Mijin Marigayiya Page 17 Hausa Novel
Ya rufe komar ya koma cikin gidan gwiwarsa a sanyaye; ya zai yi da yaran ga gidan kace-kaca musamman kitchen din, ko ina kwanuka. Tukunna ma; mura fa aka ce Ummi take yi. Inna lillahi wa inna ialaihi raji’un! Allah ya sa yarinyar nan ba Covid-19 ta kwaso ba garin yawon tsiya, don tabbas idan ta kwaso to ta shafawa yaransa.‘Subhanallah!’ ya fada a fili yana daf da karasawa cikin gidan.Bayan ya shiga gidan yayi musu bayanin Ummi bata da lafiya.Yana ji yana gani haka ya hakuri Afaf ta dafa musu jallof macaroni, bayan sun gama ci kuma ta kwaso wanke-wanke ta fice da shi waje ta wanko; duk da koakrinsa na hanata amma haka ta dage ta wankesu. Sannan ta umarci Halifa da ya share cikin gidan wanda shima nan da nan yayi, suka dawo suka zauna.Wunin ranar haka yayi shi yana gyangyadi domin ko ya rufe ido da niyyar bacci haka wani zai rugo kai kara har Afaf din ma, ko kuma azo ace masa ana bukatar wabi abu; ita kam Shukra haka kawai ma da taga ya shiga daki binsa takeyi, idan kuam a parlor ne da ya rufe ido zata kirawo sunanshi tace ya bude ido ta nuna masa wani abu. Haka har aka kusan magriba sannan ya samu da taimakon Afaf ya soya musu dankalin bature kuma ya dafa musu indomie ta dan yi dadi.Wuni yaran suka yi suna ciye-ciye amma ko da ka sha ruwa ma saka shi suka yi a gaba ana cin abinci suna masa surutu da rigingimu kala-kala; shi dai zai iya cewa ba a hayyacinsa ya ci abincin nan ba. Haka ya dinga ci yana kwarewa.Ya cika bakinsa da dankali Shukra ta mike ta jefar da dankalin da yake hannunta tana dafe duwawu tana cewa ‘Kashi Abba.’Ji yayi wani malolo ya taokare masa makogoro; wai ita Shukra bata tashi kashi ne sai mutum yana tsaka da wata sabga?Lallai yanzu ya tabbatar Khadeeja tana da kokari don kusan tunda aka fara azumin nan sai ana tsaka da cin abinci sannan Shukra take cewa zata yi kashi kuma ta tashi ta sakata; idan ma tayi jinkiri shine yake nuna damwarsa. Ya dubi Afaf wadda ya kula kamar ta bata rai me yace ‘Yaya Afaf ki saka kanwarki a toilet tayi kashi.’ Ta tashi a fusace ba tare da ta amsa ba ta dire kofin shayin da taje sha a kasa, tana daga kafa tayi fatali da kofin shayin ya zube ya fallatsa ya bata Habib wanda yake kusa da ita. Ya mike a fusace yana nunata ‘Dalla malama ji yanda zaki konani da shayi saboda kashin wata.’ Ita din ma a fusace tace ‘To ka matsa mana, ko baka gani ne?’Abbansu ya bude baki zai yi magana Shukra tace ‘Kashi Abba.’Ya tuna yanda suka yi cikin dare ya tabbatar bai shirya wanke kashi a parlor ba don haka ya mike ya wucesu ya ja Shukra ya nufi bandaki da ita. Saida ta gama kashin ya wanke mata ya fito sannan ya saka su a gaba yayi musu fada, ya sa Afaf ta gyara inda ta bara da shayi. Ya kurbi shayinsa da ya bari yaji yayi sanyi, haka daiya hakura ya shanye ya dan kara cin abincin. Haka ya hakura ya nemi waje ya zauna yana tunani don zai iya cewa ba kkoshi yayi ba ya dai hakura da abincin ne kawai, haka ya dinga binsu da kallo sunata wasanninsu har loakcin kwanciyar bacci. …….. A cikin wannan halin Mustapha ya karasa kwanaki biyu shi da yaran a jigace, gashi duk wanda yayi atishawa ko tari a cikin yaran sai ya firgita saboda gani yake kamar corona ce ta kwantar da Ummi kuma suma sun shafa a wajenta. Kamar yanda aka sanar ranar asabar aka bude gari, ba karamin dadi wannan budewar ta yiwa Mustapha ba. Tun waje karfe takwas ya shirya sannan ya shirya yaran gaba daya, sai dai da ya duba lokaci yaga safiya ta yi da yawa ya bari zuwa wajen tara da rabi sai su fita; domin so yake su je su dauko Khadeeja sannan idan ya kawota gidan ya barsu ita da yaran ya wuce gidan hajia ya gaishesu. Sai wajen goma saura sannan suka kama hanya.Tun kafin ya gama tsayar da motar yaran suka balle kofofi suka fice suks shiga gidan da gudu, bayan sun gaida Mommy wadda take zaune a parlor tace su shiga dakin Anti