazama baze iya zama ananba kullun Maryama kemishi gizo..sosai Alhaji abdussalam yatausayawa khamis domin yasan yanason ƙanwar tashi sosai…hakan Alhaji khamis yakwashi iyalanshi suka koma Nigeria a lokacin Hajiya Hannah na goyon nazeer itako Safiyya na goyon najeeb.Bayan suntafi Nigeria zama yaƙi daɗi tsakanin Safiyya da Jamila makircin yau daban na gobe daban daga ƙarshe Alhaji khamis ya karɓe najeeb daga Safiyya yabawa Jamila. Ana cikin hakan Jamila tahaifi munir tahaɗasu shida najeeb tana reno daga baya Safiyya ta haifi sajad sesuka taso kamar yan ukku najeeb ne babba…duk wannan abun da akeyi Alhaji abdussalam besan cewar Alhaji khamis yakarɓe najeeb daga Safiyya ba domin harkawo wannan lokacin Alhaji khamis nazuwa Niger wurin Alhaji abdussalam suna zumunci..daga baya ne yadena zuwa gaba ɗaya. Ana cikin hakan Safiyya taƙara haihuwar ƴamece. Aranar suna yasakawa yarinyar sunan matarshi wato Maryama amma yahana kowa yakirata da hakan sedai ummi…. alokacinda aka haifi Ummi awannan lukacinne Hajiya Hannah tahaifi Tata ƴar itama aka saka mata Maryama. Kunga kenan daga isseta har Ummi sunan mahaifiyar najeeb ne sukaci, hakan yasa itama nata yayun ke kiranta da lattey sabida sunan gwaggo su ne data ɓata Maryama taci….acan Nigeria kuwa gabaki ɗaya yaran gidan suna kiran Jamila da umma, Safiyya kuma mama, hakan yasa suka maidasu Hajiya umma da Hajiya mama…bayan shekaru sunɗan tafine Jamila ta haifi mace itama yasaka mata Maryama wannan abun baƙaramin baƙin ciki yayiwa Jamila ba hakan yasa tamayarda Ƴar Tata siyana( kufahimta siyana daban siyama daban wannan siyana ne) acewarta abin yazama hauka duka yara biyu suna ɗaya. To daga wannan lokacin kuma se zancen Maryama yafiya a kan Alhaji khamis cigiyarta ma dayake bada sadaka anayi yadena yaɗauki tsanar duniya yaforawa najeeb kuma ya ƙauracewa Niger sam har izuwa wannan lokacin.Gawanda ya manta ya duba acikin page 23 & 24 inda muka bada labarin mejo najeeb zefahinta.Tunda Alhaji khamis ya fara magana wani irin zufa kewankewa najeeb fuska dashi har isseta hakama mama bintu da mlm suma dama su general Aliyu, general Faruk kuwa tasbihi kawai yake yiwa uban giji….Ammin isseta kuwa kuka kawai takeyi itada halima dasu Ummi amma isseta kam ba bakin kuka, aranta take maimaita kenan amminta gwaggonta ce ƙanwar mahaifinta shiyasa take mugun sonta? kuma yanzu takasance Uwar mijinta? Toba isseta ba duk wanda yaji labarin isseta yaji wannan na Alhaji khamis yafahimci hakan ammin Isseta ƙanwar Alhaji abdussalam ce kuma mahaifiyar mejo najeeb.. “ikon Allah kenan wanda yafi gaban mamaki kenan kece Maryama ƙanwar mijin Hannah, mama bintu tafaɗa cikin mamaki. Azabure Ammin isseta tace “wlh nice baiwar Allah kinsan Hannah ne kinsan TANTI? Tana ina ahalin yanzu? Tana lafiya ? Ina nazeer? Ina yayana? Ina jazlan? Dan Allah kukaini garesu inaso naji ɗimin ahalina atare dani dan Allah, taƙarasa zancen cikin kuka….Abba ne yashare hawayen idonshi yariƙo hannun mejo tare da isseta yakawosu gabanta, nata hannun yariƙo yasaka nasu, “kinjima kinajin ɗimin ahalinki Maryama wannan yarinyar yar Alhaji abdussalam ce wannan kuma shine jazlan ɗinki…wani irin waro ido ammin Isseta tayi baki na rawa tace”da.dama Maryama ƴar TANTI ce? Jazlan ne wannan? Tafaɗa arikice sekuma kuka tahaɗesu duka biyun tana rusa uban kukan dake fita tun daga ƙasan zuciyarta,, ɗan da tabari tun yana cikin zanen koyon shi shine yau agabanta amatsayin cikakken mutun, ƴar da kocikinta bata bariba aduniya itace ta temaki rayuwarta tazama jigo agareta, tajima rungume dasu tana kukan itama Isseta kuka takeyi sosai. Ahankali mejo yazare