Halysaah Page 176 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 176Har yammacin ranan nan Khaleesat bata dena kukan da take ba, gashi tun da gari ya waye taki shan ko ruwan zafin da ake bata saboda miscarriage din da tayi balle kuma ta ci abinci, wankan ma sai da Mami ta sakata gaba tayi mata, duk ta fita hayyacinta, Safiyyah na dakin amma baza kace tana nan ba don far end of the room take zaune ba um ba um um, kana kallonta kasan ta shiga damuwa sosai ita ma, ko kadan bata da courage din ce ma Khaleesat komai at this Stage, Gimbiya Firdausi ta shigo dakin tana kallon Mami dake zaune kusa da Khaleesat tace “Aseeyah an zo za ayi mata ta’aziyyah ne i think his friends, kawarta ta rakota sai su fito parlorn ko?” Mami ta kalli Khaleesat dake rike da carbin da ta sake bata, Kuka Khaleesat ta fara yi tace “Dama ana yin ta’aziyyar wanda bai mutu ba?” Gimbiya Firdausi ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta fita daga dakin, haka nan Mami ta lallaba Khaleesat tace ita suka zo gaidawa da jiki ba ta’aziyya suka zo ba, a haka aka samu ta sauka daga kan gadon Safiyyah na rike da hannunta suka fita zuwa Main parlor, babu wanda Khaleesat ta amsa ma a cikinsu hawaye masu zafi na zuba idonta jin ana ce mata Allah ya ji kansa, she believe her husband is not dead shi yasa taki amsa ma kowa a cikinsu, suka gama addu’o’in su sannan Mukhtar yayi leading dinsu su kusan takwas suka fita daga parlon ko wannensu jiki a sanyaye cause Ajay is the most nicest guy to be with, Khaleesat ta daga kai ta kalli Safiyyah da ta sunkuyar da kai ita ma hawayen ke zuba idonta sosai, dai dai nan Jay ya shigo parlon, Safiyyah ta ɗaga kai tana kallonsa, sosai zuciyarta ya kara karyewa ganin yanda ya koma saboda grieve, he isn’t even looking normal, tare ya shigo parlon da Abdul dake biye da shi a baya, Khaleesat dai kallonsu take babu ko kiftawa, kallo daya Abdul yayi mata ya sauke idonsa a hankali, ya karasa cikin parlon ya zauna, Jay ya juya kawai ya fita daga parlon ya tafi jikin wani kofa ya jingina yana kallon sama, Abdul na kallon Sophie yace “Safiyyah, ya karin hakuri?” Kai kawai Sophie ta gyada masa ta kasa cewa komai tana goge hawayen dake sauka idonta, ya maida dubansa kan Khaleesat but seeing the way she is crying ya kasa ce mata komai ya sauke idonsa, lokaci daya zuciyarsa ya karaya, da kyar dai daga karshe yace “Kiyi hakuri Khaleesat, Allah Ubangiji ya gafarta masa, Allah ya sanyaya maki zuciyarki ya baki hakurin wannan rashi” Ta kara fashewa da matsanancin kuka tace “Ni wallahi mijina bai mutu ba fa….” Abdul ya sauke idonsa, can ya kwantar da murya yace “If you have that feeling Khaleesat keep on praying, duk inda yake Allah ya bayyanasa cikin koshin lafiya da aminci, mu ma za mu yi ta addu’a in sha Allah” Sai yau wani ya gaya ma Khaleesat abinda yasa taji wani salama ya sauka zuciyarta, ta gyada masa kai tana goge hawayen dake sauka idonta da sauri, ita dai Safiyyah bata daga kanta ba, Abdul yace “Amma kuma idan baki kwantar da hankalinki ba ta yaya za ki nutsu har kiyi addu’a Khaleesat, so try to be strong and confident ki ci gaba da addu’a kin ji….” Wasu hawayen na sauka idonta ta kara gyada masa kai tace “Nagode Ya Abdul” a haka Abdul ya fita ya bar su a parlon duk jikinsa a sanyaye, ya tarar da Jay tsaye yayi nisa tunanin da yake. Tun faruwan lamarin nan sai yau da