Nabila su taso Antin tasu inda take barci.Jinsu kawai tayi a kanta suna shewa, ba shiri itama ta mike. Nan take aka shiga bata labarin abubuwan da suke faruwa a gidan. Itama tayi kewar yaran kuma ta ji dadin ganinsu sosai. A farfajiyar gidan Mustapha ya tsaya sai da Mommy ta tura Nabila ta shigo da shi, ta bude parlor din baki tayi masa iso inda Baffa yake jiransa don shima fita zai yi jin isowarsu ya sa ya tsaya.Bayan sun gaisa Baffa ya tambayeshi wajen su Alhaji sai yayi gyaran murya yace ‘Yauwa, ina ga zaka bar Khadeejan ta dan kara kwana biyu don mahaifiyarta tace akwai abubuwa suke yi na gyara wanda al’ada ta tanada. Don haka ina ga ka barta ta dan kara kwana biyu mu gani.’‘Eh, kuma da zuwa mukayi mu tafi da ita Baffa.’‘Allah sarki, ina ga a dan daga musu kafa su gama shirye-shiryensu, ba zasu dauki lokaci ba suma na sani in sha Allah.’Babu yanda ya iya kwarjinin Baffa ya sa ba zai iya yi masa wani dogon musu ba, don haka sai kawai ya sunkuyar da kai. Baffa yayi masa sallama ya fice ya barshi a nan cike da takaici; yaya Baffa zai yi masa haka? Wannan din shawarar Mommy ce ko kuwa dai Khadeejan ce bata son ta koma? Amma dai bari Khadeejan ta fito ya ji daga bakinta. Ya gyara zama ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro ya dana saita fuskarsa da ya ji motsi ana taba kofar daga cikin gida, ya mike ya koma kan kujerar zaman mutum daya ya zauna.Khadeeja ce ta shigo da sallama, bayan ya amsa ta nemi guri ta zauna a kan three seater ta gefen da ya fi kusa da shi, bayan sun gaisa tace ‘Ya kuke kai da yara? Sun ce min ku kadai ne a gida ko gidan Hajia baka kaisu ba.’‘To ina zan kaisu gari yana kulle, dole haka muka zauna mu kadai; don ma dai Ummi tana taimakawa, jiya ne kawai da shekaranjiya aka ce bata da lafiya.’‘Allah sarki ai iyayenta suna mana kirki gaskiya, Allah ne kawai zai biya su.’Suka yi shiru na dan lokaci; idan ma da yana da niyyar gaya mata wasu kalamai masu dadi to Baffa ya goge masa haddarsu, yanzu haushin kowa ma yake ji. Sai dai fatansa daya ya ga ko zai iya tsaran Khadeejan ta canza wanna tsarin don yana jin idan tace tana son ta koma ba za a hanata komawa ba. Yace ‘Uhm, da ni fa zuwa nayi mu tafi amma na ji Baffa yace kamar zakiyi wanka ne ko gyara wai sai an kwana biyu zaki dawo.’Ta dan gyara zama ‘Eh, Mommy tace a barni sai nayi wankan jego kuma dai da ‘yan gyare-gyare na kara hutawa sai na komawa.’‘Wai baki gayawa Mommy cikin bai karasa wata uku ba ma, na zata haihuwa ake wa wankan jego. Ke dai idan akwai wani dalili ki gaya min sai muga yanda za ayi.’Tayi ‘yar dariya ‘Shine dai dalilin gashi na gaya maka, don kaga har yanzu ma ban gama jini ba kusan kwana biyar kenan.’‘Uhm! To yanzu babu yanda za ayi mu koma yau, na san ai duk wani gyara ba zai gagare ki ba tunda kin sami lafiya ga laulayin ma yanzu babu.’‘Gaskiya kayi hakuri kawai muyi yanda Baffa ya fada, kwana nawa ne zaka ga ma na dawo gidan.’Ya sunkuiyar da kai; tabbas wannan tsarin na Khadeeja ne sai dai bai san laifin me yayi mata ba take son tayi purnishing dinsa haka. Muryarta ce ta katse masa tunani ‘Kada ka damu in sha Allahu zuwa bayan sallah zan dawo, ka ga kafin nan ma Mommy ta samo min mai aiki.’‘Bayan sallah? Haba! Wajen sati uku fa kenan? Ai na zata duk inda aka kai nextweek kin gama hutawar. Kuma mai aiki ai Habi zata dawo bayan sallah ko?’‘Ban sani ba, wai dai don kada ta bani mamaki gara a samo min wata runda ga aikin gida ga hidimar yara sannan ga makaranta zan koma idan an bude gari ka ga ina bukatar taimakon mai aiki ko.’Sai a lokacin ma sannan ya tuna ashe tana zuwa jami’a; amma dai shi har yanzu bai gane dalilin da yasa ba zata koma yau din ba har sai nan da sati biyu. Ya dai fahimci so take kawai tace aikin gida da na yara ya mata yawa, kuma shi bai ga wani wahala a ciki ba tunda Ma’u ma ko sau daya bata taba daukan mai aiki ba haka take komai da kanta.Kawai dai ya fahimci Mommyn Khadeeja tana da son zuciya da iko shine take son ta juya shi kamar yanda take juya Baffansu, kuma gaskiya shi ba zai dau wannan ba.Haka dai ya gama kwana-kwanarsa ya tashi ya kwashi yaransa suka wuce gidan Hajia cike da takaicin Mommy Khadeeja wadda duk ita ya dorawa laifi, gani yake kamar itace take juya Khadeeja da Baffan gaba daya.Tuni Mommy ta bada umarni a samo mata ‘yar aiki.