jikinshi daga nata kana yasa hannu yajanye matarshi. Tsitt kowa yayi yana kallonshi da mamaki ɗauke akan fuskasu. “Lafiya dai najeeb cewar Alhaji Abubakar?? “Ɗan kauda kanshi yayi gefe kana yace “lpy qalau Dady tunɗazu munyi maganar zamuje gidan gwamna lokacinda aka bamu yakusa ƙarewa yadace muje domin Ni ayau zan koma Lagos da matata akwai aikinda ke banmu nida su bros gobe. Baki Abba yabuɗe zeyi magana cikin sauri Alhaji Abubakar ya dakatar dashi tahanyar ɗaga Mishi hannu. Kallon ammin Isseta yayi yace “Maryama kuzo muje gidan gwamna dama wani al’amarine me mahimmanci zekaimu domin Alhaji abdussalam da iyalanshi sunacan shiyasa zamuje yanzu kuwa tunda wannan zancen ya ɓullo kizo muje tare duka sekigansu ko…aitunkamin yakai ƙarshen zancenshi tamiƙe tsaye tana faɗar mujeto. Murmushi ƙarfin hali mama bintu tayi, aranta tana jinjina girman farin cikin da ahalin Alhaji abdussalam idis zasu shiga idan sukaga Maryama da Maryama sun bayyana garesu alokaci ɗaya.Ahakan suka ɗunguma dukkansu zuwa gidan gwamna kowa ba’abariba….general Aliyu dasauri yabu ɗewa halima motarda zeshiga yasaka ta ganin mejo yashiga mota ɗaya shida isseta se security ɗinshi…..murmushi general Faruk yayi shiko yabuɗewa ummi yasakata cikin wadda zeshiga, hakan yasa mufeedah Turo gaki gaba domin itafa ako ina take seta nuna taɓararta. Abba ne yariƙo hannunta yasakata atasu motar domin dukkansu sun ɗora ayar tambaya akan ƴaƴan nasu suna nufin kenan kowanne ya fidda gwaninshi kenan. Murmushi Alhaji Abubakar yayi yana girgiza kanshi, ahakan suka nufi gidan gwamna tare da fatan samun nasara akan iyayen Maryama karsu rabata da mijinta.LagosWata irin muguwar zabura Hajiya umma tayi alokacinda Abba yaga Maryama sabida faɗuwan dataji gabanta yayi da mugun ƙarfi. ahaukace tanufi ɗakinta na sirri sedai tana zuwa tun bata kira tsijuju ba ya bayyana agareta cikin wani irin hargowa yake faɗar “kinyi sake jamila kinyi sake seda nagaya Miki kiyi kaggawar aiwatar da naki aikin kafin gimbiya mardeeya tayi nata amma kikaƙi gashi yanzu ta ɓata Miki komai tanadin shekara da shekaru yarushe dama nagaya Miki tsuntsuwa naneman dawoma shekartaaaa, to yanzufa tadawooo najeebullah ya kusanci wata kafinkeee kuma khamis da Maryama sun haɗuuuuu hhhhhhhh hhhhhh hhhhhh yaƙasara zancen yana kecewa da wata irin mahau kaciyar dariyar basawa, kana yadubi Hajiya umma da jikinta ke tsuma tunda yafaɗi waƴannan kalaman yace “dama seda nagaya Miki kiguji zuwan wannan ranarrr bakijiba yanzu dama ɗaya tak gareki karki bari Maryama tashigo gidannan araye kuma kiyi ƙoƙarin samun maniyin najeeb koda sau ɗaya ne kuhaɗu turmi da taɓarya sa’annan kikawomin maniyin idan kuma akasamu matsala to duk abinda yabiyo baya kikuka da kankiii hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhh hhhhhh, haka yaɓace ɓatt yana wannan muguwar dariyar kamar ze tsaga ɗakin…amugun rikice Hajiya umma tafito daga wannan ɗakin tanufi bedroom ɗinta mayafinta kawai taɗauka tafice daga gidan, ko driver bata nemaba taɗauki mota tabar gidan cikin azababben gudu..GombeAcan gidan gwamna kuwa sosai suka samu tarba daga megirma gwamna jihar Gombe da ahalinshi, bayan angama gaisuwane akayiwa Alhaji abdussalam iso zuwa perlor dasuke…yana shigowa perlor zuciyarshi tafara bugawa da ƙarfi hakan yasa yafara addu’a harya isa Tsakiyar perlor idonshi ne suka sauka akan Alhaji khamis cikin mamaki yaƙara warosu waje tare da sakin murmushi yace “Khamis damakaine tafe? Gaskidai naji zuciyarta na bugawa ashe ɗan uwanane zangani dudda cewar kayi fatali dani yafaɗa cikin murmushi, adede lokacin Alhaji khamis yaƙaraso gareshi suka rungume