Hausa novels

Halysaah Page 31 By Khaleesat Haydar

Khaleesat na zaune hall din da jama’a ke jiran Luggages dinsu a Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace “Ohk” Mikewa tayi ta fita daga Arrival din tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka, gaisheta yayi da ladabi yace “Babu kaya ko Hajiya?” Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace “Bismillah, Motar na can nayi parking” Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace “Nagode” Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta gani tsaye, da ladabi Drivern yace “Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya” Yarinyar ta ɗan yi murmushi ta koma gefe tana kallon Khaleesat tace “Sannu da zuwa sister, come in” Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace “I am Inteesar” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace “Sunana Khaleesat” Yarinyar tace “Welcome Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana” Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da fara’a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace “A’a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata” Khaleesat ta koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace “Sannu da zuwa, ya hanya?” Khaleesat tace “Alhmdlh, ina yini” Ammi tace “Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?” Khaleesat tace “Suna lafiya lau” Ammi tace “Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce” Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tayi shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace “Inteesar ki kai ta daki ta huta” Inteesar tace “Ohk” Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo. Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn’t bothered da kallon don farkon haduwarsu da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi yasa bata gajiya da kallonta, sai bayan sun zama kawaye Sophie ta dena mata maganar kyanta, kuma dama da wuya taje waje bata ga mutane na kallonta ba, ba maza ba hatta yan uwanta mata haka suke kallonta, muryar Inteesar taji a hankali tace “You are Beautiful Khaleesat” Khaleesat ta ɗan kalleta sai kuma ta mayar mata da murmushin da take mata kawai, Inteesar tace “Sosai fa” Cikin sanyin murya Khaleesat tace “And you too Inteesar” Inteesar tayi dariya tace “A’a gaskiya ba kamarki ba, ni dai ina son mu zama frnds in baza ki damu ba, Ya Prince yace gobe zaki tafi Lagos da safe, don Allah ki bani numberki mu dinga zumunci ta waya, probably baza ki sake dawowa gidanmu ba” Sosai Khaleesat taji wani relieve ya zo mata bayan taji Inteesar tace zata tafi Lagos da safe, dama gaba daya hankalinta yayi gun kanwar Ummanta, Allah ya gani daurewa kawai take amma ita kadai tasan me take ji both mentally and physically, tana cikin tashin hankali sosai but she is trying her best to act normal, Khaleesat tace “Ohk amma nayi misplacing wayana ban yi welcome back, idan nayi zan amshi lambarki gun sa” Inteesar tace “Ohk to ba damuwa, amma zaki dade a lagos ne in kin je?” Khaleesat tace “Zan ɗan yi kwana biyu a can in sha Allah” Inteesar tace “Akwai sisterna dake aure can, idan baza su dawo gida for New year ba in sha Allah zan je Lagos din so that i will meet with you there” Murmushi Khaleesat tayi tace “Toh shikenan Allah ya kai mu lafiya” Inteesar ta tashi ta bude press ta dauko mata kayan baccinta don dakinta ta kawo Khaleesat, bayan ta ajiye kayan gefen gado tace “You can change to this idan kinyi wanka, i will be back later” Khaleesat tace “Alright, thank you so much” Bayan few minutes da fitan Inteesar Khaleesat ta tashi a hankali ta tafi bandaki, da ta tuna auren Abdul dake kanta tashin hankalinta ninkuwa yake, sai da ta ci kukanta me isarta sannan tayi wanka ta fito daga bandakin, ta gama saka kayan da Inteesar ta bata kenan tana kokarin daure gashinta sai ga ta ta shigo dakin, Inteesar ta wara ido tace “Waow is all that ur hair