Haihuwa Da Hanji Page 1 Hausa Novel
Wani irin ruwa ake tsulawa kaman da bakin ƙwarya, kusan duka bil’adama suna kwance lub cikin tattausan katifa lulluɓe da bargo suna bacci kaman yadda dare ya zama mahutar bawa amma ita tana duƙe a kitchen ɗin dake tsiyaya saboda rashin kyaun kwanon da aka lulluɓe kai da shi.Wuta ne take hurawa Dukda bayanta dake ta jiƙewa har hakwaranta suna haɗe wa saboda sanyin dake shigarta hakan bai sa ta damu ba sai ma ƙara mayar da hankali da ta yi ga haurawar da bata sarara ba sai da ta ga wutar ta kama yadda ya kamata, babbar tukunya ce da za’a iya naɗe ta a sanyata ciki kuma tsaf ya ɗauketa saboda rashin ƙiba da kumarinta ta shiga kokawar janyowa da ƙyar ta ɗora bisa murhun kan ta nufi wani bokiti ta fara aikin ɗibo ruwa a kimtace tana zubawa sai da ta tabbatar yayi yadda ta saba kan ta rufe ta fito, kifi ɗanye da suke sanyawa cikin ƙanƙara a wani babbar kula ta juye ta shiga wankewa don an riga an yi mata yanka tun jiya da Magrib a bakin kasuwan, sai da ta wanke tsaf ta ɗauko wani tukunyar ta zuba su sai a lokacin aka soma kiraye-kirayen sallah daga chan nesa. Na yi mamakin yadda ko tsoro babu a fuskarta haka take ayyukan nan cikin ruwa a take ta sake haɗa wani murhun ta ɗora dahuwar miyan kifin nan, sai da ta tabbatar komai ya mata yadda take so kan ta shiga tattaro kwanukan gidan don ta san in ta bari ma gari ya yi haske ta shiga uku, wanke wanke take sauri-sauri yayinda ruwan da ya koma zuba chab chab ya cigaba da jiƙata, har ta gama jikinta babu inda ba ya kakkarwa sauri sauri ta wanke shinkafa ta zuba cikin tukunyar farko kan ta yi alwala har kuma lokacin babu mahaluƙin da ya leƙo a gidan Dukda kuwa wasu masallatan ma har sun idar da sallah.Akurkin ɗakin da shi ne nata a gidan ta duƙa ta shige ta cire kayan jikinta bakkon kayanta ta janyo da kyar ta zaƙulo wata kodaddiyar doguwar riga ta saka ta janyo hijabinta ta ɗora tare da tada sallah, ga mamakina tsaf ta gabatar da Sallar ta yadda addini ya tanadar, bata jima tana azkar ba ta fito don gudun magana amma bata tsira ba domin a kitchen ɗin ta tarar da Inna larai da sauri ta duƙa ƙasa “Ina kwana inna?”Kallonta tayi ta taɓe baki ta buɗe tukwanen ganin miyan ya yi ta juyo gareta”Uban me kika shiga ɗaki kike yi har miyan nan ya nuna saura ƙonewa baki shirya kwashewa ba? Asara kike son ja min ko?””A’a inna sallah ne na je na yi”Tsaki ta ja tare da nuna mata kular da suke kwashe miyan tallar, ta je da sauri ta ɗauko inna larai ta kwashe tsaf kan ta ɗaura dumamen gidan a murhun, ita kuma ta wuce ta ɗauko kular kwashe shinkafa ta taho ta janyo ledar sugar ta buɗe a cikin kular kan ta shiga kwashewa turirin na Dakar ta yana ƙonata yadda ta saba har ta gama duk sanyin da ake ta jiƙe jagwaf da gumi, kwanukan tallarta ta cigaba da haɗawa a wani bokitin fenti har ta gama filate na roba da ruwa da gutsuren dollof da take wanke plates idan ta sayar aka ci aka dawo mata dashi. “Je ki bugawa su Iro su zo su ɗaura miki a baro su kai miki yanzun nan”Da to ta amsa cikin sanyinta ta nufi ɗakin na yaran mazan ta shiga bugawa, sai da ta kwashe sama da mintuna ashirin tana bugu da ƙiran suna kan wasu matsakaitan samari biyu suka fito ɗayan ya sa hannu ya hankaɗeta sai da ta faɗi ƙasa.”Don uban ki bamu hana ki wannan bugun bala’in ba? Shegiya kullum ba ki da aiki sai na uzzurawa mutane ko wani farar safiya…””Ɗahiru ƙaniyar ka…! Kun wuce kun zo kun fitar min da abinci ko sai kun janyo min asara?”Babu ruwanta da sun yi sallah ko ba su yi ba damuwarta kawai su kai mata kayan sana’ar ta.A hankali ta miƙe tsaye tana kaɓe jikinta dama ta sani ba dai a yi musu faɗa a kan an ci zarafinta ko an zalunce ta ba, kowa a gidan na ganinta tamkar juji da in sun kwaso sharar su babu inda suke zubawa sai bisa kanta.Sumsum haka ta taho suka kama suka ɗora suna ta mitar da kullum safiya sai sun yi haka har suka fice, tana shirin fita daga gidan kenan Inna larai ta kwala ƙiran sunanta.”Afifah Ke!”Waigowa tayi da sauri kuma cikin sanyinta “Saura in ga ba daidai ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daaɗi kuma kika sake kika ci kai ko lasa kika yi Allah ya isa ban yafe ba ki je ki dawo ga dumamenki nan zan ajiye miki”Girgiza kai tayi fuskanta ɗauke da murmushi mai nauyi da ciwo ta amsa da”Toh”Kan ta fice daga gidan.A inda ta saba zama gefen rumfar masu tura finafinai nan ta zauna