Novel Document

Asanadin Makwabta 3 Complete Hausa Novel Document

Description/Story:

Asanadin Makwabta 3 Complete Hausa Novel Document

Written By Zee Laluh

 

Description Of Asanadin Makwabta 3 Complete Hausa Novel Document

…..Bayan ta gama warware takardar, zuba ma content d’in ciki ido tay tana Karantawa, lokacin data gama a matuk’ar razane ta d’ago idanunta a waje ta kalli Hajiyar kawae sai taga tana mata dariya, kai idon ta tay kan Haisam shima taga yayi mata d’an guntun murmushi tare da lumshe ido, rud’ewa tay ta kasa Fahimtar komai hakan yasa ta k’ara maida idon ta kan takardar ta k’ara karanta abunda aka rubuta a ciki kamar haka,

_WE ARE SO HAPPY TO WELCOME YOU INTO OUR FAMILY ZARAH_

_It’s such a joy to be with u, We hope your presence will brightens up our days. You’re a Wonderful person Zarah, we are so lucky to know u._

*We look forward to all the Wonderful things you’ll bring to our lives. We love u so much Zaraah.*

Lokacin data gama d’agowa
tay ta waro idanu ta kalli Fanan dake tsaye a gabanta har lokacin kawai sai gani tay itama tay mata d’an murmushi, gaba d’aya sun rud’ata har Fuskarta ta bayyanar da hakan, d’age mata gira Fanan tayi Calmly ta furta “Nima na rama halin da Message d’in ki ya sani Zaraah” ta6e baki ta fara kawae sai ta fashe da Kuka Fanan ta kai hannu ta rungumo ta a jikinta a hankali take furta mata is okey, d’agota tayi bayan wani lokaci ta kama hannunta suka nufi ciki har lokacin Fatuu kuka take tasa gefen gyalenta tana ta goge k’wallan dake zubo mata, Kujerar data taso ta nufa da ita ta Zaunar da ita itama ta zauna a gefenta ta yadda suka saka Fatun a tsakiya har lokacin tanata sharar k’walla da gyalenta, Hannu Fanan ta kai ta dafa Shoulder d’inta tana ce mata ya isa haka kada tayi ciwon kai tayi mata wasa ne, Hajiya itama ta fara bata hak’uri tace mata sune suka shirya mata haka ita ba ruwan ta, daina yin kukan tayi ta sadda kanta k’asa har lokacin gabanta na d’an fad’uwa ganin komai take kamar a Mafarki don bata ta6a zaton haka daga Fanan d’in ba, a hankali ta d’an juyar da kanta ta saci kallon Haisam dake gefenta karaf suka had’a ido dashi ya kafeta da idanun shi dake a d’an lumshe da sauri ta maida kanta k’asa, Hajiya ce tayi d’an gyaran murya tace masu suyi ma Annabi salati (SAW), bayan sun gama ta fara masu Nasiha gaba d’aya kan zaman tare da kuma hak’uri da juna daga baya ta fara ma Haisam shi kadae kan rike amanar matan shi da kuma yin Adalci a tsakanin su, bayan ta gama dashi ta koma kan Fanan ta nuna mata kada ta dauki duk abunda ake fad’a akan kishiya ta d’auka ita d’in Alkhairi ce sai taga ta zame mata Alkhairin ta rufe idanunta ta kuma toshe kunnuwan ta daga dukkan wata zuga da za’ai mata kan Fateema, kada ta goyi bayan a cutar da ita domin tasan Allah baya barin cuta, tace ta ci gaba da yi mata kallon k’anwarta kamar yadda take yi mata a da, a matsayinta na babba ta zamo mai hak’uri sosae akan komai in taga tayi ba daidai ba ta nusar da ita…Sosae tayi mata Nasiha itama Fanan d’in dake jingina da kujera tana ta d’an jinjina mata kai, a k’arshe ta yaba mata sosae akan Namijin kokarin da tayi wurin yak’i da zuciyarta ta danne kishinta don Farincikin su ta nuna samun matan da zasu iya yin hakan yanada matuk’ar wahala ta nuna mata kar ta d’auki hakan gazawa face jarumta wurin yin abunda yake daidai, ta nuna more ma rayuwa shine ka sanya farinciki a zukatan mutane ba ka za6i ka saka kanka kad’ai ba hakan zai saya maka soyayya da k’ima a idon mutane, haka kuma ko bayan ba ranka za’a ji rashin ka baza kuma a manta da kai ba riba biyu kenan sa6anin ka za6i Farincikin kanka kai kad’ai ka cuta ma mutane su rink’a k’in ka k’arshe ka mutu aita murna tunawa ma da kai yayi wuya,

