Mijin Marigayiya Page 12 Hausa Novel
Ta juyo ta kalli kofar ta harareta kamar shine a wajen sannan ta ja tsaki ta juya. Ta San akwai cutar to amma ai ta yiwa Ummin magana, yanzu ya yake so tayi da aikin gidan nan ga azumi? Da ma ace zai tayata aikin me ko kuma ya bari yaranshi su dinga tayata to da sauki. Amma haka zai zuba yaranshi a gaba suna zaune suna kallon TV ita kuma tana kitchen ita kadai. Ta share kwallar da ta gangaro a idonta ta gyara kwanciya; bata san yanda zata kasance ba sai dai kawai ta bari taga yanda hali zai yi goben. …….. Ko da gari ya waye Khadeeja bata ma San lokacin da Ummi ta zo ba don tun daga bakin gate ya tareta yace ta koma kada ta sake zuwa sai bayan Sallah.Sai wajen Sha daya sannan ta fito ta dan gayggyara gidan, wanke-wanke ne ma ya bata mata lokaci don yana da yawa sosai. Haka ta wankesu gaba daya a famfon waje sai da shigo kifewa sannan Afaf ta tayata. Tana gamawa ta shige dakinta ta kwanta; bata taba jin gajiya irin wannan ba a rayuwarta, gashi duk wata gaba da take jikinta ciwo take yi. Tun 3pm ta shiga kitchen ta fara kokarin hada kayan Shan ruwa; dankali da kwai zata soya sai jollof sphagetti sannan ga peppersoup din nama. Da akwai ragowar zobo na jiya don haka ba zata sake hada wani ba. Yaran suna zaune a parlor ta zo ta wuce ta shiga kitchen, tana wucewa Afaf ta bi bayanta. Ta so ta Koro Afaf din daga kitchen amma dai ta hakura ta barta, suna yin aikin. Basu dade da farawa ba Habib ya shigo kitchen din, ya kalli dankalin da aka ajiye a tsakiyar kitchen din yace ‘Anti wannan ferayewa za ayi?’Tace ‘Eh, so nake na dora kifin nan sai na zauna na feraye shi.’’Kawo wuka na feraye Anti.’ Ya fada yana Bude cabinet, ya zaro roba ya tara ya debu ruwa. Tace ‘Ka barshi Habib zan feraye.’Ya sa hannu ya dauki wuka a kan sink yana cewa ‘Na iya feraye dankali fa Anti, idan na feraye miki sai ki yanka.’Bai saurari amsarta ba ya tsuguna ya fara feraye dankalin. Afaf ta ajiye kayan miyan da ta gama wankewa a kusa da Khadeejan tace ‘Anti na wanke kayan miyan.’’To ki yanka mana albasar nan, Rabi slicing za ki yi rabi Kuma ki yanka kanana sai a saka a soup da fried egg.’Ta dauki albasar ta wanke ta zuba a chopping board ta fara yankawa.Ba su ji lokacin da Mustapha ya karaso bakin kofar kitchen din ba; a dai-dai lokacin nan wukar da Afaf take yanka albasa ta goce ta Yanke mata hannu. Ta dire albasar ta make murya tana cewa ‘Waiyo Anti na yake.’Da sauri ta saki abinda yake hannunta ta nufi wajen Afaf din tana murmushi cike da kulawa tana cewa ‘Sorry, garin yaya Afaf. Ki…’Da sauri ya karasa ya kama hannun Afaf din yana cewa ‘Garin Yaya kika yanke, me ya sa kika dauki wuka?’ Ya juya ya dubi Khadijan yana cewa ‘Na gaya miki sai kin san aikin da Zaki dinga sa yaran nan Amma ke gani kike kamar kawai bana son su taya ki aiki ne. Yaushe Afaf zata iya wani yanka albasa.’Afaf ta zare hannunta daga nashi hannun ta juya ta wanke a sink, ta dubeshi tace ‘Ya ma daina jinin Abba bari naje na daure.’Yana juyawa ya dubi Habib wanda yake ta ferayar dankali ya daka masa tsawa ‘Ka ajiye wukar nan ka tashi, namiji da kai kana wani feraye dankali. Tashi ka bani waje.’Ya juya kan Khadeeja wadda ta riga ta cigaba da aikinta kamar ba da ita yake magana ba, yace ‘Na gaya miki ki daina sa yaran nan aikin da ya fi karfinsu, bana so. Shi Habib ma da yake namiji me ya hadashi da wani harkar girki? Bana so.’Bai ga alamar zata bashi amsa ba don haka ya juya shima ya fice suka barta ita kadai a kitchen din.Ta rasa me ma zata yi, ta goge fuskarta ta cigaba da aikinta.Haka ta lallaba ta gama komai, zuwa magriba ta zubawa kowa aka sha ruwa.Ta gaji iya gajiya don haka bata ma da kuzarin da zata iya wani musu da shi, ta dai riga ta gama yankewa kanta hukunci da zarar an bude gari zata tafi gidansu ba zata dawo ba sai ta haihu kuma ya dauki mai aiki.…….A haka aka cigaba da azumi, kullum cikin wannan yanayin Khadeeja take hadawa da hidimar gidan da ta yaran tayi ta fama.Kullum sai ta yiwa Shukra da Nasreen wanka, tsarkin kashi tsarkin fitsari duk ita take musu. Duk wata fitinarsu itace me kulawa. Ga shi tana fama da Shukra wadda sai yanzu ne da suka kwana biyu ta fara hanata kashin wando.’Don Allah kiyi mata a hankali, komai lokaci ne ai zata daina ne a yi mata hakuri.’ Ya fada yana shirin komawa dakin ya yiwo alwala.Ta tsuguna zata dauketa taji kanta ya biyota kamar zai fado, ta dafe goshi ta koma ta tsaye tace ‘Kai! Ba zan iya ba fa.’Ya juyo ya tsaya ‘Menene?’‘Ba zan iya tsugunawa ba fa, jiri kwasa ta yake.’ ta karasa kan kujera ta zauna ta dafe goshi. Ta dubi Afaf tace ‘Bani ruwa na Sha Afaf, ga kiran Sallah nan an fara.’ Nan da nan ta cika Kofi da ruwa ta mika mata, ta Sha kadan ta jingine kanta tana rike da ruwan. Kukan Yusra ne ya katsesu tana cewa ‘Anti na daina ba zan Kuma ba, manatwa nayi daman.’ Ta yunkura zata mike Afaf tayi sauri ta dafeta. Abbansu ya dubi Khadija yace ‘Don Allah ki lallaba ki wanke mata kashin nan, Wannan wane irin abu ne? Yanzu wa kike so ya wanke mata kashin?’Afaf ta aika Nasreen ta dauko fo a toilet ta cire wandon da yake cike da Kashi ta jefe a fo din sannan ta dauke Shukran ta nufi bandaki. Ta wanke mata sannan ta dawo ta gyara wajen, zuwa lokacin Abbansu ya fito daga alwala. Ya zauna ya sha ruwa sannan ya mike zai tafi masallaci. A daidai lokacin itama Khadeeja ta dago kanta ‘A dawo lafiya.’ Yana jinta yayi banza da ita saboda yanda yake jin haushinta, Kuma tabbas sai ya kora mata bayani in an Sha ruwa. Daga yau ma ba zata sake yin azumin ba tunda dama Mai ciki tana da damar ajiyewa. Ta mike tana gatsina fuska, kawai sai gani yayi ta sulale zata fadi. Ya zabura zai tareta yayi fatali da casserole din dankali, a lokaci guda Habib ya saki jug din zobon da ya fito dashi daga kitchen ya tarwatse a wajen ya karasa kanta. Duka su biyun kafin su karaso ta zube. Abbansu ya dago kanta yana jijjigawa ‘Khadeeja, Khadeeja, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Khadeeja.’Ko motsawa bata yi.Ya sunkuceta ya kwantar da ita a kan three seater, ya kara gudun fanka sannan ya kunna AC. Ya cire mata dankwalin da yake kanta ya fara yi mata fifita. Yaran gaba daya suka jeru a kanta suka yi tsuru-tsuru; Afaf ta leka fuskarta ta kafadar Abbansu tace ‘Abban itama mutuwa zata yi ta barmu ko?’ ‘Ke bana son rashin hankali, ba wanda zai mutu’A take yaran suka saka masa kuka mai ban tausayi. Afaf ta rungume Nasreen da Shukra suka hada Kai suna kuka.Habib ya taba shi yace ‘Abba ka Kai ta asibiti kada ta mutu ta barmu.’’Kai rufe mana baki.’Gaba daya Shima ya rude, jikinsa har rawa yake yi. Ya janyo jug din ruwan sanyi ya jika hannunsa ya Shafa mata a fuska. Ta ja numfashi ta bude idonta, sai kuma ta mayar ta rufe.’Khadeeja.’ Ya kirawo sunanta da karfi yana jijjiga ta.Da gudu su Afaf suka karasa kanta suna kira ‘Anti, Anti.’‘Khadeeja.’ Ya kara kiran sunanta a firgice.Ta bude ido ta sake rufewa.Ya mike tsaye ya dan tura yaran yana cewa ‘Ku zauna na dauko mukullin mota, asibiti zan kaita yanzu, babu abinda zai sameta in sha Allahu.’Ba tare da bata lokaci ba ya dauko mukulli ya fito, ya je ya bude kofar motar ya dawo ya dauketa bayan ya yafa mata mayafi ya wuce yaran suna biye da shi ya kwantar da ita a bayan motar. Bayan ya rufe kofar motar ya juyo ya kalli yaran yana tunani; to yanzu ya zai yi da su? Wa zai barwa su? Ya san shi kansa ma sai ya amsa tambayoyi a checkpoints gashi ma’aikatan asibitin ma kamar tsoron mutane suke balle ya kwashi yara su tafi. Ya shafa kai sannan ya sake kallonsu cike da damuwa; da ace gari a bude yake da sai ya wuce da su ya ajiyesu gidan Hajiya to amma ya san ba zai yiwu don zai yi ta bata lokaci a checkpoint. A take dabara ta fado masa.‘Ku tsaya a nan ina zuwa.’ Ya basu umarni sannan ya fice daga gidan ya turo gate din.Yana fitowa ya karasa gidan su Ummi, yayi sa’a yana tsayawa maigidan yana dawowa daga masallaci. Bayan sun gaisa ya sanar da shi so yake Ummi ta zo ta zauna masa da yara ya je ya kai Khadeeja asibiti. Ya janjanta masa sannan ya shige gidan ya turo masa Ummin.Haka ya sako ta a gaba ya dawo gidan ya bar mata yaran ya ja motar ya nufi Aminu Kano Teaching Hospital dake Kano.________Yana zuwa asibitin aka nuna masa gynae emergency inda nan ne ake karbar masu ciki wadanda suke bukatar taimako na gaggawa, nan da nan suka karbet aka fara duba ta; duk da dai su kansu ma’aikatan zaka gane cewa suna cikin yanayi na tsoro saboda Covid19….
