Uncategorized

Matar Makaho Part 5 Complete Hausa Novel

 

MATAR MAKAHO

Chapter 5

By Rukayya Ibrahim

Washhhh yace jinsa a k’asan cafet  ya zube,Bai farga ba Yana kokarin mikewa, yaji ta Fad’i a kansa  daga shi har ita Kara suka saka sai Kuma sukayi shuru tare,

 ido na ware jina a jikinsa cikin rawan jiki duk na rikice na fara chuku chukun mikewa naji yasa hannu ya zagaye hips ina,

 sosai ya kara matsota kusa dashi,

“Kai me haka” ? Ka sakeni Mana, Mena rike min……..sai Kuma tayi shuru ta kasa karasawa, 

Cikin sanyin halinsa ga jikinsa na wani irin rawa Jin mace a jikinsa a karon farko a tarihin rayuwar sa kenan, yaji mace a kwance a jikinsa, Mena rike Miki? Ya tambaye ta Yana yawo da fuskarsa a kafadar ta Yana neman fuskarta, so yake ya Hada fuskar ta da tasa,

“Wai ma Ina ruwanka ne don Allah nikam sakeni haii”   nace cikin ihu 

Jin muryarta hakan ya tabbatar Masa da inda saitin fuskarta yake hada fuskar yayi da tasa har suna Jin numfashin juna,

“Wai menene haka bazaka sak”………bai bare na karasaba naji saukan lips nashi masu uban dume akan nawa lips in wani abu naji ya tsargar Mini daga tsakar kaina har farcen kafana cikin wani irin birkita na yunkura zanbar jikinsa zan mike ji kawai tayi ya fisgoni gabaki d’ayana na  zube Akansa ,

cikin wani irin zafin nama da kuzari ya cafke lallausan bakinta cikin nasa da wani irin zafi zafi yake tsotsarta  Jin sai k’okarin mikewa take a jikinsa yasa kafa ya harde kafarta da nasa kafar,daga ita harshe rawa jikinsu yake,

Tashin hankali da nake ciki ba’a saka Masa Rana kuka nake so nayi Amma ba Hali hawayene kawai kebin kumatuna,

Jin saukar hawayenta akan face nasa ya saka sa sassauta Mata riko a hankali ya zame bakinsa cikin nata,

Ai da wani irin azabebben sauri na mike  tsalle D’aya  nayi na fita a d’akin na tsaya a baranda duk sanyi da ake da ruwanda ake zugawa na g’wammaci na kwana a waje Data kwana a d’akin nan inaaaaa, 

Sumayya!!! Sumayya!!! yake kiranta cikin tsarkewar murya shima ya mike Yana lalube ya fitoh wajen,

 ganinsa ya sakani zabura Amma tunawa da nayi baya gani yasa na tsaya naki Koh motse kirki Ina jinsa sai kirana yake Yana lulube na a baranda in yazo lalubar Gefen da nake saina matsa a hankali na koma inda ya laluba,jikina nata rawa,

Jin baijita ba don karfin ruwanda ake Bai bare yaji Koh D’an motsen taba don ruwa ake harda tsawa,sauka yayi a baranda yanakan lalube,

 ruwa na dukansa Yana zaga kofar Amma Bai jita ba har kofar shashen ya taba Jin kofar a rufe yasa ya gane Bata fita a kofar ba,

Don Allah Sumayya ki kulani Koh zanji hankali na ya kwanta don nasan kina jina kina ganina,

Wani irin tausayin sa naji ya kamani ,cikin sanyin jiki da fargaba nace “ganinan anan,”

Ai da hanzarinsa ya nufi barandan jikinsa ya jike jakaf da ruwa haryana diga ga gashin kansa da gemunsa duk ya jike ya k’wanta   g’wanin sha’awa ,

Da hanzari ya iso wajen ta cikin rawan murya ya fara magana, Sumayya pls mu koma d’aki kinji,

“Nidai yau bazan k’wana da kaiba a d’aki D’aya ba “nace Ina kuka Kamar karaman yarinya,

Kiye hakuri kinji Sumayya muje mu k’wanta Allah bazan miki kome ba kinji Koh,

“Wallahih nidai bazan shigaba” Ina fada Ina kuka, ganin Yana matsowa kusa Dani yasa na k’wala Kara Zan ruga cikin ruwa naji anyi sama Dani,

D’aukarta yayi duk yanda take kuke kukenta kin kulata yayi sai ihu take tana ya sauke ta, sosai ya riketa Gam a kirjinsa Yana lalube har suka shiga dakin ya tura kofar da hannunsa d’aya d’ayan na rike da ita  ,

A hankali yake lalube harya Iso bakin gado a hankali ya haura saman gadon kwantar da ita yayi a hankali ya lalube blanket inta ya rufa Mata ,ya sauka Akan gadon cikin lalube ya shiga neman Ghana must go in kayansa wani jallabiyan ya dauka a wanke tas ya zura ya zame jikekken gajeren wandon sa,

lalube yayi ya fita waje a aje a cikin kayansa jikakko daya aje a boket,

Nikam tunda ya saukeni a Kan gadon jikina yake ta rawa sosai naji wani irin tsoron Daren nan, zazzabinane ya  Tashi sosai nakejin kaina na Sara mini yau tension Yama kaina yawa,

Dawowa yayi Kan kujira zai k’wanta Amma yaji baho a saitin wajen, lalubawa yayi yaji kujiran a jike hakan ya tabbatar Masa lalai yo-yo wajin ya ke  filon kujiran da yake k’wanciya dashi ya dauka ya lalube cafet ya aje ya k’wanta a kasan dakin wani irin sanyi ne ke shigar sa don a lokacin baiki ya samu abin rufuwa ba Amma Bai dashi Kuma baida karfin gwuwar tambayar Sumayya tunda ba ita tayi niyar basa ba

Jin motsen yayan Khadija yaki natsuwa sai jujuyawa yake ga atishawa akai akai alamudai murace ta kamasa,

Wayarda na wancakalar  dashi na dauka na haska inda nakejin motsen sa ganinsa nayi a kwance sai jujuyawa yake alamudai sanyi yakeji,

D’an tausayi ya bani sai Kuma na tuna lokacin da bani da lfy dashi da Yar uwarsa su sukayita d’awainiya Dani Amma yau shine na Bare a kwance a kasa ga sanyi,

ni Ina kwance a gado da bargo,

 Kamar bazanyi magana ba a hankali nace “,kazo ka kwanta a gadon kasan nan akwai sanyi Kuma naji Kamar mura nason kamaka”

A hankali ya mike ya Soma lalube harya Iso bakin gadon cikin nutsuwa ya haura dai dai ta bakin ya kwanta,

Nikam Ina karshen gado ta wajen jikin gini ganin Bai taba blanket in ba bare ya rufa, yasa na mike na dauko wani a whdrp na aje Masa a kansa na wuce filina na kwanta addu’ar bacci nayi na shafa na juya masa baya ,

Jin ta aje Masa blanket yasa she d’auka ya lulluba shima addu’ar bacci yayi ya lumshe idonsa Sam yaji bacci ya kaurace Masa wani irin yanayi yau ya tsinci kansa  a ciki,Mai ban Al’ajabi

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


Daga shi harni Babu Wanda ya rintsa har 1:00 na dare kafun bacci ya dauke ni shikam bansan lokacin da yayi bacci ba,

*********

Yaukam dagani harshe sai kusan 6 mukayi sallan asuba a dadafe dukan mu biyu da ciwo Muka kwana ga yunwa don tun karyawan safe dagani harshe bamu sake saka kome a bakin mu ba,

muna idarwa gado Muka koma muka sake k’wanciya don baccine ya cika Mana ido na rashin Yi da wure jiya,

Jin Yana matsowa kusa Dani yasani matsawa da sauri ji kawai nayi ya mike zaune ya zura hannunsa ta saitin da nake ya jawoni duka jikinsa a hankali ya koma ya kwanta Dani a jikinsa ,

Yanzun Kam ban neme k’wace jikina  ba saboda zazzabinda nake fama dashi ma ya isheni,

A hankali nace Masa”Wai meke damunka ne tun jiya kake ta tabani”?