aka yi kwanaki uku Mai martaba ya fito, shi ma ta dalilin relatives din late wife dinsa da suka taho daga Ethiopia har su goma, mata bakwai sai maza uku, Mai martaba bai iya ya kalli idon ko mutum daya a cikinsu ba, kana ganinsa kasan yana cikin matsanancin damuwa, dukkaninsu da yaren turanci suka yi masa ta’aziyyar don basa jin Hausa, sosai zaka ga alhinin dake kwance fuskokinsu gaba daya, daga karshe Mukhtar ya kai baƙin mazan masauki a nan gidan sarki, matan kuma Hajiya Shafa’atu tayi masu iso har zuwa bangaren da aka gyara masu me dauke da dakuna uku manya da babban parlor har da kitchen a bangaren, cimar kasar su aka yi masu iri iri tun basu karaso ba aka kai masu bangaren, Da turanci Hajiya Shafa’atu ke sanar masu matar Junaid din tana bacci idan ta tashi sai su shigo bangarenta su yi mata ta’aziyyah, daga haka ta fita daga part din. Ita ma dai Aunty sai yau ta samu ganin Mai martaba, a duk kwanakin nan tana cikin damuwa sosai ganin har ita Mai martaba yayi restricting dinta daga shiga inda yake, to ko dai ya gano wani abu ne, banda haka ai ita ya kamata ace tana kusa da shi tana karfafa masa gwuiwa tare da kwantar masa da hankalinsa, ga kuma Walid can a asibiti scan ya fito ana tunanin ya samu matsala a spinal cord dinsa idan ba wani ikon Allah ba ba lallai ya tashi ba, yanxu haka wani asibiti a India za a kai sa, duk har da wannan ya kara birkita mata lissafi, ko abinci bata iya ci, da daddare ma bata iya bacci, a daren ranan nan Mai martaba ya tafi wajen Khaleesat for the first time tun faruwan abun…. Days went by slowly then months, amma a haka Khaleesat ke zuba ido kullum tana jiran ranan da Ajay zai dawo, abunta ya dinga tabarbarewa ta dawo kamar ta fara loosing mind dinta ne, she is always saying things that are not making sense, ko gaisuwa aka yi mata sai ta sakar maka kuka ta fara rantse rantse tace ita mijinta bai mutu ba yana nan kuma zai dawo ya gaya mata haka a mafarki, gaba daya taki tsayawa ta nutsu tayi takaba wai a haka su Mami da Aunty Faridah suna saka mata ido, ga kuma Dr dake gidan takanas saboda ita, the Dr is always by her side, kusan kullum yanda take ganin rana haka take ganin dare baccinta baya wuce minti ashirin zata farka a firgice, sai dai idan likitanta tayi mata alluran bacci shi ne zata dade tana bacci, kuma babu ranan da zata rufe ido bata yi mafarkin Ajay ba, duk ta rame ta fita hayyacinta ta dawo kamar me matsalar ƙwaƙwalwa whereas brain dinta Lafiya lau don sai da Mai martaba yasa aka kai ta asibitin ƙwaƙwalwa, abinci sai by the grace of God ake tilasta ta ko cokali daya ne ta ci, sai kuma ruwan lipton, sosai likitan dake kula da ita ke jin tausayinta da halin da take ciki abu almost 5 months amma kullum kamar sabo yake a wajenta, banbancin ta da Jay ƙalilan ne don shi baya cewa Ajay bai mutu ba tunda a gabansa aka harbesa kuma har sannan last words dinsa da yace masa he should take care of Jeeddah sun ki fita daga kunnensa kamar a lokacin yake gaya masa haka, babu ranan da bazai zubda hawaye ba a gidan nan, kullum missing din Ajay kara yawa yake a ransa, yaji ina ma ana maida hannun agogo baya ko duk abinda ya mallaka Ajay yace yake so he will sacrifice it for him wholeheartedly, he regrets everything that happened years ago, yayi da ya sanin duk abubuwan da yayi akan Halysaah… kullum Hajja kara jan Jay take a jiki tana basa baki bayan ta fahimci su fa ya kamata su fara daukan dangana kafin su daura Jay da matar Ajay a hanyar yin hakan su ma…. 