Halysaah Page 115 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 115Khaleesat na zaune gefen gado Ajay ya shigo dakin Hotel din ta daga kai ta ɗan kallesa sai kuma ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da danna wayarta alamar she is chatting, Ajay ya ajiye ledan abincin hannunsa ya nufi gaban madubin dakin ya tsaya yana cire wrist watch din hannunsa yana kallonta ta madubin, dai dai nan ta daga kai ta kallesa ganin he is backing her, hada ido suka yi ta madubin which she never expect don bata san yana kallonta ba, ta sauke idonta a hankali sai kuma tace “Good evening” Banza yayi mata kamar bai ji ba, ita dai ta ci gaba da danna wayarta bata sake dago kanta ba, ya ajiye agogon ya shiga bandaki, ta taɓe baki ta sauka daga kan gadon ta duba ledan da ya ajiye taga takeaway din abinci ne, dama yunwa take ji rabonta da abinci tun wanda ta ci around 11am na safe, kan kujeran dakin ta zauna tana bude abincin bayan ta ajiye bottle water da Gwangwanin lemon dake cikin ledan akan table, har ya idar da sallah bata gama cin abincin ba cause ta raba hankalinta tana cin abincin tana danna wayarta, daga karshe ta ajiye sauran abincin don ta koshi, ta saci kallon bangaren da yake dai dai sanda ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa a kasa, hararansa ta dinga yi cikin duhun duk da ba ganinsa take ba, kawai zai kashe wuta bayan yaga bata gama abinda take ba, can ta taɓe baki ta hau saman gadon ta kwanta, da second bedsheet din kan gadon ta rufe har kanta ta ci gaba da Chatting dinta, babu haske kwata kwata a dakin sai na screen din wayarta da ta saka cikin bedsheet, bayan kusan awa daya ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta ta lumshe ido…. Can wajen karfe biyun dare ta farka ta fara laluban wayarta a inda ta ajiye kusa da ita zata je bandaki tayi fitsari, amma bata ga wayar ba, ta mike zaune tana laluba beside drawer nan ma bata ji alamar waya ba, sauka tayi daga kan gadon tana tafiya a hankali ta zaga ta inda switch din wutan dakin yake, being careful kar taje ta buge da wani abu, tumble ta kusa yi kansa yana zaune kan darduma ya turata daga gabansa, tana komawa baya a hankali kamar zata yi kuka tace “Ni switch din wuta zan kunna fa” Jin bai tanka ta ba ta mike tsaye, a haka ta laluba ta kunna wutan dakin ta juya ta kallesa, sai kuma ta kalli kan gado, mamakin yanda wayarta ya dawo tsakiyar gado ta fara yi bayan tasan kusa da ita ta ajiye kafin tayi bacci, taga ya mike ya ci gaba da sallan sa, ta fi minti daya tsaye tana kallon wayar, can ta shiga bandaki, tana fitowa ta hau saman gadon ta dau wayar ta bude Password din don akwai password jiki ta duba abinda zata duba sannan tayi kwanciyarta wondering how the phone changed position, juyawa tayi ta kallesa taga he is still praying, idan ma shi ya dauka ba accessing wayar zai iya yi ba because of the password, a haka bacci ya dauketa. Da asuba Khaleesat tayi mika ta bude idonta dai dai lokacin da take tashi yin Sallah, tsaye taga Ajay gaban mirror wearing just short yana goge gashin kansa alamar wanka yayi, hada ido suka yi ta madubin tayi saurin mayar da idonta ta rufe kamar warce taga mugun abu, kamar munafuka ta ja duvet din jikinta ta rufe har kanta da shi ta wani turo baki, she wish she can unsee that muscular body of his, har karfe shidda da yan mintuna bata yarda ta cire duvet din da ta rufe kanta ba gashi tana son tashi tayi sallah don tasan lokaci ya wuce amma ta kasa, ji tayi kamar ya bude kofar dakin hotel din, cikin dubara ta ɗan bude fuskarta tana lekowa ta duvet din taga fita yayi daga dakin, da sauri ta mike zaune ta cire duvet din jikinta ta sauka daga kan gadon ta daure gashinta sannan ta saka hularta ta wuce bandaki, ta idar da sallah tana cikin yin azkar dinta sai gashi ya shigo dakin, ita dai bata yarda ta daga kanta ba har