Nima ban sani ba haka kawai nakejin inason kusanci dake,ya fada da muryarsa da ta dishe  don mura kamasa Tay sosai ga fuska jazur kamar ka taba jini ya zuba,

Kala bance Masa ba don ni jikina ne ya dameni,shuru mukaye gabaki d’ayan mu har bacci ya dauke mu a haka,

 sallama nake ji kamar muryar Khadija sama sama cikin bacci sai Kuma naji yayan Khadija na zame jikinsa a nawa,

Bude ido nayi Wanda nakejin nauyinsa sosai ga xaxxabi,

Khadija Kam ganin takalmin Aunty da na yayanta a bakin dakali yasa ta juya zata fita Amma dai tana mamakin har 10:10 na safe yayan ta Bai fita ba,

Mikewa Al’ameen yayi ya fita a d’akin Jin alamun Mai sallamar na kokarin fita a shashen Kuma ya shaide muryar Khadija ne,

Waalaikumu salam Khadija ya kina komawa kuma?

La Yaya Daman nace bara nazo na duba Aunty jiya kafarta tun a hanya ya kumbura Amma dai ba kome anjima Zan dawo,

Saboda me?

Naga baku tashi ba Yaya,

Ah ah ai gwarama da kikazo Nima Yanzun nakeson fita na nemi yaro ya kiramin ke,

Lafiya Kam Koh? Naga fuskarka ta kumbura tayi ja ga murya a dishe Daman Saida na tuna haka wallahih ruwan jiyan nan ya kare a kanka,

Ai bani kadai bane Khadija Aunty kima ba lfy  ,

Subhanallah meke damunta Hala kafar ke ciwo,?

Ah ah Khadija zazzabine,

Meya faru da kafartan ne da kike ta cewa Yana ciwo,?

Ba kome kasan jiya bamu samu Keke da wure ba Koh?da kafa Muka ringa takawa,

Uhmm lallai fa,yace Yana dafe kansa dake Sara Masa,

Sannu yaya kanne?

Wallahih Khadija,

Toh kaje ka kwanta Mana bara na gyara kofar,

Khadija Aunty ki tun karyawan jiya bataci kome ba zoki karbi D’arin nan ki sai Madara 50 da bornvite 50 akwai sugar n jiya da safiya da Lipton ki hada Mata tie Koh zata iyya Sha?

Toh Yaya Kaifa,

Khadija hada Mata kawai taima kayan shayen bazai Isa ba?

Zai Isa Yaya,

Toh shikinan ki hada hardani

Toh  

D’akin ya shiga yadau kudin ya mikowa Khadija ya dawo ya kwanta, tare da matsowa kusa dani

Nidai Ina jinsu shuru kawai nayi,

10:30 Khadija ta dafa Mana shaye harda k’wai  ta soya dayake jiya yasai kayan Miya na dare yazo ya samu bamu dawo ba,

Tana Gama shirya kayan Karin ta nufi dakin,

A bakin kofa ta tsaya tana sallama Bata shigo ba ,

Mikewa yayi ya zauna a bakin gadon ya sauke fararen kafarsa a kasan cafet,amsa Mata yayi hade da Bata izzinin ta shigo, Khadija ki shigo mana,yace Jin Taki shiga,

Da sallama a bakinta ta shigo d’akin aje kayan hannunta tayi akan cafet,zata juya,

Khadija d’auki baf in Kan kujiran nan kikai waje kizo ki jona fanka naji Kamar an kawo NEPA  ki juyashi saitin kujiran samun ya bushe,

Toh Yaya tace tana daukan baf in tayi waje dashi zubar da ruwan tayi ,

Ta dauki tsintsiya ta shigo dakin tire in kayan karyawan ta dauka ta daura akan kujiran ta share dakin,

  fanka ta kunna ta matso dashi Kusa da kujiran,Kamar yanda yace

Turarukan UMSAD INCENSE da ta Gani a jere akan mirror ta d’auka na d’aki jona kaskun lantarki tayi  Aiko take dakin ya dauki kamshi Mai Dadi (kowa yasan yanda Turaren wuta yake da kamshi a d’aki especially a damuna),

Khadija na fita ya matsoni a hankali hannu yasa Yana laluba ta nikam sai matsawa nake duk inda naga hannunsa zai taba saina matsa agun,.

Don Allah Sumayya ki tsaya Mana kaina ciwo yake wallahih Koh motsasa bana sonyi kina ta bani wahala yace Yana dafe Kan,

Toh ni sai ka min magana da hannune bazaka mini da baki ba saikayita tabani,

Sorry tashi kije ki wanke bakinki ga breakfast Khadija ta hada Mana yace Yana kwanciya,

Toh Kaifa bazaka wanke bakin bane kake k’wanciya sai yayi ware? nace Masa Babu alamar Wasa,

Murmushi yayi har fararen hakoransa masu tsananin kyau suka bayyana,ai kinfi kowa sanin bakina nada ware Koh babu tunda kin d’and’ana jiya , ya fada muryarsa a shake

Ohon maka dai nace cikin Jin haushi mikewa nayi a hankali na nufi kofa shima mikewar yayi yabi bayana ,

Kofata nabi da kallo tasss Khadija ta share samunta ma nayi tana wanke wanke ga kayan na data cicire a igiya ta zuba a boket,

Khadija kibar d’aurayan nan  don Allah daga kin wanke Kwanukan nan ya Isa haka ke baki gajiya da aikine,

Toh aunty tace mini,

Wanke baki mukayi muka koma daki abincin na jawo Mana ganin hadamu tayi plate d’aya tie ne kawai kowa da cup nashi,

,k’wala Mata Kira nayi”Khadija Khadija”

Na’am Aunty ganinan zuwa,, tace

Tana shigowa dakin 

“Jiki  d’auko wani cup da plate”toh tace ta fita sai gata ta dawo dasu

  Ajjyemin tayi zata fita,

“Tsaya Khadija”  nace  zuba Mata tie nayi na ibi k’wai  data soya Mana NASA Mata a plate itama” d’auka kije kici nasan dafawa kikayi baki ibi naki ba Khadija kullum Ina gayamiki in kin girka Abu ki ringa zuba rabonki kinji Koh kin manta nan ma gidanku ne”?

Toh Aunty tace tana karban plate da cup in tayi waje,

Bismillah na Masa ya matso yasa hannu kad’an naci,naji ya isheni don bakina ba Dadi sam tie kawai nashanye duka, Koh aje cup banyi ba wani irin amai ya tasar mini da gudu na fita waje na ringa shika Amain sosai,

Mikewa yayi yabi bayana daga shi har Khadija sai sannu sake mini Mika min ruwa tayi na wanke bakina na koma d’aki

 duk k’wanciya Muka sake don shima bazai iyya fita wajen sana’a ba,

Misalin karfe d’aya na Rana ana kiraye kirayen sallah azahar ya mike ya fita, wanka yayi a dadafe ya nufi waje zaije chemist in  jambusko Koh zai basa bashin  magani Koh iyya  Sumayya kawai ma in zai samu a Bata ya gode Allah duk da yasan halin inyamurin daker ya ya basa bashi,

Yana fita Nima mikewa nayi Ina Jin jiri jiri na fitoh waje Jin ana kiraye kirayen sallah Khadija na samu ta wanke Mana kayan mu daya jike jiya,tana kitchen wani aikin Kuma take,

“Khadija Wai me yasa bakiji ne nace Miki kibar aikin haka ” 

“Ke kullum kikazo guna baki abinyi sai aiki”

Toh Aunty in ban Miki ba wazan ma ba lfy bane dake ga kofa kasha kasha Koh  abincin da zakuci bazaki iyya girkawa ba toh Aunty in ban muku ba wazai muku

A gaskiya bansan dame Zan sakawa Khadija ba Allah ne kawai xai biyata 

Nagode Khadija Allah ya barmu tare ya nuna mini auren ki in ban mutuba,hhhhhh nace Ina dariya

Kai Aunty tace tana rufe fuska Wai kunya,

Yana fita gida massalaci ya shiga ana idar da Sallah yanufi chemist in jambusko,

Yana Isa sanin ba musulmi bane yasa ya ce Masa , excuse,?

Yes wanene?

Nine jambusko,ya basa amsa Dayake inyamurin ya Dad’e a Jala yanajin hausa sosai ,

Wai MAKAHO Kaine anan yau kuma?

Eh wallahih madam ce ba lfy zazzabi ke damunta……..