Khaleesat?” Khaleesat dai ta mata murmushin karfin hali tana ci gaba da daure gashinta, Inteesar that was looking at the hair with fascination tace “Bari in baki Hair net” Hair net dinta ta dauko ta ba Khaleesat, Khaleesat ta amsa tace “Nagode sosai” Washegari karfe tara da rabi na safe Khaleesat ta gama shiryawa tana jiran Drivern gidan, kayan Inteesar ne jikinta da yake yanayin jikinsu daya babu me cewa ba kayanta bane, tana zaune gefen gadon Inteesar duk da Hijab ne har kasa jikinta amma sanyi take ji sosai, ga AC dake dakin a kashe amma she is shivering, tun da ta tashi da asuba tasan she is not feeling okay, breakfast din ma da kyar ta sha shayi kawai, ko irish din bata ci ba balle bread, she is trying all possible best to look alright don kar ayi cancelling tafiyarta zuwa lagos yau, Mai aikin gidan ce ta Kwankwasa kofa ta sanar mata driver yana jiran ta, Khaleesat ta tashi da kyar ta dau handbag dinta ta fita daga dakin zuwa parlor, nan ta tarar da Ammi zaune, Khaleesat ta karasa ta duka kusa da ita tana mata godiya don sosai suka sake mata kamar da can sun taba saninta, daga karshe dai Inteesar ta bi su har Airport don rakiya, haka kawai jininta ya hadu da Khaleesat, ita kanta Khaleesat don bata cikin nutsuwarta ne amma she so much appreciate Inteesar’s care toward her, a haka dai suka rabu kamar sun jima da sanin juna, Khaleesat ta shiga cikin airport din ta amshi boarding pass dinta don Ajay ya tura mata ticket ta Email din wayar da ya bata hade da hoton National ID dinta da yayi snapping tun karfe bakwai na safe, bayan ta amshi boarding pass dinta ta nufi Departure Lounge. Karfe sha biyu saura suka sauka garin Lagos, Khaleesat ta sauka a jirgi da taimakon wata mata don zazzabi ne sosai ya rufeta but she is still pretending to be fine, a haka suka fito Airport din daga Arrival matar na tambayarta za a zo daukanta ne ko Taxi xata hau, Kafin Khaleesat tace komai ta hango wani kamar AJ tsaye jikin wata mota yana danna wayarsa, sai da ta kifta ido ta bude to be sure he is the one she is seeing, ta kalli matar kusa da ita da kyar ta sanar mata yayanta ya zo daukanta, a haka suka rabu da matar, Khaleesat ta nufi inda ta hango Ajay, sae da ta iso kusa da motar ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai a hankali tace “Ina yini” Calmly yace “Ina wayar da na baki?” Jakar hannunta ta nuna masa tace “Yana ciki, na sa silent ne” Driver seat ya bude ya shiga sannan ya bude mata daya side din motar, zagawa tayi ta shiga ta jinginar da kanta ta lumshe ido, ya tada motar suka bar Airport din, Google map yayi ta using after almost 45 mins ride Khaleesat ta fara gane inda za su, amma kuma sae ko ina yayi mata sabo a area din ko don she is not stabilize ne bata dai sani ba, ta juya ta kallesa shi dai driving dinsa kawai yake with the assistant of his google map, at last suka shigo wani unguwa yayi parking ya dau wayarsa yayi dialing number, muryar Aunty Farida taji bayan anyi picking, Khaleesat taji kamar an yaye mata ƙaso tamanin cikin damuwarta jin muryar kanwar Ummanta, bayan few minutes sae ga ta ta fito daga cikin wani gate, tun da AJ ya hangota daga nesa ya fahimci da ita yake waya don kana ganinta ka ga Khaleesat, yayi driving din motar har zuwa dai dai kofar gidan da ta fito, yana parking Khaleesat ta bude motar da sauri ta sauka da sauran last strength dinta ta nufi Aunty Farida ta fada jikita, Aunty Farida ta rikota da sauri kafin ta kai kasa, wata makociyarta ce ta taimaka mata suka rike Khaleesat suka shiga da ita cikin gidan, shi dai AJ na tsaye kusa da motarsa yana kallonsu har suka shiga ciki, sai kuma ya jingina da motarsa yana kallon yara dake wasa few houses away, wayarsa ya ciro jin yana ringing ganin me kiransa ya daga yace “Ya ake ciki?” Daga daya bangaren mutumin yace “Ranka shi dade sai daxu ya kunna wayar tasa, an kuma duba location din nasa yana cikin garin Abuja yanxu