bayan sun sauƙe mata suka buɗe suka cika fillet biyu idanunta cike da hawaye tace “Iro wallahi in…””Na uwarki ne ko na ta mu uwar? Ina ruwanki? Kuma wallahi ki sake ki faɗa mata ki ga yadda zamu yi da ke Annoba kawai”Da ƙarfi ta runtse ido sunan ba wai sabo bane a gareta sai dai a duk sadda aka ƙira ta da hakan ta kan ji zafi da ciwon fiye da ɗanɗanon maɗaci a kan harshenta.”Mai shinkafa sa min na ɗari uku..!”Haɗiye abin da ya taso mata tayi ta karɓi kudin ta saka a Jakan ƙugunta kan ta fara zuba shinkafar kaman ko yaushe fuskanta babu ɗigon fara’a ko sassauci ba kuma don komai ta ɗauki wannan mataki ba sai don kare mutuncinta.Hakan da take ya sa maza dayawa masu kawowa ‘yan mata yan tallah wargi basa samun dama kowa ya santa duk tsiyarka tana da kwarjinin da in ta tsume hakan babu mai iya kawo mata wargi… Saboda tsafta da kuma natsuwarta yasa dayawa suke tururuwa wurin sayan abincinta. Ita ɗin annoba ce kaman yadda wasu ke ƙiran ta dayawa sun santa a Mayya! Dukda ita bata taɓa sanin menene maitar ba amma ta wurin kasuwanci su kan saya abin hannunta don ko babu komai akwai zaƙin hannu muddin ita tayi girki.Kan ka ce awa biyu duk ta sayar da abincin tas ta janyo baro ta ɗora kulolin a kai tana jin jiri na fusgarta saboda rabon ta da abinci tun jiya da rana gashi yanzu ana neman goma da rabi, haka ta turo wheelbarrown ta nufi gida…Razana tayi ta daka tsalle tayi baya sun saba yi mata hakan sai dai ta kasa sabo ita “Ina kudina?”Inna larai ta miƙa mata hannu a zauren wanda ko kanta bata gama sanyo wa ba, Jakan ta sunce ta miƙa mata a wurin ta zazzage ta kirga ta ga riba yadda suka saba samu ta saɓi kayanta ba sannu bare na gode tayi cikin gida abin ta, Afifah ta bita da kallo har ta ɓace kan ta turo baron zuwa cikin gida ko sauƙe kwanonin bata yi ba ta nufi bakin kitchen inda inna larai ɗin ke zaune ta duƙa “Abincina fa inna?””Laaaa kin ga mun manta da ke wallahi ina fa ta zuci zucin ajiye miki”Runtse ido tayi da ƙarfi tana danne hawayen dake taso mata idan da sabo ya ci a ce ta saba, kusan koyaushe za su yi rabon abincinsu muddin bata gidan to za’a ce mata an manta da ita ne, wani lokacin ma sai an sauƙe sai a aiketa kan taje ta dawo an rabar kuma a hana ta, hanjinta har murɗewa suke saboda yunwa amma ya zata yi?Miƙewa tayi ta nufi hanyar akurkinta inna Asabe ta kwala mata ƙira daga cikin ɗakin ta “Ina za ki da baki karɓi kuɗin nawa aikar ba?”Bata ce komai ba ta tsaya daga kanta leda da ke kunshe da kuɗi ta jefa mata a fuska”rashin kunya za ki min ki tsaya min kerere bisa kai? Kin ɗauka kin wuce ko sai na tsinka miki mari?”Duƙawa tayi ta ɗauka ta fice daga gidan ko ɗakin bata shiga ba ta riga ta san me zata sayo, ko kan ta dawo har inna Asabe ta gama tuka tuwon tallar tata na dare, ita ta zauna ta malmala tana jin kanta na sarawa ayyukan sun fi karfin shekarunta amma ya zata yi? Mutum ɗaya take da shi a duniya Aunty zee ita ma kauyen gaba da su take kuma ta kan kwana biyu bata leƙo mata ba bare ma hakkin riƙe ta na ga dangin mahaifinta ne ita kuma ga abinda Allah ya bata, sai dai ta tashi tayi sallah har ta gama malmalar tuwon na dubu goma sha biyu kaman yadda suka saba ta ɗora miyan ta kala biyu da Alaiyahu da kubewa, bayan ta gama ne inna Asabe ta tarfa mata sauran ƙasan tukunyar tukun a cikin tukunyar miyan Alaiyahun da ta gama kwashewa ganin sai kashe jiki take saboda yunwa bata son abinda ya samu kayan tallatarta sam.Sai da tayi wanke wanke tas har da kwanukan safe na tallar inna Larai kan ta shirya ana kiran Magrib tayi sallah ta fice bakin kasuwa, yanzu ma bata kula kowa abincin kawai take sayarwa har wuraren takwas ya ƙare ta tattaro ta dawo gida dama tun shidda ta sayi kifin miyan safe ta ba almajiri ya kaiwa inna Larai za ta saka cikin ƙanƙara ji take kasusuwanta kaman ana sarawa, kuɗin kawai ta ba inna Asabe ta wuce ɗaki ta kwanta idanunta na kallon sama, shikenan ita kuma a haka rayuwarta zai cigaba da tafiya? Shikenan ita kuma haka za ta ƙare? Don dai ta san kap kauyen dutsen-wai babu namijin da zai tare ta da sunan soyayya babu kuma gidan da za su amshe ta yadda ake ganinta annoba kuma duk gidan da ta shiga sai ta wargaza kuma sai an yi mutuwa kan ta fita tayi zurfi cikin tunanin ta kawai taji ana dukan kyauren palangen dake kare kofar akurkin da ɗan banzan ƙarfi sai da ta razana ta miƙe tsaye ba tare da ta sani ba.