Bai bare ya karasa bama ya ce kaima ai harda Kai bakaga muryarka ba ga fuska yayi ja ido ya kumbura,kana mura,

Eh harda ciwon kaima shiyasa nazo wajen ka ka taimaka kaban bashi inna d’an ji sauki zuwa anjima zanfito in Allah yasa na samu kasuwa saina biyaka, ya fada cikin zullumi don shi kansa Allah ya gani kwata kwata bayason roko Koh bashi Amma ya zaiyi bazai iyya zuba ido Yar mutane ba lfy ya barta haka na shi Karan kansa Saida lfyr zai nema musu abinci

Heeeee chinekeeeee gaskiya MAKAHO nii………..

Yau da Matata Zan kwana gaskiya

Da mamaki nake kallonsa”waye matarka”?

Ga tanan ya fada Yana kwanciya Da ita a jikinsa 

“Wai menene haka ka matseni fa” nace Ina kukarin tashi a jikinsa

Fuska ta ya hada da tasa fuskar har hancin su na gogan na juna,

Karan in TV nan Kam kyakkyawa ne shiyasa yake burgeki?

Ikon Allah yanzun Kam na gane inda mutumin nan ya dosa, maganan Karan innan ya damesa”mummuna ne kamar Kai”na basa amsa,har lokacin Ina kwance a jikinsa don karfe ya saka mini sosai

Murmushi yayi a hankali yake goga Mata gashin gemunsa  a Gefen fuskarta

Wani  Abu nakeji sosai  a tare dani”Kai me haka”?

“Kana goga mini gonan ciyawa a fuskata Koh so kake ya garceni ni” 

Kinji Dadi kenan?

Kuma ni ba mummuna bane sai dai kece mummuna

Hhhh shap ai in fada maka “Kai mummuna ne sosai gaka bak’i,gajere, Mai guntun hanci, ga tumbi”

Wannan Karo Kam dariya ya kamayi don sosai yake cikin nishadi, ganin ya samu abokiyar Hira 

Farine ni, Kuma hancina dogone Ina da ido bakina irin na khadijata fuskata dogone  Mai dauke da gashin gemu Mai yawa haka na kaima, akwai tabon sallah a goshina,ya Bata Amsa yana Kai hannunsa kanta ya zame hularda ta saka a hankali ya Kama gashinta da khadija ta kitsa Mata har gadon baya,

Da Ina Tara gashi sai yafi naki yawa

“Kutt wallahih bazaifi ba duk ma Wanda ya farfada maka haka kamannin ka yake  kawai zaginka yayi Amma ba wani yanda na fadan nan dai haka kake”

Dariya kawai yayi sai Kuma yace,

Da ace ban taba ganin kaina a madubi ba dayau kinyi Dani don d’auka zanyi da gaske hakan nake

“Au Daman ka taba kallone kafun ka makance”?

Shikarata 18 na zama MAKAHO Kinga ai zuwa yanzun kamannin Bai sauyaba

“Ya sauya kam gashi harda tumbi kayi”na fada Ina murmushi haka kawai na tsinci kaina cikin farin ciki yau na samu abokin Hira Wanda rabon da nayi harna manta sai in khadija tazo

Cikin hanzari ya birkitota zuwa kasa shi kuma ya koma Saman ta,

Zaro ido nayi cikin Al’ajabi da tsoro bakina har rawa yake”yayan khadija me haka wayyo kirjina nauyi ka d’agani”

Ina da tumbi Koh Babu kinsan ba gani nake ba shiyasa na saka Miki tumbin don kiji akwai Koh Babu

“Wayyo Allah cikina kirjina nauyi ka sauka a kaina wallahih baka da tumbi washhhh numfashina xai d’auke”

Jin yanda duk tabi ta gigice yasa a hankali ya d’aga nauyinsa akanta Amma Bai sauka ba,

“Ashhhhh toh ka sauka a kaina Mana”

Shuru yayi yaki magana yanajin ta sai masifa take, ya sauka a kanta ya Mata banza don yanzun Sam baicika Jin shakkarta ba Kamar da

“Ina Jin fitsari”

Yayi shuru don yasan ba fitsarin zatayi ba muddin ya saketa guduwa zatayi

“Koh bakaji bane, ya matseni fa”

Kiyi anan kawai, ya Bata Amsa

Ganin ya manna mini hauka yasa nayi shuru ganin da gaske fa ba sauka zaiyi a kaina ba bare akan gadon,ganin baida niyar yimin kome yasa hankali na ya kwanta har kusan 1 na dare idanun mu biyu daga karshe dai bacci barawo yayi gaba Dani,

Jin saukar numfashin ta ya tabbata tayi bacci a hankali shima ya ringajin bacci na d’aukarsa zamewa yayi ya kwanta a gefe ya dagota ya d’aurata a kansa ya lumshe idanunsa har yaji babushi,

Kiran farko na Assalatu shiya sauka akan kunne na a hankali na bude idanuna na,masu cike da bacci jina ajikin mutum yasani tunawa Ashe fa jiya tare muka kwanta zame jikina nayi a hankali Zan mike

Jin tana zame jikinta a nashe ya sakasa bude ido sai alokacin yaji Kiran sallah ake

Daga ni harshe waje mukayi na ibi ruwa a buta na aje Masa”ga ruwan Alwala kar a shiga sallah baka Kama Alwala ba ka rasa jam’i”Na fad’a Wai karya tuna wani abu, don yau na iba Masa ruwan Alwala

Butan ya d’auka Alwala yayi ya tafi massalaci sai tunanin abinda zasu karya yake baida Koh sisi Kuma inya bude Mangoro da safe ma ba ciniki yake ba kwana biyu nan,   amfiya D’an Saya da rana Koh yamma

Alwala nayi na shiga d’aki,

 Ina iddar da sallah na kwanta a Kan sallayan don harga Allah bacci nakeji jiya ban kwanta da wure ba

Gida ya shigo don ya rasa mafita Sam baisan me zayi ba,a Ina zai samo musu na karyawa tsoro yake kar hakurin Ta ya Kare wata Rana ta guje sa, da sallama ya shigo d’akin Jin Bata amsa ba yasa ya fara laluben ta akan gado Amma Bai jita ba ya sauka Yanata tattaba kujira a tunaninsa Koh tana jinsa kin amsawa tayi, 

Sumayya!! Sumayya!! ya kirata baki biyu Amma shuru,hankalin sa a tashe ya shiga tattaba kome na d’akin Yana nemanta hardai yajita a kwance akasan cafet,sosai hankalinsa ya kwanta shi Karan kansa ya rasa meke damunsa akan Sumayya Sam baida jarumta akan lamarin ta, Koh  don ta kasance mutum na farko dake da kusanci dashi a duniyarsa ta yanzun ne oho,hannu yasa a hankali ya cicibeta Yana lalube harya Isa bakin gado kwantar da ita yayi,ya fita waje,boket ya d’auko ruwa ya ringa ja a rijiya harya cika Randa ya wanke kwanuka harda shara yayi Amma dai sharan Koh na yara albarka saboda kwata kwata batayi kyau ba (sharan Mara ido)

Yana Gamawa d’akin ya shigo  da lalube ya isa Kan gadon Hawa yayi,hannu yasa ya fara tataba ta Yana neman fuskarta har hannunsa ya sauka akan kirjinta 

Waro ido nayi Ina kallonsa Jin yaki cire hannunsa a kirjina yasa na buge hannun”me haka don Allah”?

Da nayi me?ya sake tambayar ta

“Ai kafini sani waima menene kake ta faman laluba ta  Ina bacci”

Nidai bansan kome ba tunda ba gani nake ba nadai San na taba Abu mai laushi Amma bansan kome Nene ba,ya Bata Amsa

Lallai mutumin nan ya Raina mini wayo ai Koh Bai taba kallo ba a rayuwar sa yasan meya taba bare harya Kai 18 Yana kallo,jin rainin wayone ma ban sake magana ba

Kin tashi lfy?

