Novel Document

Mafarkin Farida Complete Document By Asma Baffah

Description/Story:

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Document Written By Asma Baffah

 

Description

Baki ta cuno gaba tana baccinta tana mutsutsu tare da kankame jikinta waje Daya tana sake cinno bakinta gaba,Juyi tayi tare da Bude hannaye kamar zata Rungume wani tana Kara turo labbanta gaba,wata Dattijuwa ce wankan Tarwada ta fito Daga daki sanye da t-shirt da zanin wata jar atamfa Wanda atamfar da t-shirt din sun Gama Jin jiki,sun kode sun jeme sun fita a hayyacinsu,wuyan rigar har ta farke,daga bakin wuyan kamar bera ya gwigwiye,Kanta ba Dankwali gashinta Kamar shekar Ungulu,an Masa kitso Amma kitson ko jela babu sabo da Rashin gashi na wannan dattijuwa,Kitson ya Gama tsufa tukuf shima.

Yarinyar da baza ta wuce 19yrs ba wacce ke bacci a saman wata fukatacciyar Tabarma karkashin bishiyar mangoro,Dattijuwar ce ta shiga tashinta Farida….Farida….ke Faridaaaaaa……a firgice Budurwar ta farka ta Mike zaune tana wani murmushi ita kadai ta kalli kasa Kawai tayi wani mutuwar zaune tace Hajiyanmu…. Hajiyata wani mafarkin ne,wallahi wani mafarkin ne,mafarkin da nake tayi kusan kullum,mafarkin hadadden,zukeken,santalelen charming prince,the Handsome prince,The Honey Prince and Amazing prince Hajiya,Iyyeeeeee…Dattijuwar da aka Kira da Hajiya ta furta,tana wani washe Baki tana murna ka rantse itace tayi mafarkin,Farida tace Hajiya karki so ki ganshi kamar Aljani sabo da kyau,fari wani irin haske me wani sa Ido dum da shi Hajiya,Dattijuwar ta karyar da Kai gefe tana uban murna tana kallon Yarta tana Iyyeeeeee,Ehemmm….Ina jinki Farida ta…..

Farida taci gaba da furta yau mafarkin ya banbanta Dana kullum Hajiya,yau a wata duniya na hango mu Ni da shi,munsha fararen Kaya,Yana cikin wata shegiyar suit fara zata Kai million Hamsim,Eyemmmm Hajiya ta Furta da karfi tana murna tana washe Baki,Farida taci gaba da cewa Hajiya da mota fa naje Wajensa wata baka zata Kai ta Million dari da wani Abu,shi Kuma tasa motar fara zata Kai wajen million dari uku da wajen saba’in da Yan kwandaloli, Dattijuwar rawa ta fara da Juyi sabo da Murna tana Waka
Lale Iye rambada
Lale Iye Rambada
Wallahi ‘yata ta Haye,kwana Nan Zan fara gani na cikin Lace da manyan shaddoji,ai matar Gomna ma Uwata karya ne ta kaini hutawa,kwana Nan Zaki rushe Mana wannan gidan na talauci ki Gina Mansion,Takawarki Lafiya Gimbiya Farida.

Ai Farida wani Dadi ya sake kumeta Jin kirarin da Hajiya ke Mata,Farida Tace Hajiya ki tsaya kiji karashen mafarkin Mana,Hajiya tana ihun murna Tace Ina jinki Yata ta kaina,Farida tace Ina fada Miki da naje da motar million dari din Nan shima yazo data million dari uku da haya haya ai sai Muka fito Hajiya Ina Jin kunyarki Amma Zan fada Miki tunda bana boye Miki komai,Hajiya da sauri tana wangale Baki tace Allah na tuba Farida me kike boye min ai nice mahaifiyarki Kuma kawarki,wannan Abu ma da ya samu idan mafarki ya tabbata ai Zan shiga daula karki ji komai fada min ko kunyi aure ne a cikin mafarkin? Farida tana dariyar murna tace Ashe kina da kwakwalwa Hajiya ta munyi aure Muna soyayya,ya Rungume ni fa a jikinsa kam,Hajiya tana rufe Baki Amma tana tuntsurewa da dariyar murna ta furta kudi suna Kan hanya mun kusa Zama masu kudi,daga Nan sai aka Yi Yaya Kin Haihu a cikin mafarkin? Farida tace a’a an dai daura Aure Muna soyayya Ina jikinsa Hajiya yayi min wani mahaukacin Kiss sai na ganni a wata Aljannar duniya gaba Daya wajen American Dollar ne sun baibayeni sune grass din wajen,Ai Hajiya sai ta saki rawa da Juyi bilhakki sabo da Murna.

