Uncategorized

Yar Jarida Chapter 1

 ‘YAR JARIDA…  1

© Alhassan Auwal Dambatta

***

LITININ 5:40am

Sannu ahankali wata zankadediyar mota samfurin Lexus mai launin sararin samaniya tayi parking acikin tsakiyar dokar daji

  A wannan lokaci na duku dukun safiya babu wani sauti da kunne ka iya saurara face kukan kananan dabbobi da tsuntsayen dake saman dogayen bishiyun da suka yiwa dajin kawanya

Bayan da motar ta tsaya da kamar sakanni arba’in saiga wani kyakkyawan matashi ya fito sanye cikin bakaken tufafi ya rufe kansa da hular sanyi, hakanan kuma ya daure hancinsa da bakin hirami rabin fuskarsa kadai ake iya shaidawa.

Yakai kusan minti bakwai yana zagaye motar tasa yana cizon yatsa kamar mai tunanin wani abu.

 Daga can kuma sai ya tsaya cak ya soma karewa dajin kallo har izuwa lokacin da ya hango wani wakeken rami mai zurfi a can gabansa wanda ga dukkan alamu anan ne duk wani ruwan sama da akayi acikin dajin yake tattaruwa

Lokaci guda yayi wani murmushin mugunta ya koma cikin motar da sauri ya tuka ta zuwa daidai bakin gab’ar wannan rami yakuma bude booth din motar ya soma kiciniyar fito da gawar wata kyakkyawar budurwa yar kimanin shekaru goma sha takwas wacce ke sanye cikin doguwar riga fara samfurin Pakistan

Gaba daya gaban rigar ya rine da jini tamkar wacce tayi Accident, saidai ga dukkan alamu bazai wuce fyade aka yimata ba domin babu wata alama mai karfi dake nuni da samun rauni a gabobin jikinta.

 Cikin azama ya azata bisa kafad’arsa yayinda iska mai karfi ta soma kadawa kyakkyawan bakin gashin kanta yana tarwatsewa.

Cike da jarumta ya soma takawa zuwa gaban wakeken ramin duk kuwa da yanda zuciyarsa ke faman bugawa kamar zata faso kirjinsa ta fito domin gaba daya a tsorace yake, ji yake a ransa kamar asirinsa zai tonu duk da yayi imanin shi kadai ne cikin dajin a wannan lokaci.

Kyakkyawar matashiyar dake lab’e a can bayan wata bishiyar dorawa dake can nesa a yammacin dajin ta share hawayen da ya zubo daga idanunta saboda tausayin halin da gawar waccan matashiya take ciki wacce wani tantirin matashi marar imani ke shirin jefarwa, wanda kuma ga dukkan alamu shine sanadin ajalinta, gashi kuma zai hana ayi mata sutura irin wacce ake yiwa Kowanne musulmi idan ta Allah ta kasance dashi

Zai yasar da ita acikin dokar daji kamar wani mushen dabba a karshe ta zamo abincin beraye da tsuntsaye.

 Lallai wannan ba karamin rashin imani bane.

Cikin gaggawa ta fiddo Camera daga cikin karamar jakar dake rataye a kafadarta, ta soma yimasa hotuna barkatai har izuwa lokacin da ya jefa gawar cikin ramin ta dauki komai hatta motarsa kusan kati bakwai tayi mata don yadda take son isarwa al’umma kyakkyawar shaida akan wannan matashi

Tabbas taci alwashin sai ya raina kansa sai kuma ya gane kurensa akan irin laifin da ya aikata don sai ta yad’a labaransa da hotunansa aduk wasu kafafen sadarwa na duniya kafin ta gabatar da kwararan hujjojinta a gaban kotu yanda za a yanke masa hukuncin kisa cikin gaggawa domin shine mafi dacewa da tantiri kamarsa ba wai daurin rai da rai ba ko na tsawon wasu shekaru masu yawa.

Cikin hanzari ya nufi motarsa da nufin ya shiga, nan ma tayi masa kusan kati biyar, saidai adaidai wannan lokaci ne kuma tajiyo sautin tafiyar wani abu sululu…a saman kanta, tana d’aga kai tayi arba da wani zabgegen maciji yana kokarin saukowa daga jikin wani reshe.

  Saida ta kurma uban ihu sannan ta zabura ta sheka da gudu har tana kokarin faduwa saboda tsananin tsoro da razana, Sautin ihun nata yacika ilahirin dajin gaba daya har yana amsa kuwwa, tsuntsayen dake saman bishiyu suka firgita suka dinga tashi daga mazauninsu suna kokarin sauya shek’a.

A sukwane matashin ya juyo cikin faduwar gaba ya hau waige waige yana nazarin ta inda wannan ihu ya fito, can ya hangi matashiyar tana zabga uban gudu hannunta rike da Camera ta doshi hanyar fita daga dajin.