………Ransa a bace ya shiga gidan Hajia.Yana shiga ya tarar da Yaya Jidda a gidan ita da yaranta, suna zaune a parlor din Hajia suna hira. A gaggauce yaran suka gaisa da Hajia da Yaya Jidda suka shige wajen Baffa da gudu inda yake zaune yana jiran Kaman dan autan gidan ya dawo daga shan mai ya kai shi unguwa. A nan Mustapha ya zauna wajen Hajia da yaya Jidda, bayan sun gaggaisaya dubi Yaya Jidda yace ‘Ke Yaya sai kace jira kike a bude gari ki taho, har ma kin rigani zuwa.’Tayi dariya tace ‘Ni dama babu ni a lockdown in dai gidan nan ne kullum sai na zo, Alhaji ma ya gaji ya barni.’Hajia ta dubeshi tace ‘Ya jikin Khadeejan?’Ya dan karkata kai yace ‘Da sauki.’‘Jiya ma munyi waya da Mommyn tata ai, ta dawo gidan ko sai kun fita daga nan zaku daukota?’‘Mtseww!’ Ya ja gajeran tsaki sannan ya cigaba ‘Daga can muke, wai Mommyn tace bata gama hutawa ba kuma sai an mata wanka da gyara za a dawo da ita zuwa bayan sallah.’Hajia ta gyara zama ta kama haba ‘Ikon Allah, to kai kuma sai kace me?’‘To Hajia ya zan yi da su; shima baban nata bayan tuni muka gama magana da shi yace nazo na dauketa ina zuwa kuma ya canza zance; yace wai na barta. Itama kuma Khadeejan kamar haka ta zaba, kin ga kenan babu yanda zan yi da ita. Da ace ma ta bani hadin kai ne da zata iya canzawa Mommyn ra’ayi don kula kamar wannan shirin duka nata ne.’Kafin Hajia tace wani abu Yaya Jidda tace ‘Ai kuwa lallai shiri, barin ne sai an yi wani wanka da gyara? Lallai matan nan, nifa dama shi yasa yaran ‘yan bokon nan basa wani burgeni, ciki fal iyayin tsiya.’Hajia tace ‘To me suke nufi? Wannan duk ranar da ta haihu ai sai ta shekara sun gyara sannan zasu baka ita. To yanzu ya suke so kayi da wadannan ‘yayan, ko kuwa don ba ita ta haifesu ba? Tunda ia da nata ne hadawa zasuyi da su ko kuma ita da kanta ma ba zata yarda ta tafi ta barsu ba. Wannan ai ba tsari bane ba ma, sai dai da yake dama an bar gidan a hannun mace ai dole a ga son zuciya irin wannan.’Ya gayara zama yace ‘Hmmm! Su suka sani kuma.’‘To yanzu ya zaka yi da yaran? Ko kuwa haka zaku hakura kuyi zamanku tunda dama babu fita? Ko kuma nan zaka bar mini su sai muyi zamanmu, ka ga na sha allura a wajen Dr. Nasreen.’Ya dubi Yaya Jidda sannan yace ‘Da tunani nake na barsu wajen Yaya Jidda sai na koma na dauko musu kayansu, in ya so sai a barsu iyayen Khadeejan muga lokacin da zasu dawo da ita.’Har hajia ta bude baki zata yi magan Yaya Jidda ta tari numfashinta ‘Eh to kuma ka ga da sai muyi zaman mu, sai dai ka san gidan namu karami ne wajen kwanan zai iya yi musu kadan gaba daya da nawa yaran. Ko nan din ma ka barsu wajen Hajiyan ai duk muna tare tunda kullum ni nake zuwa na tsaya a kan hidimar gidan.’Suka yi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, jiamwa kadan hajia tace ‘To hakan ma ai yayi, ka bar min su a nan tunda ga baito nan tana nan zata iya duk wata hidimarsu. Tunda ka ga ai ba ma tsari ace kana zaune a gida daga kai sai yaranka yaran ma mata.’‘Ba damuwa, zan je na dauko kayansu kafin biyar din ta yi.’Ya tashi ya fice wajen Alhaji.Yaya Jidda tabi bayansa da kallo; ya bata tausayi amma gaskiya ba zata karbi su Afaf ba, gara dai a nan din. Can gidanta idama ga nata yaran wadanda iadna ta ga dama nan take turosu wajen Hajia suci abinci suyi koamia sannan kuma a kara mata wasu? Gaskiya ba zata iya ba.…..Sai da la’asar ta kusa sannan ya fita yaje gidan ya hado musu kayansu ya kawo sannan ya koma ya barsu a nan…