Farida Tace a wajen yace Baby ki bani Jerusalem naki,Ihu Hajiya ta kurma tana wayyo wannan yasan soyayya na Gane Jerusalem din da yake nufi yo in da kudi me zai Hana,Farida tafin murna tayi tare da mikewa tsaya tana Juyi tana Taku dai dai tana yanga,Hajiya tana kaga gimbiya Takawarki Lafiya ta prince ikon Allah,Alherin Allah ya Kai Miki wata tafiyar sai a Birnin tarayya,Farida Tace hmm ai kafin a Kai ga na bashi Jeru din Hajiya sai na farka,Hajiya da tausayi Tace wayyoooo banji Dadi ba,Amma karki damu Dole mu tafi gidan Malam Haru Haru ya fassara Mana wannan mafarki,wannan Bai kamata ayi ta mafarki shekara kusan biyu Amma Bamu San ma’anarsa ba,nasan ma mijinki ne,shine Zaki aure,ai tunda na tsuguna na haifeki kika Fado duniya naji a jikina ke matar manya ce,ke matar Hamshakin me kudi ce, Farida tunda na haife ki naji a jikina da ke Zan jingina,a jikinki Zan huta,kece silar arzikinmu,nasan ma ya kusa kawo Kansa gareki,nasan kwanan Nan zaizo Neman aurenki.

Farida ta sheka da gudu ta Kai karshen bangon gidan ta dawo wajen Hajiya sabo da Murna ta rasa inda zata sa kanta tana haki Tace Hajiya ya kamata na fara koyon tafiya da takalmi choge,ya kamata na iya yanga da karairaya,sannan yanzu ne ya kamata na fara canja salon Taku da magana a city din Nan,so nake kowa ya kalleni yasan Ni ba matar Kana Nan Yara bane,maganata ta koma ta Yan gayu sabo da kar Prince yazo ya Iske Ni ba Yar gayu ba,kin San su manya ne sun Saba da Yan gayu,Hajiya Tace yo ai ba ke kadai ba Farida har Dani sabo da Nima Kar Iyayensa suzo Yan gayu ban iya magana da taking gayu ba,Maganar Hajiya ta fara gwadawa itama.

Sassanunku da zuwa…kit Farida ta katseta Tace turanci fa Zaki Yi Hey ku shigo haka Zaki ce,Hajiya tace Hey ku shigo sannunku da Hanya,Sai ki Kara da Wow cewar Farida tana Gyarawa Hajiya,Hajiya Tace to Kinga dai Farida ke Baka ce Amma kyakyawa Black Beauty,Yan Uwanki Kuwa Manal da Yazed ne kadai Farare sabo da kyan Yarinyar Nan bana so ta rabe mu,to yanzu ma ke gashi Allah ya kusa yanke Mana zakiyi aurenki da wuri gobe sai mu shirya muje wajen Malam Muji Mene ke tafiya.

