Hausa novels

Gargadar So Chapter 109 By M Shakur

Cikeda jarumta Salman yadaga Khaleel chak yafice dashi yasashi abayan mota yashiga gaba yaja motar sukabar gidan….Kusan 40mins drive yakai Hawwa shari’a court, shiga tayi tai parking motan a parking space tayi shiru tana kallon ko’ina saikuma ta kifa kanta tafashe da kuka sosai kusan 5mins tana abu daya sai kuma ta dago fuskanta ta sauke mirror tana goge fuskan tace “why am I even crying sabida Khaleel sai kace sonshi kike? In the first place auren gambling yayi da ke yanuna miki he can acquire kome yakeso he’s a rich kid” gyale tasa ta gyara fuskanta saita dauki bakin glasses din tasaka tabude kofa tafito tashiga ciki tabiya kudi ta karbi number itace number 3, kusan 10min tana zaune akakai kanta tashi tayi tashiga office din wata dattijuwan matace sanye da hijabi looking very decent and modest, glasses Hawwa ta zare daga idanunta tace “good morning” matan tabita da kallo tana nunamata chair ta zauna tace “me kikeso?” Dan kallonta Hawwa tayi saikuma ahankali tace “inaso nai filing divorce ne, mijina yaki sakina” anatse matan na jawo wani drawer tace “can I know your reason?”Baki Hawwa tabude zatai magana saikuma tai shiru matan ta kalli Hawwa tace “idan bazaki iya bamu dalili mai kwari ba kotu bazama ta dauki karan da kika kawoba balle harmu mishi sammaci” cikin wani irin murya kaman na marainiya Hawwa tace “uhmmmm ban…..bana sonshi ne” cigaba da jawo drawer matan tayi tace “auren dole aka muku ne? How long da aurenku yanzu? Sannan mesa baki sonshi? Tun yaushe kika daina jin sonshi tun dane ko yanzu?” Baki Hawwa tabude zatai magana saikuma ta runtse idanunta kuka na neman kufce mata tadan fuzar da iska sannan ta kalleta tace “dole saina amsa all this tambayoyin nan? Ni yar sanda ce, I think bana sonshi alone is enough reason na nemi kotu taraba auren cus islamically ya halasta” Hawwa tadanyi shiru chan tace “Ma’am can you just tell me how to go about it batare da all this questions dinba kawai banson Khaleel” sosai matan ke kallon Hawwa sai kawai tace “okay” tazaro wata paper tayi signing akai tasaka stamp tace “fill this form ki bani nasake signing da stamping then it’s done idan har yanzu a gidanshi kike zamu baki takardan sammaci ki bashi da kanki idan ba’a gidanshi kikeba maybe kina gidan iyayenki zaki bamu adreshin sa ko inda z’a sameshi akaimasa” tabama Hawwa paper hakanan sai hannun Hawwa datakai zata karbi paper yashiga rawa sosai matan tabi hannun Hawwa da kallo, da kyar Hawwa ta iya karban takardan Matan tabata pen Hawwa ta tsaya tana kallon pen din takasa karba matan tace “karba mana” ahankali Hawwa tasa hannu ta karba hannunta yashiga rawa sosai zata fara rubuta a paper takasa wlh, duk matan tana kallonta kusan good 3mins Hawwa takasa saka ko A akan paper ahankali tadago kanta takalli matan tace “I need a moment please zan iya fita na cike a waje saina kawo?” Gyadamata kai matan tayi tace “sure tashi kije” ahankali Hawwa ta tashi tafito tawuce parking space tabude motan ta shiga ta zauna tarufo kofan takai pen kan takardan still takasa rubutu what is wrong with her? Idanunta sukai jazur, knocking motanta akayi wlh saida ta zabura dasauri ta juyo Baban Yaseer tagani yana sanye da wata faran shadda mai kyau ya kafa hula akai yayi kyau faduwa gabanta yayi ganinshi dasauri ta ijiye paper da pen a jaka tai maza ta gyara gyalenta tana kara rufe wuyanta da kirjinta da kyau like matan aure tasauke glass na motan kasa, murmushi Baban Yaseer yamata yace “Hajiya Hawwa rai kanga rai” adan kunyace cikeda jin nauyin sa tace “ina yini Baban Yaseer” anatse yace “Alhamdulillah ai tunda naji kinyi aure bansamu mun hadu namiki Allah ya sanya alkhairi ba, ai tundazu dayake nazo ne Boss dina ya aikoni nazo nasami yarsa anan na karbi this” yanuna mata wani file dake hannunshi yace “na karba zan shiga mota kenan sai gaki kin fito kin shiga ciki baki lurada ni ba, this is my car” yanuna mata motanshi dake next to nata yace “shine na tsaya na jiraki dole mu gaisa” dan gyadamai kai Hawwa tayi anatse tadan sauke kanta tace “yaya su Yaseer Da Yasmeen da Maman su?” Murmushi Baban Yaseer yayi yace “Hawwa kenan wato ko banjin za’a taba samun mace mai halinki aduniya ba, ace duk abubuwan da Ni’ima tamiki you are still asking