7 months later Mai martaba ya biya aka kai Khaleesat Turkey For therapy sannan a binciki lafiyarta don abun nata is getting too much day by day, suka je ita da Aunty Farida, likitan ta, da Mukhtar da yayi masu rakiya, a watannin da suka yi a Turkey Aunty Farida babu wani improvement din da ta gani sai kara rikicewa ma da lamarin Khaleesat ya kara yi, ga wani kakkaryewa da gashinta yake yi, kana jan gashin zai biyo ka kuma me yawa, hankalin Aunty Farida ya tashi sosai, nan ta fahimci kawai rokan Allah za a dukufa da yi mata babu wani zancen asibiti, haka nan suka tattaro suka dawo Nigeria kawai. Bayan sun dawo Nigeria Aunty Farida tayi shawara da Mami a bari ta tafi da Khaleesat kano tunda ta fita takaba, duk da bata san yanda ake yi a gidan sarauta ba amma tana son ta tafi gida da ita, a hankali Mami tace “Haka ne Farida, in tayi nisa da Emirate din nan damuwarta zai ragu ta fara accepting reality, zan yi magana da Mai martaba da Hajja sai a kai ku Kanon in sha Allah, ni kaina nayi wannan tunanin” A ranan kwana Khaleesat tayi tana kuka kamar ranta zai fita wai ita bazata je Kano ba she want to be in her husband’s part, sai da Mami ta dinga lallabata kan cewa kwana uku kawai zata yi a kanon sannan a dawo da ita duk don ta yarda ta bi Aunty Farida, a haka tabi Aunty Faridah suka koma kano tare da kayanta kala uku kacal. Mami ta fito bangarenta wajen karfe biyar na yamma ganin tun da gari ya waye Jay bai shigo ba, a kwanakin baya part dinta ya dawo kwana gaba daya yace mata he is having nightmares, wani lokacin ma a dakinta yake kwanciya duk da baccin nasa rabi da rabi ne, sai ya kai karfe uku bai yi bacci ba, wani lkcin har kusan asuba, yanxu kuma all of a sudden taga ya koma ɓangarensa, kuma sai ya kai yamma bai fito ba, tana isa ta bude kofar parlon ta shiga, breakfast dinsa ta gani a parlon da lunch da aka shigo aka ajiye duk babu wanda ya taɓa a ciki, tayi ta kallon abincin, sai kuma ta karasa Bedroom dinsa, knocking tayi hade da sallama tace “Jawwad” jin bai yi responding ba ta bude kofar dakin ta shiga, sai taji yana bandaki yana wanka, ta kalli saman gadon taga alamar tashinsa kenan, satchets din pills da ta gani kan gado ta karasa ta dauka tana juya satchets din tana kallon maganin, ta kalli kofar bandakin sai kuma ta juya ta fita daga dakin ta koma part dinta tana ta kallon maganin, wayarta ta dauka tayi snapping pills din sannan ta tura ma Likitan dake duba Khaleesat tana tambayarta magungunan menene, after a while Likitan ta tura mata feedback, Mami ta dinga kallon feedback din Dr din with shock, sosai jikinta yayi sanyi, lokaci daya hawaye ya cicciko idonta ta dafe kanta da taji yayi mata nauyi, ta fi minti goma zaune parlon cikin tashin hankali daga karshe kawai ta mike ta tafi bedroom dinta tana hawaye, After almost 30 minutes taji sallamansa a bakin kofar dakin, ta amsa tana ci gaba da gyara kayan da take yi a press dinta, ya shiga dakin ya ɗan kalleta sai kuma ya sunkuyar da kai ya zauna, a hankali yace “Ina wuni Mami?” Mami bata kallesa ba tace “Lafiya lau, sai yanxu ka tashi?” Ya gyada mata kai kawai, Tace “Tun safe?” Ya sauke idonsa yace “Ina tashi inyi sallah” Mami bata sake ce masa komai ba tana ta gyaran kayanta, a hankali