Hausa novels

Halysaah Page 35 By Khaleesat Haydar

A hankali Khaleesat ta ɗan bude curtain din dakin Aunty Farida tana leko cikin parlon ta hada ido da su gaba daya, sauke idonta tayi ta shigo parlon walking slowly ta tafi ta zauna kan kujera kanta a kasa, tun da taji sallama ta tashi ta tafi dakin Aunty Farida don saka Hijab dinta, gaishesu tayi still not looking at them, Jay ne kawai ya amsa yana kalllonta calmly yace “How are you feeling now Housemate?” Sai a sannan ta daga kai ta kallesa a hankali tace “I am much better now” Kallon Ajay tayi suna hada ido ta sunkuyar da kanta tace “Ina yini?” Yana danna wayarsa yace “Fine” Aunty Farida ta shigo parlon daga kitchen ta ajiye masu tray din Can drink da ruwa da taje dauko masu, sannan ta zauna kan kujera tana kara gaishesu, Jay yace “Ya me jiki” Aunty Farida tace “Da sauki, abinci ne dai bata ci har yanxu” Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, sauke idonta tayi ta dau plate din abincin da Aunty Farida ta zuba mata not long ago, ta bude murfin ta ajiye sannan ta dau spoon ta fara cin abincin a hankali, Aunty Farida na kallonsu tace “Bari in kawo maku abinci” Ajay ya kalli Jay, Jay yace “A’a mun yi breakfast Aunty, mun gode” Aunty Farida tace “To ai rana tayi yanzu” Bata jira taji me zai ce ba ta tafi kitchen zata zubo masu abincin, ita dai Khaleesat a hankali take cin abincin hannunta, mikewa Ajay yayi, Jay ya sa hannu a aljihunsa ya ciro wayarsa, Ajay yace “Zan yi waya a waje” Daga haka ya fita daga parlon kafin Aunty Farida ta fito daga kitchen, Jay yayi murmushi bai dai ce komai ba, bude wayarsa yayi yaga miss calls din Safiyyah har shidda, yayi dialing number dinta ya saka handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga kamar jira take, yayi kasa da murya yace “Can you hear me Safiyyah?” Tace “Ina jin ka, plss ba a san inda Khaleesat take bane tun ranan asabar, kuma ni nasan bata da inda zata je a garin kano” Yace “Where are you at now?” Da sauri tace “Nima a kano nake ai, jiya da yamma na dawo daga Maryland shi ne na zo gidansu yau nake samun labari she is away from home tun ranan Saturday after receiving the news of her marriage with Abdul, wai Abdul fa aka daura mata aure da” Safiyya na kai wa nan ta fashe da kuka, Jay yace “I mean are you at home or where?” Cikin kuka tace “A’a yanxu na baro gidansu, ina bakin titi ma haka, i am just confuse, Khaleesat bata da kawaye bata zuwa ko ina, i don’t know where she will be now, i am disturb don Allah in kasan inda take kar ka boye min plss Ya Jawwad trust me” Calmly yace “Look, this should be confidential Safiyyah, i trust you are saying nothing to anybody about this….” Da sauri Safiyyah tace “Na rantse babu wanda zan ce ma komai Ya Jawwad, trust me, i am also not in support of the fruitless marriage” Jay yace “Ohk, here is ur frnd speak to her…..” Mikewa yayi ya mika ma Khaleesat wayar, ta amshi wayar tana kallon screen din dama tun jiya take wishing ace Sophie na kusa da ita ko ba komai zata dinga Consoling dinta tana karfafa mata gwiwa da bata assurance, lkci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace “Sophie” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Khaleesat, i am so happy you are safe and sound, dama fatana kenan, plss kina ina haka yanxu in taho don Allah” Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace “Bana kano Sophie” Da mamaki Safiyya tace “To kina ina?” Khaleesat ta daga kai ta kalli Housemate dinta dake kallonta, sauke idonta tayi da kyar tace “Ina Lagos” Safiyyah tace “Lagos wajen wa? Ko wajen Aunty Farida?” Khaleesat tace “Um” Safiyyah