“Lafiya Alhamdulillah”

Uhmm Sumayya Zan fita, Koh zan samu na karyawa anjima Zan dawa insha Allah ban kwana da kudi ba

“Sai ka dawo” nace Masa Ina sauka a Kan gadon don wallahih yunwa nakeji ba kadan ba

Allah ya yasa,Yace Yana  fita a d’akin harya bude kofar shashen zai fita yaji Sumayya na kiransa tsayawa yayi 

“Am Daman nace in ka fita pls ka tura yaro ya kiramin khadija”Ina magana Ina bin kofar da kallo da mamaki 

Toh,yace mini zai juya

“Wai waye yayi aikin nan duka haka”?na fada Ina murmushi ganin sharan Kamar wata yarinya Yar 3 ce tayi 

Nine na Miki aiki yau dai ki huta

“Aiko naji Dadi na” nace Masa don na gane so yake ya burgeni 😌

Da gaske?ya tambaye ta

“Sosai ma,ka tafi Mana samun mu samu na karyawan ka tsaya surutu yanzun ana neman 8:10 na safe”

Ok.toh sai na dawo

“Yauwa”

Yana fita a kofar gida ya aiki yaro gidan Goggo Amina ya Kira Khadija

Nikam tsintsiya na d’auka na sake share kofar na gyara d’aki sosai kwana biyu nan. Nake jina a sake sosai 

Khadija ce ta shigo bakinta dauke da sallama,

Assalamu alaikum

“Waalaikumu salam”khadin Goggo

Kai Aunty ni banso sunan fa nasan a bakin Yaya kikaji duk shike Bata mini suna

“Toh khadin Yaya”

Aunty ai khadin ne banaso

“Toh khadija shikenan”?

Eh Aunty Ina kwana ?

“Lafiya khadija ya goggo”

Lafiya Alhamdulillah,tace tana zama a bakin dakali

“Wai ni khadija ya Fulani Dance in dai su kawayen Amarya jiya an rabashe kenan”?

Shuru tayi sai Kuma Naga hawaye ya cika idanunta..

Da mamaki nake kallonta “Khadija me ya faru kuma daga tambaya sai kuka wani abin na Miki”?

Aunty don Allah nida yayana muna da wani abin kyemane a jikin mu, da mutane ke wulakanta mu Koh saboda mun kasance Marayu ne, Koh Kuma don Yaya baya kallo ne, ta fada tana fashewa da kuka

“Subhanallah khadija meyasa Kika Fadin irin wannan kalaman haka”

Dole na fada Aunty kaf unguwan nan yayana baida aboki Sam ba Wanda keson rabarsa gani ake Kamar Inka jashi a jiki zai zama maka kaya, Amma wallahih Aunty yayana baida zuciyan kwad’ayi kullun so yake yaga ya neme na kansa Amma duk da haka in Kinga yayana na Hira toh ta miskinai ne irinsa Amma bayansu ba Mai son Koh Hira da yaya, shiyasa har kullum nake mamakin auren ki,

Ni Karan kaina mujiyace a cikin kawaye, me laifin mu aunty mu muka d’aurawa Kan mu Talauci ne Koh akwai Wanda yafi karfin maraici ne?

“Gaskiya Babu khadija Amma meya faru ne haka”?

Na tambaye ta idanuna na cika da hawaye tabbas khadija Allah ne ya tsare ta a irin zamanin da muke cikin nan yanda Yan Mata suka baci da son kyelekyele Amma ita ta kauda fuska ta cire buri a ranta ta zauna a matsayin da Allah ya d’aurata,samun irin khadija kalilan ne a yanzun yarinya Mai hakuri

Aunty Kinga wulakancin da kawayen Amarya suka mini jiya a wajen bikin nan? ta fada tana kuka

“Ah ah khadija me suka Miki”

Aunty’ Wai daga zuwana naje na tsaya agun da kawaye ke tsaye kawai Ina zuwa suka mimmike suka  koma wani wajen  Wai kunya suke kar abokan ango suganni a cikin kawaye za’a Raina class nasu,kinsan ma Aunty me yafi Bata mini Rai?

“Ah ah khadija”

Wai Aunty danaga duk sun watse saina koma cikin mutane na tsaya kawai kowa na tsaya kusa dashe sai ya Kama matsawa Wai kar ace tare Dani yazo, don ban saka kayan Fulani ba koma banyi ado ba

Sosai naji wani irin haushi kamar zai kashe ni

Aunty bazan sake zuwa bikin kowa ba daga yau

“Yau me za’a yi”?

Kamu,ta bani Amsa

“Zaki je bikin nan khadija har a Gama dake za’a Gama insha Allah”

Aunty ni bazan sake zuwa ba a wulakanta ni,don Yaya yace Koh mutun baida kudi in dai ya rike mutuncin sa bazai wulakanta ba

“Ki kwantar da hankalinki insha Allah bazasu sake wulakanta kiba” na fada Ina Mai Jin tausayin baiwar Allah nan

D’aki na shiga na barta tana kuka akwatina na bude Kaya na d’auka Atamfa da les masu azaban kyau a dinke sai Turare na d’auka guda D’aya na fitoh a d’akin dasu a hannuna 

“Khadija rike kayan nan Naga kamar akwai tailoli a tsallaken titi ki Kai musu wa’innan kayan su rage Miki yayi daidan ki yanzun in Kika fita,

wannan Turare Kuma kasuwa nakeso ki Kai shagunan masu Turare Koh zasu Saya kudin sa 20k ne Amma Koh 10k Kika samu Koh kasa dashe ki karba kawai”

Aunty ba Yaya yace ki daina Saida kayanki ba?

“Khadija Zan zauna da yunwa ne Ina da abinda Zan tsayar naci a cikina sai na zauna”

Gaskiya ne Aunty Amma fa Yan kasuwa bazasu Saya ba don yanzun Suma tsoron sayan kayan hannu suke karsu Saya na sata,sai dai akwai wata Mata dillaliya ta bayan kasuwa sai na Kai Mata don ance itakam Koh kayan satane Saya take don Yar rikici ce sosai

“Yauwa khadija Allah yasa ta Saya wannan kayan in kin fita ki fara kaisu shagunan dinki”

Aunty wazaki bawa kayan Kuma ai Naga daidan kine naji kince a maidashe daidai na?

“Ina ruwan Ki,nidai tashi kije mini aika na,

 sannan in ta Saya Turaren ki shiga kasuwa ki sai Gam bak’i Mai kyau ki hada da Turaren lalle,sajan,tsamiyan kanti, ki sai bakin lalle guda biyu shima”

Aunty lalle zakije ne?

“Kai Khadija banson tambaya ki sai mini kayan Miya duka,in kin dawo ki biya tailan kudinsa ki karbi kayan Saiki saimin doya soyayye  a bakin titi na karya”

Toh Aunty tace ta karbi kayan tasa a laida ta fita

D’aki na shiga Ina ta tunanin halin rayuwa da khadija ke ciki

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 2 HAUSA NOVEL”


Sai karfe 10 khadija ta dawo kayan na bubbude na Bata ta gwada Aiko yayi Mata daidai jikinta sosai kayan ya karbe ta,doyan na bude Mana mukaci tare

Kam in na manna a tire na kwaba Jan lalle, “khadija zoki zauna na Miki lalle”nace  Mata Ina zama akan dakali

Aunty Daman ni Zaki ma lallen ne har Kika Saida Turaren ki Mai tsada a naira 5k?

“Khadija bazan d’auki wulakanci ba Sam insha Allah yau saikin fi Amaryar kyau bama kawayen ba” 

Daman kin iyya lalle ne Aunty?ta fada tana zama

“Sosai ma khadija ai lokacin da nake primary school innaje makaranta sai nayita zana flower lalle a takanda na Inna dawo gida sai ummie na tace zata buge ni sai abie ya k’waceni  yace bazata bugeni ba ai batasan Koh baiwar da Allah ya mini ba kenan,

sai ya sai mini takkadar lalle daban duk lokacin da zanyi Zane saina dawo makaranta sai ya bani takardar na zana, lokacin da na Gama primary sai ya sai k’wallon dayes ya baiwa Mai aikin mu ta dafa mini da lalle,sai nayi mole na zuba a ciki,abie ke saimin hydrogen Ina ma yaran gidan mu lalle harda yaran makwanta,

harna girma Ina lalle duk yaran gidan mu da aka aurar Mata Ninake musu lallen aure da make-up haka kawaye na da Yan unguwan mu sosai nake Alfahari da lalle khadija”nace Ina manna Mata Gam a gafa

Kenan Aunty kina sana’an lalle da kwalliya?