yace “Mami kin shigo part dina ne?” Mami ta kallesa a karo na farko tace “Me ka gani?” Yayi saurin sunkuyar da kansa yace “A’a kawai tambaya nayi….” Tace “Ban shiga ba” Shiru yayi yana tunanin ko Hadiyah ce ta shiga, duk da har sannan bai maidata ba amma ta kan shigo tayi masa gyare gyare ta share ko ina ta goge, barin idan yana part din Mami idan ya koma zai ga ta gyara ko ina, to amma bai ga anyi gyara ba a part din ai tunda yana ciki, kuma yasan ta shigo taga yana baccin shi yasa bata yi gyaran ba, Mami tace “Ka ci abinci ne?” Duk da bai ci ba ya gyada mata kai kawai alamar ya ci, don yasan ba iya ci zai yi ba, Mami zata yi magana aka bude kofar dakin ta juya tana kallon kofar, Khaleesat ce ta shigo dakin tana tafiya kamar iska zai kadata ta fadi, da mamaki Mami ke kallonta har ta karaso cikin dakin ta zauna kasan carpet looking so tired, ta kwantar da kanta jikin gadon Mami, Mami ta karasa kusa da ita ta zauna gefen gado tace “Halysaah” Khaleesat ta daga idanuwanta a hankali ta kalleta, Mami tace “Daga ina kike?” Murya can kasa tace “Kwana uku ai aka ce zan yi” Mami ta dinga kallonta don shekaranjiya suka tafi, can dai tace “To ke da wa kika dawo yanxu?” Tace “Ni kadai” Da mamaki Mami tace “Ke kadai? A mota suka sa ki kika dawo? Ki gaya min gaskiya Khaleesat, basu sani ba kika taho ko?” Lokaci daya hawaye ya cika idonta, ta fara kuka a hankali tace “To baza su bar ni in dawo ba Mami” Mami ta dafe kanta, can tace “Yaushe kika bar gidan?” Tana goge hawayen dake zuba idonta a hankali tace “Da safe” Mami tace “A ina kika hau mota?” Shiru tayi, sai kuma ta daga ido ta kalli Mami tace “Bani da kudin mota, sai na tafi tashar Mariri da kafa, wata mata ce ta biya min kudin mota a tasha da nace mata banda kudi” Mami ta kasa cewa komai, shi dai Jay ya jinginar da kansa da kujera yana kallonta cike da tausayinta, Mami ta jawo wayarta don ta rufe layin da aka santa da shi tun jiya ta bar personal line dinta a kunne, tasan kilan su Aunty Farida na ta kiranta, ta kalli Jay tace “Wayar ka a kashe yake ne?” Ya gyada mata kai, Mami na bude layinta sai ga kiran Aunty Farida ya shigo, suna gaisawa Mami tace “Wallahi yanxu ta shigo Farida shi ne ma har na kunna wayar nasan kuna ta nemana….” Mami ta kasa cewa komai tana sauraron Aunty Farida, can ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Za mu yi magana Farida” Daga haka ta katse wayar tana kallon Khaleesat dake hawaye, cikin rawan murya tace “Mami ni nafi son in zauna a nan har sanda zai dawo, don Allah ayi hakuri a bar ni in zauna a nan, kar ya dawo bai ganni ba” Tana fadin haka ta fashe da kuka a hankali, Jay ya mike kawai ya fita daga dakin walking slowly, ya koma parlor ya zauna rike kansa, Mami dai ta kauda kai jin idanuwanta sun ciko da kwalla, can Mami ta share idonta tace “Yaushe kika fito daga gidan Halysaah?” A hankali Khaleesat tace “Ana sallan asuba” Mami bata sake ce mata komai ba ta mike ta nufi bandakinta tana share hawayen dake zuba idonta, ga damuwar Jay dake neman lalata rayuwarsa ga kuma na Khaleesat yanxu, duk abun ya taru ya hade mata, ruwan wanka ta hada ma Khaleesat a bandakin ta sannan ta fito tace “Ki je kiyi wanka, bari in sa a kawo maki abinci…” Khaleesat ta mike ta nufi bandakin tana tafiya a hankali, tsabar wahala har wani disashewa haskenta yayi…..
Visit Kundin Hausa Novel For More Novel