Kallon Haisam tay dake kishingid’e yana sauraran ta tace “ina son ka sani Fanan masoyiyar ka ce ta hak’ika tunda har ta za6i Farincikin ka fiye da nata don haka indai ka wulakanta ta wllh sai Allah ya saka mata duk da bani da haufi a kan ka kawai tuni nake maka” jinjina mata kai yay a lokacin Fanan tasa hannu ta d’an dafe goshinta jin kuka na niyyar taho mata ita kad’ai tasan abunda take going through don ma tana ta yin Addu’oi a cikin ranta, komawa Hajiya tayi kan Fatuu da kanta ke a sadde tace ta dawo gareta, farko maraba da shigowa cikin Family d’in su ta k’ara yi mata tace tasan halinta itama bata da shakku a kanta don haka kada ta sake ta canza daga yadda ta santa ga Fanan nan taci gaba da d’aukar ta matsayin Yayarta kar ta sake daidai da rana d’aya tace zata mata kallon kishiya, in tana da matsala ta sanar da ita tana da yak’inin zata bata shawarar kirki sannan ta taimaka ma mijin su wurin ganin yayi masu Adalci hakan shine son gaskiya, in Fanan tana yi mata abunda bata jin dad’i ta fad’i mata idan bata gyara ba ita ta fad’i mata duk da tasan in sha Allahu hakan bazata faru ba, daga k’arshe bayan ta gama yi masu nasihohin da suka tsuma masu jiki sosae tayi masu Addu’oi tasa Haisam shima yayi duk suka d’aga hannuwa suna amsawa har ya gama gaba d’aya suka shafa, shiru ta biyo baya duk suka cigaba da yin kallo saidai kowa da abunda ke kai kawo cikin Zuciyar shi, gaba d’aya Fatuu ta kasa sakewa don jikinta na bata Haisam kallon ta yake hakan yasa duk ta takura ga kuma yanayin Fanan data lura tana a cikin damuwa k’arfin hali kawai take hakan yasa duk ta sha jinin jikinta, kiran sallar Magrib da aka fara yi yasa Haisam mik’ewa hannunshi ruk’e da rigar shi ta sama daya d’auka yace ma Hajiya zai je salla tai mashi a dawo lpy, d’an d’aga ido Fatuu tayi tana kallon bayan shi har ya kusa fita sannan ta maido shi k’asa, zuciyarta ce ta shiga raya mata wani abu game da shi, bayan fitar shi Hajiya ta mik’e tace masu suje suyi salla, Fanan ce ta fara mik’ewa da d’an murmushi ta kalli Fatuu data d’ago tana kallonta ta mik’a mata hannu, a sanyaye ta kama hannun ta mik’e suka nufi ciki.