“Ban taba yin lalle kudi ba Koh make-up khadija don ba abinda na nema na rasa a rayuwa a lokacin”

Allah sarki, tace 

Lalle na tsarawa khadija sosai bak’i da ja sai bayan azahar Muka Gama, tunda nake da khadija ban taba ganin farin cikin  Dana gani a lokacin da na Gama Mata lalle ba bini bini saita duba lallen tayi murmushi

“Wai nikam khadija baki taba lalle bane”

Aunty Kenan Koh a sallah bana lallle in Kinga nayi lalle toh gaggo ne ta mini yabe

“Toh yaukam kinyi design na flower”nace Ina mikewa

 sallah Mukayi kafun Muka girka abincin Rana har lokacin yayan Khadija Bai dawo ba,

Sai biyu da rabi na Gama abinci zuba Mana nayi mukaci har lokacin fuskar khadija na d’auke da murmushi 

***Nima sai naji Ina cikin farin ciki ganinta tana walwala

“Khadija ga abincin yayanki kikai Masa”

Toh Aunty ta d’auki kulan tana kukarin fita,”yauwa khadija in kinje ki dawo da wure samun mu fara make-up in da wure”

Toh Aunty nagode,tace tana fita,cikin farin ciki duk Wanda ya ganta yau yasan Bata da wata damuwa

Tun daga nesa ta hango yayanta a zaune g’wanin tausayi sai zufa yake…………….

Karasawa tayi kusa dashi, Assalamu alaikum

Waalaikumu salam khadija

Na’am yaya, lfy Kam na ganka haka a zaune, a Rana gashi sai zufa kake

Lafiya khadija wallahih Ina cikin damuwa ne, tun safe na fita nabar Aunty ki Koh karyawa batayi ba gashi har ana neman la’asar banyi cinikin Koh biyar ba

Yaya gaskiya ya kamata ka shanja sana’a yanzun mangoro yayi a raha ba lallai bane kana cini ki sosai

Gaskiya ne khadija Nima Yanzun so nake na sare lemo in gwada na gani Amma bani da jarin,

Toh Yaya Allah dai ya Bud’a maka kaji kabar saka kanka a tunani kaje ka jawa kanka ciwo a banza

Allah yasa khadija

Yauwa gashe Aunty ta bani abinci na kawo maka

Abinci kuma?ai na ta samu kudi har taye cefene?

Ina Zan sani Yaya nidai data kirani saita aike ni kasuwa(ta Masa karya karyace Sumayya batajin maganar sa)

Koh dai kayanta ta sayar ne khadija?

Kai.yaya bana tunanin haka fa,ga abincin kaci pls kaji yayana sannan ka tashi a ranan nan ka koma Gefen shagon Haladu ka zauna

Toh khadija,yace   Yana karbar kulan da take hannunta, 

khadija Turaren wa Kika saka ne naji kina kamshi?

Hh wayyo yayana lalle ne Aunty ta mini, yanzun ma kwalliya zata mini Inna koma

Lalle Kuma khadija kuma yake kamshi?

Eh Yaya Turare aka saka sai aka kwaba dashi

Inta Miki kwalliyar Ina zakije?

Kamun Asma’u Mana Yaya ka manta

Ban manta ba sha’afa nayi khadija, Amma ya za’a yi bani da kudin machine in da Zan baki fa

Yaya za’a d’auke mu a mota gidansu Amarya,kasan yaufa zansha kyau,ta fada cikin farin ciki, zanje sai mu tafi tare…

Sai kin dawo Allah ya tsare mini ke kanwata,yace yanajin wani Annashuwa, kanwarsa na farin ciki Kuma Sumayya ce sanadi, gaskiya Sumayya Rahama ce Allah ya masa,daya basa ita

Ameen Yaya,tace tana tafiya

Bayan fitar khadija wanka nayi na chanja Kaya wando nasa da riga t-shirt   na kwanta akan kujira Ina jiranta,

Assalamu alaikum Aunty na dawo Aunty

“Waalaikumu salam khadija kiyi Alwala sai kizo mu fara make-up in Kinga Koh an Kira Sallah sai kiye kawai”

Toh Aunty, tace tana iban ruwa  Alwala tayi ta shigo d’akin 

Make-up kit nawa dana aje a cikin drawer na d’auko budesa nayi babbane ba abinda babu na make-up a ciki,zama nayi na tsarawa khadija makeover,

Kai Masha Allah duk Wanda yaga khadija mundin ba mugun sani ya Mata ba bazai taba zato Koh tsammanin ita bace heavy make-up na Mata irin na Amare, amaren ma sai agun dinner,”khadija muyi sallah sai kisa Kaya Koh”

Toh Aunty, tace sai murmushi take

Bayan mun iddar da sallah

Less in na Bata ta saka black ne Mai ratsin pink, gel na samata a gashi na d’aura Mata dankwali Mai ubansu,

sarka da d’ankunne warwaro, zube, na Bata dukansu golden colour,takalmi pink, gyale da purse black,Kai duk Wanda yaga khadija a yau Koh shakka bazaiyi ba zaice Amarya ce, Ina Gama shiryata

Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror, kamar taga abin tsoro, Innalilahih Aunty nice na koma haka? Aunty Kinga yanda na koma kamar ba ni ba,ta fada hawaye na cika Mata ido 

“Kece khadija ki share hawayen nan karya Bata Miki kwalliya kinji maza share”

Toh Aunty,tace tana goge hawayen ta

Wayata Kiran iPhone na d’auko”tsaya Khadija na Miki hoto”nace Ina gyara Mata gyelenta

Tsayawa tayi,Aunty ta ta Mata hotona harda video  sosai tayi kyau

“A Ina za’ayi kamun ne”?

A Taraba hotel ne,Wai ta hanyar government house

“Hhh ba Taraba hotel ba, Taraba motel ake cewa sannan Bata government house bane,hanyar ne Amma ta Amazon yake “

Au nikam Ina Zan sani Aunty ba zuwa nake ba, kawai nima naji jiya ana fad’ane

“Ga 200 ki hau machine kije kinji ki dawo da wure fa khadija karki Kai mangariba”na fada Ina Mika Mata kudin

Ki bare Aunty mota za’a kawo a gidansu amarya zai d’auke kawaye

“Aikam yau  a motar zaki,maza ki hanzarta Amma ki.karbi kudin Incase

Toh aunty sai na dawo,tace tana fita a d’akin 

“Toh khadija Allah ya dawo dake lfy”

Ameen, khadija na fita a kofar shashen yayanta, duk Yan gidan suna zaune a tsakar gida daga maza har Mata,ido suka bita dashe kureeeee suna mamakin bakuwar nan Sam tun safe suke zaune Amma basuga wucewar taba,baki a tsake suka bi khadija da ido harta fita,

Khadija Kam duk tabi ta tsargu don Sam tunda take da wayonta Bata taba kwalliya irin na yau ba har kofar gida ta fita duk masu shaguna suka bita da ido suna mamakin Wannan kyakkyawar meya shigo da ita gidan Adara,

Amma wasu basa mamaki in sun tuna MATAR MAKAHO fa Yar manya ce Kamar yanda akasaigunta musu, Kuma sun rasa dalilin auren nan Basu mamaki yake,mutum talaka miskini,a d’auki lafiyayye ya abasa Kuma Yar masu kudi,masu kudin ma zuriyan shugaba,abin nan na mugun Basu mamaki,Amma Basu da halin sani

Khadija Kam ganin ido caaaa akanta yasa ta ruga gida da gudu ta koma kofar Sumayya

“Kee khadija lfy meya faru Naga kin shigo kofa Koh sallama Babu Kamar an koroki”

Aunty duk inda na wuce bina fa ake da ido,ni gaskiya tsoro nake ji

“Kai khadija akwai wauta,don ana kallonki saiki kame jikinki ki nuna musu kauyanci,ai dakewa zakiye kici bom”

“Koh gun kamu kikaje neman kujira zakiyi ki zauna abinki karki kuskura kicewa kowa kome Wanda ya gaidake ki amsa Wanda Bai Miki magana ba karki Masa kinji”

Toh Aunty,tace tana fita

Sai yanzun Yan gidan suka gane ta cikin mamaki Iro yace,buran uba muna d irin wannan kayan a gida Amma ace har yanzun banyi aure ba aradun Allah Naga Mata