ya wuce ta ya tafi ya zauna kan daya daga kujerun dake dakin ya dau wayarsa yana dubawa, ta idar da azkar dinta ta mike ta linke pray mat din ta ajiye sannan ta zauna gefen gado ba tare da ta cire Hijab din jikinta ba, satan kallonsa tayi tace “Ina kwana” Danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba balle ya amsa, ta turo baki ta kwanta edge din gadon ta juya masa ba, sai a sannan ya kalleta, dai dai nan aka yi knocking kofar dakin ya mike ya nufi kofar ya bude, ya amshi tray din Hot coffee da Croissant daga hannun daya daga ma’aikatan hotel din sannan ya kulle kofar ya koma inda yake zaune ya zauna ya ajiye tray din kan table. Cikin minti ashirin Khaleesat ta gama shirin da take ta dau jakarta bayan ta saka takalmi ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, sai taga kamar kayan ma yafi na jiya kyau, yau ma dai she look expensively beautiful, kamar dai jiya yau din ma designers ne kaf jikinta, kayan yayi mata mugun kyau ba kadan ba, juyawa tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin hotel din, yana tsaye jikin Taxi yana jiranta ta fito, tun da suka hada ido ta sauke nata idon ta bude motar ta shiga, after some seconds ya dauke idonsa daga kanta ya bude gaban motar ya shiga, Drivern taxi din ya ja motar suka bar wajen, tun da Khaleesat ta lura da inda za su je gabanta ke faduwa don sarai ta gane unguwan, Taxi din na parking gaban apartment din Ajay ya bude motar ya sauka, a hankali ita ma ta bude motar ta sauka ta bi bayansa walking slowly, bell ya danna don kofar a kulle yake, Iklima ce ta bude kofar ganinsu ta koma gefe without much attention tace “Sannu da zuwa yaya” Bai ce mata komai ba ya shiga parlon, Khaleesat ta bi bayansa ba tare da ta yarda ta hada ido da Iklima da ta bi ta da ido tana kare ma dressing dinta kallo ba, juyawa yayi yana kallon Iklima fuska daure yace “Ke baki iya gaisuwa bane don uwarki?” Tayi yake tana sosai kai tace “Lahh yaya nace fa sannu da zuwa” Sai kuma ta kalli Khaleesat tace “Ohh sannu da zuwa” Khaleesat dai bata kalleta ba tace “Yauwa nagode” Cire takalmanta tayi ta bi bayan Ajay tana tafiya a hankali har suka karasa cikin parlon, Iklima ta bi ta da wani shegen kallo, Gimbiya Firdausi ce zaune parlon da Yayar mahaifin Hadiyah Hajiya Shema’u sai Hajiya Sumayya, Ajay ya gaishesu gaba daya, Hajiya Shema’u ce kadai ta amsa masa da kyau, Khaleesat ma ta gaishesu nan ma ita kadai ce ta bata attention dinta, Hajiyah Shema’u na kallon Ajay tace “Ita ce matar taka, da yake jiya bana jin dadi da wuri na bar Convocation arena din bamu hadu da ku a can ba” Ajay yace “Ya jikin yanxu?” Tace “Na ji sauki Alhamdulillah” Kallon Khaleesat tayi tace “Maa sha Allah amarya, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya, ki zauna lafiya da mijin ki kin ji, yi kin yi bari kin bari kin ji, kuma ki zama mai hakuri da kauda kai, Allah Ubangiji ya zaunar da ku lafiya ya baku zuri’a dayyaba” Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta without saying a word tana wasa da veil dinta, Hajiya Sumayya kuwa sai kallon kayan jikinta take da jakar hannunta, Ajay ya kalli Hajiya Shema’u yace “Za mu je wajen Hajja a sama” Hajiya Shema’u tace “Toh sai kun sakko” Mikewa yayi ya bar parlon, Khaleesat na ganin haka ita ma ta tashi ta bi bayansa suka nufi stairs, Gimbiya Firdausi ta bi su da kallon gefen ido har suka haura sama, Ajay ya bude kofar dakin da Hajja ke ciki ya shiga Khaleesat na biye da shi, Hajja na zaune dakin tare da Hadiyah da duk yan matan gidan sai Hajiya A’isha, Khaleesat ta zauna kasan carpet kanta a kasa, Ajay ya zauna kan kujera ya gaida Hajja da Hajiya A’isha, sauran yan matan duk suka gaishesa ya amsa masu a takaice, Hajja ce kadai ta amsa gaisuwar Khaleesat a dakin, sannan ta kalli yan matan dakin tace “Ba ku ga matar yayanku bane?” Dukansu suka kalli