Uncategorized

Cikin Aljan Complete Hausa Novel

 

ƊANƊANO

“Bahijja ki ƙara haƙuri duk wanda ki ga duniyar nan da tashi jarabawar,ƴan mata nawa kike gani a titi su na neman mazajen aure ba su samu ba? Ke fa na ki mai sauƙi ne kin aura haihuwar ce kawai Allah ya jarabce ki da ita” Natasha ke faɗawa ƙawar ta wacce tayi rub da ciki ta na sharɓar kuka.

“Matsalar ba daga wajena ta ke ba! Alio sam ya ƙi fahimta ta,a kullum ganin kasawa ta ya ke! Ɓangaren Uwar sa kuma zagin safe daban na marice daban.Babban takaici kuma shine yanzu Alio ya fara yawon dare in ya fita tunda safe sai biyu ko fiye da haka ya ke shigowa gidan nan….” Kukana da ya tsananta ne yasa ni yin shiru kafin na cigaba da cewa “na gaji! Na gaji Natasha sam ba zan zauna gidan nan ba baƙin ciki ya kashe ni tun da ƙurciyata”

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


“Kar ki ce haka! Cikin Bible…” Na  yi saurin katse ta “kar ki kawo min zancen Bible dan ba  addininmu ɗaya ba!” 

Natasha ta taɓe baki sannan tace “ku musulmi kun fiya kuri da ɗagawar ku ne masu addinin gaskiya,amman da zarar Ubangijinku ya jarabce ku sai ku fara ja da baya saɓanin mu chrestoci lokacin mu ke kusantar kan mu da Jésus duk Lahadi sai mun ziyarci coci”

Na girgiza kaina nace “mi kika sani game da Musulunci da har za ki ƙalubalance ni ? Kin ga a maida zancen nan gefe kar ma ki ƙara min tension”

Natasha tace “bari na kira Rahila naji ko ta shigo garin” wayar har ta gama ringing ba ta ɗaga ba,haka Natasha tayi ta jera kiran amman ta ƙi ɗauka can tayi tsuki tace “ƴar iska yanzu haka ta na can tare da sabon kawalinta da ta samu,tun  satin da ya wuce suke ta shirya inda za su haɗuwa mtsw kuma har ayi min kuri wai ita musulma ce”

Wayata ta ɗau ruri,na dubi Natasha nace “kin ga Alio ne ya kira ni” “to ɗaga mu ji mi zai ce”

“Allô chérie ya kike?”cewar Alio.

“Lafiya lau Bbna ya wajen ka?” Nima na ta tambaye sa.

“Alhamdullah ! Sai dai yau ina da aiki sosai ina ga ma ban zan dawo gida ba,zuwa safe in shaa Allah zan shigo ki kula da kan ki” Alio ya faɗa cikin taushin murya,hakan ba ƙaramin sanyaya zuciyar Bahijja ya yi ba.

“To Bb kai ma ka kula da kan bisou!”

“Merci bisou aussi” ya kashe kiran.

WRITTEN BY:     MRS SADAUKI

NOVEL NAME:   CIKIN ALJAN COMPLETE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         180KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:    15- SEPTEMBER -2022

CATEGORY:               SHORT STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Cikin Aljan Complete Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button