KALOLIN MATA (01)
SAHIHIYA (Saliha)
Macece mai tsayuwa kan ra’ayin kanta komai nata da gaske ta ke yinsa ba wasa mai gaskiya ce mai kuma son gaskiya ko kadan bata son raini ko qarya ko cin amana
Yadda take sahihiya tafiyarta dole sai da sahihi take dadi,ba’a gwadata misali da sunan soyayya ita da zahiri kawai take amfani yadda kazo mata kuma har ta aminta da kai to haka take sonka,idan taga sabanin haka daga baya to dole tafiyar ta watse,irinsu ba’a yaudararsu ko aci amana suci gaba da tarayyar dole a rabu sam don bata daukar raini.
Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata
Idan Allah ya sa ka samu soyayyarta to ka huta kawai,zata iya maka komai zata iya qarar da komai don ta faranta maka macece mai kamar maza akwai Sadaukarwa matuqa,ana jin dadin zama da ita musamman idan an fara manyanta an tara zuri’a kenan
Bata iya boye abu ba sam kawai ita komai ayi shi da gaske,irinsu zaka gansu ko a cikin dangi ana shakkarsu masu magana daya kuma ana tsoron su kuma suna da zumunta zasu iya tsayama kowa idan matsala ta samu.
Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata
Suna cikin mata mafi qarancin rauni a halitta.
KALOLIN MATA (02)
MISKILA
Mata masu aji kenan,ita komai nata a tsare yake tana da son kadaici da yawan shiru,bata fiye son a shige mata ba,ko a mu’amala sai ta zabi wa wanda zata yi,tana da haquri da kawaici wanda har kanta take cutarwa sanadin haka.
Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi
Tana da yawan shiru sosai,ba zaka gane yanayin ta da wuri ba saboda kullum kusan cikin yanayi daya take,bata da fara’a sosai kuma bata fiye son shiga mutane ba,in ta shiga ma bata sakewa tafi son kadaici ita daya.
Karanta>>> Amfanin Gishiri A Gaban Mace…
Tana shan wuya idan ta kamu da so,kuma wanda ke sonta ma yana shan wuya kafin ya samu kanta,sai so yayi matuqar girma a zuciyarta take bayyanawa shima a aikace kawai,dole wanda ke tare da ita sai ya nutsu ya karanceta sannan a zauna lafiya.
Karanta>>> Yadda Zaki Matse Gabanki… (Vaginal Tightening)
Amma in tana sonka gwana ce zaka sha mamaki akwaita da surprise kala_kala zata hargitsa tunaninka akwai ta da kama zuciya da hikima don yau fari gobe kuma dishi dishi haka Allah ya yi ta
Yawan mu’amala da mutanen da jininsu yazo daya yana rage musu hlayyar da kuma Addu’a.
Karanta>>> Maganin Zubewar Nono…
Allah ya sa mu dace.
✍️ Yar Makaranta.