Kutumar ubanka iro D’an iska watoh kaga kasa ya rufe idon uwarka shine bare ka karya alkawarin da mukayi akan auren ka da salame,watoh munafurcine kullum akace ka fitoh a muku aure,sai kace baka da kudi,

 ah ah sai kayi gini ashe iskancine,baba lami tace

Kinga baba lami wallahih kibini a hankali Daman ni har yanzun haushin ku nakeji,

Aini ba shege bane dazan aure kanwar Wanda tayi sanadin mutuwar inno na ba,

Koh inno ne ta dawo nasan bazata yafe mini ba Inna aure yarki, iro yace 

Kai karamin D’an Tasha wallahih karka kuskura, kace zaka zagarmin uwa inba haka ba naci ubanka a gidan nan, manu ya fada,babban yaron Inna asabe

Inka fasa shege kake,iro yace Yana huci

Ai Bai Gama rufe baki ba manu ya shakumosa suka hau dambe

Duk yanda matasan ke ta kokarin rabasu abin ya faskara abinka da tamben maza,

Mazan ma masu zuciya

Hatta iyayensu maza an Kira Amma duk sunki rabuwa sai an rabasu an Kama D’aya sai D’aya ya fizge ya shakumo D’aya Inka shiga tsakani duka ya sauka akan ka

Abin da yafi karfin Yan unguwan police aka Kira,suka zo suka kwashe su,inda sabo an Saba da ganin fiye da hakama agidan Adara

*******************

Bayan fitar khadija kwanciya nayi don yau dai naji na gaji da cin cimar mu tunda inada sauran 2k Kuma akwai kayan Miya da yawa,don haka yaudai zanci wani abin special

Duk abinda ke faruwa Ina kwance Ina jinsu sai dai.bansan ainahin abinda ya had’asu ba”garin kallon fad’a a kasheni a banxa ” nace Ina gyara kwanciya na

sai kusan 5:30 Al’ameen ya koma gida kwata kwata naira 30 yayi ciniki Sam yau Kam sai a hankali,ya shigo gidan jiki a sanyaye hannunsa d’auke da kwandon kwanuka,bakinsa dauke da sallama

“Waalaikumu salam,sai yanzun”nace masa

Eh Sumayya yau inne ba kasuwa shiyasa ban dawo Koh da Rana ba

“Toh Allah ya bada kasuwa gobe”

Ameen yace Yana aje Kwanukan a mawanki,Mika Mata talatin in yayi

“Ka rike kawai agunka”

Ok yace,boket ya d’auka ya ibi ruwa, band’aki ya shiga yayi wanka Yana fitowa yayi Alwala,daidai lokacin aka Kira mangari ba, masallaci ya wuce

“Sallan mangariba,nayi wanka Nima zani na d’auka fille D’aya na had’a da t-shirt sai hulan bacci, Jin ana kukarin shiga sallan isha’i,

Ina da Alwala hijab kawai nasa na Tada sallah,

7:40 Al’ameen ya shigo d’akin bakinsa d’auke da sallama

Amsa Masa nayi”yauwa jiranka nake ka dawo daman”nace Ina mikewa

Toh Allah dai yasa lfy?yace

“Kasan inda ake Saida tsire”?

Tsire Kuma Sumayya?

Eh “tsire de”

Hmm eh na sani a tsallaken titi akwai Mai nama, kusa damai shayi

Yauwa karbi kudin nan 2k ne ka sai Mana tsiren 1500 sai Kuma  ka sama Mana drinks Mai Dadi guda biyu yau Dadi zamuci gaskiya”

sai ka sai  Madara bornviter da sugar in change ya rage kasai bread Nokia Ina da ruwan zafi a flasks,sai mu karya dashe gobe da safe”

A Ina Kika samu kudin nan? haka Sumayya don khadija tace mini ba kayanki Kika sayarba 

Sosai naji Ina Kara kaunar Khadija yarinya Mai hankali hartasan ta rufa mini asiri agun D’an uwanta,

Amma ni bazan Masa karya ba”uhmm uhmm nidai gaskiya bazan maka karya ba Turarena na sayar”

Amma Sumayya banace ki daina Saida kayanki ba ,ni ban Kara Miki ba, Bai kamata in rage Miki ba

“Habba ya Ina da abinda Zan sayar na saka abakin salati saina zauna da yunwa tsakani da Allah fa, yau baka samu kome ba da haka Zan zauna tun safiya har warhaka banci kome ba kenan”na fada Ina Bata Rai

Ganin Kamar taji haushi sai ya sassauta murya,toh Yi hakuri kawo kudin naje na saya Miki

Mika Masa nayi bance kome Ba

Lalubar kudin yayi harya rike,ya fita

Baifi hour 1 ba ya dawo lokacin Ina kallo a d’aki 

Shigowa yayi da sallama

Amsa Masa nayi,Ina karban laidodi Daya ke mika mini, karba nayi, na mike waje na fita na d’auko plates da cups harda flasks na shigo d’akin,

bude laidan tsiren na zuzzuba a plate,Goran pineapple juice in Mai sanyi na juye Mana a cup,d’aukan NASA nayi na Mika masa,”gashi naka”

karba yayi hade da Mata godiya,a hankali yasa hannunsa a cikin plate in ya dauki Naman da Bismillah yasaka a bakinsa

,lumshe ido yayi,rabonsa da yaci tsire tun  lokacin da mahaifinsa kenan,bazai manta ba shike sayo musu duk dare, lokacin ma ba’a haifi Khadija ba

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 3 HAUSA NOVEL”


Nima cin namana nake Ina korawa da drinks ba karamin Dadi naji ba kai.talauci ba kyau talaka sai yafi wata baici nama ba,

Ashe haka talakawa keji,tabbas badon jarabawar da Allah ya jarabceta ba bazata taba sanin rayuwan Talauci haka yake ba Alhamdulillah Alah kulli halim

Daga ni harshi duk nacin mu bamu iyya cinye namarnan ba, sai da muka rage wani,nikam har zafi hakorina naji yake mini kafun na aje Naman don yau cin yunwa na masa,sabanin da, da nake ma nama cin kwad’ayi kawai

Jin ta aje plate nata yasashe magana,sumy Wai harkin cinye ne ga nawa ki Kara wallahih na kasa cinye wa,

“Kutt bazanci sauran abinda kaci ba,Kuma nima ga nawa ban ciny………

Bai bare ta Gama magana ba taji ya fizgota sosai suka zube akan gado kanta yahau cikin gaggawa ya hada bakin su waje D’aya y’awonsa ya juye Mata a baki

Ware ido nayi Jin y’awonsa cike a bakina so nake na zubar Amma ba Hali har lokacin bakin mu a hade,ji nayi kamar numfashina xai d’auke ai da sauri na had’iye Ina rumtsa idanuna

Jin ta had’iye yasa a hankali ya kamo harshen ta sosai yake tsotsarta cikin zafi zafi..

Fizge bakina nayi,”don Allah ka Bari banason abinda kake minin nan”na fada Ina ta kukarin turesa a kaina

Ni Kuma inaso,ya Bata Amsa,Yana Kai hannunsa, akan t-shirt nata Yana kokarin cirewa

Ai bansan lokacin da na Kama kokarin fizgo kaina ba ganin da gaske fa mutumin nan riga zai cire mini

Jin ta isheshe da fizge fizge shima ya biye Mata inya d’aga riga sai yaji ta jawo rigan kasa,inya cire hannu D’aya sai tasa d’ayan

Tambe muka fara sosai abin dariya abin haushi,daga ni harshi mun jikkata sosai Amma ba Wanda yayi niyar barwa Dan uwansa dama

ni naki yarda ya cire mini riga shi Kuma yaki yarda ya hakura,

Hannu yasa da karfi ya fizge zanin jikinta,

Gwalalo ido nayi jina ba zani,wani yunkuruwa nayi da karfin gaske Zan mike zaune 

Cikin  zafi nama ya maidata kwance  Yana Kara Hawa kanta,

daidai lokacin mukaji sallama na muryoyin Yan Mata a kofar mu….,…..

Ba karamin Dadi naji ba,da saurina Amsa musu sallamar muryata na rawa”waalaikumu salam”nace Ina kallonsa ganin baiyi niyar sakeni ba,”toh ka tashi Mana naje naji suwa ke sallama”

Wayace kiyi magana?