tace “Amma Umma bata san kina nan ba” a hankali Khaleesat tace “Bata sani ba” Safiyya ta sauke wani ajiyar zuciyar tace “Pls kar ki tada hankalinki kinji kawata, i know ur Housemate won’t allow u do that, kuma in sha Allah babu zaman aure tsakaninki da Abdul don bai yi deserving din ki ba, i can’t imagine what he will turn you into, in Allah ya yarda bazai ci nasara akan ki ba, Allah zai raba auren cikin gaggawa, shi kadai yasan mugun Intention din dake ransa akan ki shi yasa yayi haka, amma Allah ya fi sa” Khaleesat dai gyada mata kai kawai take hawaye na sauka idonta ta kasa cewa komai, Housemate dinta ya mike ya nufeta ya amshi wayar a hannunta ya koma ya zauna yace “Safiyyah” A sanyaye Safiyyah tace “Na’am Ya Jawwad, Please kawata bata da wanda zai tsaya mata akan issue din nan, ba da intention me kyau ya saka aka daura auren ba wallahi, mugu ne azzalumi, har abusing dinta yana yi” Jay dake sauraronta yace “In sha Allah we will try our very best ki taya mu da addu’a” Safiyyah tace “In sha Allah, but how can i be reaching her?” Yace “Don’t you have her aunt’s number” Safiyyah tace “Sure ina da shi, i will be calling her ta wayar Aunty Farida” Jay yace “Keep this confidential pls Safiyyah” Safiyyah tace “Trust me Ya Jawwad, i now have rest of mind knowing my frnd is safe” Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar, Khaleesat ta ajiye plate din abincin hannunta don ta kasa ci, iya spoon uku kawai ta iya yi, tuni Aunty Farida har ta ajiye ma Jay abincin da ta zubo ta nemi waje ta zauna, sai da ta jira suka gama waya da Safiyyah sannan ta kallesa tace “Ina Junaid din ga abincin na zuba maku” Jay yace “Aunty bamu dade da cin abinci ba da gaske” Aunty Farida tace “Ai ko in baku ci ba bazan ji dadi ba, haka jiya ku ka bar min abincin ku ka ki ci, yanxu fa karfe biyu da rabi ake nema kuma breakfast kace kawai ku ka yi” Jay dai murmushi kawai yake, can yace “Toh zan ci Aunty” Tace “To ko kai fa, ina Junaid din kayi masa magana ya shigo ku ci” Jay na shafa kansa yace “Ai shi ya ci snacks a mota bazai ci abincin ba na sani, bai fiye cin abinci da rana ba” Aunty Farida tace “Ikon Allah to saboda me?” Jay yace “Haka yake, iya breakfast da Dinner kawai yake yi” Aunty Farida tace “Iko sai Allah” Jay na kallon abincin da Khaleesat ta rage ya mike ya dauko yace “Zan ci wannan kar mu bata abincin Aunty” Aunty Farida tace “Don Allah ka ajiye ka debi abinci ga plate nan Jawwad” Yace “Aunty wannan fa ya isheni ba iya cinyewa zan yi ba ma” Spoon din ya dauka ya fara cin abincin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, Aunty Farida tace “Ai shikenan” Karfe uku da yan mintuna Ajay da Jay suka bar gidan, Jay ne ke driving din idonsa akan titi yace “To ya ku ka yi da Lauyan?” Ajay yace “He said we should meet in kano” Jay ya ɗan kallesa yace “Zuwa gobe kenan?” Ajay yace “Sure, tomorrow in the morning za mu tafi kano” Jay bai sake cewa komai ba har suka isa gida, yau dai traffic din da ɗan sauki, bayan Jay yayi parking ya juya yana kallon Ajay yace “Please since gobe za mu tafi kano ka bar maganar hotel da kace zaka koma” Ajay yace “Ai matar ne ta fiye takura da sa ido” Jay yayi dariya bai dai ce masa komai ba suka sauka zuwa cikin gidan, Ummi na zaune parlon Hadeeyah na kwance kusa da ita da daura kanta a saman cinyar Ummin, ba tare da Ajay ya kalleta ba ya gaisheta a takaice zai wuce sama Hadeeyah ta gaishesa ya amsa yana haura stairs, Jay ya zauna parlon ya gaida Ummi ta amsa tace “Sai yanxu? Ko dai ba Bar beach din ku ka je ba?” Jay ya ɗan buda ido yace “Mun fasa” Yana magana ne yana kallon Hadeeyah da