Yadda hakan ta faru, bayan Haisam sun gama Magana da Fanan kan zuwa Nigeria ranar talata, da yamma Hajiya Maryam ta kirata don ta ji halin da ake ciki game da tahowarta nan take sanar mata yadda sukai da Haisam kan zuwa Nigeria ta yi ma Hajiyar Magana da kanta, nan Hajiya Maryam taji dad’i sosae don tasan da wuya in Hajiyar bata bari an saki Fatun ba Saboda su duka sun nuna basu so kuma tasan yadda take ji dasu gaba d’aya, hakan ne yasa washe gari da Hajiya ta kira Hajiya Maryam game da zancen dawowar Farha da Maganar data yi mata sam bata damu ba, tun bayan da suka yanke zuwa Nigeria Haisam ya kasa samun natsuwa, damuwa tayi mashi yawa don yasan shi dae ba iya sakin Zaraah zai yi ba yadai biye mata ne don ya kwantar mata da hankali k’arshe kuma yasan indae suka zo Nigeria yak’i sakin Fatuu to abun zai k’ara kwa6ewa ne, hakan yasa ya yanke tunkararta akan hakan, Ranar Alhamis da daddare ya isketa a d’aki lokacin tana zaune akan gado tana latsa wayarta, tana ganin shi ta d’ago tana mashi dariya ya nufi bakin gadon ya zauna shima yana mata murmushi, aje wayar tayi ta matso inda yake ta kwanta a bayan shi ta yadda yay kaman ya goyata ta sak’alo hannuwanta a wuyan shi nan ta shiga fad’a mashi kalaman soyayya, sosae yaji fargabar sanar da ita abunda ya kawo shi k’arshe dai yay k’arfin hali yace mata magana yake so zasu yi, tana jin hakan ta sake shi ta dawo daga gefe tana kallon shi, d’an jimm yay ta kafe shi da ido daga baya ya fara magana gently, ce mata yay Alfarma yake son ya nema a wurinta for the first time a zaman su, jinjina mashi kai tay gaba d’aya ta maida hankalinta akan shi, ce mata yay ya zauna yayi dogon tunani gaskiya idan ya saki Zarah bai mata Adalci ba zai zama ya cuce ta ne Saboda shi ya fara saninta sannan tayi k’arama ace ta zama bazawara, wani kallo take bin shi dashi yanayin fuskar ta ya canza da alamun d’aurewar kai tace to mi yake nufi kenan, kauda idon shi yay tana ta kallon shi can ya juyo ya kalleta yace “I can’t divorce her……” waro ido tay hankali tashe take kallon shi, hannu ya kai zai kama hannunta da sauri ta janye ta fara k’ok’arin nufar can d’ayan 6angaren gadon ta sauka, da sauri ya idasa hayewa saman gadon ya cafkota, rungume ta yay k’am ta fara kokowar kwacewa amman ta kasa kawae sai ta fashe da matsanancin kuka ta fara fad’in ita zai yaudara bacin sun gama Magana shine zai zo yace bazai saketa ba dama tasan yana sonta ne shiyasa ya aureta yanzu kuma daya san ita tana haihuwa shine zai ce bai iya rabuwa da ita to indai ya za6i zama da ita ita Allah bazata cigaba da zama da shi ba, sosae ta tashi hankalin ta sai k’ok’arin k’wace kanta take k’arshe kawai sai ya had’e bakunan su ya fara kissing d’inta deeply don yasan hakan zai iya calming nata, ya d’an d’auki lokaci yana mata hakan kafin ya saki bakin nata jikinta sai kerma yake tana sheshsheka, kwantar da kanshi yay saman kanta cikin sigar rarrashi ya fara magana yace mata yasan ita ba mai son kai bace tayi tunani, in ya saki Zarah zai cuceta ne yasan bazata so hakan gareta ba ko kuma sister d’inta Farha tayi aiki da Hadisin manzo SAW da yace love for ur brother what you love for urself, a yadda yasani tana son Zarah sosae miyasa bazata tausaya mata ba, sai huci take ta hau girgiza mashi kai tace ita dai bazata iya zama da ita matsayin kishiya ba, miyasa zai saka mata rai yayi mata alk’awarin zasu zauna su biyu, ce mata yay ya gaya mata already da aure a tsakanin su amman yanzu zai iya yi mata wani daga Zarah bazai k’ara Auren wata ba su biyu zasu zama matan shi har k’arshen rayuwar shi, shiru tay kaman mai nazarin wani abu can ta d’ago ta kalle shi idanunta sharkaf da hawaye tace “Tell me the truth, do you love Zarah?” Shiru ya d’an yi yana kallonta can ya jinjina mata kai kawai sai ta fashe da kuka ta fad’a jikin shi tana fad’in ita daman tasan son Zarah yake shiyasa tun farko ya auretan in ba haka ba miyasa bai sa Abbas ya aureta ba daga baya ya saketa sai shi daga baya kuma yazo ya kwanta da ita, tasan itace First love d’in shi dama ita ba son ta yake ba kawai tausayinta ne yasa ya aureta don haka zata bar shi sai suji dad’in zama da juna, sosae take kuka yana rungume da ita cikin kwantar da murya yace mata wayace mata bai sonta, da farko da akai mashi Maganar aurenta Saboda yasan ba soyayya suke ba shiyasa ya nuna bazai aureta ba don bai d’auka Maganar da ta yi mashi ta zai aureta ba da gaske take Saboda lokacin a wurin shi tayi k’arama da wannan Maganar…

Asanadin Makwabta 3 Complete Hausa Novel Document txt

File Name   Asanadin Makwabta 3… Hausa Novel Doc.
Title    Asanadin Makwabta 3
Author            Zee Laluh
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/09/2024
File Size    240KB
Format Size    TXT
Book Price    400
Phone No   09013804524
Download Asanadin Makwabta 3 Complete Novel Document By Zee Laluh 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button