Uncategorized

Maryam Yahaya bata jin magana wallahi – Datti Assalafy

 Shahararren ɗan jaridar nan wato Datti Assalafy ya yi magana akan sababbin hotunan da Jaruma Kannywood wato Maryam Yahaya ta saki bayan samun sauƙin ta.

Ga abin da ɗan jaridar yake cewa:

“Maryam Yahaya mutane da yawa sun bata shawara akan ta killace kanta ta daina yaɗa hotunanta a media ta bari sai ta murmure amman taƙi.


Nayi ƙoƙarin yin magana da ɗaya daga cikin uwayen ɗakinta a masana’antar shirya finafinai ta Hausa, inda ta tabbatar mani da cewa yarinyar sam bata karɓar shawara.


Ya ci gaba da cewa a cikin wannan yanayin da take ciki abar a tausaya mata ne, Allah kaɗai ya san wa yarinyar take son ta burge a media ɗin, nasan dai zata ba zata taɓa burge waɗanda suka zalunceta ba domin sun gujeta su.


 Muna bata shawarar ta dinga sanya Hijabi idan zata yaɗa hotunanta a social media, hakan zai fi rufa mata asirin ranar da tayi sakamakon jinyar Typhoid da ta yi” a cewar sa.

Back to top button