ta hade rai tana danna wayarta kamar bata gansa ba, Ummi ta kalleta tace “Ke baki ga yayanki bane” Hadeeyah na ci gaba da danna wayarta tace “Oh, ok, Good evening” Jay yace “Ya hanya?” Tace “Lafiya lau” Ummi na kallonsa tace “Mami tana sama” Jay ya mike yace “Ohk” Sama ya wuce, Hadeeyah ta bi sa da kallon gefen ido har ya fara hawa stairs, bayan ya tafi Ummi na kallon Hadeeyah tace “Fadan ku ka sake yi kenan?” Hadeeyah ta ɗan yatsine fuska taki cewa komai tana danna wayarta, Ummi ta kyabe baki tace “Kun fi kusa dai” Jay na bude kofar dakin da yasan Maminsa na ciki ya sameta zaune tana waya, ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi mata side hug ya jinginar da kansa a shoulder dinta a hankali yace “Mami” Mami tayi ma warce suke wayar sallama ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa tace “Ina ka je tun safe Son? I was thinking zaka zo airport kayi picking din mu” Jay ya ɗan kalleta yace “Karfe nawa ku ka iso Mami?” Tace “Karfe sha daya da rabi na safe” Jay yace “Mun fita ne da Ajay, Ummi bata gaya maki ba” Mami tace “Kaga da ubansa ne zai sauka Lagos duk abinda yake yi barin sa zai yi ya tafi ya taro sa, amma kai uwarka ta sauka Lagos ya ja ka kun tafi gantali” Jay bai ce mata komai ba, Mami na kallonsa tace “Duk karatun ne yasa ka fada haka? Are you okay?” Jay yace “Stress din tafiyar da nayi zuwa Nigeria ne” Mami tace “Nasan shi zai zugaka ku dawo Nigeria kar ka biyo min ta UK” Jay ya ɗan hade rai yace “Ya fa riga ni dawowa Nigeria Mami, ni ba jiya na dawo ba, shi kuma ai tun last week yake Nigeria” Mami ta tabe baki bata ce komai ba, Jay ya mike ya nufi kofa yace “Zan je inyi wanka” Mami tace “Dama gobe ka shirya mu tafi Bauchi ban san gantalin da yake jan ka ku ke yi a Lagos ba, kai da ko ance ka sauka Lagos baka taba yarda sai gashi saboda Junaid na lagos kai ma ka zauna a lagos, to gobe za mu tafi Bauchi kuma Hadeeyah ma a can zata yi hutu” Jay ya juya ya kalleta yace “Mami ni ban gama abinda nake yi ba, kawai ku yi tafiyar ku” Bai jira me zata ce ba ya fice daga dakin. Wajen karfe biyar da rabi Jay da Ajay suka sauko downstairs, dakin dake kasa suka nufa don Mami na ciki tare da wata bakuwarta warce suka hadu da dadewa a Saudia suna zumunci sun zama kaman en uwa, jin Mami ta shigo Lagos sai matar ta taho gidan gaida Mami tunda ita ma a Lagos din take, Ajay ya zauna kan 1 sitter dake dakin ya gaida Mami sannan ya gaida frnd dinta, Jay ma ya zauna ya gaida kawar Maminsa, matar me suna Hajiya Batula ta amsa da fara’a tana kallonsu sai kuma ta kalli Mami tace “Wanne ne son din naki a ciki Hajiya?” Mami tayi pointing Jay tace “That is my son” Matar na kallon Jay tace “Maa sha Allah, ai kuwa ga kama na gani” Shi dai Ajay danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba, Jay ya mike yace “Mami za mu je Gym ne” Mami ta kallesa tace “Da yamman nan ga uban traffic din Lagos ne zaka je Gym?” Jay yace “Ai ba nisa Gym din” Hajiya Batula tace “Nan Area din ma ai da Gym ba sai sun je da nisa ba” Jay ya kalli Ajay yace “Mu je” Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa Jay ya bi bayansa suka fice daga dakin, Hajiya Batula tace “Amma ɗan uwansa ne wannan din ai ko, naga suna yanayi sosai” Mami tace “Eh Cousin dinsa ne” Hajiya Batula tayi kasa da murya tace “Ko dai shi ne ɗan sarkin dai?” Mami ta tabe baki tace “Shi ne” Hajiya Batula tace “Ya sunansa?” Mami tace “Sunansu daya Ahmad amma Junaid ake kiransa” Hajiya Batula tace “Ikon Allah, shi kam Jawwad babu ruwansa…” Cike da takaici Mami tace “Ni babban bakin cikina yanda har yanxu Jawwad bai san ciwon kansa ba, hakan na ci