Take kirjinsa ya sake bugawa da karfi saboda kallo daya yayi mata ya fahimci ‘yar jarida ce saboda irin shigar da tayi, kuma bisa ga dukkan alamu ta shigo cikin dajin ne domin daukar rahoto.

“To rahoto akan wa?”

Ya tambayi zuciyarsa

“Rahoto akan ka mana, wata kila dama taga shigowarka…”

Zuciyar ta bashi amsa cikin gaggawa

Hankalinsa yayi mummunan tashi, babu tantama ta dauki hoton komai acikin waccan Camera,  idan ko hakan ta kasance akwai babbar matsala, da dai ya bari asirinsa ya tonu gara yabi bayanta ya kama ta ta Kowanne hali ya kwace Camerar itama ya kasheta don hakan kadai shine mafita.

Yana gama wannan tunani ya rufa mata baya cikin matsiyacin gudunsa ba tare da tasan yana biye da ita ba.

Nishi take sosai tana faman haki kamar ranta zai bar gangar jikinta, gaba daya ta gama sarewa da gudun, duk wani karfinta ya kare, tunda tazo duniya bata taba yin gudu irin wannan ba hatta kuwa lokacin da gungun wasu ‘yan fashi suka taba biyota a can yankin wani daji dake jahar zamfara yayinda takai musu ziyarar bazata domin d’aukar rahoto akan su cikin wani shudadden yammaci da ya gabata baya da shekaru uku da suka wuce amma dan tsabar naci taki sarewa domin ba karamar tsorata tayi ba, a tunaninta macijin har yanzu yana biye da ita kamar yanda tayi tunanin ya biyota da farko.

Ba shiri ta waiwaya domin tabbatarwa kanta abunda take zargi.

Daga can nesa ta hangi matashin nan sabanin macijin da take tunani ya tunkaro ta da karfin gudunsa har yana kokarin cimmata ba tare da ta ankara  ba

Kirjinta yayi wata irin bugawa, yayinda tsoro mai tsanani ya yiwa ilahirin zuciya da kwanyarta dirar mikiya ya kuma soma falfala gudun famfalaki acikin jijiyoyin jininta saboda sanin cewa dafin dake jikin wannan matashi ya ninka dafin bakin maciji sau dubu, don haka ya zame mata tilas ta zage dantse matukar tana so takai labari, tayi imanin dazarar ya kama ta kasheta zaiyi itama ya jefata a wancan rami don gudun kada asirinsa ya tonu.

Idan ko ta bari hakan ta faru duk wani sammakonta ya zama na banza kenan tunda babu wata hujja da duniya zata gani a matsayin shaidar da za a yarda cewa shine ya kashe ta kamar yadda ya kashe waccan budurwa a farko.

  Idan kuwa ta rayu ya zama dole asirinsa ya tonu, don haka ya zama wajibi ya karbi mummunan hukuncin da kotu zata yanke masa daidai da laifin da ya aikata.

Tana gama ayyana hakan a ranta sai taji wani sabon karfi ya shigeta ainun, taci gaba da maka gudu ba kakkautawa, sai gashi cikin ikon Allah tayi masa Nisan da ya kasa cimmata har takai cewa sai daga can nesa yake iya hangota, daga bisani kuma ta bace masa bat ya nemeta ya rasa.

**

Tunda ta samu nasarar ficewa daga dajin ta zube a gefen titi tana faman haki da numfarfashi har na tsawon wasu mintuna masu yawa, sai a yau ta kara tabbatarwa lallai aikin jarida ba karamar kasada ce ba da saida rai, musamman ma irin nata salon da ta daukarwa kanta na zakulo manyan labarai masu gigita duk wanda ya sauraresu daga manyan masu laifin da suke aikata munanan laifuka a boye domin tona musu asiri.

Sau tari tasha jefa kanta cikin masifa da bala’i kala kala a wuraren da take kai ziyarar da ta saba a boye domin daukar rahoto, wani lokacin har sai tayi kamar zata rasa ranta.

 Gudu kam ta dade da yin sabo dashi domin ansha biyota tana tserewa sau babu adadi, don haka ta saba da kowacce irin wahala makamanciyar wannan saboda akalla kusan shekara biyar kenan tana wannan aiki a karkashin kamfanin jaridar  GASKIYA TAFI KOBO. 

Lokaci guda ta mike don ganin bakin hadarin da ya lullube sararin samaniya wanda a yanzun ya soma sakin wata iska mai karfi dake nuni da alamun saukowar ruwan sama ba da dadewa ba.

 

Cikin hanzari ta tsallaka titin tana waige waige don kokarin tsayar da motar da zata hau zuwa cikin gari, saidai babu taxi ko daya acikin irin motocin dake wucewa balle akai ga batun adaidaita sahu, duk motoci ne na alfarma don unguwar dake makwaftaka da wannan yanki unguwa ce ta manyan attajirai, Hakanan kuma duk motar da zata gifta da mahaukacin gudu take wucewa kai kace tashi sama zasuyi.