yatake” yayi murmushi yace “anyways mijinki yasa an fito da ita daga prison bayan sati daya bayan tayi signing undertaken if anything yasameki in the next 5years itane, an mata iyaka dake wai ko layinku takara zuwa za’ayi inviting nata for questioning cus basu da yan uwa alayin, bata baki, toh shine fa su Mama da Yan uwan marigayi Babanta da iyayena sun shiga maganan na yafemata sabida yaranmu wlh, so she’s at home waiting for license nata da har yanzu basu dawo mata dashi ba and it serves her right, alhakin ki ne” shiru tayi Hawwa batace komiba, Baban Yaseer sai kallonta yake kaman zai hadiyeta da idanu, kasa daurewa yayi yace “why are you here? Me kikazo yi a sharia court?” Yake Hawwa tamai tace “ahhhhh, abu……Abu nazo amsa” gyadamata kai Baban Yaseer yayi yace “tom shikenan agaida mai gidan” yajuya zai bude motanshi saikuma ya juyo daidai Hawwa na daga glass nata sama dasauri yace “Hawwa!”Kallonshi tayi tana dakata da daga glass nata sama yace “please I have few things to say to you dudda ga yanda abubuwa suka faru between us but I still consider you kanwata, the way nake kula dake ada and protected you ada I will never stop doing that Hawwa cus I mean well”Hawwa tai shiru tana kallonshi anatse Baban Yaseer yace “I don’t want to poke nose into affairs naki ko aurenki but for me to see you anan this early morning with those red swollen eyes means one thing you’re not happy in your home!”Faduwa gaban Hawwa yayi sosai bakinta yashiga rawa tace “me kake fa…fad….” Tare mata numfashi Baban Yaseer yayi yace “i know you will never admit, anyways i dig into rayuwan wanda kika aura na gano rannan shine mutumin motan nan ranan dakika cemin kin fada a pool”Baban Yaseer yace “don’t get me wrong nasan jaraban Ni’ima yasa Baba yabada aurenki desperately for peace to reign, Hawwa listen to me attentively don’t you ever think sabida kin manyanta ba miji you can just settle for any kind of miji that come your way, banwani san mijinki sosai ba but I know wat yaran masu kudi are like cus I work for one naga kalan rayuwan da yaran Boss dina keyi, they don’t respect women infact bama susan menene aure ba! Kula da mace, daraja aure sai dan gidan talakawa fakiri mai lallaba rayuwa ba irin yaran nan da sunada kudin auro mata dubu alokaci daya ba” yadan rage murya ganin Hawwa ta natsu tayi shiru tana kallonshi ahankali yace “Hawwa akwai good decent men out there da they will respect you for you! They will love you right! They will treat you like queen nasu! Maza masu tsoron Allah da sanin yakamata, don’t ever be afraid to stand up for yourself! Be you Hawwa! Leave idan you are not appreciated ko respected a inda kike, gidan miji baya nufin you make it in life, making it in life shine idan kasamu peaceful and serene rayuwa hassle free and trauma free, stand for yourself kinji Hawwa and fight for what right! Don’t compromise kanki for anyone okay!” Shiru Hawwa tayi sai kallonshi take, ahankali yanuna kanshi yana mata wani kallo yace “just like before I am always here! I will forever be here for you kinji, remember you watch rayuwana da Ni’ima bawai inada kudin bala’i ba but you saw how I treated and respected Ni’ima, that is how a husband should be, mai ilimi, mai hankali, a leader! So think about abinda nace” kasa magana Hawwa tayi yamata murmushi kadan yace “bari naje you take care” yajuya yashiga motanshi yaja yabar wajenHawwa tabi motanshi da kallo ta madubi harya fita daga building din takardan tasa hannu ta dauka tana kallo kirjinta na bugawa tun dazu she couldn’t find the courage and confidence na cikawa but maganganun da Baban Yaseer yamata gave her the confidence sai kawai tashiga cikewa tacika tass tai sigining tafito tashiga ciki tabama matar ta karba takalli Hawwa tai murmushi tai signing tai stamping sannan ta tashi tadauki wani envelop na Shari’a court tai rubuce rubuce tai sealing tabama Hawwa tace “give it to mijinki zamu ganku on the 20th na this month yau 9th” ahankali Hawwa tasa hannu takarba tawuce kofa harta daura hannu zata bude matan tace “incase you have a change of heart” ahankali Hawwa tajuyo ta kalleta matan tamata murmushi tace “you can always withdraw application din okay” gyadamata kai Hawwa tayi kadan tabude kofan dasauri tafita.

Back to top button