Uncategorized

An Zabi Maulana Sheikh Dahiru Bauchi OFR A Matsayin Ambassador Zaman Lafiya A Duniya.

Wannan babban abin alkairi ne ga Duniyar Musulunci baki daya.

 Gamayyar manyan wuraren daga Kasaahen Bangladesh, Britain da kuma kasar India, tsare wakikin su Amb.  Prof. Buhari Isah, sun karrama Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A) da nuna girmanawa har kala 4 a mabambanta kamar haka:-

 1- An bashi lamba na zabar sa kamar jakadan duka jakadun zaman lafiya na Duniya reshen Nahiyar Africa.

 2- Da lambar akan tsarkakuwa daga nau’ukan cin hanci da cin hanci da rashawa da daga sashen dake kuka da cin hanci da rashawa na Majalisar dinkin Duniya.

3- Lambar daraja akan Zaman lafiya, da da’awa cikin masalaha da salama ba tare da tayar da hankali ko jawo husuma ba tsakanin Al’umma..

 4- Lambar ta yarda da alfarma cikin kebantattun jagororin Al’umma mafiya yawan mabiya a Duniya, daga majalisar dinkin Duniya.

 Wannan dai ba shine karo na farko ba da Maulana Shehu ke karbar irin wannan kambu , domin ko a aikin da ta gabata sai da wata gagrumar Gidauniya daga kasar India mai suna “Cholan book of world record” ta karramashi da kambun Duniya a fannin da yake  a kamar shine daya tilo.

 Babu shakka wannan babban ci gaba ne, kuma abin murna ne da farin ciki ga dukkan al’umman Musulmi, kuma karamci ne daga ALLAH da bayin sa suka tabbatar dashi.

 ALLAH YA KARAWA SHEHU LAFIYA, HAKURI DA JURIYA ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W).

Back to top button