“Au amsa sallaman ne,laifi”   

Toh ai badon Allah kika.amsa ba ya fada Yana sauka a hankali ya kwanta a Gefen ta

Jin ya sauka akaina ai da sauri na mike zanina da ya yasar a kasa na tsunguna na d’auka,fita nayi a d’akin duk jikina sai rawa yake, na barsa a  kwance akan 

Gadon.

Yan matane zasu Kai su biyar gabaki D’aya bazasu wuce sa’o’in Khadija ba,”sunnunku da zuwa”

Sukam mamakine ya cikasu,wannan ne MATAR MAKAHO Mata Kamar balarabiya Aiko Mai kudi lafiyayye ba kowa bani yake sa’ar samun mace Mai kyaun Sumayya, yauwa,Ina wuni Aunty sumy? Suna had’a baki

“Lafiya Alhamdulillah bara na d’auko muku abin zama”  

La ki barshi kawai Aunty,sauri muke ma dare yayi.

“Gaskiya Kam Kuna Mata yanzun ana neman 10 na dare fa,kuna waje”

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 4 HAUSA NOVEL”


Eh wallahih Aunty nasan bazaki ganemu ba,Daman mu kawayen Khadija ne,wata acikinsu tace

“Kawayen Khadija Kuma aini Khadija batace mini tanada kawaye ba bayan Asma’u”nace musu haka don na gane kawayen Amaryar ne,ganinsu da Anko

Eh Aunty dukan mu kawayen Khadijan ne harda Asma’u,

“Toh Allah dai yasa lfy ba wani abin bane ya faru”nace Ina zullumi kar wani abinne ya samu khadija

Eh Aunty yanzun ma gidan su khadija Muka fitoh akan ta rakamu wajen ki,shine tace Wai yayanta ya hanata fitan dare

“Gaskiya ne Bata fita bayan mangariba, Allah dai yasa lfy kuke son ganina”?

Eh lfy Daman mun tambaye tane akan inda tayi lalle da make-up jiya,

Shine tace Mana Wai agun matar yayanta,.

Shine mukazo mu tambaya Koh zamu samu lalle gobe,da kwalliya in Allah ya kaimu?

“Bazaku samuba” nace Ina zuyawa na shiga d’aki Koh bin ta kansu banyi ba, saboda sanin da na musu sune suka ma khadija rashin mutunci jiya agun Fulani Dance.

Ina shiga d’aki akan kujira na zauna, gaskiya Ina son yin lalle Koh don na samu na biyan bukata Amma bazan ma Yan iskan nan ba.

Sumayya meyasa bazaki musu lallen ba? Al’ameen ya tambaye ta

“Ina ruwanka watoh ka fara sa ido Koh”

Ina Naga idon bare na saka ni duhu nake gani,ya Bata Amsa

“Watoh kaima ka iyya bakar magana Koh”

Ai agunki na koya

“Badai aguna ba malam ehen”

Amma Sumayya dakin musu lallen ai.

“Bafa Zan musu ba Yan iskan yara bakasan me suka mini bane,”

Yaushe sukazo gidan nan har suka Miki Abu?

“Kai jama’a yaushe ka koma D’an jaridane ban sani ba”

Baimin magana ba mikewa Naga yayi Yana kokarin sauka a gadon ai ihu na saka na mike zanyi waje.

Wallahih Kika fita a d’akin nan saina Miki abinda bakiso

“Me kenan”?

Kin fini sani,yace Yana nufar kofa, waje ya fita yaje ya rufe shashen mu ya dawo ya rufe kofan d’aki 

Ina dai zaune sai raba ido nake,ganin ya nufu kujiran,da nake yasa na mike a hankali na lallaba na chanja waje, zuwa gaban mirror na tsaya,

Jin motsen takunta yasa ya gane lallai tabar Kan kujiran..

Fara lalube yayi nidai sai chanja waje nake in ya nufi inda nake saina chanja waje,duk magiyar da yake min, kin tsayawa nayi.

Muna cikin zagaya d’akin kawai aka d’auke NEPA gashe ban San takamemmen inda na aje wayata ba.

Jin tsayawar fanka,yasa ya gane an d’auke NEPA ne, shiyasa ya fara tafiya a hankali Yana laluben ta sanin da yayi yanzun itama ba ganinsa zatanayi ba.

Raraba ido nake ta faman Yi banajin motsensa Sam sannan Banga wayata ba.matsawa nayi sosai jikin kujira na sunguna Zan duba wayata,ji kawai nayi ya rungumeni ta baya

“Wayyo Allah nikam ka sakeni wallahih banaso”

 yanzun dai kema baki ganin kome kamarni.

“Allah ba kamar Kai bakam”

Koma yayane dai baki gani 

“Nikam sakeni hai”

Naki yace Yana dagata 

“Wayyo nashiga uku,ka saukeni”nace Ina ta faman mutsu mutsu

Kiye shuru Mana mu k’wanta

“Niki shurun nikam ka sakeni”

Kin saketa yayi duk yanda tayi ya saketa ki yayi 

Ina ji Ina gani ya kwanta akan kujira d’aurani yayi akansa,tun Ina masifa harnayi shuru Jin ana iska da yayafi ,sanan aka kece da ruwan sama,

Baccine ya d’auke mu dukan mu biyu akan kujiran muka kwana

Da safe,shayi mukasha da bread,wanke wanke na fitar Ina wanke wa

Sanin da yayi Koh ya fita ba lallai bane yayi ciniki sai wani ikon Allah da safen nan, gashe mangoron duk sunyi labo labo.

Kayansa ya fitar Wanda Bai wuce kala hudu ba a igiyar bayan gida inda take Tara kayansa masu datti,d’aukar basket in kayan Sumayya yayi ya fitar dashe waje ya zuye a dakali,ibo ruwa yayi ya fara wanke musu kayan.

Ina wanke wanke,Yana wanki,dukan mu shuru Babu Mai magana

Assalamu alaikum, khadija ce tayi sallama hannunta d’auke da laida

“Waalaikumu salam khadija”

Ina kwana Yaya?

Lafiya khadin Goggo

Ina kwana Aunty,tace tana murmushi

“Lafiya khadija ya Goggo”

Tana gaisheki,tace tana zama a Gefen yayanta dake zaune abakin dakali da boket in ruwan kumfa

“Aiko Ina amsa wa”

Aunty kinsan me? Kai jiya Naga abin mamaki,tace d’auraye kayanda yayanta ke wankewa

“Me Kika gani haka”? Na tambaye ta

Aunty kinsan Allah Ina fita a gidan nan,na wuce gidansu Asma’u duk inda na wuce sai ayita kallona ,

Ina Isa na samu an kawo mototi sunkai ashirin,kinsan Aunty mijin Asma’u shima Mai kudine?

“Ina Zan sani khadija ai sai kin fad’amin”?

Ina isowa wajen mototi sun cika har ana kokarin tafiya,kawai saina nemi gefe na tsaya, kawai wani abokin Ango yazo kusa Dani,Wai hajiya baki samu mota bane?

Nace eh ban samu ba ku tafi kawai Zan hau machine,

Wai harda cewa Wai babban Dani ba girma na bane Hawa machine bara  a sama mini wajen zama,

Kawai yaje ya fidda kawar amarya ya sani a motar

“Hhhhhh Kai habba dai khadija”nace Ina dariya

Yanzun abin dariyane agunki Sumayya an fidda wani Ansa wata,Koh ke zakiji d’adi a Miki haka, Al’ameen ya fada Yana Bata Rai

Khadija Kam tsoro ne ya kamata Sam ta manta da yayanta agun ta sake baki tana zuba

“Kasan me suka matane”?

Koma me suka Mata hakan Bai kamata ba cin fuska ne,

Fad’a Masa kome nayi akan abinda suka ma khadija

Koma me suka Mata banji Dadi ba

“Khadija tashi mu shiga ciki muye sirri”nace Mata Ina Kama hannunta Muka shiga d’aki

“Khadija karasa mini sai akayi yaya”na tambaye ta

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 4 HAUSA NOVEL”


Ai Aunty in gaya Miki kawai na Shiga abina kawayen fa Basu gagane niba sai da Muka Isa Taraba motel in da Muka fifita a motar,duk Saida suka Raina wankan su Aunty kaf insu  harda Amarya Babu Wanda kwalliyar ta yayi kyau irin nawa,

Sai da nama Amarya magana kafun suka gane nice, wallahih Aunty baki ga yanda aka maida ni abin kallo ba masu vedion aure sai d’aukana suke harda hotuna,Kinga agun kawaye uku nayi yaran masu kudi,samari Kuma sai turawa suke Wai suna son magana Dani a waje.