Khaleesat kamar sun ga bola, shi dai Ajay daya bayan daya yake bin su da kallo, a walakance duk suka gaisheta banda Hadiyah da ta hade rai tun shigowar Khaleesat barin da taga handbag din dake hannunta da rigar jikinta, Shahuda kuwa danna wayarta kawai take kamar bata san Allah yayi ruwan Khaleesat a dakin ba, Khaleesat dai ta amsa gaisuwar su Khadijah tana ɗan murmushi jikinta a sanyaye, ita kanta tasan ba karamin gata Ajay yayi mata ba na dauketa a gidan nan, she felt really grateful da hakan da yayi mata, don kilan da bai dauketa ba tsaf zata samu heart attack kafin su bar kasar, sam bata ga alamar mutunci da daraja a gun yan matan gaba dayansu ba, as if they have grudges against her from anywhere, daga su har iyayensu ita kam bata san me tayi masu ba, hatta Hajja ba wai wani sake mata take ba, kawai babu yabo babu fallasa ce ita, Hajiya A’isha ta mike ta fita daga dakin ta tafi dakin da Mami ke ciki, zaunawa tayi tana kallon Mami tace “Lallai Fulani ba karamin jihadi kika yi ba da kika wargaza auren shegiyar yarinyar can da Jawwad, ke kinga irin kayan da ta ke saka Junaid yake siya mata kuwa? Kaf kayan nan babu su cikin lefenta don ai mun ga lefen kafin a kai mata, designers fa ta saka jiya, yau ma haka” without much attention Mami tace “To ku kuka ma lura da abinda ta saka, ni kam ban gani ba tunda ba abinda ya shafeni bane, i have no business with her as far as burina ya cika na raba ɗa na da ita, yanxu ba gashi ya hakura ya rungumi Hadiyah ba kamar ba ayi komai ba, ai ni ba abinda zan ma Allah sai godiya, dama nasan komai zai wuce, duk phases din tension din nan da ya shiga da damuwa nasan na lokaci ne, to ba gashi ya wuce ba yanxu sai labari, shi Sarki tunda yace yaji ya gani ɗan sa ya zauna da Bazawara buzuwa to ga su ga ita Allah ya bada sa’a, da yake bata gabana wallahi ban ma lura da kayan nata ba….” Hajiya A’isha ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru bata sake cewa komai ba, Allah ya sani duk wata hanyar da zata cusa ma er ta Iklima Junaid babu wanda bata bi amma abun ya ci tura, bata da wani burin da ya wuce a yau taga Iklima na auren Yarima, amma duk da haka ba hakura tayi ba yanxun ma, tasan ta yanda zata billo ma lamarin don bazata zuba ido wata matsiyaciya ta haifar masa Magaji ba, yau Iklima ta zama matar Yarima kuma Allah ya bata ɗa namiji ai mulki ya kara kusanto zuri’arta kenan duk da ita din er sarki ce, da Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayyah sai Kilishi warce ita ce Mahaifiyar Mukhtar cousin din su Junaid uwarsu daya ubansu daya kuma uwarsu ita ce babban matar marigayi sarki Ahmadu wanda shi ne babansu Mai martaba na yanxu, mahaifiyar tasu ta ma riga babansu sarki Ahmadu rasuwa kuma ita Allah bai bata ɗa namiji rayayye ba don sai da ta haifi maza biyu duk suna rasuwa kafin ta haifi Gimbiya Firdausi warce ita ce first born a family din Sarki Ahmadu, daga uwarsu Gimbiya Firdausi sai mahaifiyarsu Hajiya Shafa’atu warce ita ce matar sarki ta biyu, Hajiya Shafa’atu da kanwarta Maryam kadai uwarsu ta haifa ta rasu, sai dai sarki ya rigata rasuwa, Hajja ce ta uku a matan sarki duk da rana daya aka aurosu da Baabarsu Hajiya Shafa’atu kuma Hajja ta ma rigata haihuwa, wanda ita kuma Hajja ‘ya yanta uku kadai a duniya, da marigayi Baban Jawwad wanda is almost age mate da Gimbiya Firdausi, sai Mai martaba na yanxu sannan uwar Hadiyah me suna Maimuna da suke ce ma Ummi, bayan Hajja sai uwar Hajiya A’isha warce ita ce matar sarki ta karshe, ita kuma Hajiya A’isha ita kadai ce gun uwarta, kuma uwar tata na nan da ranta har yanxu a gidanta na Bauchi, ajiyar zuciya Hajiya A’isha ta sauke a ranta ta sha alwashin ko ta halin yaya ne sai Junaid ya auri Iklima, suna komawa zata je ta samu Baabarta da wannan batu don su san yanda za ayi.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