juna, “kayi haƙuri ɗan uwana ba’ason raina nadena zuwa Niger ba kuma bansan miyasha kainaba. Ɗan murmushi Alhaji abdussalam yayi alokacinda suke raba jikinsu dana juna yace “Nima nasan hakan khamis karka damu Allah yabamu ikon bibiyar zumunci ina ɗana najeeb koshi baka kaimin ingani…riƙo hannunshi yayi yace Bama najeeb ba yau har uwar najeeb zaka gani. Baki sakeAlhaji abdussalam ke kallon Abba cikin mamakin maganarshi amma sam aranshi bekawo Maryama yake nufiba. Seda sukazo dede gun ammin Isseta Abba yasaki hannunshi kafin yayi magana yaji saukar muryar ƙawar tashi babu zato babu tsammani tace “yaya abdoul. Amugun razane yakai dubanshi gareta tare da zaro duka idanunshi yana nunata da yatsa yama kasa magana sekawai yayanke jiki yafaɗi a sume. “Innalillahi wa’innailaihi raji’un suka faɗa arikice sukayi kanshi cikin sauri general Aliyu dake riƙeda robar ruwa ya ɓalle ta tare da miƙawa Abba yashafa Mishi har sau ukku tukunnah yaja dogon numfashi tare da ƙoƙarin buɗe idonshi, still suka sauka akan na Ammi dake gurfane kusanshi tana kuka. Rufesu yayi dasauri yariƙo hannun Abba “khamis kagayamin gaskiya dan Allah gizone Maryama kemun kokuwadai aljanace nake gani? Ƙwallah Abba yashare kana yace “ba aljana bace ɗan uwana bakuma gizo bane Maryama daice daka sani itace kake gani. “Haba khamis tayaya kakeso na yadda dakai? Maryama ta ɓata samada shekaru 30 yau kawai kacemun Maryama ce na yadda? Dan Allah idan har wasa kazo yimun kadena kar zuciyarta tabuga ayanzu hakama danake cikin wani tashin hankalin nake domin ƴata taɓata kamar Maryama itama ina neman rasata hankalina atashe yake khamis banaso narasa little Maryama kamar yadda marasa gwaggonta please karka karyamun zuciya. Duk wanda ke wurin yaji tausayin wannan dattijo domin duk meraunin zuciya seya zubda hawayenshi…cikin kuka sosai Ammi tariƙo hannun yayan nata tace “yaya abdoul nice Maryama ɗinka baka rasaniba nice dakaina ba aljanaba awancan lukacin ma ƙaddara ce tarabani dakai amma in sha Allah bazaka ƙara rasaniba itama Takwarata bazaka rasataba gata ataredani tafaɗa tana saka hannun isseta cikin nashi….da kallo yakebinsu daga ita har Isseta dake kuka, kusan minti 2 kafin yamiƙe azabure yahaɗasu duka yarungume tare da fashewada matsanancin kuka..se ayanzu Hajiya Hannah data dasƙare awurin tadawo hayya cinta saka mako taɓota da mama bintu tayi. Ahanzarce itama tahaɗasu duka tasaka ajikinta tana kuka meban tausayi, “Maryama kece dama kina raye baki mutuba Maryama kuma kindawo tare da ƴarki itamafa ɓata tayi kamar ke Maryama yau kuma dukkanku kundawo garemu, alhmdlmulillah Allah alhmdlmulillah, shine kawai abinda Hajiya Hannah ke maimaita wa. Sunjima ahakan sunata kuka kafin Suɗan saki juna Alhaji abdussalam yajuya yana waige waige ga dukkan alamu wani abun yake nema acan yahangosu tsaye suma suna kuka ganin iyayen nasu na kuka, da hannu yayi musu aladasuzo. Ba musu kuwa nazeer da Safwan suka ƙaraso wurin. Cikin farin cikin dayakasa ɓoyuwa agareshi yace “kuna ganin abinda nake gani sapwan gwaggo ce da ƙanwarku yau duka gasu agabanmu Allah yadowo muna dasu. Dukkansu ba wanda yace Mishi komai inba sapwan ba dayariƙo Isseta yana kallonta tundaga sama har ƙasa sekawai yarungumeta ajikinshi yana sauke ajiyar zuciya….nazeer ma Ammi yarunguma cikin Muryar kuka yace “gwaggo. “Na’am yarona nazeer kaine ka girma hakan? Masha allah dakai da jazlan ɗina duka kunzama zaratan samari dama kanku ɗaya wayyo Allah nagodema daka dawo dani cikin ahalina… Alhaji abdussalam naji ta ambaci najeeb yayi saurin duban Alhaji khamis yace “khamis ina najeeb yau Allah ya haɗa min kan ahalina shima inaso