haka” AJ yayi shiru kafin yace “Ohk, i will get back to you nagode” Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa, sai ga Aunty Farida ta fito daga cikin gidan, yayi ƙasa da kansa ya gaisheta, ta amsa cikin sanyin murya tace “Sannu da kokari fa, Allah ya saka da alkhairi, mu shiga ciki sai mu yi magana ko” Bai ce mata komai ba ya bi bayanta zuwa cikin compound din, Compound ne me dauke da apartment uku self contain each, AJ ya tsaya daga balcony din apartment din bai shiga ba har sai da Aunty Farida ta kara lekowo ta masa magana sannan ya cire takalmansa ya shiga parlon ya zauna saman kujera yana kallon Khaleesat da ta juya baya kan 3 seater din da take kwance, Aunty Farida ta tafi kitchen dauko masa ruwa, ya ciro wayarsa yana dannawa absentmindedly, Sai ga Aunty Farida ta fito kitchen ta ajiye masa ruwan a kusa da shi sannan ta zauna, da damuwa tace “Sannu da kokari Junaid, Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai” AJ ya daga kansa ya kalleta yace “Amma dai kince bai san inda kike a lagos ba ko Aunty?” Aunty Farida tace “Gaskiya bai san nan gidan ba, tsohon gidan da na baro ne dai ya sani, shi ma wani lokaci ne da ta zo Lagos dubani bani da lafiya, ta zo da kwana uku sai ga shi shima ya zo, to yau wata hudu kenan da barina wancan Unguwan na dawo nan” Ajay dai yayi shiru idonsa a kasa, Aunty Farida tace “Kuma ba unguwa daya bane, shi wancan Unguwan da na baro a Ojota ne, daga can zuwa nan ma tafiya ce me zaman kansa, ba kuma wanda yasan nan na dawo” Ajay yace “Toh shikenan, jikinta da zafi ne?” Aunty Farida tace “Ehh na ji da zafi sosai gaskiya, makociyata da ta rike min ita muka shigo yanzu nurse ce, tace zata rubuta min magunguna in siyo mata” Ajay yace “Ohk, bari zan fita yanzu sai in siyo magunguna da allurai da drip ayi mata karin ruwa” Aunty Farida tace “To Allah ya saka da alkhairi, amma baka sha ko ruwa ba Junaid” Ajay ya ɗan yi murmushi yace “Bari in je in dawo dai” A haka ya fita daga parlon ya tafi pharmacy ya harhado mata magunguna da drip da allurai. Wata mace ce warce bazata wuce shekaru hamsin da bakwai ba zaune wani kantamemen parlor cikin isa, mai aikinta na duke gabanta tana yanke mata kumbar kafafuwanta, cikin fada take cewa “Banda ma naci irin naka dama ina kai ina er matsiyata? Er talakawa? Wanda cin yau da kyar na gobe da kyar, ai kai ba class dinta bane ta ko ina, you just stoop ur self so low Abdul, babu wanda ya isa da kai babu wanda zai baka shawara ka dauka, na rasa irin wannan taurin kai naka, tun asali i am against you marrying that poor wretched girl, kuma har gobe ba wai nayi na’am bane kawai bani da yanda zanyi da kai ne Babana, baka jin maganata ko na ubanka balle na yayarka, yanxu ina amfanin kaskantar da kai da matsiyaciyar tayi cikin talakawa yan uwanta a gaban gidan cin abinci, abu har police station, da mutuncinka da iliminka a maka haka? In zaka dau shawarata yanzu gwara kawai ka saketa case ya dawo sabo fil, uban me zaka ci da ita kuma bayan wannan abun da ta maka a idon duniya? Idan yarinya kake so ni duk inda zan shiga zan je in samar maka yarinya karama da ta fi ta komai kuma er gidan arziki ba tsiya ba, kai ko Nijar din ne ma ni sai in shirya inje da kaina in samo maka wata buzuwar er gidan arziki ba talakawa ba, kai ga ma er wata kawata shuwa Arab yanda kaga ita wannan da makale ma ita ma haka take tass da ita, ga gashi, sannan su ba talakawa bane” Wata matashiya ce er shekara 39 dake zaune parlon ita ma ta juya da sauri ta kalli warce ke magana tace “Momy ban gane abinda kike nufi ba? Wai nufinki ya saketa kenan?” A fusace Momyn tace “Toh uban me zai ci da ita idan bai saketa ba Meema? Er talakawa ce fa, a kanta aka fara kyau a duniya ne da bazai rabu da ita ba?” Warce ta kira da Meema ta girgiza kai tace “A’a wallahi Momy, ai idan ya rabu da ita yanzu ma ita da iyayenta ne suka ci riba, duk uban hidimar da yayi mata sai kice ya saketa