Daga cikin wani dagargajenjen daki Wanda gaba Daya ya Gama rubewa dakin Kamar zai Rufta duk Kuwa da cewa na Bulon Siminti ne,wani Mutum ne ke buga Kofar ta ciki wacce a kulle take gaba Daya,sai lokacin Hajiya da Farida Suka kalli Kofar Dakin suka ja tsaki a tare ,Hajiya Tace na Gama tsanar tsohon cen wlh ban San kaddarar da tasa na aure shi ba wlh,tunda nake sai yanzu na gane tsohon Nan bashi da mutunci sam, Farida Tace kece Hajiya kika cuce mu ke da Zaki auri me kudi da yanzu a can gidan me kudi aka Haifo mu Amma sai gashi kin Kare a malam,Wai shine Baban mu,wlh Ina Jin kunya Ni bana son nuna shi ma,shi yasa bana so Kawayena su dinga zuwa suna ganinsa a matsayin Mahaifi na wallahi Ina su Alhaqatu ne da su Masatura?Hajiya tace ai duk suna makarantar Allo Falaqi ne Kawai Yana dakinsu zazzabi ya rufe shi,Ina Uban Iyayin Nan Yazed? Hmm Hajiya ta tabe Baki Tace Yana lecture Bai dawo ba sai wani dagawa yake shi a Dole ya kusa Gama Degree Dan Iskan fikalallen banza,Degree din banza ya Gama Degree dinsa yazo na bashi Aiki cewar Farida.

Wata yarinya ce ta shigo zata Kai a kalla 9yrs,Farida tace Sa’iha ta dawo ga Sa’ihar mu ta dawo,Sa’iha ta karaso da gudu da Allonta tare da fadawa jikin Farida tadagata sama suna dariya,Kofar da Malam yake ce ta sake Kara yana ta dukan kofa babu Wanda ya kulashi sai da Yazed ya dawo daga lecture sanye cikin kana Nan kayansa Wanda sun Sha jiki da gani kasan Yana fama da talauci gashi kyakyawa fari tas da shi da gani shi ya fita zakka a gidan,da gudu ya karasa dakin Malam ya bude ya Iske Dattijon har ya Fado ma daga saman kujerarsa ta guragu wheelchair wanda shi ba gurgu bane da kafafunsa Amma baya iya hasalawa Kansa komai Dan Ma Allah yasa hannunsa Yana Dan aiki,Yazed yace Malam Ina Za’a kaika kayi Hakuri bana gidan Ina makaranta,Malam Ya kalle shi cike da kauna maganarsa da kyar take fita sannan ya furta Allah ya maka Albarka Yazed,kana cikin Wanda na zalunta a baya Amma yanzu Kaine gata na Malam ya fashe da kuka sosai,Yazed lallashinsa ya shiga Yi yace Malam Ka daina damuwa wlh Ni ban rike komai ba,ya wuce kana Mahaifina Ni bana son ganin kukanka.

Turo shi yayi a hankali tare da fito dashi waje ya kaishi toilet wacce ko wanketa ba’a Yi gaja gaja da wari,Ruwan wanka ya Kai Masa,ya maida shi Kan wata kujera Dake toilet din ya zauna sannan ya fito da Wheelchair din waje,Dakin da Malam yake ciki Nan Yazed yaje ya share ya gyara Masa ko Ina fes ya fesa Masa wani Roomfreshner me kamshi Dan dari biyu da Hamsim,Sai da Malam yayi wankansa fes tare da daura Alwala sannan Yazed yaje ya fito da shi,Ya taimaka Masa ya shafa Mai tare da canja Kaya sun Sha wanki da guga wannan aikin Yazed ne.

Kafin Malam yayi Sallah Yazed ya fito ya kalli Farida Dake zaune tana Shan kunu yace me aka dafa yau? Sai da tayi minti biyu kafin tayi magana Sabo da ta rigada tayi mafarki ta Zama matar Dan sarki prince,tana yanga tace shinkafa da wake ce tana kitchen,Amma Dan wulakanci shine kuka bar Malam da yunwa tun safe da ya Sha Kunu da kosai har 5pm Bai ci komai ba,uban waye yake siyo abincin gidan idan ba Malam ba da dukiyarsa yake ciyar damu Yana tufatar damu da komai ma Amma shine za a dafa abinci baza a bashi ba? Hajiya ce ta fito Tace to jarababbe me hakkewa kannai baka da Aiki sai masifa idan Yana Jin yunwar uban waye yace Kar yayi magana a bashi abincin aikin banza,Tsaki Yazed ya ja Kawai ya Shiga Rubabben Kitchen din da Kansa ya zubowa Malam abinci a plate ya Iske Hajiya ta yanka harda salat da tumatur ya zuba,shima ya zubawa Kansa ya shige dakin Malam.

 

Download  Complete Novel Document By Khaleesat Haiydar

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button