min tuwo a kwarya wallahi, controlling dinsa kawai yake yana bin sa, ko a America din ma Junaid din ne ke juyasa” Hajiya Batula tace “A’a gaskiya bai san ciwon kansa ba naga alama, shi ko kishi baya yi, kuma gaskiya Mai martaba ya nuna son kansa a fili karara nada ɗan sa da yayi Yarima me jiran gado a maimakon Jawwad, ina ce Jawwad din ya girmi ɗan sa?” Mami tace “Ya basa watanni har uku” Hajiya Batula ta rike haɓa tace “Amma in tambayeki mana Fulani, bayan rasuwan mahaifin Jawwad wato me martaba Sarki Ahmadu Yusuf shi brother din nasa wanda shi ne sarkin yanxu bai nemi rikon Jawwad a gabansa ba?” Mami tayi shiru, can tace “Cikin Jawwad na da wata bakwai mahaifinsa me martaba ya rasu aka nada kaninsa wato mahaifin Junaid, dama su uku ne gun babansu Sarki Yusuf Ibrahim, daga Mahaifin Jawwad wanda shi ne babba sai Mahaifin Junaid sannan Maimuna warce nake gidanta yanxu suna kiranta da Ummi….” Hajiya Batula tace “Ikon Allah, to amma….” Shigowar Ummi dakin ne yasa Hajiya Batula tayi saurin canza topic din tace “Yanxu goben za ki koma Bauchi kenan Hajiya?” Mami tace “In sha Allah” Ummi ta ajiye plate din hannunta tace “Sannun ku, gashi nan kaza na tsaya gasa maku” Hajiya Batula na murmushi tace “Allah sarki, sannu da aiki” Ummi tace “Bari in kawo maku drinks din, a can parlor mai aikin ta ajiye” Daga haka ta fita daga dakin, Mami tace “Da ma kin ci gaba da maganar ki, ita ma ai bata so Junaid din da aka nada Yarima me jiran gado ba” Hajiya Batula tace “To ke sai kika zuba ido aka yi hakan Fulani? In uban Jawwad din bai mutu ba a ina kanin nasa zai samu har yayi sarauta? Kuma shine bazai yi kara ya nada ɗan yayansa da ya mutu ya bar masa sarautan Yarima me jiran gado ba sai ya nada ɗan cikin sa?” Mami tayi wani murmushi tace “Ni fa ko a jikina hakan da aka yi, Jawwad is doing fine beside shi mulki ma baya gabansa, as far as my son is okay, i think da a nada sa Yarima da kar a nadasa duk daya…” Hajiya Batula tace “To halan Junaid din kadai sarkin ya haifa?” Mami tace “Wani Junaid? Amaryarsa da suke kira da Aunty na da ɗa me shekara 29, ita in son samu ne ma a nada ɗan ta Yariman ai” Hajiya Batula ta rike haɓa tana kallon Mami. Ajay yayi parking kenan bayan sun dawo gida wajen karfe bakwai na dare ya kalli Jay zai yi magana wayarsa ya fara ring, ya dauka yana duba me kiransa ganin number wani abokinsu ne da kamar bazai yi picking ba kawai sai kuma ya daga ya kai kunne, after few seconds of listening to what the frnd was saying ya zaro ido yace “What???” Kallonsa Jay yayi da sauri don intonation din da yayi using ya nuna ba lafiya ba, Da kyar Ajay ya cire wayar a kunnensa yana kallon Jay dake kallonsa shi ma babu ko kiftawa, Nan da nan Jay yaji hankalinsa ya tashi don babu inda mind dinsa yaje immediately sai gun Khaleesat, Ya fixge wayar hannun Ajay yace “What’s happening plss?” Ajay ya kasa cewa komai tsabar yanda ya girgiza, Jay ya shiga call logs din wayar da sauri yaga Adams abokinsu ne ya kira nan yaji hankalinsa ya ɗan kwanta don yasan ba abu bane da ya shafi Khaleesat, dialing number yayi amma har ya gama ring ba a daga ba, a hankali Ajay yace “Salim aka harba” Jay bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba yace “What? Harbi kuma? Is he dead?” Ajay ya dau wayarsa shi ma ya kara dialing number Adams amma har ya katse bai daga ba, available flight to kano ya fara dubawa immediately….._Barka da sallah everyone, Allah Ubangiji ya maimaita mana Ameen, ina nan ina baza ido ina jiran goron sallah na🙄_*Next update sai bayan an gama suyan nama*😁*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button