daga karshe ko tausayinsa ba ki ji ba Momy? Ae wallahi bata isa ya saketa ba, ko don mu kuntata mata yanda ta kuntata ma Abdul baza mu yi fatan ya saketa ba, dole sai ta shigo gidan nan, balle shi ba mahaukaci bane da zae saketan, yarinyar da ya tura har America karatu duk don dai ta zama presentable cikin mutane kar a mana dariya daga karshe ta saka masa da wannan walakanci da tijara haka?” Abdul dake zaune parlon shi ma duk yana sauraronsu ya mike yace “In har aka ga na saketa to bana numfashi ne a duniya, kuma duk inda ma take zata dawo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, a nan ne zata gwammaci bata taɓa sanina a rayuwarta ba, i will make life a living hell for her” Momy ta tabe baki tace “Shi dama talaka ai bai gaji abun arziki ba, shi yasa babu ruwana da su ko da wasa, hanyar jirgi daban ta mota daban, kai ne da jajibe jajibenka kasa ubanka ya tafka asaran kusan miliyan dari akan matsiyaciyar yarinyar nan” Tuni Abdul ya fice daga parlon, Meema na kallon uwarsu tace “Ai ki ma dena maganar asaran miliyan dari Momy, don yanxu babu wannan zancen asaran nake ji” Momy dai ta tabe baki tana kallon me aikinta tace “Ke kar fa ki yanka ni inyi mugun bata maki rai yanzu, ya zaki dinga gaftare min naman yatsu” Hakuri mai aikin ta hau bata. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta ɗan kishingida a 3 seater, hannunta rike da bowl din pepper soup din da Aunty Farida tayi mata, gaba daya ta kasa shan pepper soup din Offals din, don jinsa take kamar magani a bakinta gashi har sannan jikinta babu kwari ga ciwon kai, ta kalli drip din dake hannunta taga ko quarter bai yi ba amma har ta gaji ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, tun da AJ ya kawo magungunan da drip ya ajiye ya bar gidan har sannan bai dawo ba, ga abincinsa Aunty Farida ta zuba a cooler ta ajiye a tray tun daxu tana jiransa, tambayoyi ne da yawa ke yawo a zuciyar Aunty Farida tana son tambayar Khaleesat ko shine ya taɓa biya mata jirgi kwanaki da Umma bata da lafiya amma ganin yanayin da Khaleesat ke ciki ta bar duk tambayoyin nan a zuciyarta, Aunty Farida ta kalli Khaleesat tace “Ki daure ko kadan ne ki sha, ko in dama maki custard?” Khaleesat ta girgiza mata kai, dai dai nan aka kwankwasa kofar parlon, Aunty Farida ta mike ta yafa gyalenta sannan ta tafi ta bude kofar ta koma gefe, da sallama Ajay ya shigo parlon yana kallon Aunty Farida yace “Tare da brother dina muke” Aunty Farida tace “To ku shigo mana” a hankali Khaleesat ta gyara zamanta tana kallon Jay babu ko kiftawa, ganinsa ta dinga yi kamar a mafarki, Jay ya sauke kansa ya gaida Aunty Farida ta amsa da fara’a, sannan ya juya yana kallon Khaleesat shi ma babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, walking slowly ya karasa har cikin parlon ya duka gabanta yana kallonta, a hankali yace “Are you feeling better now Housemate?” Da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, and truly she felt better immediately, shi dai AJ na tsaye yana kallonsu, haka Aunty farida da ta koma one sitter a sanyaye ta zauna, Jay yayi kasa da murya still looking at her yace “Kiyi hakuri, everything will be okay soon in sha Allah, i promise you” Ta gyada masa kai da sauri with so much hope from his assurance, yana kallon bowl din hannunta Softly yace “Take ur soup” Ba musu ta dau spoon din ta fara shan pepper soup din a hankali, Aunty Farida ta kalli Ajay tace “Baka zauna ba Junaid” Ajay ya sauke kansa ya karasa 2 seater ya zauna, Aunty Farida ta share hawayen da ya cika idonta, da kyar tace “Mu ma duk ba da son ran mu bane abubuwan nan ke faruwa haka ba, ba mu da yanda za mu yi ne kawai, amma babu nagartattun iyayen da za su dau er su su ba Abdul aure”

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500

Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman

Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge*

Back to top button