  Nan dai taga bata da zabin da ya wuce ta tare irin wannan motoci ko Allah zaisa a dace a samu wanda zai rage mata hanya kafin wancan hatsabibin matashin dake cikin daji ya iso nan ya risketa don tana da tabbacin ko kadan bazai saurara da nemanta ba.

Tsawon muntuna uku tana faman dagawa motocin hannu amma babu wanda ya saurareta balle yaji uzurinta, hankalinta ya soma tashi don gaba daya ta kosa tabar wajen saboda hakan kadai shine mafita a gareta muddin tanaso ta tsira da rayuwarta.

Ba zato ba tsammani ta hango motarsa ta ratso ta cikin daji ta hawo kan titi da azababben gudu ta nufo inda take.

Hankalinta in yai dubu ya tashi, duk wani tunaninta ya tsaya na wucin gadi, banda rawa babu abunda jikinta yake don tasan zaiyi wuya ta iya tsere masa a wannan karo don ya riga ya gama shammatarta.

Tsananin tsoro da firgici yasa ta soma karanta duk irin addu’ar da tazo bakinta har izuwa lokacin da wata bakar mota samfurin GLK tazo giftawa ta gabanta yayinda aka zuge gilasan gaba na motar aka watso tarkacen wad’ansu takardu tare da robar ruwan faro.

 Kafin gilashin motar ya gama rufewa sai kawai ta yunkura cikin zafin nama ta ciro jakar Camera dinta dake rataye a kafadarta ta jefa cikin wannan mota aka zuge gilashin da ita.

 Motar ta harba da gudun gaske cikin ‘yan sakanni ta bace mata da gani.

A ganinta wannan shine kadai abunda zaisa asirin wannan matashi ya tonu koda nan da tsawon shekara goma ne kuwa don tayi imanin muddin ya risketa a nan inda take tsaye take ta zaiyi da motarsa ya kashe ta sannan ya raba ta da wannan Camera wacce ta dauki duk irin hatsabibancinsa a ciki.

A yanzu kam bata da sauran wata damuwa tunda tasan cewa koda ta rasa ranta akwai babbar sheda da ta bari wacce duk daren dadewa zata bayyana a idon duniya a gani irin barnar da wannan matashi yake aikatawa.

Nan hawaye ya soma zuba a idanunta, ta runtse ido ta soma karanta Kalmar shahada  yayinda ya rage baifi saura taku goma shabiyar  ba motar ta karaso inda take tsaye kikam ta kasa yin koda motsi balle tayi yunkurin daukar mataki irin wanda ya dace, jira take kawai ta bude ido ta ganta a BARZAHU

Ba karamar firgita tayi da jin wata gagarumar kara ba wacce ta dagula mata lissafi ainun, har a ranta take tunanin yabi ta kanta da motar duk kasusuwan jikinta sun kakkarye ta bakunci lahira.

Amma kuma ya akayi ba taji zafi ba ko kadan a jikinta?

Saukar yayyafin ruwan saman da ya dira akan fatar jikinta shine ya tabbatar mata cewa bata mutu ba, don haka tayi saurin bude idanunta domin tantace zahirin abunda ya faru.

Nesa kadan ta hangi motar tasa ta tsaya kikam, taya daya ta gaban motar ta fashe, yayinda matashin keta faman kokarin bude kofa ya fito ya kasa.

Cikin ikon Allah kuma saiga wani mai adaidaita sahu yazo giftawa ta gabanta, har ya dan zarta ta kadan ta zabura da gudu tasha gabansa ta tsayar dashi sannan ta zagayo ta shiga.

Direban ya juyo da sauri ya kalleta da mamaki yana ashirin yayi magana ta tari numfashinsa cikin murya mai sauri tace “Na roke ka dan girman Allah ka kure malejin motar nan kayita gudu kar ka tsaya har sai idan nice da kaina nace ka tsaya, zan baka ko naira nawa kake so daga kan naira dubu daya zuwa naira dubu goma”

Kafin ta rufe baki kuwa ya cika umarninta, ainun ya figi adaidaita sahun da wani irin matsiyacin gudu kamar mai kokarin tashi sama.

Daidai lokacin ne matashin ya samu nasarar fita daga motar ya karaso bakin titin a sukwane yana haki da numfarfashi, saidai kafin kace me tuni sunyi masa nisan da sai daga can nesa yake iya hangosu, kafin kiftawar ido kuwa sun bace masa da gani.

Tsananin bakin ciki da takaici suka sa ya takarkare ya kurma wani uban ihu.

***

Real Marubuci✍🏻

07043194733

ZAKU BANI ATTENTION KU KARANTA IN DINGA YIMUKU POSTING KULLUM?

Back to top button