Kin zuwa nayi kawayen ma naki kulasu,ai Aunty badon Allah ba kenan suke Sona, tunda Basu Soni a khadija ta ba Saida suka ga nayi kyau,ta karasa maganar tana washe baki

“Gaskiya ne khadija bare ma insha Allah karatu zakiye insha Allah”nace Ina murmushi don tabbas khadija akwai kaifin tunani

Aunty jiya fa goshin mangariba na fitoh a Hall in Zan dawo gida Kinga yanda abokan Ango ke ribibin zasu kawoni gida,.

Amma naki,

“Gwara da Kika ki khadija yanzun mutum ake kiwo. Ba dabba kad’ai ba”

Wallahih kuwa Aunty kawai da dare saiga wani yazo gidan mu bansan ma waya nuna Masa ba Wai ana sallama dani,

“Lallai kanwata tayi goshi”

Allah Aunty kin fita nayi Goggo tayita fad’a 

“Don me khadija wulakanci ba kyau fa dakin fitan ai” 

Gaskiya ni Aunty banason Abu da masu kudi, 

don mudi yace mini da babban mota yazo,Kinga masu kudin nan in Kika aure su wallahih Kina Yar talaka,basa ganin daraja. Yan uwanki

Ah ah khadija ba duka aka zama D’aya ba indai da kyakkyawan Niya akayi aure badon kyau Koh kwad’ayi ba,insha Allah ba abinda zai faru

Hakane Kam aunty,au Ashe fa na had’a da Aunty a magana ta am sorry (don tace auren masu kudi basa ganin darajan Yan uwan matan su,in talaka wa ne)

“Uhmm khadija kenan,ai Nima na zama talaka yanzun”

Amma ai gidan ku akwai kudi?

“Gidan mijina babu”

Aunty jiya wasu sunzo wajenki karfe kusan 10?

“Eh Khadija”

Nima jiya suka zo gidan mu Wai na fad’a musu Wanda tamin lalle,da Wanda tamin make-up

“Kawayen Amarya Koh”?

Eh Aunty sune,suka mini wulakanci agun Fulani Dance

“Aiko shiyasa nayi maganin su nace bazan musu lalle ba”

Meyasa Aunty

“Saboda kee kad’ai Zan ma kwalliya har Agama programs na auren Asma’u”

Kiye hakuri ki musu Aunty Zaki samu kudi sosai fa yau HENNA DAY, Kuma da yamma za’ayi Algaita

“Gaskiya khadija bazan musu ba ” 

Shikinan Aunty ga kayanki nan na dawo Miki dasu

“Habba khadija ki rike na bar miki”Daman kyauta na baki ba aro ba”

Aunty’ ai yayi yawa 

“Ki rike duka”

Allah ya……….

Bata karasaba mukaji sallama na muryar mace babba

Al’ameen dake zaune a waje ne, ya amsa 

Sannu Ina kwana hajiya,yace Yana tsame hannunsa a wankin

Lafiya Alhamdulillah don Allah nan ne kofar MATAR MAKAHO?don ita Bata zata Al’ameen baya kallo ba

Kafun Al’ameen ya Bata Amsa Muka fitoh a d’akin dagani har khadija kallon matar muke hajiyace Kuma hamshakiya daga ganinta naira ya zauna

“Hajiya lfy” nace Ina kallon ta  dajin haushin sunan da ta kirani Wai MATAR MAKAHO mtwss

 yauwa wajenki nazo 

“Ok Bismillah khadija d’auko Mata darduma” nace  saboda d’akin mu D’ayane bazan iyya saka baki a ciki ba

“Bismillah hajiya ga wajen zama”

Zama tayi Muka gaisa

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 5 HAUSA NOVEL”


Ni sunana hajiya sa’a findon Asma’u kawar Khadija kanwar mijinki nasan khadija Kam ta ganeni Koh? tace tana kallon khadija

Eh Aunty sa’a, khadija tace

Yauwa Daman nazone akan in ba damuwa,Koh Asma’u zata samu lalle inda halima harda mu,don jiya na turo kawayen ta sunce Wai bazakiyi ba shiyasa nazo da kaina,

“Gaskiya hajiya ni Ina da aure bazan iyya zuwa in ma amarya lalle ba,tunda Henna day ne yau”

Habba wallahih ba kome zamu zo har gida ki Mana itama Amaryar zatazo saiki mata,tunda ba’a d’aura aure ba kuma gida baki da hanci

“Shikinan hajiya”

Yauwa nace zata iyya zuwa yanzun don anjima akwai Algaita da yamma,saiki Mata kwalliya ma duka

“Toh hajiya gaskiya bazaku samu lalle yauba don indai lallen Amarya ne Dole za’a jima ga kwalliya duka”

Saiki Mana gobe da safe,tunda Walima ne kwalliya kawai zaki Mana da yamma saiki Mana lalle da safe,

“Ku nawa ne”?

Mu bakwai Zaki ma lalle da Amarya 8 Amma bansan kawayen ta mutun nawa ba

“Ok za’a ma Amarya lalle da kwalliya yau”In yaso ku sai amuku gobe hannu bibiyu sai kwalliyar walima,saboda time”Amma banda kawayen don bazasu samu ba

Ba damuwa Daman booking mukayi har Agama bikin zakina Mana kwalliya in ba damuwa

“Ok shikinan”

Nawane kudin ki?

“Hajiya kwalliyar Amarya kashi biyu ne ana heavy make-up a dinner, bud’an Kai, kamu sai light make-up anayi a Walima, Algaita, Arab night

Kinga kenan light make-up Zan mata yau”

“Kudin kwalliyar yau 5k ne, lalle 10k na Amarya”

“Kwalliyar ku 3k ne Koh wani mutum D’aya”

Ok na gobe fa ?

“Lallen ku na gobe hannu bibiyu ne Kuma ja da baki za’a muku a hannun dubu D’aya da d’ari biyar ne, in da lalle na Kuma 2k Koh wani mutum D’aya”

Ok tace ta hada lissafi ta bani kudin a hannun,gashe kudin kwalliyar Amarya da lallen ta nayau da kwalliyar mu sai na lallen mu na gobe,in mukazo kwalliyar walima sai muyi lissafi harda na dinner,tace tana mamakin wayewar Sumayya,

 da akace mata MATAR MAKAHO ne ta d’auka Koh zatazo taga bagidajiya sai taga hatta MAKAHO ma bazaka zata baya gani ba

Ok hajiya” nace Ina karban kudin kirgawa nayi Naga ya cika,hajiya watoh harda kudin lalle Kika bayar kenan”?

Eh zuwa kawai zamuyi goben,Amma Amarya na zuwa da lallen ta,kinsan ana  kawo kayan rufi da lallen Amarya ?

“Gaskiya ne shikenan saina ganku anjiman”

Allah yasa tace tana Mike wa ta tafi

Khadija Kam da Al’ameen mutuwar tsaye sukayi,Wai kwalliyar da ake gogiwa shine za’a biya dubu biyar ayi ai gwara ma lalle zaiyi sati..

Aunty yanzun duk wannan kudin na lalle ne kawai da kitso? khadija ta tambaye Sumayya

“Kai Khadija ba abin yayi bane,Kuma kayan kwalliyar ma tsadane dashi”

Ikon Allah,tace

“Kinga khadija tashi maza kije kasuwa ki mini sayayyan lalle sai ki sai Mana semolina yau tuwo zanyi na gaji da shinkafan nan na fada Ina Mika Mata 10k ki sai Mana harda kaji biyu a gyara Miki a kasuwan,ki hada mana da kayan Miya harda su vegetable”

Toh Aunty tace tana karban kudin 

Al’ameen Kam baice kome ba ,Yana shanya kayanda yawanke

Khadija na fita Koh minutes uku batayi ba mukaji Karan faduwa timmm sai muryar Khadija data k’wala Kara,irin na azabar nan,dagani harshi da gudu Muka nufi kofar fita a shashen mu, ganin tsabar rudewa Bai gane hanyar kofa ba yasa na Kama Masa hannu na Masa jagora Muka fitoh,

 me Zan gani khadija ce a……….

Back to top button