naganshi dan Allah kakirashi yazo nan.. Murmushi Abba yayi yana share ƙwalla sa’anan yajanyo mejo batareda yace komaiba yasa hannushi acikinna Alhaji abdussalam, “ga najeeb nan ataredakai ɗan uwa, yafaɗa cikin murmushi. ido Alhaji abdussalam yazaro cikin mamaki yake nuna mejo yace “Hannah kinganiko yaron danace Miki sunzo office na shida abokinshi daga cikin sojojin Nigeria ashe ba’abanza yatsayamin araiba yaronane Hannah najeebullah ne ɗan wurin Maryama da khamis ɗina, wayyo alhmdllh Allah ashe jininane shiyasa tunaninshi yakasa barin raina. Dasauri duk suka ɗago suna kallon mejo dayayi Bala’in haɗe rai. “Ikon Allah dama shine kake bani labari? To ai ranka yadaɗe cewa kawai kayi bakagane ina kasan fuskarshiba ai dakai yake kama domin baya Kamada ƙanwata,,,tafaɗa dasigar wasa domin wani irin farin ciki takeji aranta…dan waro ido yayi kana yace “au hakane kuma fa amma wlh awancan lokacin sam bakulada hakanba, ikon Allah kenan.Murmushi megirma gwamna yayi shida Alhaji Abubakar dake gefe tunɗazu suna kallonsu cikin tausayi da birgewa bawanda yace komai a cikinsu seyanzu da gwamna yayi magana, “to ranka yadaɗe please kukoma saman kujera kowa yazauna kar masu aiki sushigo susamu gudan shugaban Niger aƙasa dagashi har iyalanshi, yafaɗa cikin sigar wasa. Kowa seda yayi murmushi amma banda mejo da isseta itadai hankalinta nagun mijinta ganin yadda yayi ne yasa itama tahaɗe ranta domin batasan mike damunshiba jitakeyu kamar taje ta rarrashi abunta. “To ai anan yafi daɗi Alhaji bakomai kosun sameni acikin ahalina nake nafi jin daɗi anan domin inaso naji ɗimin kowannensu atare dani, cewar Alhaji abdussalam, to kawai tace, yaɗago yana kallon general Faruk dake gefen general Aliyu sunyi shiru suna kallon abokin nasu cikin damuwa ganin yadda yayi dudda wannan abin farin cikin dayasameshi. “General Faruk kaga Maryama ko kagansu duka Allah ya dawo dasu gareni. Murmushi general Faruk yayi kana yace “hakane ranka yadaɗe ina matuƙar tayaka murnar samun farin cikinka acikin ahalinka ai dama bansan maryam bace yarka dakeke nema domin tuni naganta cikin aminci da ƙoshin lafiya shiyasa sam banyi tunanin ita bace duba cewar a Gombe ta ɓata itako wannan a Lagos nasanta…murmushi mekayatarwa Alhaji abdussalam yayi amma bece komaiba….shikuwa mejo jira kawai yakeyi ayi zancen aurensu da isseta yaɗauke matarshi yayi gaba danshi Bega amfanin wannan surutunba, amma ganin sunma manta da abinda yakawosu yasa yamiƙe daga jikin Alhaji abdussalam ahankali yariƙo hannun isseta dake lafe ajikin sapwan cikin Cool voice ɗinshi yace “muje maryam. Ahankali yamiƙe zatabi mijinta. Cikin mamaki Abba yace “kuje ina najeeb? “Gida yafaɗa ataƙaice…wanne irin gida kuma wai mike damunkane son naga duk kakoma wani iri daban? Cewar Abba cikin damuwa. “Bakomai kawai zamu tafine, yafaɗa tare da fara tafiya daga wurin. “Dakata najeeb, tatsinkayo Muryar Dady. Ahankali Alhaji Abubakar yaƙaraso wurinda yake tsaye yariƙo hannun isseta yamayarda ita tazauna kana shima ya zaunada shi, kwaɓe fuska yayi kamar zeyi kuka yace “Dady please. “A’a najeeb bawani please kagaya min mike damunka kaida yadace ace kana farin ciki yau Allah ya bayyana maka mahaifiyarka bayan tsawon shekaru amma kaɓata rai se ƙunci kakeyi tun wancan gidan naga yanayinka barinkane kawai nayi yanzuma baka sauyaba minene damuwar? Shiru yayi kamar bejiba yakasa cewa komai se sauraren yadda zuciyarshi ke ƙuna yakeyi. Cikin ɗan tsawa Abba yace badakai ake maganaba najeeb zaka maidamu sa’aninka. Ahankali yaɗago yana kallon mahaifin nashi kana yabuɗe baki cikin ƙunarda yakeji a zuciyarshi yace…!

Back to top button